KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿3️⃣1️⃣

*HAJIYA HAUWA*

Tana juyawa da ta yi hanyar ɓangarenta itama Nuriyya ta juya ta bi hanyar fita daga gidan ta buɗe get ta fice don gabaɗaya hankalinta yana ga tafiya makaranta.

Hajiya Hauwa a kiɗime har tana neman faɗuwa ta ƙarasa katafaren falon nata, tana shiga da ƙaran kiran wayarta ta ci karo, wani uban tsaki ta ja saboda yanxu haushin komai take ji duba da yadda ranta yake a ɓace ta sanadiyyar cigaban Nuriyya da ta ce mata za ta fara karatu. Ta lura ma yarinyar kamar bata cikin ƙunci, tana walwala haɗe da samun komai kamar wanda masu iyaye a raye kuma ƴan gata suke samu .

Tana zuwa da ta ɗakko wayar sai ta ga ashe faɗuwa ce ta zo daidai da zama, domin kuwa wacce ta taho da niyyar kira ce ta kira ta wato ƙawarta Hajiya Mardiyya. Ɗagawa ta yj ta kai wayar kunnenta har lokacin ranta gabaɗaya babu daɗi tun kafin ta furta wata kalma Hajiya Mardiyya cike da zaƙuwa muryarta tana nuni da tana cikin farinciki ta ce

"Ƙawata ina kika shiga ne, wannan shi ne kira karo da huɗu da na miki missed call, abin nema ya samu za mu takali arziƙi kashi da ƙafafunmu" Ƙaramin tsaki ta ja ta ce

"Dan Allah kar ki ɓata min rai Hajiya Mardiyya daman raina gabaɗaya a ɓace yake, wane irin arziƙi kuma mu da muka yi hannun riga da talauci, ai ina ga muma za a saka mu layin masu arziƙi ko da bamu zo a sahun farko ba, don na san ba za a saka mu a layin talakawa masu ƙarnin talauci" Hajiya Mardiyya ta ce

"Hahahaha, Hajiya Hauwa kenan, akwai arziƙi, akwai muna arziƙi domin kuwa idan wani me arziƙin ya zo wuri talaka fitik zai kiramu" Tsaki Hajiya Hauwa ta yj ta ce

"Sai surutu kike marar kai da ƙafa, baki san damuwata ba wallahi ina cikin matsalaa, ni dai na lura wannan yarinya Nuriyya ita ce ajalin farincikina a kullum, tun da sai ina cikin farinciki da walwala ta zo da abin da zai baƙanta zuciyata"

Hajiya Mardiyya ta ce

"To fa! Daman ai na faɗa miki barin yarinyar nan tana mu,amala da wannan shegen yaron Gaddafi yake ko wa? Wannan yaron dai da tsohuwarsa da kika ce suna taimaka mata, ai na faɗa miki tamkar kin sare miciji ne baki cire masa kai ba, kin ga kuwa ai kin yj ta banza domin ba lallai ya mutu ba saboda barin miciji da kai haɗari ne babba!"

Hajiya Hauwa ta ce

"Ni fa komai ya jagule ta yadda ban ma san abin yi ba, dama na taho da niyyar in kira ki mu samu mafita sai kuma na tarar kiran ki yana shigowa ashe yarinyar nan wannan tsinannan yaron ya tsaye mata har ya sama mata makarantar gaba da sakandire, ina nan zaune basho ina ganin fitar da take yawon barbaɗa take ashe dai tana neman ilimi"

Hajiya Mardiyya ta ce .

"To ai dagula lissafi ma kaɗan kika gani, ke ba kin dogara da cewar zai mata cikin shege ba ya lalata mata rayuwa haɗe da mata cikin shege ta tozarta ba ta yadda za ki saka uban ya kore ta, ta tafi can wata duniyar ta haife ɗan ta ƙare a wulaƙance, bayan kin san ke ko tsinke baki ajiye a gidam ba, to idan baki yi wasa ba bari na faɗa miki, ko na ce bari na maimaita miki abin da na sha faɗa miki a baya, wannan yarinyar kina nan zaune baki more ta ba, za ta taso ta mayar da ke abar tausayi!"

Gaban Hajiya Hauwa ga buga da ƙarfi, don kalaman Hajiya Mardiyya ya yi daidai da tunaninta na ganin Nuriyya ta samu karatu kuma idan ta samu tudun dafawa za ta zame mata ciwon ido, don har ta hango Nuriyyar ta zama cikin masu cin gajiyar karatunsu wato ta yi zurfin karatu ta samu aikin da za ta zama abar kwatance a duniya!".

Hajiya Hauwa ta ce

"Ni fa kaina ya kulle duk kin ƙara dagula mini lissafi, mene ne mafita, idan kuma kina ganin maganar ba za ta yiwu a waya ba to zan taso yanzun nan direba ya kawo ni, wallahi duk na ruɗe, kar in yi ba wan ba ƙanin, don wallahi na lura kamar yarinyar nan har yanxu ma a matsayin budurwa take bata kai ga sanin namiji ba, ina nufin babu shegen da ya lalata ta!"..

Hajiya Mardiyya ta ce

"Ƙawata ki bar wannan maganar na sama mana mafita guda ɗaya, mafitar da za ki yi alfahri da samota ɗin da na yi, domin kuwa na samo mana wata hanya ɗaya tak da Nuriyya za ta zame mana jari mau kauri kuma mai tsoka, domin kuwa lokaci ya yi da za ki yj alfahri da dukiya da arziƙin ki, saboda za ki mallaki kuɗaɗe ma masu sunan kuɗeɗe, ki yi alfahri da cewa ke ce mai kuɗi ba matar mai kuɗi ba"

Hajiya Hauwa ta ce

"Ban gane inda kika dosa ba fa ƙawata, kamar yaya, shin za mu fara siyar da naman mutane ne, kika samo mana inda za mu kai Nuriyyar mu sayar"

Hajiya Mardiyya ta ƙyalƙyale da wata mahaukaciyar dariya ta ce

"Ko kaɗan, babu wani siyar da naman mutum, abin da za mu yi ma in aka kalle shi ta wani fannin jihadi ne don kuwa haɗa sunnar ma,aiki ai ba ƙaramin lada bane!"

Hajiya Hauwa ta yo shiru ta kasa gane maganar ta ce

"Ki warware min biri har wutsiyarsa"

Hajiya Mardiyya ta ce

"Wani hamshaƙin mai kuɗi ne ya ga Nuriyya ya zo min da maganar yana son ya aure ta, saboda an faɗa masa cewar ni da ke tif da taya muke wato ƙawayen juna"

Gaban Hajiya Hauwa ya buga da wani irin mugun ƙarfi, bata san lokacin da ta ce

"Hajiya Mardiyya kina cikin hayyacinki kuwa? Ni kike faɗawa kin samowa Nuriyya mijin aure, yarinyar da nake son ta tambaɗe ta lalace, ita ce zan bari ta yi aure, auren ma a gidan naira ba a gidan talauci inda rayuwarta za ta shiga gagari ba"

Hajiya Mariyya ta ce

"Daɗina da ke wutar ciki, sannan bakya cin ribar zance, idan ana yi wa mutum bayani ba ya yanke shawara kai tsaya, yana fuskantar maganar da ake faɗa masa ne da idon basira, sannan ya nazarci kalaman, kafin ya yanke hukunci"

Hajiya Hauwa ta ce

"Ai maganar nan bata buƙatar nazari ko fahimta, saboda komai a bayyane yake"

Hajiya Mardiyya ta ce

"Auren ne za ki mata auren jari, ke za ki samu manyan kuɗaɗe, sannan za ko jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya! Na farko kin aurawa mai kuɗi ita wanda ke za a ba kuɗin haɗakar auren da kika yi, abu na biyu ita kanta yarinyar za ki yj amfani da ita idan ta shiga gidan ki cigaba da mallakar kuɗaɗe masu nauyi, sannan kuma bugu da ƙari kin baƙanta ran yarinyar tun da na farko kin hana ta karatun da take da burin zama, na biyu kin mata auren dole kin raba ta da masoyinta don wannan yarinyar ko makaho ya shafa ya san suna ƙaunar junansu da wannan yaron, saboda ta taso tun tana ƙarama da kulawarsa, shi ne ya tsaye mata ya zame mata komai a rayuwa saboda an halicci zuciya bisa son mai kyautata mata!Sannan uwa uba a ƙarshe wanda kika aura msta idan ta gama cin moriyar ganga zai yi wo waje da ita, a sannan gatan ta ya ƙare shi yaron da yake kwaɗayin auren budurcinta za ta fice masa a rai wataƙila ma ya yi zaton auren cin amana ta yi da me arziƙi ta bar shi"

Hajiya Hauwa ta yi shiru ta ce

"Maganar nan tana kan hanya amma dai gani nan zuwa gidanki, mu ƙarasa" Bata jira cewar Hajiya Mardiyya ba ƙit ta kashe wayar.

Mayafi ta ɗakko da jaka ta saka takalmi ta fito tana ba ƴan aikin gjdan nata umarnin a kula da gidan ta je ta dawo. Tana fitowa harabar gidan direba ya ɗauko mota aka wangale musu get suka fice.

Tana zuwa gidan Hajiya Mardiyya ta same ta zaune a falo da lemo a gabanta a kofin glass tana kurɓa hannunta ɗaya riƙe da remote tana kallo. Tana shigowa ta ajiye kofin lemo da remote ɗin suka zauna kuda da juna.

Hajiya Hauwa ta ce

"Babu wani dogon zance ɗora daga inda kika tsaya min a waya, don ni gabaɗaya yanxu ba komai nake ganewa ba, ki fito da ni hanyar ɗoɗar!"

Hajiya Mardiya ta kwashe da dariya ta ce

"Ƙawata baki da dama, ga azarɓaɓi"

Hajiya Hauwa ta mata hararar wasa.

Hajiya Mardiyya ta daina dariya ta sauya fuskarta zuwa alamu na maganar da babu wasa a cikinta ta ce

"Kin san Alhaji Ahmad Jarma mai dollar? Hajiya Hauwa ta ɗan ƙanƙance ido ɗaya tana kallon Hajiya Mardiyya ta ce

"Kina da matsala, ina maganar da za ta fishsheni kina min wata magana mai ya haɗa ni da wannan mutumin, kuma in sani ne waye zai ce bai san Alhaji Ahmad Jarma ba, baban siyasar da yake kula da harkokin kwangilar titu, gadoji, makarantu da sauransu," Hajiya Mardiyya ta kalle ta ta ce

"Alhaji Ahmad Jarma ya ga Nuriyya kwanaki uku da suka shuɗe, a ƙogar gida ta fito shi kuma an zo wucewa da shi a mota, lokacin da ta fito sai ta tsaya daga bakin kwaltar tana jiran gwanon motocin da suke wucewa, a sannan ya ganta ya ji ta kwanta masa, ko da ya sa aka masa bincike aka gano cewar ke ce mahaifiyarta kuma ke ɗin ƙawata ce, ni kuma bazawarina shi ne yardajjen direban abokinsa, shi ne fa uban gidan bazawarin nawa ya sa aka tambaye shi ke take yanke ma gidan hutawarsa suka sa aka kaini jiya suka min tambayoyi a kan Nuriyya na faɗa musu gaskiya cewa ƴar mijinki ce, abin da ma ya san ban faɗa miki ba lokacin da na dawo da daren duk bakinciki da takaici ya cika ni a kan cewar yarinyar nan me kudi ya ganta yana so, to kawai yanzu ina zaune sai ga kiran Alhaji Ahmad ɗin daman ya karɓi lambata yake sanar da ni idan har zai samu yarinyar nan a aura masa zai baki miliyan ɗari!" Jikin Hajiya ya hau karkarwa ta ce

"Miliyan ɗari fa kika ce?" Ta faɗa tana zare ido kamar an kama kwarto a ɗakin matar aure, ta ce

"Yadda kika ji haka na ce, wallahi miliyan ɗari ni da farko ma na dauka dubu ɗari ya ce sai da ya maimaita na gane shi ne muna gama wayar da shi na shiga kwaɗawa wayarki kira tun da na lura mu ne da riba, abin da ya sa ma ya biyo ta hannuna saboda mai binciken ya ce masa maganarki mahaifinta yake ji, idan aka biyo ta hannunki tamkar an samu auren Nuriyya ne"

Hajiya Hauwa har tana in,inna ta ce

"Kuttt to Allah na tuba ko siyar masa Nuriyya ya ce in yi zai yanke mata kai ya ban miliyan ɗari ai zan bashi ita, bare kuma aure, ai wallahi kamar ya auri shegiyar yarinyar nan"

Hajiya Mardiyya ta ce

"To kin ji dai arziƙin da ya tunkaromu"

Hajiya Hauwa ta ce

"Wa zai yi wa arziƙi dundu, ni wallahi gabaɗaya ma kin wanke min ɓacin ran cikin zuciyata tasss da wannan kalaman naki masu daɗi da ɗanɗano kamar zuma"

Hajiya Mardiyya ta ce

"Hummm mganar kuɗi fa ƙawata, kuɗin ma miliyan ɗari, sannnn uwa uba idan ta shiga gidan muke samun salala"

Hajiya Hauwa ta ce

"Ai wallahi kamar Nuriyya ta aure shi ta gama, don babu abin da zai hana auren nan, ke ko gawarta sai an kai gidan nan, daman shi wannan sha ka tafin uban nata da sai yadda aka yj da shi, ai ina bashi shawara shikenan kuma sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci!".

Suka taf a suna ƙyalƙyalewa da dariya Hajiya Mardiyya ta ce

"Baki da dama ƙawata"

A ɓangaren Nuriyya tun da ta fito daga gida, gidan Kaka ta fara zuwa ta ci abinci a gaggauce saboda ƙawarta Hafsa tana ta mata waya a kan malami ya shiga lacture. Kuɗin makaranta Kaka ta bata saboda Ammar iya kuɗin abin hawa ya bata. Ko da ta tafi ranta fari tass. Ko da ta je ta ji daɗin yadda ake koya musu karatu kuma tana fahimta sosai, tana ganin burinta yana dab da cika saboda za ta yi karatu kamar yadda take so.

Sai daj a gefe ɗaya tana ta tuna Ya Ammar ɗinta saboda yanayin da ya shiga na sadaukarwar da ya yj mata ta dalilin haka gashi ya tsinci kansa a wani hali.

Da suka tashi sun rabu da Hafsat inda ita kuma ta nufi gidan Kaka, da sallama ta shiga gidan Kaka da take sharar yamma ta amsa mata don lokacin kusan biyar da rabi. Kaka ta miƙe tsaye daga sunkuyan da take ta ce

"Lale da ƴan makaranta, sannu da zuwa" Tana dariya ta ajiye jakarta a kan tabarma tana faɗin

"Yawwa Kakata ni da Ya Ammar" !Kaka ta yi dariya tana faɗin.

"Da alama da ɗan ƙarfinki yunwa bata kama ki ba shi ya sa har bakin ki bai mutu ba"

Ta ce

"Ai in faɗa miki Kaka bana jin yunwa na yi biskit da lemo" Suna ta zantawa har Kaka ta kashe sharar. Ita kuma da ta ɗab huta ta shiga ta yi wanka ta fito ta saka wasu kayan ta linke wancan ɗin da yake akwai kayanta a gidan.

Tuwon da Kaka ta bari yana dahuwa ta kwashe ta haɗa kauan miya ta ɗora miyar. Tana fifita wutar Ammar ya shigo bayaj ya yi sallama ama amsa masa, ya xauna yana faɗin

"Wash Allahna" Ya faɗa yana zama a kan tabarma.

Nuriyya ji ta yi tausayinsa ya kama ta, don babu ko leda a hannunsa baya ta san matuƙar ya fita sai ya siyo wani abun amfanin gidan amma yanzu duk abubuwa sun caɓe.

Ya ce

"Nury ƴan makaranta an dawo, zo ki bani labarin makarantar" ,Ta zo ta zauna a kusa da shi Kaka tana ta musu tsiya ya ce

",To me aka koya miki? Makarantar tana da daɗi ko bata da shi" Ta yi shiru kamar mai tunani ta ce

"Ya Ammar ai daɗin ma har ya yi yawa"

Kaka ta ce

"Wannan uwar ƴan son karatun ce za ta ce maka makaranta babu daɗi" Su duka suka saka dariya, tashi ta yi ta ɗakko masa abincinsa ta haɗo da ruwa, ta kawo masa ya ce ta buɗe kwanon ta buɗe dambun masa ne da ya sha zogale duk da bashi da yawa amma yana yin loma ɗaya ya ji daɗin dambun domin ya yi laushi sosai. Yana lumshe ido ya ce.

"Nuryra kin iya girki ƙwarai" Nuriyya ta tuntsure da dariya saboda ta san Kaka yake tsokana.

Kaka ta ce

"Au Allah, wato Nury ta iya girki za ka gani kuwa yanzu sai dai idan Nuryn ta fama tuwo ta zuba maka" Ta faɗa tana miƙa hannu za ta ɗauke kwanon abincin, daga Ammar har Nury da sauri suka danne kwanon a tare suna ƙyalƙyala dariya.

Kaka ta ce

"Da kun saka yau da kun fa tsiya don da ɗaukewa zan yi in ci kayana ko in ba almajiri, haka kaaai ban da shegantaka in dafa dambun tana can a makaranta ka ce wai ta iya dambu" Ta faɗa tana dariyar itama.

Yana gama cin abincin ya je ya yi wanka ya fito lokacin Nury tana kaɗa miyar tuwon da aka gama.

Ɗakinsa ya je ya shirya ya fito ya dawo ya zauna yana faɗin

"Kaka lamarin kasuwar nan fa ya rikice sai a hankali duk abin da zan kasa na kasuwancin sai in ga ba ya tafiya ko dai akwai abin da na yi wa ubangiji..."

Kaka ta katse shi da faɗin

"Kar in ƙara jin furucin nan a bakin ka jarabawa ce"

Ammar ya ce "To shikenan in sha Allan Kaka, ga wannan cinikin ne " Ya faɗa yana zaro ɗari shidaya miƙa mata yana faɗin

"Wallahi ba ciniki shi ya sa ko abincin ban auno ba, sai dai a sayi garin kwaki "

Kaka ta ce

"To ba damuwa Ammar kana ƙoƙari ma, rashin ciniki kuma jarabawa ce"

Nury ta ce.

"Allah ya kawo maka kasuwa Ya Ammar"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Amin Nury"

Ana kiran sallar magriba ya yi alwala ya tafi masallaci, Nury da Kaka ma suka yi tasu.

*** [9/5, 7:22 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH