BOOK 1
🅿3️⃣4️⃣
*HAJIYA NAJA,ATU*
Ta yi farincikin jin Mom za ta kaisu wurin wani wanda zai mata aikin, haka Mom ta yi ta kwatantawa direban har suka iso fitowa suka yi suka bar direban a cikin motar suna fita a fili ya ce
"Allah sa duk inda kuka je kar ku dace, mararsa tsoron Allah kawai duk abin da za ku nema ba za ku nema a wajen Allah ba sai wajen wani " Ransa duk a ɓace.
Suna zuwa boka ya yi gyaran murya ya ce
"Ba sai kun faɗi komai ba na san mai yake tafe da ku kuma indai aure ne Alhaji sai dai ya ga ana yi amma shi dai ya gama aure a duniya, ke kaɗai ce shedu suka taɓa taruwa suka ɗaura muku aure, wannna e kuma auren da zai yi har abada ba zai sake wani ba" Wani irin murmushin murna da farinciki su Mom suka sakarwa juna ita da Hajiya Naja,atu.
Boka ya gama surƙullensa ya ɗakko wata ƙaramar ɗiya kamar ƴar tsana ya ɗakko wani ɗan tsanan amma mai suffar namiji, ya ɗakko allura ya cakawa kowanne a tsakiyar ciki ya ƙara ɗakko wasu alluran guda biyu ya caka musu a ƙafafun hagu ya miƙawa Hajiya Naja,atu ta karɓa hannunta yana karkarwa ya ce
"Wannab namijin shi ne mijinki wannan macen kuma ta haɗa kowacce mace ta duniya indai ba muharramarsa ba ce to ta haramta aure a gare shi don babu wani da zai taru ya haɗa musu aure" Wani shu,umin murmushi ne ya suɓucewa Hajiya Naja,atu ta ce
"Aikin ka yana kyau boka"
Boka ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya ya ce
"Indai aiki ne mu nan har kisan kai muna yi"
Mom ta ce
"Bar kisan kan nan boka, mu ma nan ba imanin garemu ba idan ta kowane fannin cimma burin duniya ne, sai dai wani lokacin idan ka kashe mutum ka ga ya huta tun da mutuwa ya yi mus idan kuma ka bar shi da ransa yana ganin takaici sannan yana ganin abin da ya fi ƙarfinsa ya gagare shi wannan kaɗai ya fi komai ciwo a rayuwa"
Boka ya jinjina kai alamar gamsuwa, Hajiya Naja ta ce
"Mom shi ya sa nake sonki, kuma nake alfahri da ke a matsayin uwa saboda bakya taɓa barina na yi ƙunci ko baƙinciki komai nake so sai burina ya cika, ni kuwa mai zan yi in ba ganin na faranta miki ba, ai hausawa ma cewa suka yi gaida mai gaisheka ko ba zai amsa ba"
Mom ta ce
"Ai ko a birnin sin ake samun biyan buƙatuwa sai na je nema miki Naja, ai kin fi ƙarfin wulakanci a gidan aure, in dai wulakanci ne ko kuma a miki wata aba kishiya to ki sani sai dai idan na kwanta dama, amma muddin ina numfashi sai dai ki ga ƴa mace kishiya a gidan wasu ba dai gidanki ba"
Boka ya ce
"Ai tun da kuka san wurin nan, kuma za kuke fitar da kuɗi yadda ya kamata to ni kuwa zan yi iya yina na biya muku buƙatu"
Hajiya ta ce
"Indai kuɗi suna maganin matsala, suna maganin baƙinciki da wulakanci to ni kuwa zan buɗe bakin jakata wayam na cika maka aljihu da su, in dai za ka yi aiki tuƙuru" Ta faɗa tana buɗe jaka ta ɗakko wasu kuɗaɗe masu nauyi ta ajiye a gaban boka don ko farashin kuɗin aikin da aka mata ba a faɗa mata ba kawai ta ɗauki kuɗin da take ganin sun dace ta biya aikin ta bada, kuma kuɗin sun amsa kuɗin don kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu a wajen boka saboda kusan kuɗin sun linka wanda yake shirin ambata idan an tambaye shi.
Sai da ya ɗauki kuɗin ya jefa cikin wata babbar kwarya wacce take ɗauki da manyan kuɗaɗen da yake samu idan an biya shi kuɗin aiki ya saka ya rufe da faifan ƙwaryar. Gyaran murya ya yi ya fara magana da faɗin
"Babu batun aure a kwana uku, sannan babu batun aure a har karshen rayuwarsa, kawai ki yi abin da na ce ki koma gefe ki zuba ido" Hajiya ta kalli Mom ita ma Mom ita ta kalla suka yi dariya mai bayyana hakora.
Boka ya ce
"Wannn mutum mutumin da na baki masu allurarnan, kar ki yarda wata allura ta fita daga inda na dasa ta, abin da za ki yi shi ne a talatainin dare ki je tsohuwar makabarta, ina nufin makabartar da aka daina binne mutane saboda ta cika, makabartar da wasu kaburburan ma tudunsu duk ya zagwanye saboda daɗewarsu" Gaban Hajiya Naja ne ya buga da mugun ƙarfi jin ta ambaci ta je tsohuwar maƙabarta, ita a tunaninta aikin iya nan zai tsaya ashe dai tsugunne bata ƙare ba!. Mom kuwa da farko ta ji tsoro amma daga baya da ta ji an ce Naja,atun ce za ta je sai ta ji dama-dama wai KIBIYA A IDO.
Boka ya cigaba da faɗin
"Ki tabbatar babu wani mahaluƙi da ya ganki a lokacin da za ki binne wannan abun, sannan idan kin je ki samu kabari wanda bai gama zagwanyewa ba wato yana da ɗan sauran tudu kaɗan, ki saka abu ki ƙwanƙwala ya yi rami yadda mutum mutumin zai shiga ciki, sai ki saka, idan kin saka kafin ki binne ki ɗura ashar masu maiƙo sau uku, sannan sai ki ambaci sunan mijinki sau bakwai, kina gama faɗar hakan sai ki mayar da ƙasa ki rufe, ki yi saurin barin makabartar, indai maganar aure ce babu ita har abada babu wanda zai ƙara tada maganar ma" Yana gama faɗar haka Hajiya Naja,atu ta saki wata ajiyar zuciyar da ita kanta bata san ta sauke ta ba, hannunta kuwa da take riƙe da abin da ya bata duk ya jiƙe da lemar gumi!.
Mom ta ce
"Boka kuma dole sai tsakar dare?" Hajiya Naja,atu ta shiga ciccira idanun tsoro kamar an kama kwarto a ɗakin amarya.
Boka ya ce
"Haka ƙai,dar aikin take!"
Hajiya Naja,atu ta yi saurin faɗin
"Boka da dai an bar wannan ka bani wani lakanin, ni wallahi tun da uwata ta haifeni ban taɓa shiga makabarta ba, barw makabartat ma ka ce sai tsohuwa watakila tana cike da manyan aljanu, wallahi tsoro nake"
Boka ya ce
"Wannan ai karamin aiki ne, mu indai za mu faɗa a yi to akwai biyan bukata, don cikin ayyukana ina iya miki aikin da zan ce daga nan wajena ki cire kayanki ki tafi gidanki tsirara ba tare da kin shiga mota ko wani abun hawa ba" Hajiya Naja ta dafe kirji da hannu ɗaya, hannun da bashi take rike da kayan aikin ba.
Mom ta zaro ido, boka ya ce
"Tabbas na wa mata irin aikin sun fi a ƙirga amma da yake ƴan neɓan duniya ne amincewa suke, kuma su tafi tsirara, idan an gansu sai a kama su a matsayin taɓin hankali ya same su, wasu a kaisu gidan mahaukata daga baya sai su nuna sun samu lafiya, haka zaki ji mace ta zo tana cewa aka yi ta cewa asiri aka mata aka haukatata basu san cewa neman duniya bane, amma fa daga wannan ranar ko mene ne bukatarsa ta biya"
Hajiya Naja,atu da sauri ta kalli kayan jikinta tana tunanin kenan sai a e ka cire ka tafi babu kaya. Tana cikin wannan tunanin ya ce
"Ba kallon na ce ki je makabarta ki binne abu ba, akwai aikin da in za a yi wa mace sai ta je ta kwana a makabarta, wata kuma in ce ta yi rami a kan tsohon kabari rami sosai sai ta taddo kashin gawar cikin ramin, sannan ta saka kafafunta a ramin na tsawon daren ranar amma a haka suke yi, neman duniya ai babu abin da ba a yi"
Mom ta ce
"To ke Naja naki da sauƙi ma" Hajiya ta gyaɗa kai don duk jikinta ya yi la,asar.
Sun yi wa boka godiya suka fito suka tafi, bayan Mom ta tambaye shi ,a su iya zuwa tare ya ce mata ita kaɗai za ta je, Hajiya ta tambaye shi cewar za ta iya saka direba ya kaita tun da bata san tsohuwar makabartar ba ya ce ta yi takatsan tsan, direban ya tsaya daga nesa sosai da makabarta yadda ba zai ganta ba, ta ji daɗin wannan magana haka suka yi godiya suka fito.
Sun samu direban yana ta bacci a motar, suna shiga ya ja suka tafi bayan sun tada shi a baccin. Sakon wajen bokan yana cikin jaka, a ajiye basu iso cikin gari ba sai la,asar, shi daman direba da ruwa a motar ya yi alwala ya yi sallar azahar a ƙasa a dajin bayan ya yi sallah ne bacci ya ɗauke shi. Sallar la,asar ce ta same su a hanya.
Ko maganar da ta danganci abin da ya kaisu basu yi ba bare har ya ji wani labari, gidan Mom suka wuce ya ajiye su ta ce ya jira ta, da ta shiga gidan suna gama shawara da Mom a kan cewar ta zauna ta kwana a gidan, domin idan ta tafi gida ba zai yiwu ta fito tsakar dare aiwatar da aikin ba kuma za a zargeta har a samu wanda zai bi bayanta ma, jin haka ta ɗakko wayarta ta nan ta ga missed call ɗin mutane ciki har da mijinta ta doka tsaki ta shiga kiransa, damana a silent ta bar wayar.
Ko da ya ɗauka ta sanar da shi cewar sun tafi wani ƙauye ita da Mom za ta rakata wajen wata mata ta bata maganin ciwon kai, saboda ciwon kan ba na asibiti bane, wataƙila su yi dare idan sun dawo sai za su wuce gidan Mom ɗin da safe za su taho, har direban, Alhaji ya amsa da a dawo lafiya tare da mata fatan dacewa da kuma samun sauƙi, tana kashewa ta doka uban tsaki tana faɗin
"Munafuki ai aure sai dai ka ga ana ƙarawa"
Mom ta ce
"Kin fa mun manta ba a mana maganin uwar tasa ba, mai bakin reza uwar ƴan bada umarni"
Baki Hajiya ta taɓe ta ce
"Kash wa ma yake ta wannan ƙaramin alhakin ai in dai an dakatar da ƙarin aure magana ta ƙare!"
Direban ta kira a waya ya shigo, daman masallaci ya je ya gabatar da sallar la,asar, su kuwa suna zaune babu wanka babu sallah sai warin dauɗa suke.
Ya shigo cike da girmama, nan take faɗa masa sai gobe za su koma gida saboda tana da wajen zuwan da zai kaita kuma ta sanar da Alhaji, ya amsa mata cike da girmanawa ta ce ya tashi ya je idan an gama abinci za ta kira shi ya karɓa ya amsa tare da tashi ya fita, a zuciyarsa kuma yana Allah wadai da halayya irin tasu ta bin malamai da bokaye.
Sai magriba aka kira shi ya karɓi abincin ya shiga wani ɗaki da aka nuna masa wajen bakin kofar gida ya ci abincin, bayan ya gama ya fito ya fita waje, wajen wasu samari ya zauna inda suke zaune a bancin bayan sun yi sallar isha,i. Sai wajen tara ya shiga gidan ya shiga ɗakin da ya ci abincin ya kwanta a kan tabarmar da aka ajiye masa.
Yana jin lokacin da Mom ta zo ta rufe ƙofar gidan, zuwa can har bacci ya fara ɗaukansa ya ji Hajiya tana kwala masa kira, ya amsa tare da fitowa ta ce
"Idan an jima zan tasheka akwai unguwar da za ka kai ni idan dare ya raba" ,Ya ɗan zaro ido ya ce ..
"Unguwa Hajiya a tsakar daren?"
Ta haɗe rai ta ce
"Ko ba za ka je ba?" Ya girgiza kai yana faɗin
"Tuba nake Hajiya, Allah huci zuciyarki" Bata ƙara cewa komai ba ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma ya koma ɗakin ya san dai zancen gizo ba ya wuce na koki, wato ya fi zaton ko wajen wani bokan za ta koma don daman hankalinsa bai kwanta da kwanan da ta ce xa su yi a gidan ba tun da ba wani gari bane suka je kuma sun dawo da wuri.
Hajiya Naja ido biyu ta kasa bacci na farko tana jin daɗin burinta zai cika har tana hango irin tsiyar da za ta ɗiga idan ta samu wata damar, don hatta Goggo sai ta gasa mata aya a hannu. Na biyu kuma tana tunanin zuwa tsohuwar makabarta amma kasancewar cikar burin ya rinjayi tsoron sai bata ji wani abu sosai ba.
Ko da ta taso ta buga ƙafar Mom da ta cika ɗakin da munshari, Mom dakyar ta ɗago kanta saboda nauyin baccin da ya ɗauke ta.
Ta sanar da ita za ta tafi nan ta ce mata sai ta dawo, haka ta fito rataye da jaka kamar zabirar aski.
Direban kira biyu ta masa ya amsa tare da fitowa da mukulli a hannunsa, suka shiga suka tafi a talatainin dare yana mamakin inda za su je tamkar dai wanda za su baƙunci aljannu, in dai mutane ne ai ba za a je bakuntar dare ba amma dai yana jira ya ga gudun ruwanta.
Sun fara tafiya cimin dakakkiyar murya ta ce
"Tsohuwar maƙabarta za ka kai ni" Da sauri ya juyo a kiɗime, har motar ta so ƙwace masa, sannan ya nutsu ta daidaita kansa.
"Tsohuwar Maƙabarta kuma Hajiya?"
Ta ce
"Eh can na ce kai dai ba aikin ka bane kai mutum duk inda ya bukata, to ba huruminka bane jayayya da inda za ka kai mutum" Ki ya gyaɗa.
Ya kama hanya tiryan-tiryan a zuciyarsa yana addu,ar ubangiji ya sa indai za ta je wurin ne don ta cutar da wani Allah ya ruguza duk wani mugun nufinta da abin da ta saka a gaba. Tun kafin su je wajen makabarta da yake ya kwatanta mata ta inda ƙofar take, ta fita maƙale da jaka tana faɗin
"Kake lura kar wani ya biyu hanyar da na yi har na je na dawo, addu,a zan je na yi wa mamata, wani kakanmu ne na yi mafarkinsa yau kuma a makabartar nan yake, shi ne na tashi don na je na masa addu,a don kar na koma bacci na sake mafarkinsa"
Direba ya ce
"Allahu akbar, Allah haɗa rai da gafara gwara ki je ai mamaci babu abin da ya fi buƙata sama da addu,a, in sha Allah zan kula babu wanda zai biyo hanyar barw ma kina gani babu kowa a wajen nan tun da muka biyo" Ya faɗa cikin jimantawa, ta tafi tana yi tana waiwaye kai da ganinta ka san marar gaskiya ko a ruwa sai ya yi gumi.
Direba tana tafiya ya ja uban tsaki yana faɗin
"Jahilan banza da wofi, duk ranar duniya da safiya baki je addu,a makabarta ba sai tsakar dare, saboda kin mayar da ni sha ka tafi, ni za ki rainawa hankali"
Tana tafiya tana faɗuwar gaba, tana dab da shiga ƙofar wani kare yana ta mata haushi, amma haka ta jure ta shige maƙabarta, sai da ta ɗan yi tafiya sannan ta samu kabari wanda bai gama zagwanyewa ba ta shiga haƙa rami a jikin kabarin sai da ya yi zurfin da zai biya mata buƙata ta fito da mutum mutumin nan mace da na miji ta saka, na ta shiga kurma ashariya masu maiƙo adadin yadda bokan ya faɗa mata, tana gamawa ta ambaci sunan mijin ta mayar ta rufe yadda aka faɗa mata, gabanta yana ta lugude.
Ta ɗago kai tana kallon wajen don tabbatar da babu kowa haka ta tashi tae fito daman hasken wata tarrr kamar safiya shi ya sa ko fitilar wayar ma bata kunna ba.
Gudu-gudu sauri-sauri ta dawo ta samu direban zaune a mota ta shiga tare da masa umarnin tafiya, ya ja suka tafi, yana jinta tana ta faɗin
"Allah sarki kakana ubangiji ya haɗamu a aljanna yau sai na ji mutuwarka ta dawo min sabuwa dal"
Dakyar ya samu faɗin
"Allah jikansa"
Ta ce
"Amin"
Ko da suka dawo wajen ƙarfi uku da rabi tana zuwa ta tashi Mom tana bata labari komai ya tafi kamar yadda suka tsara, sosai Mom ta ji daɗi don a ganinsu sun jefar da ƙwallon mangwaro sun huta da ƙuda, babu Alhaji ba aure Hajiya za ta ci karenta babu babbaka.
*FALMI*
Aunty tah ta same ta da magana mai daɗin gaske kan yadda suka yi magana da babanta a cewar ta sanar da shi game da wanda yake neman aurenta, kuma ya yi murna matuƙa da yadda aka sanar da shi mutumin kirki ne. Sai dai ta faɗa mata cewar ko kusa bai amince da auren a nan da kwana uku ba.
Ya sanar da ita zai sanya abokinsa ya yi bincike, sannan yana so ya ganshi ido da ido kafin ma ya amince da auren sannan a saka rana. Ta ji daɗi sosai ta rungume Aunty nata cike da farinciki da annashuwa, domin ta san duk wannan abin da ta yi, ta yi ne dominta kuma domin farincikinta, da a ce ana samun ƴan uwan irinsu wanda suke son junansu sannan ba sa yi wa juna hassada kowanne yana son cigaban ɗan uwansa ko da kuwa shi bai samu wannan abin ba ko bashi da hanyar samun ko ma mene ne idan ya ji ɗan uwansa zai samu yana farjnciki irin farincikin da idan ka ganshi tamkar dai shi ne ya samu abin.
Ko da ya kira ta da daddare ta sanar da shi yadda suka yi da Aunty tah, sai dai jikinsa ya yi sanyi da ta sanar masa cewar auren nan mahaifinta bai yarda a ɗaura shi a kwanaki uku kacal ba.
Ya san daman komai yana tafiya da bincike ne, kuma da a ce kowane iyaye haka suke jajircewa wajen binciken wanda za su aurawa ƴaƴansu ba tare da la,akari da mai suke da shi ba da kuwa an samu raguwar lalacewar aure saboda wasu babu bincike ake auren sai daga baya abubuwa barkatai wanda hankali ba zai ɗauka ba za suke fitowa zaman a karshe ya lalace!.
Ya ji daɗi matuƙa da ta yi kokarin sanar da Aunty nata har ta amince ta sanar da mahaifinta. Sai dai shi yana jin nauyin Goggo ya tinkare ta da maganar cewa auren ba zai yiwu a kwanaki ukun da ta ƙidaya ba.
Washe gari ko da ya sanar da Goggo abin da mahaifin wacce ya ce yana neman aure ya faɗa, Goggo bata nuna masa komai ba, ta ji daɗin cewar ya samu wacce zai aura kuma ta masa addu,a cewar Allah sa haka ne mafi alkairi!
Lokacin da suka tattauna maganar nan, Ruma tana wanka don haka bata san wainar da aka toya ba, ita dai tana kan bakarta na cewar an tsayar da magana cewar da ita za a ɗaura aure!.
Sun cigaba da mannewa a waya suna soyayya mai tsafta kuma mai tsayewa a zuciya, tamkar sun kwashe shekaru suba tare!. Suna tsara irin yadda za su yi rayuwar aurensu yana sanar fa ita irin riƙon da zai mata da gata da kuma tarairaya, ita ma tana faɗa masa yadda za ta masa biyayya sai abin da ya ce domin za ta zame masa raƙumi da akala sai inda ya yi da ita za ta bi.
Ya ji daɗin wannan maganar musamman da ya kasance wanda bai isa da matarsa ta gida ba, uwa uba shi ne yake biyayya ba wai shi ake bi ba. Yanzu ne yake jin zai yi sabuwar rayuwar da yake jin shi ma zai ji shi kamar wanda ya yi auren fari.
A tsakanin kwanaki ukun na da aka yi maganar za a yi aure su ne kwanaki mafi muhimmanci a rayuwarsu su duka biyun, domin sun zame musu kamar shekaru uku ne ba kwana uku ba sun shaƙu sosai irin shakuwar da sai wanda ya gansu ne zai adar da ita. Kullum sai ya je hira kuma sai sun yi waya suna soyayya mai tsayawa a zuciya.
Ranar da aka yi kwana uku ba a yi ɗaurin aure ba, rayukan mutane biyu suka kasance ƙunshe da murna da farinciki marar misaltuwa.
Mutum na farko Ruma wacce take ganin Alhaji Muhammad ya zama mallakinta saboda tana ganin an bari ta gama idda ne shi ya sa aka fasa ɗaura auren a kwana ukun da Goggo ta ambata. Wato ana jiran kwanakin iddarta su cika a ɗaura da ita, ranar da kwana ukun ya cika suka ji shiru ita da Mama Magajiya sai waya suke cike da farinciki haka Ruma ta tambayi Goggo za ta je gidan Mama ta kai mata wuni, haka ta tafi suka je suka runga murna ita da Goggo tare da shirye-shiryen yadda za su tsara abubuwan bikin. Ranar Goggo har tsire ta siya musu da lemuka suka ci don murnar Ruma ta kusa zama mallakin Alhaji su samu yadda suke so.
Mutum na biyu shi ne Hajiya Naja,atu wacce ranar ta zame mata tamkar ranar babbar sallah, don kuwa ganin babu maganar ɗaurin aure ta tabbataAR da aure ya fasu kuma ba komai ne ta yi yaƙinin fasuwar hakan ba illa aikin bokan da ya ci.
Cike da murna ta caɓa ado da kwalliya ranar take ta yawo a gidan tana wani bada faɗi ita ala dole bata da kishiya a gidan duniya har ƙarshen rayuwarta. Haka suke ta waya suna ɓaɓɓakar dariya kamar taɓaɓɓu ita da Mom suna ganin duk wanda ya ce ya ci tuwo da su to miya ya sha!.
Washe gari ma haka suka saɓi hanyar gidan boka ta je ta masa wata kyautar mai tsoka na cikar aikinsa da ya yi! Ya yi murna matuƙa yana ra faɗa mata cewar ai inda shi ne kaɗan ma daga aikinsa.
Ranar da ya cika kwana huɗu wanda yake sati idan aka haɗa da kwana ukun wancan auren da aka saka aka janye, a ranar ne Alhaji Muhammad da abokansa guda biyu da wani ɗan uwan Goggo amma dai ba na jini ba suka nufi Maiduguri domin ziyartar mahaifin Falmi kamar yadda suka tsayar da ranar a matsayin ranar zuwa su nemi auren.
Sun je an tarɓe su cikin aminci da mutuntawa, a inda abokin Alhajin guda ɗaya ya kasance ɗa ga abokin karatun mahaifin Falmi ɗin.
Bayan an yi komai cikin girma da mutunta juna, daman ana gobe za su zo mahaifinta ya sa aka je aka yi bincike a kan Alhajin kuma an samu sakamako mai kyau don ba a samu wanda ya faɗi aibinsa ko wani hali marar kyau ba, wannan ne babban dalilin da ya ji ya ƙara kwanta masa a rai.
An yanke ranar aure a matsayin sati mai zuwa wato sati ɗaya, wanda an yi hakan ne saboda Falmi ba budurwa ce da za a tsaya saka dogon lokaci ba, sannan mahaifinta ya sanar cewar ba za a yi wata bidi,a ba bugu da ƙari ya sanar cewar sai Falmi ta tare washe gari za a yi mata jere!.
Alhaji ya ji daɗin maganar nan don kamar an duba zuciyarsa, saboda shi tun ranar da Hajiya ta yi sakko ta fita sannan ta kira shi ta ce wai za ta kwana ya ji bai gamsu da lamarin ba, sannan ya saka a ransa ko aure ne sai dai ta ji an ɗaura saboda yadda ya ga tana ta wani fallin rashin mutunci da kuma gadara tamkar dai ta taki wani abu.
Ya san in dai za a yi jere dole za ta san da maganar auren, amma ya fi so sai ta sakankance kawai a ɗaura, musamman yanzu da aka ce sai washe gari za a yi jere hakan ya sa ya ɗauki alƙawarin sai dai ta ga kishiyarta a gidan kamar yadda Goggo ma ta faɗa masa a cewarta saboda kar a yi tashin hankali!.
Falmi ta ji daɗin tsayar da sati guda a matsayin ranar aurensu, don ni take ta yj amanna da shi ɗari bisa ɗari, ta amince ya zama abokin rayuwarta na har abada!.
*Book 2 za a biya 1k ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta ****
MAMAN AFRAH *** [9/9, 7:55 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH
🅿3️⃣5️⃣