BOOK 1 END
*RAMLA*
Idanu ta zuba musu cike da jiran jin abin da yake tafe da su kamar yadda Abban Humairar ya ce abokinsa ya mata bayanin abin da yakr tafe da su.
Alhaji Abdullahi ya gyara zama, tare da gyara zaman babbar rigarsa ya zauna da kyau ya kalli Abdulsalam, Abdulsalam ya faki idanun Ramla ya kashe masa ido ɗaya alamar ya yi bayani kawai ban da ƙumbiya, ƙumbiya don shi bai ga wani abin ɓoyewa ba.
Ya yi gyaran murya ya ce.
"Ramla mun zo da wata babbar magana, amma idan kika dauke ta ba wata magana ba ce, kin san an ce abin da ka ɗauka da sauƙi to yana zuwa maka da sauƙi a rayuwa, haka ma idan ka ɗauki abu da wahala yana zuwa maka da wahala"
Abba ya ce
"Wannn haka yake, gwara ma ka ɗauki komai ba komai ɗin ba tun da a lokuta da dama in ma ka tsaurara abin sai dai ya xo ya dameka tun da ba za ka saka ba kuma ba za ka hana ba!" Furucin nan nashi ya matukar bakanta ranta amma haka ta danne zuciyarta domin idan ta biya abin da Abban Humaira ya mata tabbas zuciyarta tana dab da bugawa.
Alhaji Abdullahi ya cigaba da faɗin
"To ina fatan za ki fahimcemu, saboda bahaushe ya ce fahimta fuska!"
Ramla ta yi wani murmushi mai faɗaɗa fara,arta ta ce
"Haba kai kuwa Alhaji ai kawai ka faɗi abin da ya kawo ku, don duk wannan bayanin naka basu da gurbi a wajena, ma,ana ni ba zan kasa fahimtarku kamar yadda kuke tunani"
Cikin wasa Alhaji Abdullahi ya ce
"Kar dai kin ɗauka wani albishir ne mai daɗi kike washe baki, inaso ki sani idan kika ji wannan labarin zai baƙanta ranki matuƙa, amma ina baki shawara ki yi haƙuri!"
Abban Humaira ya ce
"Haƙurin ne ya fi kam"
Ramla ta ɗago daga jinginar da ta yi a jikin kujera, ta sauke mayafinta daga yafawar da ta yi a kanta, ta gyara zamansa a kafaɗarta, ta saka hannu biyu ta ɗago ɗankwalinta daga ƙeyarta sai da ya zo gaban goshinta ma,ana ta yi ture ka ga tsiya ta murmusa don a ganinta kunyar marar kunya asara ce, kuma tun da har suke ganin abin zai bakanta ranta za ta nuna musu a Abdulsalam da babu uwar ubansu ɗaya, in dai har saboda Hasiya ne suke wannan za ta nuna musu bata gabansu ko don su je su kora mata bayani"
Ta ce
"Allah sarki, ko dai abin ne ya matso? Ko in ce ko dai abin ne ya zo in ji mai faɗar aurensa"
Baki sake Alhaji Abdullahi yake kallon yadda take magana kamar wata ƴar bariki ya ga ma sai wani falli take duk da dai ta saka su a duhu basu gane inda ta dosa ba amma wanka mai kamar jirwayen da ta yi ya nuna kamar dai ta san abin da yake tafe da su, amma dai sun ma san ba dai a kan maganar auren bane da a kan auren ne ta san abin da yake tafe da su da ta fara tada jijiyoyin wuya tun kafin ma su nema ta za ta fara furta bakaken magananu don shi, Abdulsalam ya san sai ma ta masa gori har ma da gore-gore.
Abban Humaira ya ce
"Ramla wane abu kike magana?"
Ta yi murmushi mai sauti ta ce
"Wane abu ne kuwa da ya wuce maganar aurenka" Idanu ya zaro cike da mamaki, abokin nasa yana taya shi mamaki.
Alhaji Abdullahi ya ce
"Aure Ramla wane auren,?"
Ta gyara zama ta ce
"To wane aure kuwa ban da aurensa da Hasiya matar ɗan uwanka kuma abokinsa Zahraddin, ko ba wannan ce maganar da ta kawo ku ba" Su duka sun cika da mamaki, Abdulsalam ya yi fiƙi-fiƙi da ido musamman yadda ta gabatar da maganar ta hanyar falar wacce zai aura!.
Alhaji Abdullahi kuwa kunya ce ta kama shi, ya ɗan sunkuyar da kai ƙasa yana faɗin
"To,to,to, ashe ma kin sani Ramla"
Ramla ta ce
"Ai da baku ɓata bakinku kun zo faɗa min ba tuni na sani, Allah sa a yi a sa,a ya bada zaman lafiya" Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Alhaji Abdullahi ya ce
"Ramla daman kin san da wannan maganar amma baki tunkari Abdulsalam da ita ba? Yau fa saura kwana uku a ɗaura aure kuma a ranar ne za ta tare a gidan nan" Ramla wacce bata san bikin ya matso dab haka ba a zuciyarta ta ji fargaba kasancewar bata taɓa zama da kishiya ba sannan bata san ya zaman zai kasance ba, daman ana wulakanta ta ne a iya ita kaɗai kuma ta jure ta shanye amma yanzu tozarcin zai yi yawa idan ya zamana a gaban kishiya ne, duk da dai tana ganin aski ya zo gaban goshi wato ba za ta taɓa ɗaukan abin da ta ɗauka a baya ba, idan kuma har ya kasance za a cigaba da uin hakan to zaman aure zai ƙare tsakaninta da Abdulsalam ko da ya kasance shi ne autan maza!.
Ta murmusa ta ce
"Sara da sassaƙa ai ba ya hana gamji toho, sanina da rashin sanina mai zai ƙara? Ai ba a so a in sani ba to a kan me zan nuna na sani? Na san da maganar nan tun wasu kwanaki da suka shuɗe" Abdulsalam sai a lokacin ne ya ɗan ji nauyinta da ya tuna ta bashi ƙodarta sananna ta sadaukar da dukiyarta wajen magance masa cutar mafitsara wanda idan ba don ita ba da tuni wajen ya ruɓe lafiyar mafitsarar ta salwanta wataƙila shi da mace ma sai dai kallo, sai dai ya ga ana yi, sannan uwa uba ƙidar da ta bashi daga cikin sassan jikin ɗan adam da suke da mahimmanci, ko makusancinka ba kowa ne zai baka ba, sai dai wani ɓangare na zuciyarsa ya shiga faɗa masa cewar ai ba sakinta ya yi va kuma aure ai sunnar ma,aiki ne.
Alhaji Abdullahi ya miƙa hannu ya ɗauki dubu hamsin ɗin nan ta kan ledar ya ajiye a kusa da shi, ya buɗe Viva ɗin ya ɗakko leshi guda biyu atamfa guda biyu sai takalmi da jaka, yana fitowa da su Abban Humaira ma idanunsa a kan kayan da ake fitowar suna ɗagowa suka ga babu Ramla a wajen da take, da sauri suka kalli hanyar ƙofa suka hange ta tana dab da fita tana takunta cikin nutsuwa.
Abban Humaira ya kira ta da
"Ramla"
Ta juyo a hankali tana faɗin
"Na,am"
Alhaji Abdullahi ya ce
"To ke da ba a sallame ki ba kya tafi wannan fa kayanki ne muka taho mili da shi" Ta zubawa kayan ido na tsawon minti biyu, a zuciyarta ta ga sun raina mata hankali, kamar wata uwar gidan ƴar tsana kayan faɗar kishiya ne za a kawo mata a ledar Viva, ban da tozarci ai yana da halin da ko set ɗin akwati zai iya mata a matsayin abin faɗar kishiya, amma don ya nunawa duniya bata da wani muhimmanci ya ɗakko leda da kaya ƴan tsirarru a ciki.
Murmushi ta yi ta ce
"Au nawa ne ashe"
Alhaji Abdullahi ya ce
"Naki ne mana kina gani har da fa dubu hamsin" Ya faɗa yana ɗago rafar ƴan ɗari biyar biyar ɗin.
Ta ce
"Aikuwa dai na gode, godiya ma ta gode, sai dai ni na wadatu da gabaɗaya abubuwan nan, ku haɗawa ƙanwata a kayan lefenta" Kafin ɗaya daga cikinsu ya furta wata kalma, Ramla ta ɓacewa ganinsu ta habyar juyawa cikin saurin takunta mai nutsuwa ta bar musu falon.
A tare suka sauke ajiyar zuciya, suka kalli juna Alhaji Abdullahi ya ce
"Bata buƙata fa"
Abba ya ce
"Ni wallahi ban san ma ina Ramla ta ji maganar nan ba"
Alhaji Abdullahi ya ce
"A gari mana ai zancen duniya ba ya ɓuya"
Abba ya ce
"Amma ta shayar da ni mamaki, ban taɓa zaton har za ta ji magana irin wannan ta yi shiru ba"
Alhaji Abdullahi ya ce
"Gaskiya Ramla daban ce a cikin mata"
Sun jima suna ɗab tattaunawa a ƙarshe ya mayar da kuɗinsa a ljihunsa, ya ɗauki kayan, sula fito ya saka a mota suka fita tare da abokinsa, ba tare da ya bi ta kan Ramla ba barw ya lallashe ta ko ya nuna ya yi ba daidai ba kamar yadda ta ce su ba Hasiya kayan kuwa can suka nufa daman don zuwa su faɗa mata daman sun yi da ita a kan za su je sanar da Ramla duk da ita ta san abin da ta ashshaka na ɗora hoton tun ba yau ba a status Ramla ta gani.
Suna zuwa ta fito ita da Karima sai wani yauƙi take tana kashe masa ido tamkar ta rungume shi haka take wani tsayawa dab da shi, saboda fitowa suka yi daga motar, shi kuma kansa sai fashewa yake yana gani Hasiya ta kere Ramla da abubuwa da dama ta fannin kula da miji, yana ganin za su huta su yj rayuwa cike da kulawa da soyayya.
Ya kalle ta yana washe baki ya ce
"Kin ga yadda kika yi wani irin kyau Hassy tah sai wani sheƙi kike fatarki kamar an canja miki ita lumui-lumui da ita kamar ta jariri" Ta ɗan murmusa tana shirin magana Karima ta ce
"Tsabar gyara ne ka san mata sai da gyara, wata macen bata damu da gyara kanta ba"
Alhaji Abdullahi ya ce
"Kai dai duk ka zauce ne kamar dai wannan ne auren ka na farko"
Ya ce
"To da maraba?, Ai wannan auren shi ne na farko "
Su duka suka ƙyalƙyale da dariya, Hasiya ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha a rayuwa tana so ta ga miji yana yinta ya ɗaga darajarta fiye da ta wata macen lallai ta san Ramla za ta ƙunshi baƙinciki.
Alhaji Abdullahi ya ce
"Haka ka ce?"
Ya gyaɗa kai yana faɗin
"Ai hassy tah mace ɗaya ce tamkar da miliyan ita ce ta farko ita ce ta karshe, Ramla kuma ƙaddarar ƴaƴa ce ta haɗa aurena da ita" Hasiya da Karima suka kalli juna suka kashewa juna ido.
Alhaji ya ce
"Wai kun san Ramla ta san da maganar nan" A zuciyar Hasiya ta ce
"Allah sa ma auren naka da ita ya ɓalle ta ƙara gaba kowa ya huta.
Karima ta ce
"A ina?"
Abba ya ce
"Bata faɗa ba fa" Karima da Hasiya suka sake kallon juna Hasiya a zuciyarta ta ce
"Lallai matar nan ba ƙaramar ƴar bariki bace wato bata faɗa a status ɗina ta gani ba.
A fili ta ce
"Allah sarki Ramla kenan dai yau ta nuna muku kurenku" Ta faɗa tana musu sariyar wasa a zuciyarta kuma bugun cikinsu ne ta yi don ta ji yadda aka kwashe.
Abba ya ce
"Za ki yi mamaki fa ko a fuska bata nuna ba, ke ƙarshe ma kayan da muka kai mata ta ce a kawowa ƙanwarta kin ganshi can a mota" Ya faɗa yana kallonta, Alhaji Abdullahi kuma ya ɗakko ledar da sauri don ta ƙara ɓata Ramla a idonsu don ta ji haushin kissar da ta yi ta nuna bata damu ba, hakan ya nuna mata ashe dai za a sha gwagwagwa a zaman don ita ma kissar za ta yi sai dai a yi ta bugawa ɗan halak ka fasa!.
Cikin karya murya ta ce
"Ko dai rainawa ta yi?" Suka girgiza kai suna tabbatar mata da cewar ba haka bane. Duk da uban kuɗin da ta basu suka jibgo lefe haka suka saka hannu suka karɓe ledar suna rayawa a ransu, gaba ta kaisu gobarar titi.
Sun jima suna tattaunawa a cewar gobe za su je jere, don dama ana jiran yadda komai zai kaya tun da ba a faɗawa matar gida ba.
Bayan sun yi sallama sun tafi, su Hasiya suka shiga gida suka faɗawa Dada yadda aka kwashe da uwar gida Ramla Dada ta taɓe baki ta ce
"Munafuka, almunafunfun wato bariki alalar gero ta yi wa mutane, aikuwa ta yi wa kanta ta wa arziƙi dundu"
Bayan sun ƙule a ɗaki, Hasiya ta shiga faɗin
"Ƙawata kin dai ga yadda mutumin nan yake rawar ƙafa a kaina, to na tabbata kwaɗayin amarci ne, da giyar amarci suka masa jagoranci, don haka fa dole na yi gyara na fitar hankali da zai sanya ya manta cewar yana da wani auren ke inaso ma ya manta ya taɓa yin wani abu wai shi aure!!!"
Karima ta ce
"Kina dai ji yana batun ke ce ta farko ta ƙarshe alamu sun nuna ba ya ma ta tata"
Hasiya ta ce
"Ai shi ya sa zan zage dantse na yi gyaran da zan gigita shi, ya yi sambatu ya san ya yi aure!"
Karima ta ce.
"Tun da dai kin sha ƴan dake daken nan da abin da ba a rasa ba, to yanxu kin san duniyar kayan mata nema take ta bar hannun mata ta koma hannun malaman zaure!"
,Hasiya cike da mamaki ta ce
"Ban gane ba"
Karima ta ce
"Ina hufin yanxu malamai ma suna bada laƙanin maganin da zai riƙe miki jiki ya gigita mai gida, ba tare da kin sha wahala wajen siyan wasu abubuwan ba sai dai inaso ki sani sai kin buɗe bakin jaka!"
Hasiya ta ce
"Kuɗi ba matsala ta bane!"
Karima ta ce
"To tashi mu je akwai wani wanda na san yana yin aikin ya bada maganin, ai mace bata da makamin da ya wuce ta gyara kanta a wajen miji wannan wajen dai shi ne mutuncin mace idan ta riƙe ta zauna lafiya idan ta banzantar da shi miji ya banzartar da ita"
Haka suka fito suka yi wa Dada sallama, napep suka hau suka kama hanyar gidan malamin da yake wata unguwa can ƙarshen gari gidan da nisa. Ko da suka je sun same shi zaune a kan tabarma a ƙofar gida suka yi sallama ya amsa nan suka sanar da shi abin da suke tafw da shi, don Karima ta taɓa rako wata ƴar unguwarsu kuma aiki ya ci. Tashi ya yi suka shiga ɗakinsa na cikin zaure, suna shiga ya zauna su ma suka zauna daga gaban tabarmar ya yi gyaran murya ya ce
"Kina da kishiya?" Ta amsa masa da eh tana da akwai, ya jijjiga kai ya ce
"Aikin ba ƙarami bane, amma ni wurina mai sauƙi ne" Ya ɗakko wani ƴar ƙaramar roba da bata fi girman ƙaramin yatsa a tsawo ba ya ce
"Wannan ne maganin matsalar da kika zo da ita, idan kika yi amfani da wannan tana ɗauke da matsi, ni,ima, mallaka sadidan, jan hankalin miji ya dawo kanki, daga ranar da ya kusance ki to duk wata mace salam zai ji ta, kwatankwacin bambancin da yake tsakanin macen da ta yi amfani da wannan maganin tamkar ki dafa nama ne da kayan miya da kayan ɗanɗano da mai da komai da komai, to haka ne bambancin ɗaya bambancin tamkar ki dafa nama ne babu komai a ciki sai farin ruwa shin za a samu bambanci?"
Suka haɗa baki da faɗin "Akwai bambanci mai girma " Ya gyaɗa kai ya ce to haka zai cigaba da jin kishiyarki salam har abada!. Su duka suka yi murmushi.
Ya faɗa musu kuɗin Hasiya duk da akwai tsada amma bata ji tsadar ba don biyan bukata ya fi dogon buri!.
Ya karɓi kuɗin yana faɗin "Karki damu da kuɗin da kika bayar, za ki mallaki kuɗin linkin ba linkin idan kika yi amfani da maganin" Suka murmusa suna ta zabga godiya kamar su ari baki.
Malam ya ce
"Idan aka kai ki ɗakin miji, bayan kowa ya watse sai ki ɗakko wannan abun ki raba shi a uku, ki ɗauki kashi ɗaya ki saka a cikin jikinki, ina nufin ƙasanki, sauran bayanin kuma za ki ba kanki labari, sai dai fa kar ki yarda ki sha wani abu da ya danganci maganin mata don wannan ya haɗa komai da komai"
Sun sha godiya kafin suka baro gidan, daman tana faɗin ɗan dakan da ta sha duk sun bi sahun al,ada saboda ta yi al,ada ta san kuwa komai ya wanke.
Ramla ko da ta koma ɗaki sai da ta yi kuka sannan ta ji salama a zuciyarta, tana kiyasta irin rashin adalci na Abdulsalam ko kunya ba ya ji ya manta halaccin ta. Da dare bayan yara sun dawo ta zaunar da su ta musu nasiha mai ratsa jiki, sannan ta sanar da su babansu zai yi aure, sannan ta ja hankalinsu ta ja musu kunne a kan girmama ko ma wace ce suka gani a matsayin matar ubansu bata da bambanci da ita duk uwa ce a wajensu tun da matar mahaifinsu ce. Sun ji ba daɗi tun da da wayonsu, musamman Humaira ta ji haushi saboda kasancewarta mace mai kishi. Sun yi na,am da nasihar mahaifiyar tasu. Washe gari bayan sun tafi makaranta da safe, Abban Humaira ya kira ta don daman sakko ya yi ya fita, shi ne da ya kira ta yakr faɗin za a zo a yi jere ta amsa masa da Allah kawo su lafiya.
Haka aka zo aka shiga ɓangaren amarya aka yi jera, tana jin hayaniyar maza da guɗar mata da suke saki lokaci zuwa lokaci sai dai ita bata fito ba ta kama kanta.
An sha bidiri bireɗe, an yi bikin kece raini tamkar na budurwa don an yi shagulgula kamar ba gobe.
Ranar asabar ɗin misalin ƙarfe goma aka ɗaura auren, Hasiya da Abdulsalam, sun yi farinciki sosai da kasancewarsu ma,aurata.
Da yamma ya je gidan ya yi kwalliyarsa don tin da aka fara bai shirya a gidan ba kayansa kawai yake ɗauka akwai inda yake shiryawa gidan abokin Abdullahi wanda bashi da aure don ba ya so yake ta zuwa gidan idan ma ya fito sai dare zai koma gidan.
Ya shiga ya sako wata shadda sai buɗaɗa ƙamshi yake ya wuce ɓangarenta ya same ta zaune tana danna waya, sai Asma,u da wata ƙawar Asma,u suna hira, suka amsa sallamar da ya yi ya ce
"Sannunku da hutawa, yau za a kawo ƙanwar taku ai" Asma,u ta yi murmushi mai ciwo ta ce
"Wai daman ba sai gobe ba ne?" Da sauri ya zabura kamar ta watsa masa fetur da ashana ya ce
"Gobe kuma? Yau ne fa" Ta yi murmushi mai ciwo ta ce
"Allah sarki, muna maraba da ita"
Ramla ko kallo bai ishe ta ba, shi ma kuma bai damu da halin ko in kula da ta nuna masa ba don shi yanxu yana ganin ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba!
Da daddare a can gidan Dada ana ta shiri motoci sun yi ayari a ƙofar gida, Dada sai shiga ɗaki ake ana fitowa tsakar gida, makota da suka shigo don rakiyar amarya da kawayen abokan arziƙi sai kallonta ake yadda suka samu dami a kale ita da ɗiyarta, Dada sanye da wata tsalekiyar atamfa da ta sha uban gwaggwaronta ga sarka da ɗankunenta sai walwali suke.
Jerin gwanon motocin amarya ne suka doshi gidan Abdulsalam, Ramla suna zaune suka ji shigowar motocin bayan an wangale get, goɗa ake saki kamar ba gobe, suna ji ake ta rufe ƙofofin motocin.
Ƴan kai amarya sun gama dibdibtun su, suka fito suna yaba gida da ɗakunan amarya, sun fito ya rage daga Hasiya sai Karima, Karima ta sunkuyo tana yi wa Hasiya magana cikin yin ƙasa da murya.
Ta ce
"Muna tafiya ki ɗakko maganin nan naki RABA GARDAMA ki saka, kin ga dai babu wani gyara da kika yi, tun da wanda kika sha sun bi duniyar al,ada, kuma malam ya ce ba sai kin sha komai ko kin yj amfani da komai ba wannan komai da ruwanka ne"
Hasiya ta ce
"Kin ganshi a cikin jakata ina zan yi wasa da shi taɓ, kuna tafiya zan je in saka, ko dai in bari sai mun yi sallar nan ta nafila sai na shiga banɗaki na saka kin san dai kar na je na saka ya ce in yi alwala kin ga kar na wanke, kai yau zai san ya yi aure ai mantawa ma zan yj na san da marigayin mijina rayuwa sabuwa ji ɗakin nan kamar a ƙasar waje" Suka ƙyalƙyale da dariya ta fita da sauri jin ana horn.
Tana fita Hasiya ta tashi tana kewaya ɗakin tana dariya tana faɗin
"Ramla a yau zan mayar da ke salam, kin daina ɗanɗano a wajen miji za ki koma tamkar ruwa saboda rashin ɗanɗano!" Ta faɗa tana sheƙewa da dariya cike da shekiyanci!".
Ango yana can shi da abokinsa Alhaji Abdullahi yana ta bankaɗawa cikinsa maganin maza ya sha sun fi kala biyar, har da na ƙarfi duk son saboda zai koma hannun sabuwar amarya muradinsa ta daɗewa!.
Da suka zo ya musu nasiha da amarya, ya raka shi zai tafi ya ce .
"Ai sai na yi wata uku ina dirzar amarci ba wai kwana uku ba" Suka kwashe da dariya ya ce
"Kai haba dai, ita kuma fa uwar gidan" Ya yi dariya ya ce
"Kash ba ta ita nake ba wannan tanadin amarya ne" Suka sheƙe da dariya.
Yana tafiya ya rufe get ɗin don su Asma,u ma tuni sun tafi saboda dare ya yi, ita kuma tana ɗakinta tana shirin kwanciya ya shiga riƙe da leda bayan ya kwankwasa ta masa izini. Yana shiga ya ajiye a kan madubi ya ce
."Gashi kuma kwa ɗan lasa kaza ce!"
Ta yi ƴar dariya ta ce
"Yanxu haka ina da kaji a freezer to lasawar me zan yi ni ai ba bakuwar kaza bace" Ya yi shiru yana tunanin wane sabon salo ne ta shigo da shi haka ya juya ba tare da ya bata amsa ba.
Ko da ya koma ɓangaran amarya gabaɗaya ya cika da farinciki, ita ma a nata ɓangaran haka ne, ko da ya bukaci su yi alwala su yi sallah, haka ta ɗauro alwala sai wani rawar kai take ko kunyar amaren nan babu, a ganinta ai ba za take wata kunya ba tun da so take ta janye hankalinsa dole sai ta zage dantse.
Bayan sun kammala ɗan lashe lashen kayan amarcin aka dara shirin kwanciya, sai da ta gama saka kayan baccinta masu kaɗan da bambanci da babu ta ce za ta je fitsari, daman ƴar robar maganin tana damke a hannunta, kan gado ya hau, yana faɗin
"Ki kula dai na matsu in fara karɓar saƙonni" Ta murmusa ba tare da ta ce komai ba, shi kuma ya zame ɗan gajeran wandon da ta rage a jikinsa yana jiran fitowarta.
Tana shiga banɗaki ta rufo ƙofar ta zame wandon ta tsugunna ta lakuto maganin nan bayan ta raba a uku, ta nufi ƙasanta ta zambaɗa shi a ciki ta ƙara turawa.
Alhaji da yake kwance rashe-rashe a zuciyarsa yana kissima cewar ba fitsari ta je yi ba wataƙila ƴan dabarunsu na mata za ta yi, kamar daga sama ya jiyo sautin Hasiya ta dage ƙarfinta ta zambaɗa uban ihu ta ce
"Wayyo Allah, na shiga uku!!!"
*NURIYYA*
Bata san wainar da ake toyawa ba, ita dai tana sabgar gabanta ne, yau ma kamar kulluɓ bata runtsa ba haka ta tashi cikin dare ta duƙufa tana yi wa Ya Ammar ɗinta addu,a a akan Allah ya kawo masa mafita ta alkairi.
Yau tana a sati na biyu ne da fara zuwa makaranta gabaɗaya ta mayar da hankali kan karatun ne, misalin ƙarfe biyar da rabi da tawo gidan, a gida ta same shi don tun ana sallar la,asar ya dawo, ta gaishe shi ya mata sannu da dawowa, ta zura masa ido duk ya yi baƙi ya rame ta kalle shi ta ce
"Ya Amma ina Kaka?"
Ya ce
"Nury Kaka ta fita can tsallaken layi barkar haihuwa" Ta yi shiru tana kallonsa bisa tausayawa ya kalle ta idanunsu suka sarƙe da na juna ya ce
"Kallon fa?"
Ta ce
"Ya Ammar wallaho tausayi kake bani, tun da ka siyar da keken ɗinkin ka duk ka zama abin tausayi kuma duk ta dalilina"
Ya yi shiru na ƴan sakanni kamar ba zai ce uffan ba, ya ja dogon numfashi ya ce
"Nury har yau ba za ki gane irin matsayin da kike da shi a wurina ba, zan iya zama bani da komai idan har ke zan mallakawa ko mene ne matukar dai za ki yj farinciki, Nury yanxu bani da burin da ya wuce na samu tudun da zan dafa ya kai ni ga tsira wato na samu makamin da zan riƙe wanda ko bayan kin kammala karatu in aure ki, ki dawo ƙarƙashin kulawata, ina sonki ina kaunarki bana jin zan iya jure rashin ki a rayuwata, da in rasa ki Nury gwara na san na bar duniya ne gabaɗaya, zuciyata da sonki ta taso zuciyata da sonki na raine ta, don haka gwara na fara shirin auren ki kin san hausawa sun ce mai zurfin ido da wuri yake fara kuka!"
Tun da ya ambaci aure ta ji gabaɗaya ya mata dabaibayi da jijiyoyin jikinta, don wata irin kunya ce take mamaye ta idan aka yi maganar aure, ta ɗan murmusa tana kawar da kai gefe ta ce
"Ya Ammar to akwai wanda ya cancanci ya aure ni ne bayan kai, ai ni daman da soyayyarka na tashi tun ban san mene ne so ba, gabaɗaya rayuwata ta ginu ne a kan sonka, ban san kowa ba sai kai, ban san kyautatawar kowa ba sai taka, kai ne kake sadaukar da abu domin ni na samu, kai ne kake haƙura da abu don ka bar min na amfana ina sonka Ya Ammar kuma bana jin shayi ko kunyar faɗar ina sonka a gaban kowa don haka bani da mijin da ya fika, ina maka addu,a in sha Allah za ka samu buɗi na alkairi, wahala za ta kau, daɗi zai wanzu a rayuwar, saboda bayan wuya sai daɗi,"
Tun da ta fara magana ya kafe ƙaramin bakinta mai ɗauke pink ɗin lips, kawai murmusawa yake gani yake tamkar ba da bakin take magana ba.
Tana ɗagowa suka haɗa ido ya kashe mata ido ɗaya ya ɗaga mata giza ta ƙyalƙyale da dariya tana saka hannu ta rufe fuskarta cike da kunya shi ma dariyar yake.
Suna cikin hakan Kaka ta shigo ta same su, itama aka jona hirar da ita tana ta musu tsiya, tana faɗin itama idan aka yi auren ba za ta zauna a wannan tsohon gidan ba da ita za a tafi sabon gida.
A ɓangaren Hajiya Hauwa tun da suka yi magana da Hajiya Mardiyya kan maganar Alhaji Ahmad Jarma mai dollar, a kan auren Nuriyya gabaɗaya ta kasa samun nutsuwa da maganar miliyan ɗarin nan gani take dole ne ma ta san yadda za a yi ta tunkari mahaifin Nuriyya da maganar nan ko don cimma burinta na hana yarinyar karatu.
A ranar bata samu sun yi magana ba, saboda ta rasa ma ta inda za ta fara sai washe gari yana zaune a falonsa ta zo bakinta ɗauke da sallama ta zauna tana masa barka da hutawa, ya amsa ta kalle shi bayan shiru ya gifta ta ce
"Alhaji daman a akan maganar yarinyar nan ce Nuriyya, ya kamata ka yi wani abu a kai, kullum tana fita babu kakkautawa sai ta kai dare bata dawo ba watarana ma ta kwana a titi, ƴan unguwa sai yi da kai ake ana faɗin ka kasa kulawa da ita" Yanayin yadda ta yi maganar sai da ya ji kansa ya sara masa amma bashi da yadda zai yi haka ya daure yana faɗin
"Yanzu mene ne abin yi ni idan ma na ce zan yi tunani kan yarinyar nan wahala nake sha, wani lokacin ma mantawa nake ina da wata ƴa"
Hajiya ta ce
"Kawai tun da ta gama sakandire ka aurar da ita a ƙalla ka damkata a hannun wani riƙonta da nauyinta ka sauke"
Ya ce
"Haka ne ai gwara auren ma da yawon da ba a san inda take zuwa ba"
Wani daɗi ne ya baibaye mata zuciya tana jin tamksr ta tashi ta yi ta rawa, don burinta yana dab da cika.
",Gwara mana, gata yarinyar aljanna ce mai masoya da yawa, har da fa Alhaji Ahmad Jarma mai dollar a masu sonta, sai da ya kira Hajiya Mardiyya ma ya ƙara sanar da ita take faɗa min na ce ai kuwa zan sanar da kai ka ga idan aka aura mata shi gidan hutu ne kuma mai arziƙi ne babu wanda zai ce an mata auren son zuciya!"
Ya ce
"To shikenan in sha Allahu zan tuntuɓe ta"
Hajiya Hauwa ta ce
"Ai kawai bata da wani zaɓi ka faɗa mata cewar aure za ka mata kuma ga mijin da kake so ka bata" Ya amince da duka batun Hajiyar, da daddare yana zaune yana kallo sai ga Hajiya ta shigo ta zauna, ta sake tuna masa ya sanar da ita ta bashi lokaci haka dai ta ɗaga masa ƙafa ba don ta so ba.
Sai da aka yi sati biyu tana bin kansa, har tana faɗar cewar za ta danganta shi da wajen malamai ta sa a kama mata zuciyarsa kan maganar aure, kawai sai gasho da kansa ma ya mata maganar, ko da ya faɗa mata ta ji daɗi.
Washe gari da safe Nuriyya ta shirya za ta tafi makaranta Hajiya Hauwa ta zo kiranta, da mamaki ta take mata baya don ta ga ta nufi ɓangaren mahaifinta. Suna shiga ta samu mahaifinta zaune a kan kujera ta durƙusa ta gaishe da shi cikin girmamawa bai amsa ba amma ya ɗago ya kalle ta, a cikin idanunsa ta ga wata irib ƙauna da baki bai iya furtawa tana iya hango tamkar an katange ƙaunar ne itama sai ta samu kanta da tsura masa idanu gabanta yana faɗuwa. Hajiya Hauwa da ta zauba ta kame a kan kujera ta ga sun zubawa juna idanu a take gabanta ya harba da mugun ƙarfi har zuciyarta ta gama raya mata cewar ba dai laƙanin asirin da ta yi na tsawon shekaru ne ya karye ba har ya fara kallonta yana son ƙwaƙwalwarsa ta yuno mata da ita da sauri murya na rawa ta ce
"Alhaji" Kamar wanda aka tsikarawa alluwa haka ya zabura yana amsawa, itama Nuriyya ta zuba masa ido ganin ya zabura tamkar wanda aka sheƙawa ruwan zafi.
Ta ce
"Kai da za ka faɗa mata saƙon amma ka zauna kana kallonta kamar baka santa ba, Nuriyya ce fa wannn marar jin maganar da bibiyar samari" , Ajiyar zuciya ya sauke ya ce
"Nuriyya inaso ina faɗa miki lokaci ya yi da zan aurar da ke don haka ki fito da miji... Bai ƙarasa ba Hajiya Hauwa ta tashi tsaye daga zaunen da take cikin ɗaga murya take faɗin
"Alhaji kamar ya ta fitar da miji bayan ga miji ya kawo ƙoƙon bararsa a kan a bashi ita, mutumin kirki mutumin arziƙi" ,Nuriyya tun da take a rayuwarta wannan ne karon farko da gabanta ya yi wata irin faɗuwar da ta ji tamkar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito, jikinta gabaɗaya ya shiga karkarwa ta ma kasa gane mai ake faɗa sai dai ta ga falon yana juya mata.
Daga bisani kunnuwanta suka shiga mata amsa kuwwa mahaifinta yana faɗin
"Eh mana ai daman ina nufin wannn ɗin Alhaji Ahmad ɗin ai ita bata da manemi na kirki ma kamar shi duk taron yuyuyu ne"
Hajiya ta ce
"Kawai tun da ba wani abu za a nema a rasa ba kuma ba wani bikin kece raini za a yi ba a ganina kawai ka saka sati ɗaya ko ka hita daga wannan ja maka maganar da take yi"
Alhaji ya ce
"Haka ne" Ya kalli Nuriyya yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa wanda baki ba zai iya furta abin da yake son faɗa ba ya ce
"Nuriyya ki shirya nan da sati guda, za ki zama matar wani ba ƴar wani ba" ,Bata san lokacin da ta tashi tsaye tana girgiza kai ba hawaye suka mata tsinke suka wanke mata fuska, ta shiga faɗin
"Don Allah karku min haka, idan auren za a yi mini ina da wanda nake so" Hajiya kamar za ta kai mata duka ta ce
"Rufe mana baki, ke wanda kike so ai yawa ne da su, wannan kuma mutum ne na gari babba wanda ya san darajar aure inda za ki huta ai gata ake miki"
Alhaji ya ce
"Ki daina kuka " Hajiya a zuciyarta tana raya dole sai ta tashi haiƙan an sake yin farraku tsakaninsu wataƙila laƙanin da aka yi aikin farraƙun ya fara sanyi ne shi ya sa har yake fara tausayinta.
Cike da ɓata rai ta ce
"Ban da ma zamanin nan yara babu kunya ubanki kike kallo kina faɗa masa kina da zaɓinki, to aure babu fashi kuma ki sani ɗan siyasar nan Alhaji Ahmad Jarma mai dolla ne zai zama mijinki" Dumm kunenta ya tsaya cak daga sauraren komai da komai.
Alhaji ya ce.
"Ki tashi ki ba mutane wuri nan da sati mai zuwa za a ɗaura miki aure" ,Da baya-baya ta fara tafiya tana kuka kamar ranta zai fita ta bar falon. Tana fitowa ta nufi hanyar fita daga gidan ma, gidan su Ammar ta nufa ranta a dagule tana tafiya tana share hawaye dakyar take ganin gabanta.
Sallamar da ta yi ma basu ji ba saboda shaƙewa da muryarta ta yi, sai ganinta Kaka da Ammar suka yi ta shigo kamar an jefo ta, Ammar wanda yake kwance tun da ya tashi yau yake jin wani iri kamar dai kasala kamar bashi da lafiya ya rasa mene ne yakr damunsa, ya tashi tsaye hankali tashe yana faɗin
"Nury mene ne? Mai aka miki, ina ji a jikina wani abu marar daɗi zai faru"
Nury tana jin haka ta faɗa jikin Kaka ta fashe da kuka, Kaka ta shiga lallashinta tana bubbuga bayanta.
Kuka take suna tambayarta ta ƙi bada amsa, Ammar wanda yake jin kamar ya fincike damuwar ya mayar kansa gashi ta ƙi faɗa sai kuka take, hannu biyu ya sa ya ɓanɓarota daga jikin kaka ya tsayar da ita da ƙafafunta ya ce
"Nury waye ya saka ki kuka mene ne?"
Bata san lokacin da ta kifa kanta a jikinsa ba ta fashe da kuka, duk jarumtar Ammar yadda ya ji zuciyarsa ta yi tsananin karaya shi ma bai san lokacin da kukan ya ƙwace masa ba, ya san kawai wnanan damuwa ce mai girma da ta shafe ta amma bai taɓa kawowa maganar aure ba ce.
Kaka wacce jikinta ya yi sanyi ta rasa ma mai za ta ce hakan ya sa ta shiga lallashin su har ta samu suka yi shiru, ta rungumo Nury ta zaunar da ita a kan tabarma ta zaunar da Ammar itama ta zauna ta ce
"Nury mene ne wanda ya sa kike kuka, ko hana ki zuwa makarantar aka yi" Ta girgiza kai hawaye suna ci gaba da zuba, Ammar kusa ya kafe ta da ido yana jin wani ɗaci a zuciyarsa na zubar hawayen da taken zubarwa.
Cikin shaƙewar murya ta ce
"Kaka za a rabamu da Ammar" Ammar da Kaka suka zaro idanu ,ta ɗora da faɗin
"Kaka aure za a min nan da sati ɗaya kuma ba da Ammar ba"
Kaka jikinta ne ya ɗau karkarwa shi kuma Ammar kansa ne ya fara juyawa. Kaka ta ce
"Da gaske Nury in ji wa? Innalillahi wa inna ilaihi raji,,un"
Nury ta zubawa Ammar idanu wanda shi ma ita yake kallo ta ce
"Nan da sati ɗaya za a ɗaura min aure da Alhaji Ahamad Jarma mai dolla" Kaka ta dafe kirji da hannu biyu cike da tashin hankali jin wani faɗa wanda ya fi ƙarfin iyawarsu su, Ammar kuma yatsansa manuniya ya nuna Nury da yana son furta wata kalma amma bakin ya ƙi bada haɗin kai, basu ankara ba sai ya yanke jiki ya faɗi daga zaunen da yake, tamkar wanda rai ya bar jikinsa don ba ya numfashi!.
Nury wani ihu ta ƙwala tana yin kansa tana kiran sunansa, Kaka ma haka ta shiga kiransa cikin tashin hankali, Nury ganin ba ya numfashi ita ma sai ta yanke jikin ta faɗi.
Kaka tana tsakiyarsu tana kallonsu cikin tashin hankali tana rafka salati tsoron da take ji guda ɗaya shi ne kar dai rai ya yi halinsa su duka su mutu wato daya ya bi ɗaya!.
*HAJIYA NAJA,ATU*
Sai da ta je har ɓangaren Goggo cike da gadara ta zauna a kan kujera, lokacin Goggo tana cikin bedroom tana buɗe ƙofa sai ta ga Hajiya Naja tamkar an jefo ta cike da mamaki ta ce
"To Naja ce yau a ɓangaren nawa?"
Hajiya Naja,atu ta kauda kai gefe ta yi wata dariyar raunin hankali ta ce
"Eh ni ce Hajjaju Goggo" Ta faɗa cike da sheƙiyanci. Goggo ta ƙarasa kan kujera ta zauna tana faɗin
"To sannu da zuwa"
Hajiya ta ce
"Na zo isar da saƙo, ko dai in ce na zo in jajanta miki"
Cike da mamaki Goggo ta ce
"Jaje kuma? Jajen me?"
Hajiya ta ce
"Jajen ɗanki bai ji maganarki ba mana, kin saka doka ya saka ƙafa ya yj datali da ita, tun muna jira har muka gaji da gafara sa bamu ga ƙaho ba" Hajiya ta faɗa tana ƴar dariyar rainin hankali don ta cusawa Goggo haushi.
Goggo a zuciyarta tana ganin Naja bata da hankali amma a fili sai ta sanyaya murya ta ce
Kin san komai sai Allah ya yi, Allah ne da lokaci ba mutum ba"
Ta miƙe tsaye ta saki ƴar dariya ta ce
"Wannan kaɗai ya isa ya sa ki gane ni dashen Allah ce, kuma babu mai ɓanɓareni, sannan zama daram kuma haihuwar ba zan yi ba" Ta faɗi hakan tana tashi tana tafiya da gadara ta je ta kama handle na ƙofar za ta buɗe ta juyo ta kalli Goggo ta taɓe baki.
Goggo ta ce
"Ta yaro kyau take bata ƙarko"
Hajiya ta ce
"Hehehehe ta babba kuma faɗa ake ba a cikawa sai cika baki" Tana faɗar hakan bata jira cewar Goggo ba ta buɗe ƙofar ta fice.
A ɓangaren direban da ya kai Hajiya makabarta, tun lokacin da ta kama hanyar don zuwa ta aiwatar da aikin shi ma ya bi ɗaya hanyar amma ba inda ƙofar shiga makabartar ba. Hajiya ce ta bi ta hanyar shiga makabarta, sauri yake kamar ya ci da ka haka ya ƙarasa, taimakonsa da Allah ya yi yana zuwa ya samu wani waje inda katangar ta tsage sosai ma ana iya hango cikin makabartar. Laɓewa ya yi a kan idanunsa ta aiwatar da komai, sai da ya jira ta kammala kafin ya zuga da mugun gudu kamar zai tashi sama, yana ƙarasowa wajen motar ya shiga ya zauna kenan jim kaɗan sai gata ta dawo, don bata saurara a maganarsa da ta ji muryarsa da alamar hakin gudun da ya yi.
Bayan ya kaita gida, da ya fito masallacin asuba ana salancewa ya ja motar ya nufi makabartar a sukwane sai da ya tabaatar babu wanda ya ganshi gudun matsala kar a je a ganshi a zaci wani abun zai yi ko a ce sassan jikin gawa ya zo tona. Cikin sauri ya tone ramin da ya gani ta yi ta saka ya fiddo abin mutum mutumin yana cike da mamaki haka ya mayar da ƙasar ya rufe ya taso da sauri sauri ya baro makabartar ya nufi inda ya ajiye motar ya saka abin a aljihunsa yana mamakin irin yadda wasu mutanen suke ɓata a neman duniya!.
Sai bayan sun koma gida ya saci hanya ya je ya sayi ashana ya ƙone abin ƙurmus!.
Su Mama Magajiya duk abinnnan da ake basu san da maganar auren Alhaji da Falmi ba, don yanzu mutuntawa suke shi da Auntyn Falmi ita ya ba kuɗin kayan lefe ma suka je suka haɗo komai da komai na girma, shi ma babansu da suka gani a waya ya ce ba sai an kai Maidugurin ba kawai a barsu a gidan Aunty nata. Ana jibi ɗaurin aure suka tafi da abokansa suka sauka a hotel kasancewar karfe goma ne ɗaurin auren, ya sanar da Hajiya zai yi tafiya ita dai bata kawo komai ba tun da sai an bar maganar aure komai ma ta famjama fanjam.
Maiduguri Falmi ta koma tun ana saura kwana uku, aka shiga tsuma amarya ban da tsumatan da Auntyn ta ta yi don har Aunty suka koma saboda bikin duk da ba wani abun bidi,a za a yi ba saboda babansu ya hana. Gyaran amarya da turaruka kana doso inda Falmi take za ka ji kamar an yi ɓarin turare. An mata ƙunshi maroon ta fito a amaryarta sak gashin nan ya sha gyara har gadon bayanta sai sheƙe yake a inda aka bi shi da ƙananan kitso.
Ana ɗaura aure aka taho da amarya, da motocin da wasu daga cikin abokansa suka tafi da su da za su je ɗaurin auren, sai mota ɗaya da take ɗauke da kayan tuntum da kafet da sauran abubuwan.
A gidan Aunty ƴan kawo amarya suka suka yada zango inda ango ya wuce gida.
Goggo sai da la,asar sakaliya ta dokawa ƴar uwarta Mama Magajiya waya take sanar da ita yau fa aka ɗaurawa ɗanta aure a maiduguri, Mama zaninta har faɗuwa yake tana kamowa tana ɗaurawa, Allah ya sa ma ita kaɗai ce a gidan su Umar sun fita, dakyar ta samu cewa Allah sanya alkairi. Tana kashe wayar ta shiga kiran wayar Ruma wacce tun safe ta tafi gidan kawarta wuni bata ma san halin da ake ciki ba, Mama ta doka mata waya ta ɗaga tana faɗin
",Uwata ta kaina"
Mama ta ce
"Ke dawo hayyacinki dan ubanki, Muhammad an ɗaura masa aure a maiduguri" Cinyar naman da take hannunta ce ta suɓuce daman abinci suka ci ita da kawar kasancewar baa kammala abincin da wuri ba, cike da tashin hankali ta miƙe tsaye bata ma san ta goga miya a jikin rigarta ba ta ce
"Mama ki bar irin wasan nan""
Mama ta ce
"Wasa ni na ce miki wasa nake miki, to wallahi Goggonsa ta kirani a waya yanzu take faɗa min har da cemin yau amarya za ta tare!"
Ruma ta ce
"Na shiga uku na lalace an shammacemu"
Mama ta ce
"Rufewa mutane baji sakaryar banza da wofi, bake kika ce ke yake jira ki gama idda ba, yau saura kwanaki kalilan ki yi idda amma gashi ya yi aure ya barki da sakakken baki"
Ruma hannu a ka take runtuma kukan takaici kawarta tana ta tambyarta mene ne, ta kashe wayar bayan ta ci alwashin wallahi ko ana muzuru ana shaho sai ta shiga gidan nan a mace ta uku!.
A ɓangaran gidansu amarya, tana zaune gaban yayun mahaifinta suna mata nasiha, tare da jaddada mata riƙon addu,a mazaunin makaminta, tana ta gyara kai tana ɗan kukan, sai baya ta gama ta sake wanka, aka ƙara bata ruwan turare ta yi wankansa, aka ɗakko wasu turarukan ana ta turarata, ga na kabbasa da ake turara kayan da za ta saka, aka feshe mata kai da turarukan gashi, wata madara mai ɗumi tana ɗauke da sinadarai yayar mahaifinta ta bata ta kafa kai ta shanye. Sai da aka gama gabaɗaya shiryata, aka bata wani dunƙulallan turare a kan garwashi akance ta shiga banɗaki ta yi tsugunno. Bayan ta fito aka bata kayanta ta saka, aka naɗa mata laffaya coffee mai fulawa maroon, aka sake fesheta da turaruka ana ta guɗa.
Motoci ne reras a kan hanyar gidan Alhaji Muhammad ɗauke da amarya Falmi da ƴan kai amarya, wanda direban da yake cikin motar da take a sahun gaba shi ne yake musu jagora duk inda yabyi sauran motocin suna biye da shi, sai guɗa suke cararawa.
Hajiya tana zaune a falonta ta harɗe ƙafa tana sanye da wata doguwar riga duk ta cukurkuɗe kasancewar bacci ma ta yi ta tashi kan na nata duk ya kama gabansa kasancewar kan a tsefe babu gyara. Waya suke da Mom, Mom tana jaddada mata ta ci gaba da tsulatsiyarta ita kaɗaice dole ya yi haƙuri da ita sai yadda ta yi bai isa ya auri wata ba don ya huce takaici, ko a haifa masa ƴaƴa haka zai dawwama, ita kuma wani daɗi yana ratsa ta tana ƙara tabbatarwa da Mom cewar ai yanxu ma ta fara gasa masa aya a hannunsa.
A daidai wannan lokacin da suke waya, a sannan ne gwanon jerin motocin suka yi wa ƙofar gidan Alhaji tsinke, mai gadi ya ji horn ya tashi da sauri ya wangale get daman Alhaji ya faɗa masa baki suna nan zuwa lokacin da zai fita.
Yana buɗewa ya ga motocin da yawa ai kuwa ya jingine get ya koma ya tsaya motocin suka fara shigowa cikin gidan a jere. Sai ƙaran guɗar mata ne yake tashi
"Ayyiriri yiriiiiii"
Goggo da take zaune a ɓangarenta ta ɗaga hannu sama ta ce
"Alhamdulillah, Allah na gode maka kai ne abin godiya, kai kaɗai ka cancanci a gode maka".
Sai da motocin suka gama shigowa gabaɗayansu, har lokacin ana guda, sannan suka shiga buɗewa suna fitowa, ƴar uwar mahaifin Falmi da wata yayarta su ne suka saka Falmi a tsakiya sun kama hannunta, suna ta sanyata yin addu,a.
Matan riƙe da kaskon turaren wuta a hannayensu an zuba turaruka masu ƙamshi hayaƙi yana tashi.
Hajiya Naja,atu da take waya ta ji shigowar motoci da yawa ana ta horn, sai dai guɗar da ake yi ce ta ɗauki hankalinta, da farko ma ta ɗauka a waje ne take jiyowa sai da ta saurara da kyau ta ji a cikin gidan ne.
*Book 1 ya ƙare book 2 1k ne za a biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta ****
*Pls shaidar biya za ki tura min idan kin sa kuɗin. Ngd sai mun haɗu a paid grp domin book 2 mu ji ya za ta kaya da kowane ɓangare.* *Kar ki bari a yi cakwakiyar nan babu ke don akwai gurmi* 😂
MAMAN AFRAH ***