BOOK 1
🅿3️⃣0️⃣ *GOGGO* Goggo ta ce "Alhamdulillah, haƙiƙa na ji daɗin wannan magana" Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah zan yi ƙoƙarin cika miki burin ki Goggo a kwanaki ukun nan za a ɗaura min aure kamar yadda kika buƙata" Goggo ta ce "Samun ɗa na gari babban abin alfahari ne ga iyaye, na ji daɗin samunka a matsayin ɗa ubangiji ya maka albarka ya baka zuri,a ɗayyiba" Ya amsa da amin yana ji a ransa ko dai ya sanar da Goggon ainihin maganar cewa wacce ya furtawa son iyayenta ba a gari suke ba sai an je an sanar da su, amma da ya yi tunanin kar ta ga ko ba ya son cika umarninta ne sai ya ja bakinsa ya yi shiru, kamar ta san tunanin da yake ta ce "Amma ita yarinyar ta amince da kai" Ya hurar da iska daga bakinsa ya ce "Eh ta amince tun da ta yi na,am amma dai za ta sanar da na gaba da ita tukunna akwai buƙatar yin shawara tun da bamu daɗe da haɗuwa ba" Goggo ta yi shiru tana nazarin umarnin kwana ukun da ta bashi wanda ta yi hakan ne don ta nunawa Hajiya Naja bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne, sannan ta takawa ƴar uwarta Mama Magajiya birki ita da ƴarta Rumasa,u saboda neman shiga hanci da ƙudundunen da suke, gabaɗaya ma ta rasa cewa shi Muhammad ɗin gida nawa za a raba shi, duk da dai ɗa namiji Allah ya halalta masa auren mace huɗu!. Ta ce "In sha Allah haɗuwarku alkairi ce ina ji a jikina ba za ka yi zaɓin tumun dare ba!" Sun ɗan jima suna hira daga ƙarshe ya mata sallama ya baro ɓangarenta. Ruma tun da ta yi laɓen amma ba wata magana ƙwaƙƙwara da ta ɗauka, don bata ji komai daga furucin da suke ba sai dai jikinta ya bata a kanta ake magana wannan fa sanya ta ji wani irin daɗi da sanyi a zuciyarta. Tana tsayen wayarta ta shiga neman ɗauki, tana dubawa ta ga sunan Mama, ta amsa daga ɗaya ɓangaren Mama ta ce "Ƴar albarka yarinyar da za ta yi auren gidan arziƙi" Ruma ta katse Mama daga wannan kirarin ta ce "Mama albishirinki " Mama ta ce "Gori fari ƙato" Ruma ta kasa magana saboda farincikin da yake ratsa ta. Mama jin shiru ta ce "Ruma ki kiyayeni da shegantaka, ya za ki lasa min zuma a baki ki ƙyaleni, ka ji ja,irar yarinya" Ta faɗa cikin sigar wasa tana ƴar dariya. Ruma ta ce "Mama albishir ɗin ne da nauyi, amma dai tun da kin ce haka bari na warware miki biri har watsiyarsa" Mama ta ce "Faɗa min ina sauraro, Allah sa dai Muhammad ɗin ne ya kira ki ya sanar da ke yana sonki, ita kuma Goggon ta ce ki kirani ki min albishir ta amince da aurenku ya jira ki gama idda" Kalaman Mama suna shiga kunnuwan Ruma cikin wani sanyi don daɗi ne ya xiyarceta tana fatan hakan amma dai ta tabbatar da wannan abin da Mamar take faɗa shi ma yana hanya, don kuwa kusan hakan ne. Ta ce "Mama ga shi can fa a falon Goggo suna zaune suna magana a kan auren" Wata wawiyar guɗa da Mama ta saki sai da Ruma ta yi saurin cire wayar daga kunenta tana dariya saboda har tsakiyar dodon kunenta ta ji guɗar. Ruma ta mayar da wayar kunenta ta ɗora da faɗin "Don ko abin da suke faɗa bana ji, ƙusƙus suke yi, ƙasa-ƙasa suke magana" Mama ta yi ɗiff tare da doka wani uban tsaki da ya sake shiga kunnen Ruma ta ce "Ashe baki da hankali Ruma, to albaishir ɗin na uban mene ne tun da dai baki tabbatar da cewar maganarki ake yi ba?" Ruma ta yi ɗiff ta ma rasa abin da za ta ce sai kuma ta ce "Haba Mama na faɗa miki wataƙila suna son bamu mamaki ne don kar maganar ta bazo ko kuma suna yi a hankali ne don kar Hajiya Naja,atu ta yi laɓe kamar yadda na musu laɓe, ta ji abin da ake faɗa". Mama ta ce "Ko kuma suna yi a hankali don kar ki ji a kan wa ake maganar ba" Jikinta ya yi sanyi da furucin Mama amma dai zuciyarta tana sake gaskata mata cewar a kanta ake magana ta ce "Mama fata nagari lamiri ne fa, ki faɗi alkairi ko ki yi shiru" Mama ta ce "Ruma ai na fi kowa son alkairin nan ya same ki" Ruma ta ce "To ki dage da adsu,a kawai kairan za mu saurara" Sun jima suna hira Mama har wani tunani ya faɗo mata ta ce "Ruma anya ba za mu rage kwanakin iddar nan taki ba kuwa?" Ruma ta ce "Kamar ya Mama?" Mama ta ce "Mu yanke wasu adadin mu matso da iddar kusa, don kar wannan damar ta wuce mu" Ruma ta ce "Mama kin manta kin faɗawa Goggo lokacin da aka sake ni, to tana sane kin santa dai da lissafi, kuma ni a ganina indai har ya amince zai aure ni ai ba zai gagara ya kasa jirana na gama idda ba!" Mama ta ce "Kuma fa haka ne." Sun jima suna tsara abubuwan da za su gabatar idan Ruma ta samu damar auren Muhamamd ɗin daga ƙarshe suka yi sallama bayan sun gaisa da su Umar, tana gama kashe wayar ta jiyo muryar Goggo tana ƙwala mata kira, ta taso kafin ta buɗe ƙofar ɗakin sai da ta tsaya ta yi addu,a ta shafa sannan ta buɗe ta fito, sai wani murmushin farinciki take wanda ta kasa ɓoye shi. Ta zo ta zauna a ƙasan kafet, tana ɗan sunkuyar da kai ta ce "Gani Goggo" Goggo da ta rasa sunkuyar da kan na mene ne ta basar tana faɗin "Daman cewa na yi ki fito yayan naki ya tafi, tun da daman ganinsa ne ya sa kika koma ɗaki" Ta faɗaɗa murmushinta jin furucin Goggo ta ce "Eh ai na baku wuri ne ku tattauna" Goggo ta ce "Ayya ai mun gama tattaunawa" Ruma ta yi shiru tana jiran jin ta inda Goggo za ta fara mata bayanin cewar ya zaɓe ta amma shiru maƙatau, tun tana saka rai har dai ta kalli Goggo ta ce "Goggo Yayan bai bada saƙo a bani ba?" Goggo ta mata kallon rashin fahimta ta ce "Saƙo kuma? Kun yi maganar saƙo ne ke da shi? Ko kin tambaye shi kuɗi ne za ki yi amfani?" Kai ta shiga girgizawa don ta ma rasa bakin magana amma duk da haka bata cire rai ba wani ɓangaren na zuciyarta yana faɗa mata cewar ɓoye mata Goggon ta yi wataƙila sai a gaba za ta sanar da ita. A ɓangaren Falmi tun bayan da suka gama waya da Alhaji Muhammmad, ta yi shiru tana nazarin kalamansa, bata ankara ba ta tsunduma duniyar tunani. Ta yi nisa a tunani Auntyn ta ta shigo ɗakin ganin tana mata magana bata amsa ba, sai ta tsura mata idanu, a nan ta gane cewa ƙanwar tata bata ma san tana yi ba, wai kunu a maƙota!. Ganin ta lula duniyar tunani idanunta kafe a saman silin, hakan ya sa ta ji wani irin rausayin ƴar uwar tata ya tsarga mata har tsakiyar zuciya. Cike da tausayawa ta taka tana mai ƙarasawa kusa da ita ta yi wa kanta masauki a kusa da ita, sai dai har ta zauna Falmi bata san ta zauna ba, don tunanin Alhaji Muhammad ɗin da take yi ya cakuɗe da tunanin tsohon mijinta, wanda a har kullum idan ta tuno da shi da irin uƙubar da ya gana mata a zamansu na aure sai ta ji gabaɗaya tsoron maza ya cika mata zuciya duk da tana yi wa wannan sabon mutumin da ya kira kanshi da suna Muhammad kyakkyawan zato!. Hannu Auntyn nata ta miƙa ta ɗora a kafaɗar Falmi, lokacin har idanun Auntyn sun cika da ƙwalla, saboda tausayin Falmi duk tunaninta tana tuna damuwa ne don ta san tsohon mijinta ya bar mata tabo a zuciya wanda ba za ta so mikin wannan yake motsawa ba. Da ta dafa kafaɗar tata ma sai da ta ɗan jijjigata, haɗe da kiran sunanta ta ce "My ƙanwa Falmi!!!" Falmi ta ji saukar maganar kamar daga sama. Da sauri ta yi ɗan firgigit tana dawowa hayyacin ta. Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune tana faɗin "To Aunty?" Ta faɗa tana kallon cikin ƙwayar idanunta da ta ga sun yi ƙwalla. Ta ce "Aunty lafiya?" Ta tambaya gabanta yana faɗuwa. Aunty ta ɗora ɗaya hannun nata a ɗaya gefen kafaɗar Falmi ta ce "Ina fa lafiya Falmi kina cikin damuwa, ba zan gaji da maimaitawa ba ba zan taɓa yafewa tsohon mijinki cutar min da ke da ya yi ba, na tsani na ganki cikin damuwa Falmi zan yi yaƙi da ko mene ne don ganin kin yi farinciki" Dariya ta yi har hakoranta kyawawa suka bayyana ta ce "Kai Aunty wai ke mutum ba zai yi tunanina ba sai na abu ɗaya, ni fa na manta ma da damuwar da ya saka ni, ai tun da dai babu aure tsakaninmu yanzu kuma na gama iddarsa tun daɗewa" Auntyn ta, ta ce "Falmi na san dai baki da wata damuwa, mu dai kullum burinmu kowa ya sanya ki farinciki" Falmi ta ce "Aunty ki yarda da ni ba wai tunaninsa nake ba, akwai wani gagarumin al,amari da ya shigo rayuwata, shi ne tunanin da nake" Cike da rashin fahimta take kallonta ta ce "Mene ne shi Falmi?" Falmi ta dafa kafaɗun ƴar uwar tata ta ce "Aunty..." Sai kuma ta kasa ƙarasawa ta yi shiru Aunty ta ce "Tsakanina da ke ai ba shamaki mene ne" Ta sauke hannuwanta daga saman kafaɗarta ta fara wasa da yatsunta ta ce "Aunty wani ne ya ce yana sona da aure!!!" Wani irin cire hannunta ta yi daga kafaɗar tata, tana jifanta da wani mugun kallo mai kaɓar harara ta ƙanƙance idanu ta ce "Falmi kin cikin hayyacinki kuwa, alamu sun nuna kina son nuna min cewar kamar wanda ya ce yana son naki ma kin yarda da maganarsa, ta yanayin furucinki, ko gama dawowa daga suman allurar sanƙarau ɗin wulaƙancin da ɗa namiji ya miki baki yi ba amma har wani namijin ya samu damar furta miki kalmar so har yake miki ikirarin da aure yake sonki kika yarda???" *HAJIYA NAJA,ATU* Yadda ta ga safe haka ta ga dare, domin kuwa ta kasa runtsawa ko kaɗan, ba komai ne ya mata karan tsaye ba a ƙahon zuciya sai maganar ɗaurin auren Alhaji Muhammad nan da kwanaki uku rak masu zuwa. Tana ta tunanin yanzu kenan idan gari ya waye saura kwana biyu, aka sake kwanciya aka tashi zai zamana saura kwana ɗaya, idan aka sake kwantawa aka tashi a ranar ne za a ɗaura masa aure, wato daga ranar ya zama mallakinsu ita da wata. Wannan tunanin da ya cika mata kwanya ne ya sanya ta tashi zaune daga kan gadon ta zauna dangargar a fili ta furta "Wallahi ƙarya ne! Ba za ta taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa, ƙaryarki ta sha ƙarya Goggo! Mijina ne na ni kaɗai da ni kaɗai zai rayu ni kaɗai zan gaji dukiyarsa idan ya mutu lokacin ke kuma ƙasa ta daɗe da cinye namanki bare ki saka ran kema za ki dandali arziƙi daga cikin arziƙin da ya tara ya tafi ya bari!" Ta faɗa tana jin wani irin tuƙuƙin baƙinciki da ɓacin rai, bata taɓa zaton haka kishi yake da zafi da ƙuna haɗe da raɗaɗi a zuciya ba sai yau, ko don ita ta riga ta saka a ranta cewar bata da kishiya a duniya. Ta muskura ta zaro ƙafafunta daga kan gadon ta ce "Shi ya sa na zo na auri maraya, wanda bashi ma da uwar a raye bare ta zo da ƙauli da ba,adi, amma wannan uwar mijin nawa ta zo da wani batu da a ce zan iya da na kawar da shegiya" Haka take ta saƙe-saƙe bata ankara ba ta ji ana kiran assalatu ashe kwanan zaune ta yi don bacci ko ɓarawo bai ɗauke ta ba, kai ko gyangyaɗi bata bari ya sure ta ba. Ta tashi dakyar take ganin gabanta ta shiga bayi aka yi alwala aka fito, sallar da sai rana ta yi gaɗau-gaɗau take yi watarana, sannan daga haka tana iya jiyo yadda jikinta yake tashin warin gumi. Haka ta zo ta kabbara sallar bayan ana shiga masallaci, rabi tana karatu rabi hankalinta a wani wajen tunane-tunanen da ya cika mata zuciya fal. Tana zuwa sujada ta ce "Allah kana ganin uwar mijina, Allah ka mini maganinta, Allah ka sani mijina ya haramtawa kansa auren wata macen, amma mahaifiyarsa tana son tozartani ta tilasta shi ya mini kishiya, Allah na kawo ƙaranta ka mini maganinta ka tarwatsa ƙudurinta, mugun abin da take bina da shi ya ƙare a kanta" Ita kaɗai ce addu,ar da take furtawa, gabaɗaya sujadar sallarta addu,a ɗaya ta yi ra maimaitawa. Tana sallamewa ta ɗaya hannuwa sama ta fara zayyano addu,ar nan guda ɗaya a kan ƙarin auren Alhaji. Tana rufe da yin addu,ar Allah ya bata nasara a kan zuwa wajen malamin da Mom za ta yi. Tana shafa addu,ar ta tashi, buguzum-buguzum aka koma bakim gado ko damar cire hijabin ba a samu ba hankali ya yi gaba. Waya aka ɗakko aka kamo sunan Mom har kiran ya tsinke ba a ɗaga ba. Sai da ta kira sau huɗi a na biyar ɗin sannan aka ɗauka. Mom wacce bacci ne ya hana ta ɗaukan kiran, saboda ƙaran wayar ne ma ya tashe ta a bacci, ganin sunan Naja,atu ya sa maganar ƙarin auren mijin Najar ya faɗo mata da sauri ta tashi zaune tana murtsuke ido ta ɗaga wayar, aikuwa muryar Hajiya Naja,atu da take raɗau kamar wanda take magana da tsakar rana babu alamar bacci ta ce "Mom ba dai bacci kike yi ba" Mom da ta san idan ta c bacci take Hajiya za ta ce bata damu da maganar auren ba, don tun da ta ji ta yi wannan furucin ta san da alama ita idanunta ma basu ga baccin ma, ta ce "Ash-sha Naja,atu ina na ga damar bacci ina saƙe-saƙe,, da na ga baccin bai daukeni ba na tashi na ringa jero nafili da mana addu,ar Allah ya ɗoramu a kan maƙiyan nan naki ya bamu ikon cin nasara a kansu" Ajiyar zuciya Hajiya Naja,atu ta sauke don da har za ta fara yi wa Mom faɗan bata damu ba. Hajiya Naja,atu ta ce "Mom nima da ni za a je wurin boka me da ko malami, duk dai wanda ya samu, saboda hankalina gabaɗaya a tashe yake, ta kasa kwanciya" Mom ta ce "To shikenan bari idan na yi wanka sai na jiraki ki zo mu tafi" Hajiya Naja,atu ta ce "Mom har damar wanka kike da ita, ai ba wani maganar wanka abin da yake gabanmu ya fi gaban wasa, nima wannan babu wani wanka da jikina zai gani, ai wanka ma ɗan ta yi daɗi ne!!!" *RAMLA* Wasa -wasa ciwo yake gaba duk da magungunan da ya siyo a kyamis amma ciwon kamar ƙaruwa yake, daga ya saka wando idan wandon yana taɓa wajen sai ciwon yake ƙaruwa. Rashin kuɗin zuwa asibiti ya dakatar da komai ga hankalin Ramka da ya kai ƙololuwar tashi, ta haɗa ɗan cinikin da take yi ta bashi ya je asibitin, aka rubuto masa magungunan sannan likitan ya ce yana zuwa ana wanke ciwon. Duk da yana zuwa ana wankewa amma kaaancewar ciwo ne a matse -matsi to haka yake sake komawa baya har dai ya zamana ya daina saka wando sai dai ya saka jallabiya kawai don fita ma daina yi ya yi, saboda daga ya wuni a haka sai dai wurin yake ɗoyin silgewar da wurin ya yi. Saboda ciwon Abdulsalam Ramla ta daina zuwa makaranta domin komai ya cunkushe bata da kuɗin abin hawa bare a yi maganar abin da za ta ci, ga ƙaramin goyo hatta famfas ita za ta siyawa Humaira, duk cinikin da ta yi kuɗin suna tafiya a siyan maganin Abdulsalam ne.Dan dai Zahraddin ma yana iya ƙoƙarinsa yana yawan zuwa ya duba shi, haka ma yana turo matarsa Hasiya ko su xo tare su duba shi, sai dai wani lokacin yana ɗan bata wasu kuɗi duk da dai shi ma ta kansa yake ga talauci ga iyali. Wani lokacin yana zaunar da Ramla ya yi ta kwantar mata da hankali yana faɗa mata komai zai wuce wata rana. Sannan idan suna tare da Abdulsalam yana faɗa masa ya riƙe ta da daraja saboda a wannan zamanin ba kowacce mace ce za ta jure abin da Ramla ta jure ba domin wata ma idan ta ga ciwon ya ƙi ci ya ƙi cinyewa za ta nemi saki ne. Mahaifiyarta ma tana mata nasiha, sai dai itama tana bata ɗan wani abun don yanzu gabaɗaya Ramla ta zama abin da tausayi saboda ɗaukan ɗawainiyar gidan ga kuma rashin lafiyar miji wanda ita ce take kula da shi. Tsawon wata guda yana fama da rashin lafiyar nan, watarana ya je asibiti za a wanke sai likita ya ce wannan ciwon dole sai an yi masa aiki an cire inda ya ci, in ba haka ba ciwon yana gaba duk da wankin da ake yi. Ko da ya dawo gidan ya faɗaw Ramla hankalinta ya tashi, tana zaune a kan kujera ya kama hannunta ya ce "Ramla na san kina ƙoƙari a kaina, kuma na gode miki ba zan taɓa mantawa da karamcin ki a gare ni ba, saboda kin yi min halacci. Amma inaso ki sani likita ya ce matsawar ba a yi aikin nan ba to in dab da rasa ƙuzarina na namiji a wajen aikata sunna, idan jijiyoyin suka mutu to zai zamana sai dai na haƙura da iyali, duk da yanzu Alhamdulillah ga Humaira na haifa, amma ba zan so na shiga haƙƙinki ba tun da dai ni ga yadda Allah ya yi da ni, ya jarabceni da ciwon mafitsara inaso ki faɗi yadda kike so a yi don gudun shiga haƙƙin ki amma dai ki sani Ramla ina sonki, so na har abada" Ta ɗago fuskarta ta sauke a kan fuskarsa sannan ta sanyan idanunta cikin nasa, yadda wasu ƙwalla suka taru har sheƙi suke, a take ta ji wani irin mugun tausayinsa ya ratsa mata zuciya, lokaci guda ta ji wani sabon sonsa yana yunƙuro mata. Ta ce "In sha Allah za ka samu lafiya, ni ina tare da kai duk runtsi duk wuya" Ya ce "Ramla ke fa mace ce mai ƙarfin sha,awa duk da wani lokacin baki fiya samun biyan buƙata daga gareni ba, amma dai ta yaya za ki rayu a haka bayan ke kina da lafiyarki," Ta ce "In sha Allah za a dace idan an yi aikin, amma dai ka sani na maka alƙawarin ko da ba a dace da aikin ba duk da dai ana fatan a dace ni to ko ba a dace ba ba zan taɓa rabuwa da kai ba Abdulsalam, zan zauna da kai har ranar da numfashina zai bar gangar jikina" Gabaɗaya ya ji tausayinta ya kama shi, tabbas ba kowace mace ce za ta yi hakan ba. Ya ce "Haka ne Ramla amma inaso ki sani kuɗin aikin ne ma wahalar samu, saboda ni ban ajiye ba kuma ban ba kowa ajiya ba, kuɗi naira dubu ɗari da hamsin da a ce gidan nan da muke zaune nawa ne da siyar da shi zan yi lafiya ai ta fi komai musamman lafiya ta mafitsara idan ta samu matsala shikenan sai dai a yanke min ita duka" Salati Ramla ta ɗauka tare da fara tunanin idan har tana raye kuma tana da abin da za ta sama masa lafiya kar ya rasa abin da kowane namiji zai yi tunƙaho da shi, ai kuwa za ta tabbar masa yana da ita. Ya ce "Allah sarki rayuwa da iyayena suna raye da ko gonar ce da sun sayar sun nema min magani" Tsaye ta miƙe har lokacin hannunsu a sarƙe da na juna ta ce "Karka damu, zan baka kuɗin da z aa yi aiki"......... Ya kalle ta da mamaki ya ce "Kamar ya Ramla ina za ki samo kuɗin nan?" !Ramla ta ce "Zan siyar da sarƙa da ɗankunnena" Bai san ma ƙwallar idanunsa sun gangaro ba da sauri ya miƙe tsayen shi ma ya saka hannu biyu ya rungume ta. Sun jima a haka yana ta sanya mata albarka da mata godiya. Ta siyar da sarka da ɗankunnen miliyan ɗaya da dubu ɗari, ta taho da kuɗin gidansu ta wuce daman ita da su Amal suka je, sannan sai da ta faɗawa mahaifiyarta maganar ta shawarce ta da amincewarta ta siyar saboda ta yarda ta taimaki mijinta uban ƴarta. Mahaifiyarta ta karɓi dubu ɗari biyar ta ce wani ɗankunnen za a siyo mata ko zobe ta mayar da girbinsa, ta ba mahaifiyarta dubu ashirin ta ba su Amal dubu ashirin su biyu. Gida ta wuce da duka sauran kuɗin, ko da ta faɗa masa yadda ta sayar ya washe baki saboda yana saka ran kaso mai tsoka a kuɗin. Ta ɗora da faɗa masa cewar ta bar wa mahaifiyarta dubu ɗari biyar ɗin za a yi amfani da ita, nan yansauya akalar murmushinsa zuwa ɓata rai da ta tambaye shi ba a si sai ya wayince yana faɗin "Ai shawarar da suka yanke ta yi saboda kar kuɗin ya salwanta. A daren ranar aka shiga gidansu Ramla aka sace wannan kuɗin da ta bari. Ko da mahaifiyarta ta sanar da ita ta ce ta fawwalawa Allah, ta yarda da ƙaddara Allah zai musanya mata da mafi alkairin abin da ta rasa. Ko da ta faɗawa Abdulsalam maganar ya ji haushi don gani ma yake sakaci ne ya sa aka sace. Bayan kwana biyu ya biya kuɗin aikin da komai da komai. Aka yi masa aikin, an yi cikin nasara Alhamdulillahi. Da aka sallamo shi ƴan dubiya suka ringa zuwa ciki har da mahaifiyar Zahraddin don ita ma ta kawo masa wasu ƴan kuɗaɗen duk da daman itama ta kanta take ciwon ƙafa ya sakota a gaba, itama kuma Zahraddin ɗin ne yake ɗaukan ɗawainiyarta. Yana cikin jinyar ma ta faɗi a ƙofar banɗakinta lokacin ta fito daga banɗaki wannan en sanadin mutuwarta don kwananta ɗaya da wuni ɗaya ta koma ga mahalacci Zahraddin ya sha kuka kuma ya fi Abdulsalam damuwa, ko kuwa don shi ba mahaifiyar bace. Aiki ya yi kyau don sosai take kulawa da shi tana masa abinci wanda yake so saboda da ta biya kuɗin aikin aka siya masa magunguna ta siyo musu kayan abinci ta ƙara jarin kayanta da suka ƙare!. Ya warke sarai amma ya ƙi nuna mata ya warke, saboda ba ya so ya nuna ya warke ta dakata da dafa masa abun daɗi. Sannan uwa uba ba ya so ta nemi haƙƙinta na auratayya a wajensa. Har abin ya zo yana damunta tun tana hakuri ƙarshe da ta same shi da maganar sai ya ce "Amma ke da bakin ki kika ce ko da ba a dace da aikin ba ko kuma na rasa mafitsarae ma gabaɗaya , za ki zauna da ni zama na har abada! Amma yanzu lin kasa jurewa haba Ramla!" Yadda ya mata maganar cikin wata isa-isa sai abin ya mata ciwo amma bata ce masa ƙala ba... Sai da ya ɗora kusan sati uku a bayan warkewarsa, bayan luma likita ya tabbatar masa cewar zai iya komawa iyalinsa. Bayan ya koma ya ga ya dawo garau babu wata matsala komai lafiya lau, daga nan kuma sai ya cigaba da gudanar da harkokinsa tun da zuwa lokacin ya tabbatar yana nan a namijinsa, sai ya cigaba da zuwa wajen ƴan mata yau wajen waccan gobe wajen waccan. Wataranar litinin tana zaune tana shafawz Humaira fara powder a wuyanta bayan ta gama mata wankan yamma, saboda ƙurajen gumi da suka fito mata. Ya zo falon ya zauna a kan kujera ya wani kame tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ramla ta kalle shi ta ga fuskarsa babu yabo babu fallasa ta ɗauke kai ta ci gaba da abin da take ya ce "Ramla inaso za mu yi magana" Ta ce ina jinka" Ya ce "Kuɗin aikin na da na magunguna da jigilar zuwa asibiti da kika yi da ni bashi ne ko kyauta?" Tambayar ta zo mata a bazata, musamman kuma yanayin da ya yi furucin cikin wani gadara-gadara amma da ta tuna don Allah ta yi sai ta ce ""Kyauta" Ya ce "Ok" Ya faɗa tare da ɗan yin jim, ya cigaba da faɗin "Tun da wancan kyauta ne ba bashi ba, daman kuɗi nake so ki ranta min to don kar ki ga ban biya wancan ba na ce ki aramin wani shi ya sa nake nannagawa" Ta ɗora Humaira a kafaɗa ta ce "Aron kuɗi kuma? Wane kuɗin? Kuɗin da nake juyawa ina siya mana abinci da hidindimun gida? Kana ganin inaso in koɓa makaranta ma ya gagara saboda na rasa wancan samester a zaman jinyarka ka rashin kuɗin abin hawa ga ƙaramin goyo ga dai abubuwa barkatai, shi kuma kuɗin da na siyar da sarƙar daman gadon Babanmu ne da aka raba mana dubu ɗari biyu ne ya yi saura shi kuma wani abu nake so na siya na ajiye nake gani" A zuciyarsa ya ce '!Babu wani abu da za ki saya, wato don ki yi arziƙo ko ki ajiye wani abu da za ki fini ki xo nan gaba kina rainani' A fili ya sassauta murya ya ce "Ramla ba sai kina min gori ba na san ke kike ɗawainiyar gidan nan, shi ya sa nima da na ga rashin jari ne da bani da shi na ce bari na nemi ki aramin in samu wata sana,ar na yi, kin ga sai na karɓi ɗawainiyar da kike wacce daman ni ya dace na yi duk da ba laifi bane idan mace tana taimakawa a gidan miji, da kaɗan-kaɗan in na samu sai na mayar miki" Ta yi shiru tana nazarin maganarsa, amma ba za ta iya hana shi ba, sai ta ce masa ya bata zuwa dare. Da ya fita ta kira mahaifiyarta ta zayyane mata ta ce "Ramla amma mijin nan naki yana neman wuce gona da iri, yanzu duk hidimar da kika yi da shi da kuɗim gadon mahaifinki da kika sayar bai gode ba ɗan sauran wanda ya rage mikin ma sai ya biyo ya karɓe, anya wannan yana da tausayi da imani Ramla, yanxu kuma tun da ya san da kuɗin idan aka hana shi cibi ya zama ƙari" Ramla ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Nima dai abin ya ban mamaki, amma ba komai zan bashi da zuciya ɗaya, duk da gani nake ba lallai ya biyani ba wallahi kuma idan na hana shi mu ringa faɗa kenan" Mahaifiyarta ta ce "Tun da dai ya ce ɗawainiyar zai ke ɗauka ki bashi, kin ga idan ɗawainiyar ta bar wuyanki daman saboda rashin aikin yi da sana,a ne da ya rasa aikin gwanati in ya so abin da za kike samu na sana,a sai kike tarawa aki samu wani abin ki ajiye ba tare da ya sani ba" Da wannan suka yi sallama, da ya dawo ta ɗakko kuɗin ta bashi ya lissafa ya ce "Allah bani ikon biya!!!" Book 1 zai ƙare a page 35 in sha Allah, wanda yake da buƙatar cigaban labarin har ƙarshe zai iya biya. Ban son surutu kuma😒 MAMAN AFRAH ***
[9/2, 6:49 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH