KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣9️⃣ *RAMLA* Kwance tashi asarar mai rai, awanni suka shuɗe kwanaki suka wuce aka yi sati guda da aurensu soyayya suke gwadawa junansu irin soyayya mai tsayawa a rai. Kasancewar bai mata kayan lefe ba kuɗi ya bayar a ƙa,ida ba a yi kayan gara ba, daman idan an yi lefe sai a yi kayan gara. Lokacin da ta zo gidan ta tarar da taliya katan ɗaya, indomie katan ɗaya sai shinkafa wacce a ƙalla bata fi kwano uku ba, sai su maggi gishiri da mai. Sannn tun da ta zo Abdulsalam bai fita da sunan zuwa wajen sana,a kullum yana gida sai ta yi tunanin saboda amarci ya ɗauki hutu. Ranar da ta cika sati biyu da tarewa ranar ne za ta koma makaranta ta tashi da wuri ta yi komai da komai ta shirya, yana kwance ya yj male-male a tsakiyar gado ta taɓa ƙafarsa tana jan yatsun ƙafarsa ya yi juyi yana buɗe idanunsa ta ce "Ni fa na shirya ka ga lacture ɗin ƙarfe takwas zan shiga" Ya ɗan yatsina fuska ya ce "Gashi ba na so ki yi nesa da ni" Ta kalli jikinsa yadda gabaɗaya ma shi a matsayinsa na namiji ba ya tunanin fita nema kawai ya auri kwanciya a gida, lalacinsa ya yi yawa. Ta ce "Ai makaranta zan je, bana so ake yin abubuwan bana nan saboda jarabawa" Ya ce "Haka ne kuma to sai kin dawo"Yana faɗar haka ta ga ya juya alamar zai ci gaba da bacci, cike da jin nauyinsa ta ce "Amma baka bani kuɗin abin hawa ba, sannan baka bani kuɗin makaranta ba" Ta faɗa ganin yanzu makarantar da tazara ba kamar daga gidansu da take kusa ba za ta iya zuwa da ƙafa. Ya juyo yana ɗan mata kallon mamaki ya ce "Ina kuɗin nan da kika xo da shi Ramla, akwai kuɗi wurinki sai kin tambayeni kuɗi bakya tunanin ko bani da shi, kina gani dai jiya na siyo kayan miya" Ta yi shiru a zuciyarta tana tunanin, lokacin da take gida, mahaifiyarta babu ruwanta da kuɗinta ko nawa take da shi sai an bata kuɗin makaranta amma yanxu da take ganin da yi aure ɗawainiyarta ta koma hannun mijinta shi ne zai ce ta yi wa kanta bayan ma kuɗin jari ne da za ta fara sana,a idan an kwana biyu. Ta ce "Kuɗin sana,a ne fa" Ya ce "Amma me za ki yi da kuɗi a jari haka, sana,ar ku ta mata ta cikin gida ya fi ki siyar da kuka da maggi da abubuwan da ba a rasa ba" Ta kalle shi ta ce "Ni bana sha,awar wannan zan yi dai tunanin sana,ar da zan yj" Ta faɗa tana tashi daga bakin gadon da ta zauna kanta duk ya kulle ganin za ta fara ɗaukan ɗawainiyar kanta daga yin aure. Ta ce "Ni zan tafi sai na dawo, amma ba za ka fita wajen sana,a ba" Zaune ta miƙe tana fuskantar ta ya ce "Ramla hutawar da zan yi shi ne kike idonta, ni ko yau da asuba sai da na yi addu,ar Allah ya kawo min aikin gwammanti inda zan je office na zauna in ɗan yi rubutu a takarda wata yana ƙarewa in ji musulmin alert ya sauka a wayata, amma kina batun aikin wahala ai ba a sabo da wahala duk runtsi kuma ai na ga muna da abin da za mu ci ko?" Gabaɗaya jikinta ya yi la,asar har ta rasa martanina da za ta yi amfani da shi wajen furta masa amsae tambayarsa tun da dai ta san taliyar an dauka sosai kuma ko don ya ajiye kudin saboda da wasu buƙatun ai ya nema Sanin bata da abin cewa ta ce "Asma,u tun dazu take kirana ta ce za a shiga aji na tafi" Ya ce "A dawo lafiya" Ta amsa tare da ɗaukan jakarta da mayafi ta je ta ɗakko dubu biyu a kuɗin ta saka a jaka tana tunanin idan har a ciki za take ɗaukan kuɗin makaranta da na abjn hawa to zara ba za ta bar dami ba in ji bahaushe. Har ta fito ta saka takalmi ta dawo ta ce "In ɗauki mukullina ko?" Ya ce ,"A,a ba ma sai kin dauka ba ai ina gidan har kya dawo" Baki buɗe take kallonsa amma ta kasa magana haka ta juya ta fito daga gidan ra ja masa ƙofar ta tare napep ta hau suka nufi makaranta tana ta sake -sake. Ko da ta zo makaranta suka haɗu da ƙawaye ana ta tsokanarta, amarya har ta murmure saboda amarci, ita kuma tana da murmushi. Bayan sun fito daga lacture suna zaune da Asma,u, Asma,u ta dube ta ta ce "Gaskiya kin yi kyau abinki, gaskiya auren ya karɓe ki" Ramla ta ce "To sarkin ƴan sa ido" Asma,u ta ce "Ango an fita yau ba zai ji daɗin komawa gida ba gimbiya bata nan tana makaranta" Ramla da ta dan cewar tana gida sai ta ji wani iri amma ta yi ƙoƙarin danne damuwarta saboda kar Asma,u ta fahimci wani abu kasancewarta mai zurfin ciki. Ƙarfe biyar suka tashi, Asma,u ta ganganra ita kuma ta hau napep, a ƙofar gidan ya ajiye ta, ta shigo gidan da sallama don gidan a buɗe alamar yana nan ɗin kamar yadda ya faɗa mata da safe. Amsa sallamar ya yi yana zaune yana danna waya abinsa, ya ce "Ƴan makaranta an dawo?" Ta amsa masa tana shiga ɗaki ta ajiye jakar ta core zanin gadon ta canja ganin gabaɗaya ya cukurkuɗa shimfiɗar wataƙila ma a kan gadon ya wuni. Ta fito falon tana faɗin "Mai za a dafa na ɗora?" Ya ce "Ki tafasa taliya kawai ta fi sauƙi sai a ci da mai da yaji" Ta ɗan yi shiru sai ta ce "Ai akwai kayan miya ba sai na yi jallof ba" Ya ce "A,a Ramla a cancanta kayan miyar nan a ajiye ya yi amfani da shi a hankali" Ta rasa bakin magana ta ce "Ni wallahi ban fiya son cin yaji ba, jiya ma fa shi aka ci" Kamar wanda ta masa wani gagarumin laifi ya fara faɗin "Ni dai kina son ƙure min samuna, in ba haka ba kin san wa kika aura don na faɗa miki talaka ne ni ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, amma in kin ga ke za kike sayan kayan miyar to sai ki yj amfani da wannn idan ya kare sai ki ban kudin in siyo" Galala take kallonsa hankalinsa a kan waya ta ce "Wai lafiyarka kuwa? Ni ce zan ke sayan kayan miyar ina na ga kuɗin kuma ko da a ce ina da kuɗin ai ba haƙƙina bane" Ya ce "Kuma ai ba laifi bane mace idan tana da shi ta taimaki mijinta, bayan fitarki ma na duba drower ɗinki na ɗauki dubu da ɗari biyar rance bani da data ne shi ne na saka" Ta ce. "Ka ɗauki dubu da ɗari biyar?" Ya ce "Eh aro ne" A wane kudin?" Ya ce "A wannan kudib da kika ajiye dai wanda kika ajiye da safe, to ina zaune a cikin gida kamar maye wayata babu data na rasa ya zan yi na ce ai kayan Allah na annabi ne, kayanki ai nawa ne don ma dai rance ne na yi" Ita mamakin ta ma yadda aka yi har ya san inda kuɗin yake, saboda a drowe ma a cikin ƙaramar jaka suke kuma sai da ta ɗaga kaya ta ajiye. Haka dai ta daure bata ce masa komai ba, ta tafi ta tafasa taliyar ta gama ta soya manja ta yanka tumatur da albasa. Bayan ta haɗa komai ta zuba masa yana ci ta shiga wanka don bata daɗe da cin cincin da.lemo ba da ta saya a makaranta shi ya sa bata jin yunwa. A haka ana kwana ana tashi har aka yi wata guda da auren, har zuwa lokacin bai taɓa ɗaukan kuɗin makaranta ya bata ba, barw na abin hawa, ta fara sana,ar siyar da sabulun wanki da klin saboda unguwar babu shago sai an ɗan yi tafiya kafin aje saboda haka mutane suke shigowa ana siya. Sai kuma ta saro ɗankunnaye na ƴanmata da zobuna da ɗan abin da ba a rasa ba take tafiya da su makaranta. Sai dai yanzu bata zuwa makaranta kullum a napep a sati sau biyu take zuwa a napep kwana ukun kuma ta je da ƙafa ta dawo da ƙafa saboda tana ganin idan tana taɓa kuɗin sana,ar za ta karye. Ga kuma Abdulsalam da yakr takura mata da rance yau ya karɓi dubu gobe ya karɓi ɗari biyar, kuma idan ta tambaya sai ya tsiri cewar bashi da shi. Tana zaune ya shigo da rana rai a ɗan ɓace yana ɗauke da wani buhu mai dauke da garin turo na masara ya ce "Ramla ga wannan garin gwara ake haɗawa da tuwo kar koyaushe ake cin taliya da shinkafa, kina dai gani dakyar na samu wanda na siyo jiya ma" Ramla ta kalli buhun bai fi kwano biyu ba niƙan ta ce "To ba damuwa amma ina kayan miya, don hatta maggi duk babu" Ya mata kallon tsaf ya ce "Ramla kina sana,a kina samu to a kan me don su kayan miya daddawa kuka da maggi ma sai kin tilasta min in kawo bayan kin san ba shi gareni ba, wannan ma wasu takalma ne na siyar su ma Zahraddin ne ya ɗinka mini ya ce in sayar in samu wani abu, to da gabaɗaya kuɗin na siyi masara aka niƙa" Ta yi shiru sai ta ce "To" Ya shige ɗaki ya cire kaya tana ta kokarin hura gawayi don gas ɗin ma da ya ƙare bai siyo wani ba. Ruwa ta kai masa banɗaki ya shiga wanka, ta shiga ɗaki ta fito masa da kayan da zai saka, wanda ya cire ɗin ta yi ƙoƙarin ɗaukewa za ta saka a kayan wanki, tana ɗagawa kuɗi suka faɗo, da mamaki take kallon kuɗi da sauri ta sunkuya ta ɗauka ƴan ɗari biyar-biyar ne da ɗan dubu ɗai-ɗai kusan dubu takwas ne ko bakwai don ba irgawa ta yi ba ƙiyastawa ne ta yi. Da sauri ta mayar da kuɗin cikin aljihun ta ajiye kayan a inda ta ɗauka ta fito daga ɗakin tana cike da mamakin mene ne ribarsa a matsayinta na matarsa don ya faɗa mata samunsa ko dai yana zargin za ta ɗora masa nauyi ko kuwa yana ganin za ta masa sata, a ganinta babu wanda ya cancanci sanin samunsa fiye da ita tun da ita ce ta san babunsa, kamata ya yi a ce samun ma ta sani. Ko da ya fito tana zaune tana yanka klin da almakashi, wato da yake a harhaɗe suke take cirawa ɗai-ɗai. Ko da ya shige ɗaki bata bi bayansa ba don ta rasa abin da za ta yi tunani gabaɗaya ya kulle mata kai. Tun daga tsakar gidan take jin ƙamshin turaren da ya fesa, wanda turarenta ne. Sallamar wata budurwa daga maƙota ta zo, amsa mata ta yi ta shigo, Abdulsalam da yake ɗaki jin zazzaƙar muryar mace da sauri ya fito dan kashe kwarƙwatar idanunsa. "Aunty ina yini" Cewar budurwar. Ramla ta amsa budurwar ta ce "A bani sabulun wanki guda biyu klin guda uku" Da to ta amsa mata, za ta shiga falon ta ɗakko shi kuma ya kawo kai zai fito suka yi kiciɓis. Kamar wanda zai je wajen jana,izar mutuwa haka ta ga yana sauri don da lura ma hankalinsa ko kaɗan ba a kanta yake ba. Yana fita tsakar gidan ta jiyo muryarsa yana yi wa yarinyar magana yana faɗin "Ƴan mata ado gari" Ta jiyo sautin muryar yarinyar ta ce "Ina yini" Ya amsa mata yana wani washe baki ya ce "Ai kam ke kina mana ciniki" Ta ɗan yi dariya ta ce "Ba komai ai nima daga gida ake aiko ni" Ya shiga janta da zance amma ta haɗe rai tana ganin shi ko kunyar matar shi ma ba ya ji. Ramla ta fito riƙe da ƙaramar bakar leda da ta zuba mata sabulun da klin ta miƙa mata tare da bata canjin ta karɓa, ta juya ta fita shi kuma gogan yana tsaye ya zubawa hanya fita ido har sai da ya daina hango ta Ramla ta ce "Yanzu don Allah masoyi wannan abin da kake bai kamata ba, zubar da kima ne... Bata ƙarasa ba ya katse ta da faɗin "Kedai kishin ki ya yi yawa wallahi, kuma kishi babu abin da yake janyowa a tsakanin ma,aurata face rashin jituwa da rashin zaman lafiya, uwa uba kishi yana saka zargi" Ramla ganin ya haƙiƙance kuma bayan ta san a lan gaskiyarta take, sau tari sai ya ringa kallon mata ko da ƙawayenta ne suka zo sai ya ringa musu kallon ƙurilla yana rawar jiki, ba damar ya ga mace duk sai ya ringa shishshige mata, hat kunyar ƙawayenta take ji idan suka zo gidan duk runtsi duk wuya sai ya tsinkata ta yi da lallamin ta nuna ɓacin ran a banza. Ta ce "Allah baka haƙuri, wallahi yawan kallo yana zubar da kima sannan ma... Bai ma jira ta gama maganar ba ya yi gaba yana gyara hular kansa. Abubuwa su cunkushe mata gabaɗaya ta kasa gane kan lamuran Abdulsalam wasu abubuwan sai ta ga kamar mugunta yake mata wani lokacin sai ta ji gabaɗaya karatun ma ya fice mata a rai. Wata rana ta tashi da zazzaɓi gabaɗaya bakinta babu daɗi sai yawu take tarawa a bakinta, ko da ta tambaye shi zuea asibiti biyar bai bata ba, tana zuwa da ta dawo ta sanar da shi cewa an ce ciki gare ta gabaɗaya yanayinsa ya canja, babu wani ɗoki irin na cikin fari ko kuma murna, haka ya ɗauki katin da ta kawo na magungunan ya ce "Ƙirgo kuɗin ki bayar in siyo miki maganin" Ta ɗaga ido ta kalle shi ta ce "Maganin ma ni zan siyawa kaina?" Ya ce "To ni ina na ganshi ko ana bada babu ne" Kuɗin ta ɗakko ta bashi dubu uku ya ce amma da da kawo maganin a jikin katin ta ga total ɗin dubu biyu da ɗari biyu amma ko canjin bai bata ba da ta tambaye shi ya ce "Kin san dai ba a ƙafa na je ba to kuɗin mashin na yi da shi" Ya fita ko sannu bai mata ba yana fita wani kuka mai zafi ya kuɓuce mata, ta shiga raira kukan a fili tana faɗin "Ni dai wannan auren babu daɗi kwata-kwata daman ba a min ba" Laulayi ya sako ta a gaba ko makaranta bata iya zuwa, saboda kuɗin abin hawa ita kuma bata da kuzarin zuwa makaranta a ƙafa gashi cikin ya bayar da ita da kwaɗayi ciye ciye kuma ko mai take so sai dai ta bayar da kuɗin ya siyo mata. Sannu sannu ya zamana gabaɗaya nauyin gidan ya dawo kanta, tun daga siyan kayan miya, mai maggi siyan ruwan amfanin gida, tafiya ta yi tafiya idan kayan abinci ya ƙare sai garin tuwo, haka zai nemi wuri ya kwanta ba ya fita aikin komai sai dai ita ta ɗauki kuɗinta ta auno garin kwaki ta auno shinkafa da sauran abin da za su yi amfani da su daman klin da sabuli tuni a cikin na sana,arta ake ɗauka. Sai ya zamana nauyin da miji zai ɗauka ita take ɗauka, kawai don Allah ya saka mata albarka ne ma a kasuwancin nata shi ya sa amma da tuni ta karye. Tun tana jurewa tana ganin abin na ƙare ne tun da shi kullum.batunsa ɗaya zai samu aikin gwamnati har dai ta kai idan ta masa magana sai ya rufe ta da balai yana faɗin "Tun farko sai da na faɗa miki bani da aikin yi sai sana,ar aikin ƙarfi da ɗan ɗinkin takalmi kika yi na,am yanzu kuma ki zo kina wasu maganganu kawai saboda kina taimaka min a cikin gida, ai ba ni kaɗai nake cin abincin ba har da ke" Ta ce "Na san ba kai kaɗai kake ci ba amma dai kai Allah ya ɗorawa ɗawainiyar gidan" Ganin abin ya ki ci ya ƙi cinyewa ta je ta samu Zahraddin ta faɗa masa, da ya same shi ya masa magana kamar ma ya zuga shi ne, ya hau masifa da ya dawo gidan yana faɗin ta je ta tona masa asiri saboda ta ga bashi da shi. Watarana ta je gidansu wuni, mahaifiyarta ta kalle ta ta ce ",Ramla anya baoi da damuwa kuwa" Wasu hawaye ta ji sun taru a kwarmin idanunta, amma ta danne su bata bari sun zubo ba ta ce "A,a bani da wata damuwa" Mahaifiyarta ta ce "Ramla ni fa na haife ki, na san halinki, kuma na sanki da zurfin ciki, kallo ɗaya na miki na san akwai abin da yake damunki" Kawai bata san ma ta faɗa jikin mahaifiyarta tata ta fashe da kuka ba. Wani iri mahaifiyarta ta ji kukan yana sosa ranta, ta saka hannu tana bubbuga bayan Ramla tana faɗin "Ki yi shiru Ramla, ki yi haƙuri shi aure ɗan haƙuri ne amma ba a ce mutun ya tare damuwa a zuciyarsa ya barta ba, hakan illa ce babba, don haka ki faɗi abin da yake damunki" Bata amsa ba haka ta cigaba da kukan har sai da ta ji zuciyarta ta yj sanyi sannan ta raba jikinta da na mahaifiyarta ta shiga share hawayen tana ta shashsheka da ajiyar zuciya ta ce "Ni wallahi abubuwan ne duk sun wuce lissafina, bani da wanda zan faɗawa sama da ke, ke ce mahaifiyata kuma sirrina, ke ce wacce na san duk abin da na faɗa miki ba za ki fallasa ba sirri ne, wallahi kawai na gaji da ɗawainiyar gidan ne" Mahaifiyarta ta jima bata ce uffan ba, sai da ta ɗauki ƴan mintuna tana nazarin ta sannan ta ce "Ramla ya kamata ki zama mai koyi da ni, kina ganin yadda na zauna a gidn mahaifinki ko yaji ban taɓa zuwa ba, sannan duk abin da na samu tamkar ya samu ne, ɗaukan ɗawainiya ko taimakawa namiji daga mace ba sabon abu bane, sannan kin san wa kika aura, tun da bashi da shi" Ramla ta ce "Na sani kuma ina kan koyi da ke, amma abin da nake so ki gane zkwai bambanci tsakanin mazan yanzu da mazan da, ke duk abin da kike yi a gidaan nan lokacin mahaifinmu bashi da wacce yake ganin mutuncin ta ko yake ganin kimarta, sannan yake jin daɗin abin da kike taimaka masa ya gode miki ya sanya miki albarka bai taɓa nuna miki wani abu ko da a fuska ne, amma Abdulsalam bai san duk abubuwan nan ba kamar ma dole haka ya ɗauki abubuwan da nake yi a cikin gidan" Mahaifiyarta ta kalle ta da idon basira ta ce "Na fahimci maganarki amma daman halaye basa taɓa zuwa ɗaya, amma abin da nake so da ke ki yi haƙuri idan da kuɗi a hannunki kike yin abin da ya dace ki masa uzuri tun da babu" Ramla ta ce ,,"Yana da halin yin buga-buga amma ya langɓe yake zaune a gidan" Gabaɗaya tausayin ƴar tata ya kama ta kuma ta fahimci cewa abin ya taɓa ta tun da duk zurfin cikin Ramla amma bata faɗa ba sai yau, ta sanar da ita ta ƙara haƙuri zuwa nan gaba kaɗan idan har bai canja ba sai a ɗauki mataki tunda nauyi a wuyan namiji yake, kuma duk runtsi sannan duk ƙasƙancin abinci gwara ya kawo a kan a ce ya bar mace da ɗawainiyar gidansa. Tun da ta faɗawa mahaifiyarta maganar sai ta ji nauyi ya ragu a zuciyarta. Daman babu wanda ta faɗawa ciki kuwa har da Asma,u. Bayan sati biyu da faruwar hakan mahaifiyarta ta fara rashin lafiya, ana zuwa asibiti aka ce hawan jini ne!. Tun daga wannn rana Ramla ta ɗauki alƙawarin komai runtsi daɗi ko wuya ba za take faɗawa mahaifiyarta damuwarta ba, saboda gudun ƙara mata damuwa a kan hawan jinin da take ɗauke da shi. Rayuwa tana tafiya, abubuwan suna shuɗewa har cikin jikinta ya isa haihuwa a lokacin da ta haihu da kwana tara mai gidan ya ce ya basu sati ɗaya su tashi saboda kuɗin da aka biya hayar na shekara ɗaya ne!. Ta kalli ƴarta Aisha wacce suke kira da Humaira ta ga daga haihuwarta za a fara jigilar yawon neman wajen zama, don shi ya ce bashi da kuɗi ragon suna ma bashi ya ci. Haka ta haɗa gudunmuwar da ta samu a suna, sda wasu kuɗaɗen ta biya musu kuɗin hayar. Bayan ta zubar da wanka, Abdulsalam ya kwanta jinya, wasu ƙananun ƙuraje ne suka fito masa a jikin mafitsara, sai kuma jikin mafitsarar ya yi luhu-luhu kamar tashin wuta... MUN KUSA GAMA BOOK 1 BAI FI SHAFI 6 BA MAMAN AFRAH .*** [8/31, 6:57 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA MAMAN AFRAH