KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣8️⃣ *RAMLA* A daidai gaɓar da mahaifinta yake cincintun sama mata karatun makarantar gaba da sakandire a wannan lokacin ne rai ya yi halinsa!. Sun yj kuka sun yi jimami saboda sun rasa jigo, haka ma mahaifiyarsu Inna Mairamu ta shiga damuwar rashin mijinta abin kaunarta, mijin da ya maye mata gurbin iyaye mijin da bata taɓa samunsa da wata manufa ko saka ta damuwa a rayuwarta ba, mijin da ya san halacci kuma ɗan halak. Gonar gadonsu wacce yake ajiye da ita saboda auren su Ramla da ƙannenta idan ya tashi, a cewarsa idan za a yi wa Ramla aure a siyar da wani ɓangaren, haka idan auren su Amal ya tashi a siyar da wani ɓangaren. Saboda a sauke masa nauyi ya sa aka siyar da gonar nan aka raba musu gado!. . Kowa ya faɗi abin da yake so, su Amal fili aka siya musu, saɓanin Ramla da aka siya mata sarƙa da ɗankunnen na gwal. Saboda gonar ba aarama bace sannan lokacin komai yana da daraja. A wata rana mai cike da ɗimbin tarihi a rayuwarta, ita ce ranar da suka haɗu da Abdulsalam, sun dawo daga makaranta suna tafiya ita da ƙawarta Asma,u kasancewar babu nisa sosai daga gidan titi kawai take tsallakawa, lokacin ta fara level 1. Abdulsalam wanda ya zo wucewa bai gani ba ya bige ta, har littafin da yake hannunta ya faɗi ƙasa, ta sunkuya ta ɗauka ƙawarta tana mata dariya, rai ta haɗe ta turo baki don a duniya ta tsani jikin namiji ya taɓa mata jiki. Shi kuma haƙurin da zai bata kawai ya ga ta tafi da nutsuwarsa kasancewarsa mai son mata. Tun da ya ringa bata haƙuri har sai da Asma,u ta.ce "Bawan Allah ba fa ita ka bige ba littafin ta ne ka bige hannunta ya faɗi, amma haƙurin da kake bata ya yi yawa kamar wanda ka mata gagarumin abu" Ya maƙale hannunsa a ƙirji duka biyu yana gyara tsayuwarsa ya ce "Ba dole ba kin san su kyawawa haƙurin da za a basu da ban yake, ni a rayuwa inason in ga mace mai kamun kai da nutsuwa ki ga yadda ta haɗe rai kawai saboda bige ta da na yi daga gani tarbiya ta samu wajen zama" Ya faɗa cike da daɗin baki. Duk da maza basu cike birge Ramla ba amma sai ta ji wannan saboda yanayin kalamansa da iya tsara magana sai ta ji gabaɗaya ya birge ta. Asma,u ta ce "Taɓ kaima da wani fasa kai kake wannan ƙawar tawa fa jiji da kai ne da ita amma sai wani yaba mata kake kana koɗa ta kamar ka shekara da saninta" Ya ce "Ai ji na yi kamar na shekara goma da sanin ta fa" Ramla ta ɗan yi taku biyu uku ta bar inda suke saboda wani murmushi mai bayyana hakura da ya so kuɓuce mata, sai ta ji ya iya magana kamar ya shekara yana yi. Kafin Asma,u ta bashi amsa ya bar kusa da ita ya sha gaban Ramla ya kao hannunsa biyu duka ya kama kunnuwansa ya ce "Tuba nake gimbiya, na san na yi laifi amma ki yafe min idan baki haƙura ba zan zubar da gwiwoyina a ƙasa in baki hakurin har sai kin haƙura!" Idanu ta zaro tana kallonsa yana ƙoƙarin zubar da gwiwoyin a ƙasa cikin sauri ta ce "Wallahi na haƙura" Murmushi ya yi ya fasa durƙusawar don daman ya lura da yanayinta ba za ta bari ya tsugunna ba, hakan ya sa ya ce "Na gode" Asma,u ta matso kusa da su ta ce ",Lallai ka ciri tuta, Ramla ko tsayawa ba ta son yi inda maza suka tsaya kuma bata yarda a tare ta a hanya ma amma kai gashi har ta saurare ka" RAMLA ta mata hararar wasa ta ce "To sarkin sututu aku mai bakin magana waye ya tambaye ki" Ita ma ta rama hararar tana faɗin "Ai dole na yi mamaki na ga abu kamar almara" Tare suka jera suka tsallaka titin, sai da ya rako su har unguwar tasu, kasancewar gidan su Asma,u yana gaba da na su Ramla. Sun tsaya suna sallama, ya ce "Ni sunana Abdulsalam" Idanu Ramla ta lumshe don har ƙoƙon ranta ta ji daɗin sunan. Ya karɓi lambarta Asma,u tana ta mata tsiya, ya musu sallama ya tafi don dama lokacin la,asar ce. Tun daga wanna rana ya shiga jikin Ramla sosai suke zuba soyayya a waya, hakan nan yana zuwa gidansu su yi hira ƴan gidansu sun san shi ya san su, mahaifiyarta kuwa ta san ba ƙaramin so Ramla take yi wa Abdulsalam ba kasancewarta mace mai aƙidar rashin kua samari sai ta kammala karatu don tana cewa aure ma ba ya gabanta, sai gashi lokaci guda soyayyar Abdulsalam ta rushe mata duk wannan ƙuduri da tsarin da ta taso da shi. A ɓangaren Abdulsalam tun daga loakcin da soyayya ta yi ƙarfi tsakanin Zahraddin da Hasiya, har ta kai ga ba sa ɓoyewa a gaban kowa, a lokacin ya gama yarjewa cewar ya rasa Hasiya duk da tsananin soyayyar da yake mata. Yana ji yana gani har manya suka shiga, aka ɗaura aure tsakanin Zahraddin da Hasiya, ya yi baƙinciki da takaici tamkar zai mutu, yanayin yadda ya sha nunawa Zahraddin har sai da ya sha tambayarsa ko fa masa wani abu ne amma ya ce babu abin da ya masa. Ranar da Hasiya da Zahraddin suka tare a matsayin ma,aurata tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu. Kuma tun daga ranar ya ƙi saka ƙafarsa a gidan Zahraddin wanda ya kama haya yake ƴar buga buga yana sama musu abin da za su rufawa kai asiri tun da ita ma ba wani hali iyayenta suke da akwai ba, bare ma idan har mace ta yi aure duk ɗawainiayrta ta koma kan mijinta. Dakyar ya yi yaƙi da zuciyarsa har ya zo yake iya shiga gidan Zahraddin amma dai ta ciki na ciki kuma kullum in ya je ya ɗora idanunsa a kan Hasiya sai ya ji ya ƙara sonta domin shaidan tana ta masa jagora da nuna masa kyanta da komai nata bai dace da mijinta ba da shi ya dace!. Bayan shekara biyu da auren ne ya haɗu da Ramla a lokacin ma yana tare da wasu ƴan matan, don shi ƴan mata kam ba ya rabuwa da su yau in ya ga waccen gobe sai ya ga waccen ta fita, idan ya ce yana son wannan gobe in ya haɗu da wata sai ya sake cewa yana sonta, bashi ma da alƙibila. Haɗuwarsa da Ramla ya tunatar da shi abubuwa da dama a rayuwa, ya lura kamila ce ta sha bamban da sauran ƴanmata domin tana da kamun kai, bata da wata wayewa ta zamani da wasu ƴanmatan suke da su wayewa wacce ba ta addini da al,ada ba sai ta bin hanyar shaiɗan. Ramla ta mutu a kan soyayyar Abdulsalam, sannan uwa uba ba komai ne ya sanyaya jikinta ba sai maganar aure da ya zo mata da shi, gashi tana da burin karatu, amma son da take masa ya lulluɓe komai, sannan ita a gida tana sana,a sai dai ita abin da ya ɗaure mata kai shi ne yadda Abdulsalam ɗin ya nuna mata bashi da wata tsayayyar sana,a ta lura koyaushe sai dai su yi ta waya amma bata jin yana faɗar zai je wurin kasuwanci. Ko da ya zo mata da maganar aure ta sanar da shi ita karatu take, sai ya nuna mata cewar shi ma zai tsaye mata ta yi karatu har ta ga ƙarshen biro da takarda ba zai hana ta ba. Tana wannan halin tunanin sana,a ko aikin da yake yi duk da ya sanar da ita ya kammala karatunsa. Zahraddin da samu da maganar yana son ya auri Ramla, son da Zahraddin yake masa ya sa, ya yi cincintu ya sama masa jari ya bashi a kan ya kama sana,a, sannan kuma duk da yana da son jiki amma da ya sa a ransa zai aure ta sai yake bin Zahraddin wajen aikin ƙarfi, wajen gini ko sauke kaya a manyan shaguna idan an kawo su sauke kaya daga kan mota su shiga da su shaguna a biya su. Jarin yake sarar yadika da wannan ya samu ya ɗan samu abin da yake ganin ko ya yi aure ba zai rasa abin da zai riƙe matarsa ba kafin dai ya samu aiki. Suna hira ya kira sunanta cikin sanyin murya, ta ɗago ta amsa tana kallonsa, ƙwalla ta gani a cikin ƙwayar idanunsa, lamarin da ya tayar da hankalinta ta shiga tambayarsa ba,asi ya raunata muryarsa ya ce "Ramla ina sonki, irin son da uwa take yi wa ɗanta, Ramla na yi iya yina don in barki ki gama karatu kamar yadda yake a cikin burikan ki amma son da zuciyata take miki ta matsa mini a kan sai kin dawo kusa da ita matsayin abokiyar rayuwa za ta samu nutsuwa" Ƙwallar idanunsa suka gangaro kan kuncinsa, a wannan lokacin Ramla ji take kamar ta saka hannu ta ciro damuwarsa ta sanya a tata zuciyar, bata kaunar ganinsa cikin damuwa" Ya ɗora da faɗin "Ni maraya ne kin sani, kamar yadda na baki labari ban ɓoye miki komai ba, sannan ban da uwar riƙona da kuma Zahraddin kin san bani da kowa rayuwar yanxu kowa kansa ya sani, don haka inaso kamar yadda nake kaunarki kike kaunata ki amince mu yi aure mu rayu a inuwa ɗaya, ba zan ci amanarki ba zan riƙe ki na maye miki gurbin da kike so a rayuwarki amma ki sani ni ba kowa bane talaka ne, idan zuciyarki ta ƙudurta ki zaɓeni ki aureni a halin yanzu to a shirye nake na aure ki, duk da na san akwai wanda suka mini fintinkau a cikin manemanki, duk da ba kula su kike yi ba ina ganin yadda manyan motoci suke zuwa ƙofar gidan nan, wani lokacin ma muna tare samari masu hannu da shuni za su zo su yi ta magiya a kan ki saurare su, wasu su zo da manyan ledoji da waya su kawo miki amma ki ƙi karɓa saboda kin zaɓe ni" Ya saka hannu ya sharo hawayen, gabaɗaya ji yake idanunta sun cika da ƙwallar tausayinsa. Bai bata damar magana ba ya cigaba da faɗin "Na yi karatu ina jiran ranar da Allah zai kawo min aikin gwamnati, amma yanxu ina ƴar buga buga da sana,ar da bata taka kara ta karya ba, wacce nake ganin za ta iya riƙe mu kafin Allah ya bani aikin yi, na miki alkawarin zan nuna miki gata Ramla, a duk lokacin da na samu aiki zan nuna miki halacci kamar yadda kika so ni don Allah kika ƙi masu arziƙi kika kulani duk da bani da komai!" Ji ta yi saboda son da take masa da wanda yake mata, ta aminci ko da ba zai taɓa samun aiki ba in har dai za su rayu tare. Cikin sanyin murya ta ce "Abdulsalam!" Ya ɗago ya kalleta cike da rauni ta ce "Na amince da kai, kuma ni na zaɓe ka a matsayin abokin rayuwa, sannan karka damu da rashin aikin gwamnati shi komai lokaci ne da shi, sannan shi arziƙi na Allah ne, samu da rashi duk nashi ne, matuƙar za ka barni in cigaba da karatu to ko ƙasa za a ci a rayu inaso in nuna maka mafi ƙasƙanci abinci ko da ana cin ƙasa a rayu to zan aure ka!" Ya sauke ajiyar zuciya yana ji kamar ya rungume ta saboda farinciki, ya ce "Na yi alƙwarin duk wani gata da farinciki da mace take samu a gidan aure zan baki shi Ramla, kuma zan yi amfani da gumina na faranta miki, duk wuyar da zan sha sai na sauke nauyin haƙƙin ki" Bai bar gidansu Ramla ba ranar sai da suka yi wa juna alƙawura da dama!. Ko da ta sanar da mahaifiyarta ta ce mata "Ramla muma talakawa ne, kuma ni bani da bakin da zan kira ɗa namiji ba ya halacci ko in ce masa butulu kasancewar ban ci karo da rashin halacci ko adalci ba, mahaifinku mutum ne, yana da sanin darajar aure da mutunta ƴa mace bai yarda ko a danginsa wani ya wulaƙanta matarsa ba duk da talaka ne amma ban rasa farinciki ba, duk da ba a taru an zama ɗaya ba sannan nasihar mahaifinku a cikin wasiyyarsa ya ce duk lokacin da kuka samu nagartaccen wanda kuke so a aura muku, shi daman daga sakadiri ma ya so miki aure amma kika ƙwallafa rai a karatu, ganin kina so kuma shi mutum ne mai ba kowa dama don haka tun da kin samu mijin aure kuma kin aminta da shi, to za a yi bincike a kansa tund a zai barki ki yi karatun ki, idan har aka samu nagartarsa duk da daman sai da aka san waye shi ya fara zuwa wajenki amma bincike na aure daban yake saboda aure rayuwa ce ta har abada! Idan mace ta dace da gidan miji rayuwarta za ta inganta idan aka samu saɓanin haka to tabbas rayuwarta za ta zama cikin garari ta rasa nutsuwa ta dawwama a damuwa, Allah sa abokin arziƙin rayuwa ne Allah miki albarka" Ko da aka yi bincike aka ƙara tabbatarwa, aka yi maganar gemu da gemu aka saka rana wata biyu. Abdulsalam ya cigaba da dasa soyayyarsa da tausayinsa a zuciyar Ramla. Ba a yi lefe ba kuɗi ne suka yi haɗin gwiwa shi da Zahraddin suka tara duk da shi ma yana ta kansa amma dai sai da ya tabbatar an fita kunya. Kuɗin da aka kawo wanda yake mazaunin na aure, ita da mahaifiyarta suka haɗu, mahaifyarta ta fasa asusun sana,ar abincin da take yi ta cika suka je kasuwa suka siyo akwati set ɗaya mai sauƙin kuɗi sannan suka sayi ƴan atamfafo da leshi da mayafai da sauran abubuwan da ba a rasa ba, cikin ikon Allah sai ga kaya sun haɗu daidai na me ƙaramin ƙarfi. Ɗan uwan mahaifinta ya mata kayan ɗaki, don hanawa ya yi a siyar da sarka da ɗankunnen ya ce a bar mata saboda halin rayuwa. Daman mahaifiyarta tana tara kayan kicin tun daɗewa haka aka mata jere a gidan hayar da Abdulsalam ya kama, asusun da ta fasa na sana,ar da take yi ta tafi da kuɗin dubu ɗari a cewar mahaifiyarta ta tafi da kuɗin a matsayin jari ta kafa sana,a a gidanta don da dogara da kanta kamar yadda ta saba don sana,a tana taka muhimmiyar rayuwa a rayuwa. An kai amarya ɗakinta, wanda ya sha jere daidai gwargwado, ga labulaye masu kyau domin wajen Maman Afrah marubuciya suka sayi zannuwan gado da labule saboda tana siyar da zannuwan gado da labulaye irin na amare daidai da kuɗinka, wato iya kuɗinka iya shagalinka, hatta kayan fitar biki na amarr wato na kamu ko dinner da sauransu Maman Afrah tana ɗinkawa mai buƙata zai tuntuɓe ta a lambar ta ***. Gidan ciki da falo ne sai banɗaki da kicin. Asma,u tana ta mata tsiya cewar Abdulsalam ya ciri tutar da sauran mazan da suke rububin sonta basu cira ba, aka watse aka bar su. Rayuwa mai daɗi, suke yi cikin kulawar juna da soyayya,. *NURIYYA* Bayan shekara takwas, lokacin Nuriyya tana da shekara goma sha shida a inda Ammar yake cikin shekara ta ashirin da ɗaya. Lokacin ta kammala karatun sakandire, shi kuma ya kammala karatunsa na sakandire inda ya ɗora da NCE bayan ya gama yana son samun level two a digiri sai dai son samawarwa Nuriyya ta fara karatun gaba da sakandire ya dakatar da nashi karatun. Duk da yanzu yana da sana,ar yi bai fiya fita talla ba, tun da ya kammala karatub ƙaramar sakandire ya yi fafutuka ya biya kuɗi a shagon koyan ɗinki, a inda ya mayar da hankali ya koyi ɗinkin maza da na mata. Sana,ar ɗinkin da ita yake ɗaukan nauyin ɗawainiyar Kaka. Da taimakon Allah, ya samu ya sayi keken ɗinki na kansa, don a da dana shagon yake yi, yana biyan ɗan wani abu, Ammar ya ƙware a ɗinki matuƙa gashi da farin jinin mutane kowa idan ya kawo ɗinki sai ka ji ana nemansa ko da ba ya shagon, wasu idan ba ya shagon suna komawa a ɗinki a maimakon su ba sauran masu ɗinkin na shagon har karan kansa Ogan nasu mamallakin shagon. Hassada da ƙyashi suka fara shiga tsakaninsa da mutanen shagon abokan sana,arsa, tun da suna ganin ya fi kowa samun ɗinki. Wani babban abu da ya faru da shi da ba zai taɓa mantawa ba shi ne, giftawar wata rubutacciyar ƙaddara, wata rana wata mata ta kawo masa ɗinkunanta kala biyar, manyan atamfofi na kimanin dubu tamanin guda biyu, da lace na dubu casa,in sai shadda wacce bai san kuɗinta ba, ta kawo masa ne ta sanadin wata customer ɗinsa. A ranar da aka kawo ɗinki da magriba, washe gari da ya xo shago ko ledar kayan babu bare a yi zancen kayan ciki, don kuwa ɓarayi sun ɓalle musu shagon sun yi sata sai dai kayan da aka ɗaukar masa sun fi yawa don akwai na wasu ma don dai basu da tsada. Matar nan ta ce sai ya biya ta, mutum biyu ne suka ɗauki ƙaddara suka yafe masa, tun da ya san yanzu a wannan gaɓar biyan wanann kuɗin ne damuwarsa hakan ya sa komai ya tsaya masa cak dangane da hidindimunsa da kuma na Kaka da Nuriyya. Duk ɗinkin da zai yi kuɗin kawai yake tarawa, sai da ya haɗa kuɗin nan kaf sannan ya kai wa matar babu kunya ta karɓe tana faɗin "Ɗan saurayi ka taimaki kanka domin da ka saɓa alƙawari baka kawo ba sai ka yi gidan kaso a kan wannan kuɗin" Kallon ta kawai ya yi ya ce "Allah ya min jagora na samu na haɗa miki" Ya faɗa yana tuna irin addu,ar da ya yi a kan ya samu kuɗin nan su haɗu kafin lokacin da ta ƙayyade masa, har wayarsa ya siyar. Lokacin da ya gama haɗa kuɗin ƙarfinsa ya ƙare saboda samun ɗinki ya fara masa wahala, gashi kuma Nuriyya za ta ahuga makarantar gaba da sakandire saboda kuɗin registration. siyan hand out da sauransu, ga kuma akwai buƙatar ya mata ɗan ɗinkin hijabai da mayafai saboda ta zama budurwa. Kansa ya kulle ya rasa yadda zai yi gashi ba ya so lokaci ya ƙure a rufe registration ɗin. Kwance yake a ɗakinsa ya yi reran kansa a sama ya yi nisa cikin tunanin yadda zai samu mafita, Kaka ta shiga ɗakin da sallama har sau biyu amma bai ma san tana yi ba, ta je ta zauna a kusa da shi ta tsura masa idanu tausayinta ya kamata ganin nisan da ya yi cikin tunani kuma ta san lamarin damuwar bai wuce na tunani a kan karatun Nuriyya ba. A zuciyarta ta ce 'Ya Allah ka bawa yaron nan mafita, ka buɗa masa ka cire shi a damuwa ko don nauyinmu da yake ɗauka' Ta faɗa tana kai hannunta ta ɗan taɓa shi figigit ya dawi hayyacinsa ya kalleta yana ɗan ƙoƙarin tashi zaune yana faɗin "Kaka yaushe kika shigo?" Kaka ta ce "Ina za ka san lokacin da na shigo Ammar ka yi nisa a cikin tunani" ,Ya saka hannunta a goshinta tare da murtsuke idanunta ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Wallahi na rasa ya zan yi ɗinkin tamkar wanda aka tsayar da samunsa sai na je shagon na wuni amma bana samu duk abubuwa sun cunkushe min yanxu tunanin abin da za a ci a gidan nan ma nake yi" Kaka ta ɗan kawar da kanta gefe jin ƙwalla ta taru a idanunta na tausayinsa a shekarunsa amma ya san ɗawainiya tun yana yaro yake fafutukar ciyar da su da sauran buƙatunsu, shi ba magidanci ba amma kullum cikin yin wahalhalun da magidanci zai yi. Ta ce "Ammar ita fa lamarin sana,a haka take daman, sannna rayuwa ma ba kullum ake kwana a gado ba, yau samu gobe rashi ita sana,a ta gaji haka wani lokacin sai ka ga kana ta ciniki mutane kamar ana tittiɗo maka su wani lokacin kuma cinikin ya tsaya cak, to mutum ya fawwalawa Allah lamuransa ya sanya a ransa shi yake bashi kuma shi ne mai hanawa sannna uwa uba dagewa da adsu,a Allah zai kawo mafita" Kai ya gyaɗa mata sun jima suna ɗan tattaunawa Nuriyya ta yi sallama ta shigo, lokacin ya tashi zai fita tana shigowa ta tsaya a ƙofar ɗakin sai da Kaka ta mata izini sannan ta shiga, saboda tana tunawa da maganganun da Kaka take faɗa mata a kan cewar take dakatawa da shiga ɗakin Ammar sai da izininsa sannan Kaka ta hana ta riƙe masa hannu da sauran abubuwa saboda ta zama cikakkiyar mace shi kuma b muharraminta bane, ga kuma uwa uba soyayya da suke yi da shaƙuwar da take tsakaninsu tamkar shaƙuwar ɗa da uwa. Duk da ta gama karatun sakandire ta zama mace baliga amma ko ƙarfe nawa za ta kai a waje babu ruwan kowa da ita, idan ta koma gidan mahaifinta, sau tari ma sai ta jera kwana biyu uku tana kwana a gidan Kaka amma babu wanda zai nemi inda take, Hajiya ita kuma tana ta jin daɗi domin a tunaninta Nuriyya ta siyar da mutuncinta, don ita a nata hankalin ma tana jiran ranar da Nuriyya za ta kawo musu abin kunya ta yadda uban zai haɗa ta da cikin ya kore ta ma gabaɗaya!. Bata san cewa Nuriyya tana tattala mutuncin ra kuma ta san darajar kanta sannan duk wata hidima da ɗaukan ɗawainiyarta da Ammar yake yana mata ne don Allah ba don wani abu ba da kuɓa ƙaunarta wacce ya tashi tun yana ƙarami da ita a ransa. Washe gari lokacin ya rage saura kwana ɗaya a rufe registratio. Da daddare bayan ya raka Nuriyya gida a hanya yana ta faɗa mata ta kwantar da hankalinta in sha Allahu zai san yadda zai yi a mata registration ɗin. Sun jima suna hirar soyayya dakyar suka rabu. Yana dawowa gida ya zauna ya ce "Kaka Gobe in sha Allahu zan siyar da keken ɗinkina" Kaka ta tashi zaune daga kishingiɗar da ta yi ta ce "Amma kana cikin hayyacinka kuwa?" Amma ya ce "Rass nake, kawai dai inaso in biyawa Nury kuɗin makaranta ne in siya mata sauran abubuwan da za ta buƙata, kin ga ba a bari wannan damar ta wuce ta ba tun da ta ci jamb kuma takardunta ma sun yi kyau" Kaka ta ce "Allah sarki haka ne, da wannan don wannan amma fa karka manta wannan keken ɗinkin dakyar ka samu ka saya sannan shi ne rufin asirinmu" Ya ce "Eh haka ne, amma dai yanzu dole zan haƙura, in ya so sai nake buga-buga ina sama mana abin da za mu ci, zan iya sadaukar da komai saboda Nury Kaka, wallahi zan iya sadaukar da rayuwata don Nury ta rayu, sannn zan iya haƙura da farinciki in dawwama a baƙinciki matuƙar dai ita za ta yi farincikin" Shiru ta yi tana kallonsa ta rasa wace irin shaƙuwa da soyayya ce a tsakaninsu tana jinjinawa Amma, sannan tun da har ya furta cewar zai siyar don ya taimakawa marainiya da bata da gata sai Allah, ita ba za ta hana shi ba. Kaka ta ce "Ammar Allah ne kaɗai ya san irin ɗimbin shaƙuwarka da Nury ina roƙon ubangiji ya tabbatar da alkairi a cikin tarayyarku" Da amin ya amsa yana mai tashi ya nufi ɗakinsa yana jin daɗin amincewar da Kaka ta yi duk da daman ya san ba za ta ƙi amincewa ba!. Washe gari da sassafe ya nufi shagon ɗinkinsu da mai baro ya ɗakko keken ya je ya siyar da shi, wasu da suke shagon daga cikin abokan sana,arsa yana fita suke ta masa dariya a kan cewa ruwa ya ƙarewa ɗan kada tun da gashi har ta kai shi ga siyar da keken. Daman yana siyarwa ya auno musu abincin da za su ci ya taho da kayan miya, yana zuwa suka tafi tare da Nury ya ware kuɗin komai suka je tana ta murna aka mata komai. Ranar litinin ita ce ranar da Nury za ta fara zuwa makaranta tana ta murna saboda cikar burinta na son yin karatu. Hajiya Hauwa tana zaune a falonta tana kallo ta hango wulgwar Nuriyya wacce take sanye cikin doguwar riga me mayafi sabuwa ce dal Ammar ya siya mata cikin kuɗin keken da ya siyar, ta mata matuƙar kyau kasancewarta fara rigar kuma purple ce, Hajiya Hauwa ranta ya yj fari kasancewar tunaninta Nuriyya wani Alhajin ta samu wanda yake karɓar mutuncinta shi ne har ya kai ga siya mata kaya. Da sauri ta taso lokacin ma har Nuriyya ta gota tana tafiya, cike da gadara ta ce "Keee" Nuriyya da yanzu ta yi wayo ta san ciwon kanta kuma ta gama karantar wace ce matar mahaifinta wato ko kaɗan bata ƙaunarta. Sai da ta ƙara cewa "Ke Nuriyya" Sannan ta dakata da tafiya ta juyo, Hajiya Hauwa ta kama haɓa cike da mamaki ta ce "Iyeeee lallai yarinyar nan har ina miki magana kike wani ƙyalewa alhali na san kina jina" Nuriyya sai da ta tako ta sanyaya murya ta ce "Na,am ai ina sauri ne shi ya sa ban ji ba" Ta taɓe baki ta ce "Ƙaryar banza dai, in banda ƙarya ya za a yi ki ce baki ji me na ce ba, kina so dai ki nuna min, ƙulaƙulai biyu sun fito miki a ƙirji kamar yadda nawa ƙirjin yake sannan kina al,ada kamar yadda nake yi, uwa uba kin san namiji kamar yadda na sani shi ya sa kike ɗauka kanmu ɗaya" Lokacin da ta yi furucin ta san namiji da sauri Nury ta ɗago ta kalleta don ta tsorata da furucin. Ta ɗora da faɗin "Eg mana yanzu ai ke karuwar gida ce, tun da watarana ma bakya kwana a gidan nan, abin da ya rage kawai ki kawo ɗan gaba da fatih... Kafin ta ƙarasa hawaye ya wanke fuskar Nury da sauri ta katse ta da faɗin "Allah mini tsari sa sabon Allah" Harara ta doka mata Nury ta ce "Ni watarana a gidan Kaka nake kwana" Hajiya ta ce "Humm kya faɗa ma da kalmar hausa, shafawa zan yi in ji a gidan kakar kike, ko ita kakar saninta aka yi baki da wani haɗi da ita, ko dai kina kwana a gidan wannan shegen yaron yana ɗaukan... Wani irin abu ta ji me tsini ya cakar mata xuciya da ta cewa Ammar shege a duniya tsani a aibata mata Ammar ji take kamar ta mari wanda ya yi masa wani furuci marar daɗi. Idanunta taf da ƙwalla ta ce "Ammar mutumin kirki ne" Hajiya ta ce "Oho ke ai wuyanki ya yi kauri tun da kina faɗi in faɗa da ni, yanxu wannan kwalliyar da kika ci wane hotel ɗin za ki je" Ta tambaya tana kallon wata jaka rataye a kafaɗar Nuriyya. Nury ta danne abin da ta ji saboda baƙincikin furucin danganta ta da zina da Hajiyar take yi tana saka gefen mayafin doguwar rigar ta ce "Makaranta zan je" Cike da mamaki ta ce "Makaranta kuma? Wace makaranta?" Ta tambaya cike da mamaki tun da ta san yau ba asabar ko lahdi ba bare ta ce islamiya za ta je da safe, sannan ita dai a iya saninta Nury ta kammala karatun sakandire, amma tunaninta takardunta ma ba a karɓo ba na sakandiren tana ganin da me za ta shiga wata makaranta ko kaɗan bata taɓa zaton ma har za ta yi wata jamb ta samu admission ta fara zuwa wata makaranta ba. Kamar daga sama ta ji amsar Nuriyya ta ce "Eh makaranta zan ci gaba da karatuna ne, Ya Ammar ne ya min komai da komai" Cike da kiɗima a zuciyarta ta ce "Kam bala,i wato ina zaune a gidan nan yarinyar nan har ta samun damar yin karatu irin na masu gata, irin na wanda yake da mai tsaye masa lallai yaron nan ya shigar mini hanci da ƙudundune, wato dai burina na tozartar yarinyar nan ba zai cika ba tun da gashi dai ta samu ilimin addini har da na boko, nan gaba kaɗan sai in ji ta kammala karatu, idan ma da rabo sai na ji ta samu aiki' Bata san ta yi furucin a fili ba lokacin da ta ce "Wallahi ba zai yiwu ba sai na ɗauki mataki!" Nuriyya da take tsaye jin furucin sai ta ji wani banbarakwai wai namiji da suna Hajara cike da son sanin manufar Hajiyar ta ce "Mene ne ba zai yiwu ba?" Tsabar takaici ma kasa magana ta yi, juyawa ta yi cike da tashin hankali ta koma ɓangarenta da ƙudurin ashshaka wani abun don Ammar da Nuriyya sun shammace ta!. *ALHAJI MUHAMMAD* Shiru ya ɗan yi yana tunanin furucin ta, ransa cike fal da mamaki musamman da ya ji ta ce ita bazawara ce ta taɓa aure, sannan a yanayin furucin nata ya ji damuwa sosai a muryarta lallai ko da bai sani ba akwai wani gagarumin ɓoyayyan lamari a mutuwar auren nata wanda gashi idan ma za ta faɗa abin yana taɓa mata zuciya, kuma shi a yadda ya ganta bai taɓa zaton wai ta taɓa aure ba don babu wanda zai ce ba budurwa ba ce!. Kafin ya furta wani abu maganarta ta katse shi da faɗin "Na san a zato da tunaninka ni budurwa ce shi ya sa ka furta kalmar so a gareni, yanzu kuma da ka ji bazawara ce akalar tunaninka ya canja!" Kamar an tsikare shi ya ce "Falmi zuciyata ce take sonki, kuma ita ke take so ba budurcinki ba don haka ki sa a ranki duk runtsi ina sonki, na yi shiru ne ina tunanin yadda na ji kin yi maganar ne cikin raunin zuciya shi ya sa abin ya taɓa ni ba wai don na janye kalamaina a kan son ki da na ce ina yi ba" Idanu ta ƙanƙance jin furucinsa, mutum ne kamili da za ta so ya kasance abokin rayuwarta, musamman da yake ƙara jaddada mata son da yake mata duk da ta faɗa masa ta taɓa yin aure!. Cikin sanyin murya ta ce "Na gode da ƙaunar gaskiya, amma zan shawarci Aunty na" Tuno da wace ce Auntyn nata da ya lura bata da girmama mutane kamar ma vata san inda mutunci da dosa ba ya ce "Falmi" Ya kira ta cikin wata murya da ta sanya ta amsawa cikin sanyin tata muryar wanda furucinta ya ji shi har tsakiyar cikin dodon kunensa ya ce "Shin bakya shawara da zuciyarki ki yanke hukunci sai kin shawarci ƴar uwarki?" Wata ƴar dariya ya ji ta yi sai ta ce "Saboda ƴar uwata ita ce jigona, ƴar uwata ta fi ƙaunata a kan kanta, tana min so irin na ƴan uwan taka tana sadaukar min da komai a rayuwa, abin da da sa kenan ka ji na faɗa maka kuma ɗaya ba ya yanke hukunci sai fa sanin ɗaya" A zuciyarsa ya ce "Shikenan matsala ta ganni na rasa ki ma Falmi don wannan yayar taki daga gani ba za ta ce ki zaɓe ni ba' A fili ya ce "Allah sarki, Allah bar danƙon zumunci!" Ta amsa da "Amin" Duk da ta fahimci ya yi furucin ne kamar dai bai gamsu da ta sanar da ita ba, ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya ta ce "Mai ya sa kake son na yanke hukunci ba tare da ita ba, ai ko na yanke sai na sanar da ita" Ya ce ba komai, kawai sai na ga ita bata da sakin fuska, sannan sai in ga kamar va za ta amince da ni ba, kamar ma ba za ta so alaƙar ki da ni ba" Falmi ta ce "Ba haka bane, ita da tsaurin hali, kuma bata son raini, tana da taurin kai amma tana da daɗin sha,ani, abin da ya sa ka ga tana maka haka saboda kai namiji ne ita kuma saboda abin da mijina na farko ya min, wannan dalilin ne ya sa duk wani abu da ya shafeni dangane da namiji bata so gani take za a cutar da ni" Gabaɗaya sai ya ji tausayinsu ya kama shi, sannan ya ji ya rage jin haushin yadda take masa tun da yanzu ya gane ashe dai tana da hujja, kuma hakan ya birge shi domin yana so ya ga ƴan uwa suna yi wa junansu soyayya ta gaskiya. Ya ce "Ashe ban fahimce ta bane, amma dai ni akwai wani abu da nake so na faɗa miki" Ya faɗi hakan a fili a zuciyarsa kuma yana taraddadin cewar ko za ta amince da adadin kwanakin da Goggo ta gindaya masa, ko kuma za ta zaci cewar ya yi amfani da wannan damar ne ya ce yana sonta don ya cikawa mahaifiyarsa ƙudurin kwanaki ukun da ta faɗa masa, sannan ya tsoron ma ya ce mata an bashi kwananki ukun saboda gudun kar ta zargi cewa ba don Allah yake sonta ba tilasta shi aka yi shi ya sa ya yi furucin, wanda shi kansa ya san da a da ne zai ce tilastashin aka yi don ko a mafarki ba zai zaci zai so wata bayan Naja,atu ba sannan bai taɓa zaton zai mata kishiya ba amma dai yanzu ya yarda cewar zuciyarsa tana son Falmi!. Sassanyar muryarta ta katse shi da faɗin "Gaskiya kam baka fahimce ta ba" Ya ce "Allah ya sani, kuma ya ga zuciyata tun ranar da na fara saka ki a idanunta, na ji kin kwanta min a rai, sai dai da kaɗan kaɗan har na fahimci cewar sonki ne ya min kamun kazar kuku, ba zan ɓoye miki ba baya na karɓi lambarki da zummar zan kira ki in sanar da ke, sai kuma mahaifiyata ta zo min da wani babban lamari" Iya lafuzzansa da yadda yake da kalama kaɗai ya sa tun daga ranar da ta ganshi ta ji ya kwanta mata yana birge ta, sai dai wannan furucin da ya yi na cewar mahaifiyarsa ta zo da babban lamari ya sanya ta ji gabanta ya yi mummunar bugawa tunaninta ko cewa ta yi kar ya aure ta, hakan ya sa ita kanta bata san ta ce "Wane babban lamari kuma ? Mai ta ce?" Ta faɗa cike da zaƙuwar son ganin ya faɗa mata domin ya rage mata fargabar da ta ji ta mata ƙawanya a xuciya da jikinta. Tana jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Mahaifiyata ta bani umarnin na da kwana uku za a ɗaura min aure! Wallahi Falmi ba zan rantse miki don ki soni ba, ko don ki yarda da ni wallahi ba don mahaifiyata ta ce in fitar da matar aure a ɗaura min nan da kwana uku va na zo gare ki, daman can ina da burin furta miki shi ya sa har na karɓi lambarki, da ta faɗa min hakan kuma shi ya sa na yanke shawarar faɗa miki" Wani irin daɗi ta ji itaa dai bata san dalili ba sai dai ta san hakan ba ya rasa nasaba da jin cewa ba hana shi auren ta aka yi ba. Ta ce "Na yarda da kai ba sai ka rantse ba, mutum mai gaskiya Allah yana sanyawa mutane yarda da shi a zuciyarsu don haka ba sai kana rantsuwa ba na ji hankalina ya kwanta da furucinka, amma dai gaskiya zan faɗa maka wannan magana ba za ta yiwu a kwana uku ba, tun da ni mahaifana suna Maiduguri sannan aure ba zai yiwu a yi shi babu bincike ba don haka dole sai mun fahimci juna sannan manya sun shiga!." Muhammad ya ce "Haka ne gaskiya kika faɗa, to Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkairi" Ta ce "Amin" Tana jin kamar bata kyauta masa ba, domin ba sai ya faɗa ba tana jin yadda a muryarsa za ka fahimci bai ji daɗin furucin ba, wataƙila yana jin tsoron mahaifiyar tashi ta ce wani abu. Sallama ya mata yana mai mata fatan alkairi, ta amsa ya yanke kiran, duk da dai daman ya san da wuya wai gurguwa da auren nesa, wato auren har ya ɗauru a kaana uku, amma dai da ta furta masa sai ya ji babu daɗi, sannan ba ta ƙaunar saɓawa alƙwarin mahaifiyarsa na kwana ukun duk da Goggo mace ce mai fahimta amma dai zai so a ce ya cika mata umarninta ya yi abin da da dace wanda ta ce a lokacin da ta ce ɗin!. Gabaɗaya kasa aikin ma ya yi. Bayan ya dawo daga wajen aikin ya yi wanka ya shirya ya zauna yana cin abincin sa Mero ta jera a dining bayan ya dawo daga masallaci. Shigowar Hajiya Naja,atu kamar wanda wani ya wurgota shi ne abin da ya so bashi dariya, tana zuwa ta yi tsaye a kansa hannunta duka biyu a ƙugunta tana jijjiga jiki tamkar mai shirin a hau dambe. Ya ajiye fork ɗin hannunsa da yake gutsurar alkubus yana dangwala miya yana ci, ya ce "Barka da dare ranki ya daɗ... Bai ƙarasa ba ta katse shi da hanzari tamkar za ta hau shi da duka ta ce "Ya isa malam ni ba neman zan ce na zo ba, na zo ne a kan jin ba a sin maganar auren da aka gindaya maka kwana uku rak, shin iyayya ce maganar ko kuma ba me yiwuwa ba ce?" Ya mata kallon mamaki ya ce ."Mun dai zubawa sarautar Allah ido, muna jiran mu ga yadda zai yi da lamarin kin san ai shi komai daga Allah yake, abin da ya yi kuma shi za a gani" Cike da mamaki take kallonsa da sakakken baki ganin ya yi maganar hankalinsa kwance, kamar ma shi ƙara auren ba wani gagarumin abu bane a wajensa ko don ba shi za a yi wa kishiyar ba, ita kuwa saboda tashin hankalin da take ciki tamkar ta yi yawo tsirara haihuwar uwarta!. Tana zare ido tamkar wacce ta tauna barkono ta ce "Wai da gaske kake ko wasa, ni da na kasa gane kanka, anya Alhaji ba rubutun allo na malaman zaure aka shayar da kai b, alamu sun nuna ka manta wace ce Naja,atunka ko?" Ya haɗe hannuwansa biyu ya ɗora gwiyoyin hannun a kan dining tafin hannuwan kuma ya tallafi haɓarsa ya ce "Rubutu kuma haba Hajajju mutan maka, ina ni ina sha wani rubutu, sannan ni na isa in manta uwar gida sarautar mata... Bai kai ƙarshen maganar ba ta saka hannu ta buge plate ɗin gabansa ji kake tarrrrtsats ya yi masauki a kan tiles ya tarwatse, ya shiga ƙare mata kallo da mamaki kafin ya dawo daga duniyar mamakin da ta shayar da shi ya kwankwaɗa ta ce "Wato dai ta tabbata ka mayar da ni mahaukaciya, saboda raini da wulakanci har ka fara kirana da uwar gidan sarautar mata? Ni ban ga amfanin kirarin da ake yi wa mata na uwar gida sarautar mata ba, to uwar gida sarautar mata ko kuwa dai an mayar da uwar gida mahaukaciyar mata?" Tsaye ya miƙe yana wani kakkaɓw riga ya ce "Wannan kuma ke kika faɗawa kanki, don ni sai na san yadda na faɗa haka ake faɗawa mata, sannan wannan plate ɗin da kika fasa ki sa a share wajan" Yana faɗar hakan ya fara taku zai fita don zuwa masallacin isha,i daga na ya wuce ɓangaran Goggo. Ji ta yi ma ya raina mata hankali, hakan ya sa ta yi wani taku ɗaya biyu amma bata cimma sa ba ya rufo ƙofar ya juya ya tafi hankali kwance, tamkar wacce ta samu gushewar hankali haka take ji, ta lura lallai Alhaji ya daina shayinta sannan ta rasa inda mugun son nan nata da yake mata ya tafi. Ko ƙofar bata rufe ba ta fita, Mero da ta zo kwashe kaya ta ga an tarwatsa plate hakan na ta share tana ayyanawa a ranta cewa ba kowa bane ya yj aikin sai uwar ɗakinta a zuciyarta ta ce 'In sha Allahu, sai Alhaji ya miki kishiyar nan sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu" Ɓabgarenta ta nufa ta je ta ɗauki waya kamar sabuwar mahaukaciya ta shiga kiran Mom, Mom wacce ita ma abubuwa sun caɓe mata tana ganin kiranta gabanta ya faɗi don yanzu tana yi wa kiran Naja,atu kirari da tauraro me t wutsiya don ta lura yanzu babu wani labari mai daɗi. Tana ɗauka ta rushe da kuka ta ce "Mom na shiga uku an shiga tsakanina da Alhaji ba ya ma damuwa da damuwata kuma wallahi har kirarin uwar gida sarautar mata ya mini" ,Mom ta harzuƙa ta ce "Shi Alhaji?" Hajiya Naja,atu ta ce "Shi fa" Mom ta ce "Ah ya tabbata dai auren nan yi zai yi ɗan jakar uba, to kuwa bai isa ba zuwa zan yi a saka musu takunkumin mantuwa shi da uwar tashi, kamar yadda na miki alkawari zan share miki hawaye, gobe zan yi sakko ai wannan magana ta zama tarihi" Da wannan ta samu ɗan salama a zuciyarta don ta san Mom ba dai zuwa a mayar da fari baƙi ba a mayar da baƙi fari tasss. Alhaji da ya dawo ɓangaren Goggo ya wuce ya same ta suna zaune da Ruma wacce ta sha doguwar riga aka yi rolling da magribar fari duk don a ja ra,ayin Muhammad ya zaɓe ta a fasa auren kwana ukun ya jira ta gama idda. Yana shigowa ta tashi daga zaunen da take a kan kafet ta durƙusa a kan gwiwoyinta ta ce "Yaya sannu da zuwa, ina wuni" Sai da ya kalle ta ya ga sai wani sunkuyar da kai take kamar baƙar munafuka tana wasa da yatsun hannunta duk hakan cikin alamomin hankali da nutsuwa ne ake nuna masa. Bai amsa ba sai da ya durƙusa ya gaishe da Goggo ta amsa ya samu wuri ya zauna sannan ya ce "Yawwa sannunki, lafiya ƙalaw kin dawo lafiya?" Ya tambaya ta ɗago da kanta idanunsu suka sarƙe da na juna ta yi saurin sunkuyar da kai ganin kamar ma kallon tuhuma yake yi mata, shi kuma ganin Goggo tana nan shi ya sa ya amsa da ba zai amsa ba. Goggo ta ce "Ya wurin aikin naka?" Ya ce "Alhamdulillah" ,Ta ce ",Allah taimaka ya yi jagora" ,Ya ce "Amin" Goggo ta ce "Ina magana da muka yi da safe ta kwana" Ta faɗa don auna hankalin Ruma ta ga ko za ta bash wuri, shi kuma jim furucin Goggo ya sa ya kafe Ruma da idanu, da sauri ta tashi tsaye tana faɗin "Yaya zan shiha ciki mu kwana lafiya, Allah ya kare ka ya maka katangar ƙarfe da maƙiya da mahassada" Wannan duk addu,ar neman wuri ne tana fatan idan ya tashi ya zaɓe ta. Ya ce "Amin ya Allah" Ya faɗa yana tunanin dalilin da ya sa ta dawo gidan, bayan da kansa ya kaita gida. Ya kalli Goggo ya ce "Goggo magana tana nan, kuma na samu yarinyar da zan aura ɗin sai dai bamu gama daidaitawa ba" Goggo ta ɗaga hannu sama tana faɗin "Alhamdulillah" Ruma wacce ta yi laɓe a jikin ƙofa daga cikin ɗakinta, ya kasa kunnuwa kamar na zomo sai dai ko kaɗan bata jiyo abin da suke faɗa kasancewar a hankali suke maganar. . A nan za mu kwana sai gobe in muna raye, kar don na yi da yawa yau gobe ma ku sa ran samunsa haka a toh😒 MAMAN AFRAH *** [8/30, 6:10 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA MAMAN AFRAH