KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣7️⃣

*GOGGO*

Alhaji cike da tashin hankali ya yi kanta don ya ɗauka ko rai ne ya yi halinsa, ganin ruɗewar da ya yi Goggo ta ɗaga masa hannu alamar ya dakata, dakatarwa ya yi Goggo ta ce

"Ka je ka tafi wajen aikin ka, a rayuwa ana so mutum ya damu da wanda ya damu da shi, wannan abin da ta yi ta yi ne a kan lamarin umarnin da na baka wato bata so ka yi auren kuma ita ba za ta samar da abin da ake so a gidan aure ba" ,Kai ya gyaɗa ya mata sallama ta masa addu,a tana sanar da shi za a kula da Naja,atun.

Direba ne ya buɗe masa ƙofa ta shiga ya koma ya tuƙa me gadi ya buɗe get suka fita.

Goggo ta juya tamkar bata san da iskar da ta ɗakko Hajiya Naja,atu ba, sai dai ba wai ta tafi bane tana tsaye a wajen sai dai ba Naja,atun take kallo ba, amma tana kallonta ta wutsiyar ido. Naja,atu ganin Goggo ta juya ta ƙyallara ido a zuciyarta tana kwashewa Goggo albarka na dakatar da Alhaji da ta yi da zai nuna damuwarsa a kanta. Goggo kuwa daman daga yanayin yadda Hajiya ta faɗi ta gane ba wai suman gaske bane ta yi, ta yi hakan ne don ta tadawz Alhaji hankali, kuma da ta faɗi tana lura da yadda saman idanunta suke ɗan motsi alamar ba a rufe suke ba idanunta biyu. Shi kuma da yake bai san kissa da kisisinar mace ba shi ya sa ya yarda da suman da ta yi.

Hajiya Naja,atu ji ta yj kamar ta saka ƙafa ta kwalfa Goggo in ya so ƴan sauran haƙoran da suka rage a bakinta su zube uban kowa ma ya huta idan kuma da karar kwana idan ta kwalfe ta sai rai ya yi halinsa gabaɗaya maganar auren ta wargaje ta ga tsiyar saka ɗa ƙara auren.

Goggo cikin ƙasa da murya ta ce

"Allah sarki Naja, Allah tashi kafaɗunki, ni dai na yi raunin taufa ba zan iya ɗaga ki ba, na san su Amira ma ba za su iya cicciɓar ki ba, amma bari na kirawo me gadi da masu ban ruwan fulawa su kawo miki ɗauki, su kinkimeki su kai ki ɓangaren ki, in ya so sai in kira Malam mai sittin wata kan wata ya miki ruƙiyya ya cire miki jinnu don na lura su ne suka ture ki ba wai faɗuwar Allah da annabi ba ce" Ƙululuuuu cikin Hajiya ya bada wani sauti, ta san dai muddin mai gadi da masu hidimar gida suka ɗauke ta, to duk wani girma da take da shi a idanunsu zai zube, bara kuma aka kira malamin na duk da bata san shi ba amma in dai malamai masu cire aljannu ne da wuya a samu wanda ba zai zane maka jiki ba, uwa uba ta san mao gadi da masu ban ruwan fulawar ne za su riƙe ta a mata ruƙiyyar kuma ita dai ta san bata da wasu aljannu.

Ganin Goggo ta ɗan dara tafiya Hajiya ta miƙe ƙafa daga kwancen da take, ta yi ɗan kotsi tarw da furta

"Alhaji, Alhaji" Don bata ma son kiran suna Goggo saboda haushin ta da take ji. Da ɗan sauri Goggo ta juyo tana faɗin..

"Naja kin farfaɗo?" Sannu Naja ta faɗa tana sunkuyawa a kanta. Idanunta a rufe har lokacin ta shiga gyaɗawa Goggo kai kamar wata ƙadangaruwa. Fitowar Mero ya sanya Goggo ƙwala mata kira, a kan ta zo ta kama mata Hajiya su tashe ta zaune.

A ɓangaran Mama Magajiya tun fitar Hajiya Naja,atu Mama take zabga faɗa da zage-zage tana ta kiran an ci mata mutunci saboda an ga makwancinta bata da wasu kwantattun kuɗaɗe masu gidan rana. Ruma kuma sai kukan takaicin dawowa take ba tare da cikar buri ba.

Mama ta ja numfashi ba tare da ta ce komao ba ta ɗan yi jim kaɗan ta ce

"Ba kin ce bata san kun fito daga gidan ba"

Ruma tana share shawayen takaici ta ce

, "Wallahi bata sani ba tana can ɗakinta da na shirya shi ne na fito don mu haɗu da shi tp daga fitowa ya ce in zo mu tafi da farko ma tunanina wani wajen za mu je, amma da muka nufo nan sai na yi tunanin aurena zai tambaya a wajenki" Mama ta goge gumin goshin ta ta kalli Ruma ta ce

"Wannan Muhamamd ɗin ai shegiyar aƙida ce da shi, in ba haka ba kai da aka maka abin da za a ɗauki hankalinka sai ka haɗo mutum ka dawo da shi gida, to wallahi in ya san wata bai san wata ba, zan biyo mata ta bayan gida, za su ga ƙwawa ita ce maita ba dai ya dawo da ke ba tun da uwar tasa bata sani ba zuwa za mu yi da zummar in ce Naja ta zo har gida ta ci min mutunci tun da na tabbatar ba a san da zuwanta ba, kin ga sai mu jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya" Ruma jin za a sake shiga wata gwaramar da sauri ta goge hawayen nata tass ta tashi tsaye daman su Umar suna tsakar gidan da Mama ta tura su su yi wasa.

Tana tashi ta cire hijabin Mama ta dube ta ta ce

"Kema daman Ruma kin zurma da yawa wanna kaya sun yi tsuku da yawa, wato sun ɗame ki sosai, ai sai ki yi saisa -saisa ki saka wanda basu ɗame ki sosai ba, amma wannan kamar inyamura ko ina a ɗame ba dole ya yi tunanin nemansa kike da iskanci ba" Ruma ta kalli jikinta.

Mama ta ɗora da faɗin

"Yanzu ki samo atamfa riga da zani ki saka" Da to ta amsa ta saka atamfa, suka fito suka tura su Usman maƙota a kan su zauna za su je ungiwa su dawo. A ƙofar get mai napep ya ajiye su, lokacin da suka buɗe get din Hajiya Naja,atu tana tsakiyar harabar gidan a kwance da Mero da Hajiya sun kama ta za su tada ta zaune. Sun shigo suka ƙaraso wajen suna zuwa Hajiya ta haɗe rai tana aika musu wani kallo. Mama kuwa ta haɗe rai Goggo ta ce

",Sannu da zuwa Magajiya" Mama ta kauda kai gefe, Ruma sai ɗan sharw ƙwalla take.

Goggo ta ce

",Ruma mai ya yi zafi shi ba wuta ba?"

Mama Magajiya kamar jira take ta fara faɗin

."Haba Goggo ai a ganina ko akuya zan iya kawowa ta zauna a gidan nan, tun da ina ganon ƴan uwantaka ai ta fi komai, amma shi ne na kawo ƴata washe gari Muhammad ya mayar da ita da sanyin safiya, yana tafiya wannan Najar marar kunya ta je har gida ta min ɗaukan albarka a matsayina na kanwar sirikarta anya wannan ta san mutunci ta je ta mini tatass a kan mijinta" Mama ta faɗa tana rushewa da kukan kissa.

Goggo ta saki kafaɗar Hajiya da take ta muzurai, tana wani kakkauda kai, baya san yanxu jin haushinsu ya ruɓanya a wajanta ba saboda an yi maganar ƙarin aure a nan da kwana uku, ji take tamkar hawan jini zai kamata.

Goggo tana tashi tsaye ta ce

"Haba Magajiya ai kya tambayeni kafin ki yanke min hukunci, amma ita Ruma ai ba yarinya bace da za a kasa tambayarta bayani ta yi, ko kaɗan ban san ma Muhammad ya mayar da ita gida ba sai daga baya, idan har zan ce a mayar da ita yau ai da ba sai ta kwana bama, kuma batun Naja wallahi ban san ta je ba, ta yaya zan yarda a wulakanta ki ai kamar an wulakanta ni ne!" Mama a zuciyarta ta ce

'Kifi na ganinka me jar koma, ai wallahi sai Ruma ta zauna a gidan nan sai dai abin da za a yi duk a yi mu bama zuciya a kan abin da bamu da shi, ko kuma a kan abin da muke son cimma burinmu'

A fili ta ce

"Ni wallahi duk sai na ji jikina ya yi la,asar da na ga haka kamar wanda na kai Ruma baren wuri"

Hajiya da ta yunƙura ta tashi tana ƙwace hannunta daga hannun Mero ta kama ƙugu ta ce

"Ta Allah ba ta mutum ba, wallahi na ci dubu sai ceto, duk wani gutsuri tsomar mutum zai yi ya gama nan gani nan bari farar tumfafiya, babu wata mace da za ta rayu a gidan mijina, babu mai mini kishiya duk abin da mutum zai shirya a kansa zai ƙare" Tana faɗar haka ta kama hanya fuuuu ta tafi ba tare da ta sake ko da kallonsu bane da aniyysr zuwa ta kira mahaifiyarta ta faɗa mata wannan jawabin da Goggo don ba za ta taɓa yarda da wata mace ta shigo mata gida ba!.

Mama ta ce

"Wannan yarinya dai so take ta kama gida bata so ko kaɗan a mata kishiya, shi kuma aure ai nufi ne na Allah"

Goggo ta ce

"Ai kuwa sai dai ta haɗiyi zuciya don wallahi Muhammad ba zai zauna da ita kaɗai ba dole ya ƙara aure" Mama da Ruma suka faki idon Hajiya suka dara, Ruma har da ɗan dillo harshe alamar gwalo, wani daɗi take ji tamkar ta doka tsalle.

A ɓangaran Mama ma haka ne don ta san dai tun da har suka fitar da maita da zalamarsu ta son Ruma ta auri Muhammad babu yadda za a yi Goggo ta zaɓi na waje ta ba hana na gida.

Mama ta ce

"Wallahi ina goyon bayanki Yayata ta kaina, ai cikakken namiji shi ne mai mace sama da ɗaya ai me mace ɗaya abokin gwauro ne!"

Duk abin na da ake ita Goggo bata da niyyar ɓoyewa Mama cewar zai yi auren kamar yadda ta sanar da su ɗazu, tun da ita dai ta ƙayyade a kwana kusa ne za a yi ba za a saka Ruma a layi ba ita da ko idda bata gama ba, ba ma wannan ba ita ko kaɗan duk da Ruma ɗiyar ƴar uwarta ce amma har ga Allah tarbiyarta bata mata ba a kan zama matar Muhammad.

Goggo ta ce

"In sha Allah, nan da kwana uku za a ɗaura masa aure, na gaji da juya mu da matarsa take tana nuna masa bashi da wata kima shi ma fa mutum ne namiji yana so ya ba iyalinsa umarni su bi ai hakan shi ne aure amma ba wannan auren na Naja ba fa ko kaɗan bata san kimar miji ba, a rayuwar mace idan har ta samu gata da soyayyar ɗa namiji kamar yadda Naja ta samu ai ba za ta yj watsi da wannan damar ba, amma ita kuwa ta yi sake, to tunda haka ne zan nuna mata ta yi sake ɗan zaki ya girma!"

Mama da ɗan ƙarfi ta furta

"Alhamdulillah" Har sai da Goggo ta kalli ƙwayar idanun Mama.

Sai dai hamdalar ta tsaya ne iya jin zai ƙara aure, amma tana tunowa cewa Ruma babu damar a ɗaura mata aure nan da kwana uku a take ta ji murnar ta koma ciki, ita ma Ruma a nata ɓangaren haka ne, don haka Mama da sauri ta ce

"Kwana uku kuma? Amma dai ba kwanaki uku da na sani na, gobe, jibi, gata ba ko?" Goggo ta ce

"Haba Magajiya akwai wasu ƙayyadaddun kwana ki idan aka ce kwana uku da suka wuce wannn da kika lissasa?"

Mama duk ta diririce ta ce

"Amma kin san Ruma bata gama idda ba!"

Goggo ta mata kallon rashin fahimta ta ce

"Haba Magajiya auren dole kike so a haɗa ko yaya?"

Mama ta ce

"Shi ai Muhammad mai biyayya ne ba kallon mutum ba ko aljana kika ce ya aura zai aura ai yana da biyayya"

Goggo ta ce

"Haka ne amma ni aan tauye masa haƙƙinsa ba na ce ya samo wacce zai aura"

Wani salati da Mama Magajiya ta kwasa tamkar an ce uwarta mahaifiya ta mutu, ta ce..

"Kika bashi damar zaɓi bayan ga bazawara a gida, a ganina idan gida bai ƙoshi ba ai ba a ba daji ba"

Goggo ta lura lamarin akwai son kai a ciki, ko kara ma Mama bata yi ta gama harbo jirginta kawai akwii wata manufa da suke son cimma ita da ƴarta Ruma, don ta ga itama Ruma ranta in ya yi dubu ya ɓaci, tun da suka ji zai yi aure na da kwana uku gabaɗaya yanayin fuskarsu ya sauya.

Goggo ta ce

"Magajiya shi komai a sannu ake binsa, tun da har aka bashi zaɓi kuma ya san ƴar uwarsa tana gida to idan har Muhammad ya zaɓi Ruma a matsayin zai aure ta to babu wanda zai hana kuma za a ɗaga ranar ɗaurin auren har ta kammala idda!" Daga Ruma har Mama basu san ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ƙwace musu ba sia da suka ga Goggo ta kalle su bisa kallon mamaki Mama ta wayince da faɗin

"Yawwa Allah sa ma ya zaɓe ta"

Goggo ta ce

"Mu yi dai fatan Allah zaɓa abin da ya fi alkairi"

Mama ta ce

"Ai wannan haɗin alkairin ne ma"

Goggo a zuciyarta ta ce

'Ban ga kyan wuri a kunnen jaka ba!'

A fili ta ce

",Haka ne" Daga haka suka shiga ciki da Goggo da Ruma don Mama ta ce ita komawa za ta yi gida, ta baro su Umar a maƙota, ita dai Goggo lamarin har ya fara bata tsoro ganin ita Ruma da aka mayar da ita takanas ta kano aka kaita gida amma babu wanda ya yi batun ta xauna sai dai gashi nan an barta a gidan, tamkar dai auren ta ƙarfi da yaji ake son a haɗa.

Tana fita ta samu napep ta hau, tana ta addu,a a zuciyarta Allah sa Muhammad rabon Ruma ne. A ɓangaran Ruma ma ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda tana ganin kakarta ta yanke saƙa, sai dai za ta yi taka tsantsan kamar yadda Mama ta faɗa mata wajen kiyaye saka kayan matsatstsu don kar a kuma wato mace ta haifi mace!.

Hajiya Naja,atu tana shiga falonta ta ɗauki waya ko zama ta kasa yi ta kira Mom, Mom ta ɗauka tana mata wani kirari, hankali tashe Hajiya ta ce

"Mom akwai gagarumar matsala, wallahi wannan uwar tasa bata son a zauna lafiya, ta sanya mishi sharaɗin nan da kwana uku za a ɗaura masa aure na shiga ukuna Mom" Mom kofin hannunta mai lemo ne ya suɓuce ya faɗi, har sai da Hajiya Naja,ati ta jiyo sautin ƙaran fashewarsa ta ce

"Naja kwana uku fa kika ce? Kuma aure? Ina son da yake miki ina alkawarin naku, amma ya yi fatali da umarnin nata ya faɗa mata gaskiyar lamari ba zai miki kishiya ba a rayuwar aurenku ko?"

Naja ta ce

"Mom ina ga yaƙi kina ga ƙura, kin san fa mutum ne mai biyayya ga wannan ƙeƙasassiyar uwar tashi baƙauya, wallahi a take ya amsa har yana mata kirarin farar uwa mai farar aniya" Ta faɗa wannan ksron har da kukan takaici da ya ƙwace mata.

Mom ta jero ashariya sahu sahu, sannan ta ce

, "Ka ji baƙin munafuki wato ya amince, anya daman ba yana son auren bane, in ba haka ba mene ne na saurin amincewar ko musu bai yi ba bare jayayya?" ,Hajiya Naja ta kasa magana hankalinta gabaɗaya ya tashi ji take kamar ta ɗauki wuƙa ta je ta daɓawa Goggo a ƙirjinta saiton zuciya, ko ta margaya lahira a fasa batun auren.

Mom ta ce

"Ni wallahi na kasa gane kan lamuran nan duk abubuwan sun cakuɗe, Naja,atu kin san fa daman sai da muka biyo ta bayan gida sannan aka samun dashen soyayyr taki ya zauna zuciyarsa ya daina rawa, ni dai da da yadda za a yi da an yi amma in wata ta shigo gidan na akwai matsala babba ma kuwa don kin zama hotiho tamkar sosuwar masara za ki koma" ,Hajiya ta yi shiru Mom ta ce .

"Ki danne zuciyarki zan yi yadda ya dace babu wanda zai ɗaura auren na zan sa a kwantar da maganar gabaɗaya ma ba u wanda ya isa ya sake tada kalmar aure" Da wata irin dariyar Naja ta fashe tana sanyawa uwarta albarka tana alfahri da kasancewarta mahaifiya a gareta da take share mata kuka bata bari ta yi ko da ƙwalla ce bare kuka!.

A ɓangaren Alhaji da saƙe-saƙe suka ƙarasa wajen aiki, direban yana yin parking ya fito ya nufi office ɗinsa ma,aikatan kamfanin suna ta masa sannu da zuwa tarw da gaishe da shi cikin girmamawa.

Ko da ya shiga office ɗin ta zauna, direban wanda ya biyo bayanshi da jakarsa ya ajiye masa ya juya ya tafi. Ko da ya zauna a kujerar ya fara juyawa gabaɗaya kansa ya cunkushe ya rasa wane tunani zai yj a kan maganar nan ta Goggo. Sai dai ko da a ce awa uku ne Goggo ta bashi to tabbas zai yi iya yinsa wajen ganin ya cika mata burinta ya faranta mata kasancewarsa mutum mai tsantsar biyayya da kuma gudun ɓacin ran mahaifiya.

Wayarsa ya ɗakko yana son kiran abokinsa ya faɗa masa halin da ake ciki don ya taya shi samun mafita, sai dai kuma fasawa ya yi so yake ya samu mafita da kansa. Zuciyarsa tana ta masa wasi wasi a kan matar da zai aura a kwana uku kacal, shi kuma yana ganin bai kamata ya nemi mahaifiyarsa ta ƙara masa wasu kwanakin a kan wanda ta bashi, sai dai zai yi iya yinsa ya yi abin da ta ce a lokacin da ta ce.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya tuno da matar nan mai kiransa da bakuwar lamba tana furta masa kalmar so, da yadda ta mace a kansa sai dai shi bai taɓa jin ta kwanta mada ba, hasali ma shi a nashi ra,ayin ba ya son mace matar aji da kamun kai, ba wai hakan haramun ne cewa mace ta furtawa namiji so ba, a,a amma mace an santa da kunya sannan ba kowane namiji ne za ki ce kina son sa ki yi daraja a idonsa ba wani daga lokacin ya samu abin rainawa wani kuma ya samu yadda zan ringa ja miki rai duk da ba a taru an zama ɗaya ba.

Wani ɓangare na zuciyarsa ya ce

',Falmi, Da sauri ya tashi daga jinginar da ya yi a kan kujera, ya zamana yana zau e dangargar. Gabansa yana matsanancin bubu ya ce

"Eh Falmi, amma ai ban furta ina sonta ba, kuma bani da tabbacin za ta amince da soyayya ta, sannan wannan yayar tata mai tsaurin tsiya bana jin ma za ta bari a nemi auren ƴar uwarta bare da aka ce ana son auren ya kasance a kwana uku!.

Ya yi shiru wata zuciyar tana ingiza shi a kan cewar tun da har yana da lambarta kawai ya kira ta ya fala mata abin da yake ransa tun da dai ya sanar da ita za su yi magana, duk da a lokacin da ya karɓi lambar, bai sa a ransa cewar a kwana kusa zai kira ta, kuma ko da ya kira za suke ɗan gaisawa ne kafin ya samu ya furta mata kalmar so duk da yana jin kalmar kamar wata baƙuwa ce a gunsa tun da bai taɓa zaton zai sake furtawa ƴa mace ita ba.

Cike da azalzala wani ɓangare na zuciyarsa ya ce

'Kawai ka kira ta yanzu, idan har kana son cika umarnin mahaifiyarka, idan ya so ko su ɓangaren macen basu amince da kwana ukun ba a ƙalla dai ka cika umarninta ka samo matar auren'

Sunayen ya fara bi, ya zo kan sunan kamar yadda ya yi savinga "Falmi" Sai da ya yi addu,a sannan ya kira, wayar tana ringin ne haɗe da faɗuwar gabansa.

Falmi tana kwance a ɗakinta hannunta riƙe da ayaba tana shirin ɓarewa, da yake ba a kwance sosai take ba ta dai jingina ne a jikin filo. Tana jin wayarta tana ƙara amma bata ɗauki wayar ba don a tunaninta ma ƙawarta ce Bintu, kuma ɗazu suka yi faɗan nasu da suka saba ta yi fushi so take sai ta wana Bintun za ta ɗauki kiran.

Alhaji ajiyar zuciya ya sauke da kira ta yanke, don daman faɗuwar gaban da yake ji duk ta addabe shi. Amma haka ya daure ya kira a karo na biyu a ransa yana ƙiyasta cewar in dai ba a ɗaga ba zai bar kiran sai da dare.

Kamar an ce ta kalli wayar ta ga baƙuwar lamba, da kamar ba za ta ɗauka ba kiran yana dab da tsinkewa ta ɗaga, ta ce

",Assalamu alaikum" Sai da ya lumshe idanunsa jin zazzaƙar muryarta da ta masa sallama, da sauri ya aro nutsuwarsa ya ce..

"!Wa alaikumus salam barka da wannan lokaci" ,Da sauri ta cire wayar daga kunnenta ta kalli wayar, idanu ta zaro don tabbas ta shaida muryarsa, don muryarsa ba za ta ɓace mata ba, sai lokacin ma ta tuna ya karɓi lambarta, don gabaɗaya ma ta shafa,a cewa ta bashi lamba.

Cike da kunya ta ce

"Barka dai ya aiki" Ya amsa da

"Aiki gamu a cikinsa"

Ta ce

"Allah taimaka ya yi jagora" Ta faɗa cike da jin nauyinsa don ita bata san dalili ba haka kawai sai take jin nauyinsa, gashi yana da cikar kamala tana kyautata zato a kansa daga gani mutumin kirki ne, wannan dalilin ne ma ya sa tun bayan da aka kaɗe ta da ya zo bata taka masa birki ba.

Ya ce

.",Amin na gode" Shiru ya ɗan ratsa wayar, kafin ya ce...

"Idan ba za ki damu ba, daman akwai saƙon da nake tafe da shi, ina fatan za ki saurareni sannan za ki amsa min abin da nake tafe da shi" Duk da ba wannan ne karo na farko da aka ce ana sonta ba amma ta san yanayin kalamansa ya nuna yana son isar da kalmar so ne.

Ta ce

"Ba damuwa"

Ya ce

"Ok na gode, daman ina tafe da magana ne a kan ina son ki, na so na sanar da ke a zahiri amma kuma na yanke hukuncin sanar da ke a waya saboda wasu dalilai ina faran za ki amshi tayin da na miki don na miƙo miki ƙoƙon bara ta, sannan ni da aure nake son ki!" Tun da ya fara magana take jin tamkar wanda yakr rera waƙa, ko kuma mai busar sarewa, saboda iya magana da kuma yin maganar cikin ƙwarewa da sanin ya kamata.

Shiru ta yi, har sai da ya nemi ba,asin shirun kafin ta ce.

"To na ji abin da kake tafe da shi, amma dai ina so ka ban lokaci na yi tunani da nazari kafin na yanke hukunci, sannan zan yi shawara da Aunty nah" Gabansa ne ya faɗi don ya san idan aka sako Auntyn na tata kamar maganar za ta rushe ne. .

Ta ce.

"Baki amince da ni ba da sai kin yi tunani" Ya faɗa saboda shi ya san bashi da ishashshan lokaci tun da kwana uku aka bashi, kuma dai yana jin nauyi ya sanar da ita.

Ta sauke ajiyar zuciya har yana jiyo sautin ta ta ce

"Ba haka bane, ka san an ce idan miciji ya sare ka to idan ka ga tsumma ma tsoro kake, duk da ina maka kyakkyawan zato, amma inaso ka sani ni ba budurwa ba ce na taɓa aure, wata ƙaddara ce ta sanya na bar gidan mijina!!!"

A min afuwar ɓangaren Nuriyya na kwana biyu ban taɓo ba zan taɓo gobe in muna raye.

MAMAN AFRAH ***

[8/29, 6:19 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA MAMAN AFRAH