BOOK 1
🅿3️⃣3️⃣
*RAMLA*
Kwanci tashi asarar mai rai, da sabbu suka warke sumul kamar ba a yi ba, komai ya dawo yake tafiya yadda ya kamata a wannan lokacin ne Ramla za taiya bugar ƙirji ta faɗi yadda Abdulsalam ya san darajarta, don bayan ta ɗauki ƙodarta ta bashi ganin ya cire rai daga rayuwa amma ta ceto shi wannan ta sa ya sassauta mata yake ɗan ganin girmanta, sannan lokacin da ya warke sai yake kulawar da sana,ar ɗinkin takalman yana ɗan samun wani abu yana kawowa a ƙalla dai ko da bai ɗauki ɗawainiyar gidan gabaɗaya ba ya rage mata wasu abubuwan ba kamar yadda a da ya dakar mata ragamar riƙon gidan ba.
Ba kowane ya ja hankalinsa ga hakan ba sai Zahraddin da ya sha jaddada masa cewar a duniya Ramla ta masa abin da kowace mace ce za ta yi wa namiji ba tun da har ta sadaukar da rayuwarta ta iya raba ƙodarta guda biyu ta ɗau ɗaya ta bashi ɗaya, wannan kaɗai ya isa ya nuna masa cewar ba ƙaramun muhimmanci yake da shi ba a rayuwarta.
Wannan kawo kayan abinci da yake sai ya zamana iya cefane kaɗai take yi, da yake kuma Allah ya dafa mata a kan sana,ar tata tana samun ciniki sai ya zamana tana yin ɗinki da yi wa Humaira, sannan a cikin ɗan abin da take samu take yi wa ƙannenta su Amal alheri, tun da shi alheri ba ya kaɗan ba ya yawa. Wannan dalilin ne ya sa sai suka fi Zahraddin rufin asiri tun da lokacin Hasiya ƴaƴanta biyu, tun da lokacin Nasira tana da shekara huɗu Zainab tana da shekara biyu.
Ganin tsananin talauci da su Hasiya suke ciki wani lokacin abincin da za su ci ma gagararsu yake yi, amma Abdulsalam ba ya taimakawa Zahraddin ɗin, iya kuma tana jin nauyi da kunyar ganin yana ɗan uwansa amma yana buƙatar taimako ba ya taimaka masa, sai ya ce ai shi ma nawa samun nasa suke, ai wanda yake da mugun kuɗi a ganinsa shi ne yake taimakawa ba wai wanda yake cikin halin fafutukar rufawa kansa asiri ba. Ita kuma ganin kasuwar Zaharaddin ɗin ta yi ƙasa ba ya samun cinikin takalman tun da Hasiya wani lokacin tana koka mata tun da suna mu,amala sosai. Wataran ma da kanta idan t aje gidan za ta tarar da yaran suna kukan yunwa amma babu abinci. Hakan ya sa take ba Hasiya wasu ƴan kuɗaɗe ta ce ta auna musu garin kwaki da garin tuwo, wani lokacin ma ita take aikawa a auno mata masara ta yi ɓarjen dambu ta kai musu, Zahraddin ya yi ta mata godiya don ya dan Ramla mutum ce ba ta jefarwa ba.
Haka cikin sabulun wanka da klin ɗin da take siyarwa haka take bata don su yi wanki, sannan idan ta ga tana da hali tana siyawa su Nasira kayan gwanjo wani lokacin har ɗinkin ƙaramar atamfa tana musu.
Lokacin da ta samu cikin Aslam da Aslamiyya a lokacin da cikin ya isa haihuwa Abdulsalam ya ƙeƙashe ƙasa ya ce bashi da kuɗin abin yanka, sai kayan gadonta ta siyar ta siya musu abin yanka ta yi hidimar suna da sauran. Ya zamana ɗakinta sai katifa, a sannan ne kuma ya fito da wani sabon salon rashin mutuncin, wato ya koma falo da kwana a kan kujera a cewarsa wai tun da babu gado a ɗakin shi bai ga amfanin kwana a katifa ba, ai kowace mace a ɗakinta akwai gado sai ita ce za ta ɗauke gado ta siyar saboda ta fita kunyar mutane wato ta yankawa ƴaƴanta rago, ai shi bai ce ba zai musu ba ya dai ce a bari sai lokacin da ya samu kuɗi zai musu daga baya.
Abin ya mata ciwo saboda shi bai ma ga ƙoƙarin da ta yi, domin ta san matsawar aka yi sunan nan bai yankawa yaran abin yanka ba to ba lallai ya musu yanka ba, don duk wani tattali da mutuntawa da ya tsiro da shi bayan masa dashen ƙoda daga baya watsarwa ya yi, sai dai ba kamar da ba. Ganin haka ya fita harkarsa saboda ta lura ita ce kawai ba ya so ya kusanci inda takr, sannan uwa uba renon yaran nan ƴan biyu da take yi, ba ya so ya taya ta wataran ma idan suna kukan da dare sai ya ce laifinta ne ta ƙi saka musu nono a baki su yi shiru saboda kawai tana baƙincikin baccin da yake.
Haka rayuwa ta ci gaba da gurgurawa yau fari gobe akasin haka. Kwasam wani babban kamfani ya fitar da sanarwar neman ma,aikata, kamfanin wani baban abokin Zahraddin. Ba a san ma da wannan maganar ba, sai da abokin Zahraddin watarana sun haɗu da shi ganin abokin nashi cikin baƙin talauci ya ce ya kawo takardunsa, akwai kamfanin mahaifinsa da za a ɗauki ma,aikata duk da shi abokin Zahraddin ɗin ba a Nigeri,a yake da zama ba. Zahraddin ya yi matuƙar farinciki sai dai ya ji babu daɗi ganin zai samu aiki Abdulsalam bai samu ba, kuma ya san Abdulsalam ya ci buri a kan samun aikin gwamnati.
Zahraddin ya tuntuɓi abokinsa a kan cewar za su kawo takardun shi da ɗan uwansa, ya nemi amincewarsa ya ce masa babu damuwa su kawo, cike da farinciki ya je ya samu Abdulsalam ya sanar da shi, saboda tsabar murna Abdulsalam ya rungume Zahraddin yana ta saka masa albarka, saboda har ya fara hango yadda zai rabu da talauci ya shiga cikin ni,imar arziƙi!.
Zahraddin har ya fi shi jin daɗin walwalar da ya ga yana yi, haka ya haɗu takardunsa da aka buƙata ya kaiwa Zahraddin gidansa, gidan da har ya manta rabon da ya saka ƙafarsa a ciki, daman idan har ya je so yake ya ga Hasiya ya ɗan samu sawaba a zuciyarsa, sai dai a duk lokacin da ya je ya ganta yana tsintar kansa cikin tsantsar tsanar Zahraddin ganin shi ya raba shi da wacce yake so da ƙauna.
Ramla da ya faɗa mata sosai ta ji farinciki har kiran Zahraddin ta yi ta masa godiya.
Zahraddin yana kaiwa abokinsa takardun, washe gari ya bar ƙasar bayan ya damƙa takardun a inda suka dace!.
Bayan wani lokacin an ɗauki ƴan aikin, amma sunan su Zahraddin bai fito ba, bayan ya yi masa waya ya sanar da shi cewa sunansu bai fito cikin wanda aka ɗauka ba, ya ce kar ya damu zai san yadda za a yi, a takr bayan sun gama magana da Zahraddin ya kira mahaifinsa ya nemi alfarmar a dauke su, sai dai mahaifinsa ya sanar da shi cewa basu da gurbin ɗaukan mutum biyu sai dai mutum ɗaya, don haka ya kira Zahraddin ya sanar da shi abin da mahaifinsa ya faɗa masa, Zahraddin ya yi shiru yana nazarin maganar amma idan ya tuno yadda ya saka farinciki a zuciyar Abdulsalam da yadda Ramla ma ta shiga farunciki har take masa godiya da sanya albarka, sai ya ji ba zai iya cewa a ɗauke shi a bar Abdulsalam ba!.
Cike da yaƙini ya sanar da abokinsa cewar, shi fa ɗazu aka kira shi a waya, sunansa ya fito a wani aiki da ya nema da daɗewa, don haka ya saka sunan Abdulsalam, haka abokin ya amsa masa ba tare da ya fahimci kawai ya sadaukar da aikin ne ga ɗan uwan da ba ya taimakonsa ba. Shi kuma ganin yana son faranta masa rai saboda irin halaccin da Zahraddin ya masa lokacin suna makaranta duk da ba aji ɗaya suke ba, amma saboda yana taimaka masa wataran ya raba kuɗin makarantarsa ya bashi, wataran su ci abincinsa tare hatta littafi Zahraddin ya sha bashi sabo wanda bai yi rubutu a ciki ba ya soke sunansa ya ce ya karɓa ya saka nashi, kasancewar mahaifinsa lokacin yana talaka kuma mahaifiyarsa bata gidan, a lokacin suna primary sun kusa kammalawa ma.
A take abokin ya kira mahaifinsa ya bada sunan Abdulsalam.
Bayan sati biyu aka nemi Abdusalam daga kamfani a inda ya fara ƙafafa tare da jin kansa wani ganin an ce shi kaɗai aka ɗauka. Lokacin da suka haɗu da Zahraddin ya faɗawa Zahraddin an kira shi a waya, Zahraddin ya masa fatan alheri buɗar bakin Abdulsalam ya ce
"Shi rabo rawani ne, rabonka ko gudu kake samunka yake, ka ga dai yadda gabaɗaya takardunka suka fi nawa kyau amma da yake ina da rabo gashi an ɗaukeni ba a ɗauke ka ba" Ya faɗa yana ƴar dariya" Zahraddin ya ji babu daɗi a ransa jin lafazin da ya masa da kuma dariyar da ya yi kamar hakan yana nuna dariyar sheƙiyanci ce, ya san ya sadaukar masa da gurbin aikin ne don Allah hakan ya sa ko faɗa masa bai yi.
Tun daga lokacin da ya samu aikin nan aka bashi matsayi kuɗaɗe suke shigo masa daga wannan lokacin ne komai ya canja, idan na ce komai ina nufin komai. Sannu a hankali har ya yi gidan kansa, ya saka yaransa a makarantar kuɗi, ya zo daga baya ya sayi mota. Rayuwa tana tafiya yana sake samun buɗi, ya manta komai na halaccin Ramla bare kuma ya gane cewa ta dalilin Zahraddin ya samu aikin, duk da ma bai san cewa shi ya haƙura ya bashi gurbin ba.
Sai dai Ramla ta taimaka musu, amma shi halin ko in kula take nunawa musamman ma yadda yake yi wa Zahraddin Ramla har kunya take ji. Shi kuma Abdulsalam bai damu ba duk da wani lokacin yana zuwa da buƙata idan ya takura amma Abdulsalam zai ce shi bashi da kuɗi, ya sha zuwa neman kuɗi wurinsa ko da rance ne amma ya ce babu, sannan idan ya ji tana kewar ganin Ramla haka zai je ya ganta ya mata kyauta mai tsoka amma ba zai iya ba Zahraddin ɗin ba, shi ma Zahraddin idan ya ga ya bata kuɗin ba ya jin komai domin yana ganin saboda shi ne aka yi. Itama idan a gaban idanunsa ne aka bata tana tsakura wani abun ta bashi ko ta sayi abin amfanin gida, amma idan a bayan idanunsa ne sai ta murƙushe kuɗin ba tare da ya sani ba.
A haka har ta kai ga ya ɗauki lambar ta a wayar matarsa ya ajiye a wayarsa amma bai taɓa kiranta ba.
A wata rana ne daga zazzaɓi Zahraddin ya zarce matsananciyar jinya a inda tun ana magani a gida har aka kwashe shi aka kai asibiti. Duk yawan ziryar da abokan arziƙi suke amma sai a kwana uku Zahraddin bai je asibiti ba sai dai Ramla ta je. Sannn sai dai ita ta kai musu kuɗin na daga sana,ar da take yi don bata daina sana,a ba ko da suka samu buɗin daman shi ba mai bayar da kuɗi bane ita kuma bata damu ba tun da tana neman na kanta, sannan da kuɗu da ta biya ta koyi snacks kala kala da birthday cake da sauransu, ya zamana tana samun oder da kuma masu taimaka mata idan an yi oder snacks na biki ko suna ko wata hidima.
Lokacin da aka ambaci wasu kuɗaɗe masu nauyi a kan lamarin jinyar Zahraddin amma Abdulsalam ya murɗe kunnensa ya ce, a mayar da shi gida a masa maganin hausa shi ba shi da kuɗi!.
Ba a daɗe ba da wannan maganar rai ya yi halinsa wato Zahraddin ya mutu.
Ramla tana ta taraddadi a zuciyarta na cewar anya za ta samu namijin da zai zauna da ita ya yi haƙuri ya juri halayyarta kamar Zahraddin? Tana wannan tunanin a ranta tun da ya mutu don ta san ta yi rashin miji mai tausayi haƙuri kawar da kai da sauransu, a wannan gaɓar ne Abdulsalam ya shigo rayuwarta da maganar aure don bata san irin daɗewa da soyayyarta ta yi a zuciyarsa ba shekaru goma sha, yana dakon soyayyarta.
*DAWOWA DAGA LABARI*
*RAMLA*
Ta dade tana kukan da ta kasa tsayar da shi, Asma'u tana jin yadda kukan yake dukan dodon kunneta da tsakiyar zuciyarta, ta san ba ƙaramin abu bane zai sanya ƙawar tata kuka haka tun da ta san tana da jajircewa da juriya. Ta kasa dakatar da ita daga kukan itama ji take tamkar ta yi kukan idanunta sun kaɗa sun yi jawur sai kukan zuci take wanda ya fi na zahiri ciwo.
Har sai da Ramla ta tsagaita da kukan, cikin sanyin murya da lallashi ta ce
"Ramla ke ce kike kuka haka? Mai ya faru ? Mene ne wannan da ya karya jajaitacciyar zuciyarki har kika yi kuka wallahi na tsorata ki yi shiru ki yi haƙuri sannan ki nutsu ki faɗa min damuwarki" Ta faɗa tana dakatawa take saurarenta
Ramla ta ja iska, ta saka bayan hannunta ta share hawayen amma kafin ra cire hannun waninhawayen ya biyo hannun daga cikin idanun nata. Cike da jin wani irin rauni ta ce
"Asma...u na gani"
"Wane ne mai kika gani?" Asma'u ta tambaya cikin damuwa jikinta sai karkarwa yake.
Idanun ne suka ciko da hawaye ta fara ganin kayan falon nata dishi-dishi saboda yadda hawayen ya cika idanun ta ce
"Hoton... Abdulsalam da Hasiya"
Wani irin bugawa ƙirjin Asma,u ya yi, gabanta ya shiga faɗuwa babu ƙaƙƙautawa, cike da ƙunar rai ta ce
"Ramla, hoton Hasiya fa kika ce da Abdulsalam?" Ta tambaya cike da kokwanto, hoton mai yaushe a ina? Ta tambaya a ruɗe.
"Yanxu kawai. A status ɗin Hasiya. Suna rungume da juna Asma,u... yana mata kallon da ni bani da matsayi ko martabar ya mini" Tana faɗa sai a lokacin ne wani kukan ya sake ƙwace mata.
Cikin muryar kuka ta ce
"Asma,u hoton da na gani a ɗayan biyu take ko dai an ɗaura musu aure ko suna dab da zama ma,aurata!!!"
Asma,u ta ce
"Mutum mugun icce! Ɗan adam mai wuyar gane hali, lallai bahaushe ya yj gaskiya da ya ce kuɗi mai canja mutum! Duk da shi Abdulsalam can ma yana talaucin lamarinsa ba sauƙi ciwon arne! Amma dai wallahi Hasiya ta cika ƴar adam butulu mai manta alkairi ke ba ma ita kaɗai ba wallahi har shi Abdulsalam ɗin dukansu butulu ne masu manta baya!"
Ramla ta rasa bakin magana gabaɗaya kanta ya kulle ta rasa wane kalar tunani za ta yi, lamarin ya bata tsoro matuƙa!.
Asma,u ta ce
"Matar ban lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi, kuma ita lamba ɗaya ce a cikin masu cin amana ma, ta rasa mijin wa za ta aura sai mijinki shi ma ya rasa wa zai aura sai matar marigayin aboki kuma ɗan uwansa!"
Ramla ta ce
"Ni wallahi ban san sau nawa zan ce na tsani Hasiya da Abdulsa... Asma,u ta ce
"Karki ce haka Ramla ya za a yi ki ce kin tsane shi ko ba komai mijinki ne kuma uban ƴaƴanki"
Ramla ta ce
"Da ce wata ce zai aura ko ya aura ba zai dameni sosai ba amma wannn hoton da na gani abin ya taɓa mini zuciya sosai, kuma maganar wai uban ƴaƴana ne shi bai duba cewar ni uwar ƴaƴansa bace ko ya manta wace ce Ramla a gare shi?"
Asma,u ta ce
"Kam bala,i faɗa da aljani ba daɗi, ai sai na je har gidan uwarta na ci buhun tattasan uban ta shegiya mai fuska kamar an kwaɓa lalle"
Ramla ta ce
"Asma,u ki ƙyale ta kowa ya yi na gari kansa, kowa ya yi da kyau ya sani, idan dai gidan Abdulsalam ne gashi"
Asma,u ta yi shiru zuciyarta tana zafi tana tsananin jin ciwon cin amanar da aka yi wa ƙawarta bayan sadaukarwa jajircewar da ta yi na tsawon shekaru amma yanzu daga jin aljihunsa ya ɗauki nauyi sai ya ga gwara ya samu wacce za ta taya shi jin daɗin rayuwar kuɗaɗen da ya samu saɓanin wacce ta ci baƙar wahalar zama da shi tun yana faƙiri!. Asma,u ta numfasa ta ce
"Ramla"
Shiru ya tsara wayar sa da ta kira ta a karo na biyu sannan ta ce
"Na,am"
Asma,u ta ce
"Ramla inaso in roƙe ki alfarma, don Allah ki daure ki danne zuciyarki karki tunkari Abdulsalam da wannan maganar, idan har bai faɗa miki ba ki zuba masa ido kamar yadda ya zuba miki"
Ramla ta ƙanƙance ido tamkar Asma,u tana ganinta ta ce
"In yi shiru fa kika ce? In yi shiru in zuba ido, wato sun taka ni sun taka banza kenan? Saboda yana ganin ya shuka dusa da bata tsiro shi ya sa har yake shirin aure bai faɗa min ba auren ma na cin amana, sannan na yi imani da Allah Hasiya tana sane ya ɗora hoton nan a status don in gani, saboda ai tun tana da ƙaramar waya nake da number ta har ta yi babbar waya ban taɓa ganin tana ɗora status ba sai yau, sanann da ta ɗora in rasa wanda zan gani sai hoton ta da mijina? Ko kunyata bata ji ai a nawa ganin ana barin halal don kunya!"
Asma,u ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Ramla kenan har yau baki san waye mutum ba, mutum fa mugun icce ne babu mai iyawa ɗan adam sai ubangijin da ya halicce shi, sannan shi wani namijin ai abin kunya gaba ya bashi ba baya ba wani fa babu ruwansa indai zai samu abin da ransa yakr ƙulafucin samu to babu ruwansa ko da kuwa duniya za ta zage shi"
Ramla ta ce
"Haka ne amma har yanxu ina cike da mamakin abin da suka min, lallai sun zama ciki mai manta kyautar jiya, duk da cewar duk abin da na yi, na yi ne domin Allah, amma ban taɓa tunanin su duka biyun za su zama silar zubar hawayena wata rana ba"
Asma,u ta ce
"Ramla na tabbata Hasiya ta yi haka ne don ki gani ta cusa miki haushi, tana nan tana jiran sakamakon da zai biyo baya, don ta san kowace mace ce ta ga wannan abin da mijinta da kuma wacce ta ɗauke tsammani a kan za ta iya cin amanarta dole abin zai girgiza ta, kuma ba za ta taɓa yin shiru ba wataƙila a yi ta tafka bala,i to inaso ki daure ki mayar da komai ba komai ba wannan zai ƙara saka ta a tsananin tafkin mamaki ta kasa fitowa, shi ma karki nuna masa ko da wata alama ce ki ci gaba da sabgogin gabanki sannan ki dage da addu,a kamar yadda na sanki, in sha Allah ubangiji zai sassauta miki abin da kike ji a cikin zuciyarki!"
Ramla ta runtse ido hawaye suka kwaranyo, tana jin tamkar dai Asmau ta ɗora mata dutse ne a kanta saboda ta sanyata ta yi abu mai wahalar gaske amma dai ba za ta bata kunya ba, za ta ba marer ɗa kunya tabbas!.
Sun jima tana kwantar mata da hankali, tana ta buga mata musali da kanta, irin yadda namiji ya shallake tunaninta duk da ita bata wani yi masa sadaukarwa ko halacci ba, daga ƙarshe ta bata hakuri a kan rashin zuwa wajenta, ta faɗa mata dalilinta shi ne kar Abdulsalam ɗin ya fahimci wani abu hakan ya sa za su yi basaja.
Bayan sun gama waya Ramla ta tashi daga falon ta nufi ɗakin ta, gudun kar yara su dawo daga makaranta su same ta a wajen, tana dab da shiga ɗakin ta ɗaga kanta ta suke a kan tangamemen hoton yaran nata da aka ɗauke su suna dariya su duka cikin farinciki, daga gefe hoton Abbansu ne an sha wata fari yadi an saka hula, bata san lokacin da ta yi wani murmushi mai ciwo ba ta shige ɗakinta ta rufe gudun kar yara su dawo su same ta.
Tana shiga ta hau gado ta kwanta rana dafe kanta da hannu biyu jinw asu tunani da suka dabaibaye mata kwanya tamkar kanta zai rabe biyu.
A ɓangaren Hasiya lokacin da ta ga Ramla ta ga hoton ranta ya cika da farinciki tana ciki ta yi saurin faɗawa Karima ta ce
"Shegiyar gari ta ga hoton wallahi" Ta faɗa tans yin screen short ta turawa Karima, cike da farinciki Karima ta buɗe ta ga sunan Ramla a wanda suka ga status ɗin just now.
Da saurin ta sauka daga wtsappa ɗin ta kira Hasiya, Hasiyantana ɗagawa ta ce
"Kai ƙawata kin iya haɗa bom na bala,i na san yau wannan sai ta yi da gaske idan zuciyarta bata buga ba"
Hasiya ta sheƙe da dariya ta ce
"Ai kam sai ta yi da gaske don ko nice sai zuciyata ta kusa bugawa in ma bata buga ba"
Karima ta ce
"Idan tana da tsayawa a kan addu,a ba lallai ta samu buguwar zuciya ba kin san akwai mutanen da idan suka ga abin da ya tada musu hankali suke faɗin, innalillahi wa inna ilaihi raji,un, su ringa ambaton sunan Allah da duk addu,ar da ta zo bakinsu to yawanci wannan za ki ga ko tashin hankali ne yana zuwa musu da sauki kuma ba zai gigita su ba saboda sun mayar da lamarin ga Allah, akwai kuma wanda daga sun ga abin da ya ɗaga musu hankali sai kiran na shiga uku na lalace suke ta sambatu suna hauka har suke neman yin saɓo, to idan dai ta ambaci Allah abin zai zo da sauƙi a zuciyarta"
Hasiya ta ce
"Ko da ta tsallake wannan suraɗin to na san dai dole za ta tunkare shi da bala,i a kan zai mata kishiya kishiyar ma ni, to na san a nan gixo yake saƙa kuma tsiya za ta afku domin kuwa wataƙila shi ma ya harzuƙa a yi ta tafka bala,i marar yankewa"
Karima ta sheƙe da dariya tana faɗin
"Allah sa garin tirzawa ma ya rangaɗa mata saki ta fita ta baki sarari ki je ki baza mulkinki ke kaɗai a gidanki, daga ke sai ƴaƴanki, ita idan ta ga za ta tafi da ƴaƴanta to a ja a je an hana tsohuwa shiga mota, idan kuma za ta bar su ne sai ki sallami ƴan aikin gidan ki mayar da ƴaƴanta masu miki hidima"
Hasiya ta ce
"Ƙawata kin san ta kan tsiya, aikuwa da kina kusa sai na baki hannu mun tafa"
Karima ta ce
"Yanzu dai mu jira mu ga yadda ƙwallon da muka jefa a raga zai faɗo ƙasa ya ragargaje ne ko kuwa, ai mace da kissa da kisisina aka santa, ko auren kika yi ai cikin ruwan sanyi za kike gasa ta, idan ma Allah ya taimakake ki kafin ki je ta cikawa rigarta iska kin ga ta hutar da ke jiran zagayowar ranakun bakin girkin ki, ke kaɗai ce da miji" Suka ƙyalƙale da dariya a tare suka yi sallama da zummar idan har ta samu wani labari ta kira ta ta faɗa mata.
Tun da suka gama waya da Karima take jiran ganin kiran mutum biyu, na farko kiran Ramla don gani take Ramla ba za ta huce ba sai ta kira ta ta zazzage ta sun yj kaca-kaca saboda cin amanar da ta mata, kira na biyu kuma kinra gogan take jira, wato Abdulsalam don ta san muddin dai Ramla ta faɗa masa ta ga hoton sai ya tuntuɓe ta, shi ya sa ta gama tsara karyar da za ta masa.
Shiru -shiru tana jiran kiran Ramla amma bata kira ba, jim kaɗan ta buɗe data ta hau whatsapp ta duba amma ta ga ko uffan Ramlar bata ce mata ba. Kuma dai ta ga Ramla har sau biyu a online tana hawa tana sauka amma shiru ba amo ba labari.
Ko da ta faɗawa Karima halin da ake ciki, Karima ta ce
"Rabu da ita ba ƙaramar ƴar bariki ba ce tun da kika ga haka, wataƙila so take sai ta gama da shi za ta dawo kanki, tana can tana shaƙar baƙinciki kamar zai kashe ta, tana jiran dawowarsa gidan su kwashi ƴan kallo idan ta gama sai ta kira ki wataƙila ma waya ta muku kaɗan sai dai ta taho har gida ta same ki ta shuka miki rashin mutunci"
Hasiya ta ce
"Da kuwa ta ga ƙarshen rashin mutunci don wallahi rufe idanuna zan yi ba manta ma na santa tun da ai mijin nata ba don ita kaɗai aka yi shi ba.
A ɓangaren Abban Humaira bai san wainar da ake toyawa ba, haka ya dawo gida a ranar yana wani babboƙara irin shi ya isa ɗin nan.
Ita kuma Ramla abin da ya fi bata takaici ma sai yadda ya zage dantse ya karkace mazaunai ya sheƙa mata ƙarya game da maganar zoben nan, ashe dai duk abin munafurci ne, ya sa ta kira Hasiya a kan maganar da ta san haka ne da bata ma tunkare ta ba, yanxu tana ganin za take mata kallon an faɗi babu nauyi, ta san ma wataƙila sun yi maganar da Abban Humairar suna mata dariya sun mayar da ita mahaukaciya.
Lokacin da ya dawo gidan sai ta tsinci kanta da kasa zuwa ɓangarensa ta masa sannu da zuwa, bare har ta tuntuɓe shi ko akwai abin da yake buƙata a masa. Bata taɓa gane cewa a raine yake kallonta ba sai yau da ta gama gane da wacce yake tare, ta yi ta binsa ita a matsayinta na matarsa amma yana share ta yana mata wulakanci.
Ko da lokacin cin abinci ya yi sai da ta yi yaƙi da zuciyarta ta samu ta je saboda yaran kar su ga canju, sannan shi ma bata so ya fahimci wani abu bare ya zargi ko ta san da maganar yana tare da Hasiya. Duk da ta san ba lallai ya san Hasiyar ta ɗora hoton ya sani ba, kuma dai a ganinta ko da ya gani ba lallai ya ga laifin Hasiyar ba, saboda ba kasafai maza suke ganin laifin amaryar da za su aure ba saboda lallaɓa ta da ake yi.
Wannn karon sai da Aslam ya ce mata Abba bai fito ba sannan ta tashi tana faɗin bari ta dubo shi, ko da ta je ta ji yana magana kuma ta san dai zancen gizo ba ya wuce na koki ma,ana ba zai wuce da bazawararsa yake waya ba, haka ta ja ta saya ta ɗan ƙwanƙwasa har sai da ya yi na,am da ta shiga, a nashi ɓangaren lokacin da Hasiya yake waya, saboda munafurci tana tambayarsa ina yayarta, shi kuma ya ce tana lafiya, ta ɗauka zai faɗa mata wani abu saɓanin haka amma ta ji shiru bata san ma shi bai san wainar da ake toyawa ba.
Ta shiga da sallama tana kokarin danne abin da ya yunƙuro mata na ɓacin rai game da shi, sai ta ji ta kasa ɗaga idanh ta kalle shi ,don tana kallonsa gani dake hawaye ne za su wanke mata fuska din zuciyarta ce take son bayar da ita domin kuwa ta karaya matuƙa!.
Ta ɗan siranta muryarta haɗe da lanƙwashe harshe ta yi maganar cikin wani irin salo, ta ce
"Abinci ya kammala kai kaɗai muke jira!" Da sauri ya ɗago jin ta yi maganar a dake cikin halin ko in kula ba kamar da, da ya saba ta yi maganar cikin fadanci tana bin kansa tamkar a cikinta zai saka. Da sauri ya ɗago ya kalli fuskarta sai dai a mamakinta ba shi take kallo ba, ga shi yanayin yadda ta yi maganar kamar dai an ƙarawa muryarta zaƙin ɗanɗano ne.
Kafin ya bata amsa sai ra samu kanta da juyawa ta baro masa ɗakin, daman bata rufe ƙofar ba lokacin da ta shiga. Kansa ya samu da bin bayanta da kallo, ya ji kansa ya ɗaure da lamarinta ya fara tunanin ko dai ta fara hankalta da wulaƙancin da yake mata ne ta fara kama kanta? Babu mai amsa masa wannan tambayar domin bai taɓa tunanin wai ta ga hotonsa da Hasiya ba.
Haka ya fito daga ɗakin yana wasi-wasin cewar ko dai wayar da yake yj da Hasiya ta ji, sai dai ya shiga kokwanto saboda ya san ai ba yau ta saba kama shi da irin haka ba amma ta toshe kunnuwanta kamar bata ji ba ta rufe idanunta tamkar bata gani ba.
Haka ya taso ya fito ya ja kujera ya zauna ya ga suna ta raha abinsu ko da ta xuba masa abincin ta miƙa masa plate ɗin gabansa, yana ci yana ɗagowa yana kallonta amma sai ya ga kawai da ƴaƴanta take uzurinta ba wai ta share shi ko ta nuna masa wani abu ba kawai dai bata mayar da hankali kansa kamar yadda ya saba gani ba.
Yau ya kama saura kwana uku ɗaurin aure, ɓangaren amarya da ango ana ta shirye-shirye, ta je an mata gyaran kai an mata ƙunshi na gani na faɗa don wancan sai da ta dirje shi sisai ya fita sannan aka mata wani ita da Karima, Dada ma ta sha ƙunshin ta Nasira ce vata yi ba Zainab kuwa an yi mata Dada tana ta yj wa Nasira jarabar wai bakinciki take yi wa uwarta.
Ɓangaren Abba yau suka gama yanke hukunci shi da abokinsa Abdullahi a kan za a sanar da Ramla maganar bikin. Su biyu suka je gidan suka zauna a falon Abba lokacin yaran suna makaranta, ida dai Ramla bata san ma bikin ya matso haka ba.
Ko da ta shigo sanye take cikin dakakkiyar gezna, an mata aikin beadwrk sai sheƙi take ta sha ɗaurin ɗankwali kanta yane da mayafi da ya dace da shaddar. Da sallama ta shigo domin amsa kiran nashi, amsa mata suka yj a tare suna masu ɗago kai suka zuba mata ido. Karan farko da Abba ya ji ta masa kwarjini sannan yau tamkar an ƙara mata kyau duk da kasancewarta mau zama cikin gayu da kwalliya koyaushe.
Alhaji Abdullahi wanda daman kalar zaren kalar yadin shi da Abdusalam, don shi ma shegen kallon matan ne da shi, ji ya yi da shi ne da Ramla va lallai ya sake ƙara aure ba don ta haɗa komai da ake buƙata a jikin mace!
Ta zauna ta gaishe da Alhaji Abdullahi, ya amsa yana wani murmushi, da ya ganta sai ya ji kunya ta kama shi. Ta kallesu ta ga wata baƙar ledar Viva a gabansu a ajiye ita dai tana jiran ji daga bakinsu domin ta ga iya gudun ruwansu.
Abba ne ya saka hannu a aljihu ya ciro rafar ƴan ɗari biyar biyar dubu hamsin kenan, ya ɗora a kan ledar ya kalli abokin basa ya ce
"Abokina bismillah ka gabatar mata da abin da yake tafe da mu"
Saura page biyu mu gama book 1 mai bukatar book 2 shi ne har ƙarshen labarin zai biya 1k ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay, shaidar biya ta *** idan kin saka ki tura min shaidar biya kawai.
MAMANA AFRAH
*** [9/8, 6:32 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH