THE THRONE OF THORNS

LEEKAH

by @maryam730



MASARAUTAR TAAZEERA

Masarauta ce mai girman gaske, gari guda ce. Daga wajen ta, farkon ginin kawai ake iya hangowa, ƙarshensa ya ɓace bayan dogayen gine-gine da manyan bangarorin masarautar.
It was an ancient royal estate brought into the modern world. An gina Masarautar Taazeera tun shekaru da dama da suka shuɗe, kuma generations of rulers had continued expanding it, preserving the traditional architecture while adding modern technology and unimaginable luxury.
Daga waje, manyan arches, dogayen pillars da tsoffin zane-zane suna ɗauke da tarihin sarautar. Amma an modernize komai, merging traditional royal architecture and modern engineering, which gives a perfect collaboration.
Babban gate ɗin ya fi tsayin mutane goma. Blue-black ne, an kawata shi da silver ornaments, sai walƙiya da ɗaukar ido suke, kamar diamond. Dogayen fences ne suka zagaye masarautar, blue-black da silver, sun miƙe har inda ido ba zai iya gano ƙarshensa ba, yayin da CCTV cameras da security systems suke ko'ina. Even before entering, you could tell this was not an ordinary palace.
Manyan black SUVs, luxury sedans, da armored vehicles suna ta shigowa da fita, yayin da guards ke tsaye a ko'ina, which proves that powerful people had gathered behind those walls.
Da ka shiga cikin masarautar, sai ka ji kamar ka bar wannan duniyar ne, ka shiga wata.
Blue-black and silver dominated everything — dogayen gine-gine, grand halls, royal residences, chandeliers, da manyan courtyards. Wasu buildings tsofaffin gine-ginen kakanni ne, wasu kuma completely modern, cike da fasahar da ordinary people ba za su iya fahimtar ta ba. Gaba ɗaya, ginin Palace ɗin an yi shi da blue-black da silver, which was screaming of power and luxury — shi ya sa ake kiranta da "DARK PALACE."
A cikin masarautar, maza da mata ne sanye da blue royal uniforms suna ta zirga-zirga (daga ganin su, kasan fadawa ne da bayi), yayin da busar algaita da drums ke cika iska da wani irin heavy royal aura. Ancient sounds, modern power, generational wealth.
Gaba ɗaya, wannan baa shiga cikin masarautar ba ne kawai — wanda ya haɗa da hundreds of parts, da part ɗin bayi da fadawa da gidan sarki.
Ta wajen kuma, Babbar Fadar Masarautar Taazeera ce, sai manya-manyan ɗakin taruka, historical rooms, makarantu, asibiti, gidajen wasu bayin da fadawa, kasuwa — duniya guda, babu abinda bazaka samu ba.
Masarautar Taazeera ta rabu gida uku: EXTERNAL PALACE, da INTERNAL PALACE — wacce ta rabu gida biyu, inda jinin Taazeera ke rayuwa (Royal Internal Palace), da kuma inda bayi da sauransu ke rayuwa.
Babbar fada, ta cika daɗam sakamakon naɗin sarauta da ake yi na lokaci guda. Ba a gano komai ba, saboda yawan mutanen da suka zagaye wanda ake naɗawa.Sai kuma tashin muryar Sarkin gida dake shelar cewa, "An tabbatar da Yarima ZAHRAAN kan kujerar Chiroma! Zaki bawa maza tsoro! Ingarman namiji firgita mazaje! Magajin Taazeera! Goben Taazeera! Jinin Taazeera! Alfaharin Taazeera! Jigon Taazeera! Zomon zaki wanda ba a haifa biyu ba! Dutsen da babu iska mai iya girgiza shi!"
Wani tsoho ne, shi ma ya taso yana ɗauke da wani zobe a farantin zinare, yana zuwa cikin cunkoson. Mutum ne a zaune, ya ɗurƙusa kansa ƙasa, wanda ya hana a gano fuskarsa. Zuwa yayi, mutumin, ya sa masa wannan zoben mai masifar ɗan banzan kyau, sai ɗaukan ido yake. Nan da nan a ka ɗauki kabbara...
Kafin wani tsoho ma ya taso, yana ɗauke da wani rawani da aka yi shi da yadi mai masifar tsada, da ke kan fatantin azurfa. Yana taku uku da ɗaukan rawanin, bai ma kai gurin ba, kawai ya yanke jiki, ya faɗi matacce, hannu ɗaya riƙe da rawanin dashi yayi DARK BLUE............   
______________________________

Fitowa Atti tayi cikin jalbab fari har ƙasa, da jakarta black, da takalmin ta Crocs black, tayi kyau sosai, MashaAllah. Sallama suka yi da Ummu, suka fita. Kamar kullum, mai napep suka tara, inda ya kai su Bright Star Academy. Sauke su yayi, gaba ɗayansu, a ƙofar makarantar. Biyan shi Atti tayi, suna ƙarasawa gate ɗin makarantar. Haɗuwa suka yi da Antin su Ammar, mai kirki, wacce ta yi directing ɗinsu har ofishin proprietress ɗin.
Ciki Atti ta shiga, inda su kuma suka tsaya a bakin ƙofar ofishin. Wata ƙatuwar mace ce, a zaune akan kujera, tana shan kwaskwas a kanta. Tana ganin Atti, ta haɗa rai. Gaisawa suka yi, sai wani daddaƙirewa take, wai kar ma a tambaye ta alfarma. Atti ce ta fito da kuɗi daga jakarta, tana ƙirgawa. Nan da nan matar ta saki fuskarta, ta fara washe baki, ko kunya. Miƙa mata kuɗin Atti tayi, karɓa tayi, ta sake tisawa, ganin sun cika cif — yasa ta ƙara washe baki, tana rubuta mata rasit ɗinta. Zubar da zance take, tana ta yabon ƙoƙarin su Ammar da Husna, sai bori kunya take. Sallama Atti tayi mata, tayi ficewarta, tarar da su Ammar tayi a bakin ƙofar, inda tambaye su, Ummu ta ba su kuɗin komawa? "Eh," suka amsa mata, kafin ta ciro ₦200 ta ƙara musu. Karɓa suka yi, suna mata godiya, kowa ya nufi ajinsu.
Ficewa tayi daga makarantar, napep ta kuma tara, tace, "mai UNILAG." Hawa tayi har ƙofar makaranta ya kaita, ta sauka, ta biya shi kuɗinsa, ta nufi cikin makarantar. Tun daga ƙofar makarantar, suka fara gaisawa da mutane. Ofishinta ta nufa, saboda sai ƙarfe 10 suke da class. Zamanta bai daɗe ba, sai ga Fatima ta shigo, sai ga Nadiya ma haka, suka zauna suna hira, suka ƙarasa tsara yadda meeting ɗinsu da DEAR zai kasance.
Ƙwanƙwasa ƙofar akayi daga waje, permission Nadiya ta bayar, sannan aka shigo. Musty ne ya shigo (shine mai kula da ƙorafe-ƙorafen ɗalibai, ya kawo su gaba). Zama yayi, yana cewa, "Da girman kujerar ki, President, kwana biyu ina ta shigowa bakya nan." Atti ce tace, "Wallahi Musty, abubuwan namu sai a hankali, Allah ya sa dai lafiya, dan na san ganinsa akwai wata a ƙasa." Gyara zama yayi, yana ƙara zama serious, yana cewa, "Queen, akwai matsala. Kam dan ƙorafe-ƙorafe sun yi yawa daga ɓangaren mata, akan ana haurowa hostel ɗin mata da ake yi cikin dare, a shaƙa musu wani abu, a yi abinda za'a yi, duk basu sani ba. Basa dawowa hayyacinsu sai bayan komai ya gama faruwa. Da farko bamu ɗauki abin serious ba, amma yanzu kam ya girmama sosai — dan akwai wata 'yar level 3 an yi mata ciki, yanzu haka iyayenta sun zo makaranta suna cewa bazasu yarda ba, haka ma hukumar makaranta suna cewa ba a makarantar su ya faru ba, 'yar su ce yawon banza. Yanzu dai haka suke, so suke su kori yarinyar ma gaba ɗaya. Toh jiya kuma aka ƙara kawo min wani ƙorafi, wata ma yanzu tana asibiti sakamakon aikace-aikacen da aka mata, na yoyon fitsari, nason ka ma ta."
Shiru gaba ɗaya ofishin ya ɗauka, ana sauraron Musty har ya gama bayaninsa. Magana Atti zata fara, amma ta katse sakamakon knocking ƙofar da akayi. Salman ne ya shigo, gaggaisawa akayi, kafin su ɗora da tattaunawar da suke yi, da yadda ya kamata su shawo kan matsalar.
Sai wajen 9:45 suka tashi, akan ƙarfe 1:30 zasu sake haɗuwa anan, su tafi gurin DEAR. Tashi Atti da Fatima suka yi, suka ƙarasa department ɗinsu.
Da ƙarfe 10:00, lecturer ya shigo theatre ɗin. Lecture ya fara, kafin, nan da awa ɗaya, ajin ya ɗauki zafi sakamakon zazzafar muhawarar da ake yi akan mulkin soja da mulkin dimokraɗiyya (democracy). Tsayar da lecture ɗin akayi saboda lokaci ya cika, akan za'a ɗora a aji na gaba.
Atti da Fatima ne na farko-farko fitowa, inda suka nufi motar Fatima, suka ɗauko lunch ɗin da ta taho musu da shi. Ofishin suka koma, suka ci abinci, da yin sallar Azahar saboda har ƙarfe 1 ta shige. Zama suka yi, suna hira, kafin su Nadiya suka shigo. Rankayawa suka yi, nufin ofishinsa, inda messenger ya musu ido, suka shiga.
Meeting suka fara, inda suka tattauna abubuwa masu muhimmanci da kuma shawarwari, damuwar ɗalibai, da yadda za'a shawo kansu, da abubuwan da ba'a rasa ba. Tun ƙarfe 1:30 suka fara, sai da aka fara kiran sallar la'asar, suka fito, inda mazan suka yi masallaci, Nadiya ita ma tayi gaba, Atti da Fatima suka koma ofishi don yin sallar la'asar.
Bayan sun dawo daga ofishin DEAR ne, suka yi sallar la'asar, shirin tafiya gida suka fara kamar kullum. Fatima ce ta kalli Atti, tana cewa, "Bestie, dama ay yau tare zamu tafi," ta faɗa direct don kar Atti ta kawo wani uzuri. Girgiza kai Atti tayi, tana mamakin wannan ƙarfin halin, tace, "Naji." Fatima kuwa, ganin ta samu shiga, ta ɗora da cewa, "Uhmm, amma don Allah, zaki rakane ni gidan wata friend ɗin Moma, zan karɓo mata wani saƙo." Atti ce ta yi saurin girgiza kai, tana cewa, "Kema kin san ba zuwa zanyi ba ko? To, ki bar ma wannan zancen tun wuri, dan babu inda zani." Fatima ce ta maimaice, ta dinga haɗa ta da Allah, tana roƙon ta, kafin Atti ta yarda da ƙyar. Huh, ajiyar zuciya Fatima ta saki, tana cewa, "Ke dai wallahi, wannan mijin ki ya shiga uku ace mutum sai taurin kan tsiya." Atti ce ta harareta, tana cewa, "In ba ki yi wasa ba yanzu, zan fasa sai kiga taurin kan gaske." Fatima ce ta yi saurin ɗaura hannunta akan baki, tana cewa, "Tuba nake, na jenye kalamai na."
Inda Fatima tayi parking motar ta ƙirar Maybach, suka nufa. Shiga motar suka yi, inda suka fita da gudu. Lekki Phase 1 suka nufa, suna tafe, suna hirarsu cikin nishaɗi.
Parking suka yi a ƙofar wani luxury flat house irin ginin turawa. Fatima ce ta kalli Atti, tana cewa, "Fito, mu shiga." Atti ce ta ce, "Ina ɗin tabdijan?" Nan ma dai haka, Fatima ta kuma lallaɓa ta, da ƙyar ta kuma ci nasara — haka suka fito, suka shiga cikin gidan, da ke da gadi wanda ya san Fatima sosai, kuma ya san zuwanta. Direct, sashen matar gidan suka nufa, Hajiya Falmata. Da sallama suka shiga cikin palour ɗin, Bafulatanar tsohuwa ce, a ƙalla za tayi shekara 90, a zaune, da wani farin gilashi a fuskarta, da jarida a hannunta — da ka ganta, kaga goggagun 'yan boko. Sai wani ɗan farin saurayi a gefe, wanda tun shigowarsu, idonsa akan Atti yake, ko ƙiftawa bai yi ba.
Amsa sallamarsu ta na cewa, "Ah ah, yau Fatima ce a gidan nan? Kar dai mafarki nake." Ƙarasowa ciki, suka gaishe. Amsawa tayi, tana kallon Atti — irin kallon "ita kuma wannan, daga ina?" — kafin ta taɓe baki, ta ɗauke kanta, tana mayarwa kan Fatima, tana tambayarta akan mamanta. Ita kuwa Atti, tun kallon farko da tayi wa matar, taga kamar tasanta, amma bazata iya tuna a ina ta santa ba.
Mai aikin gidan, Hajiya Falmata ta ƙwallawa, tana kira, "Miemie, Miemie!" Wani ƙatoton gardi ne ya fito, Inyamiri, sai karairaya yake, yana wani zuƙe murya, yace, "Na'am Hajiya, gani." Hajiya Falmata ce tace, "Kawo wa baƙin mu ruwa mana." Cikin sauri, sai wani murguɗe-murguɗe yake, haka ya koma, abin takaici, ya ɗauko musu ruwa da snacks, ya kawo musu.
Shi kuwa wannan saurayin, har yanzu kallon Atti yake, har kowa ya lura. Ganin hakan yasa Fatima ta ce wa Hajiya Falmata za su tafi, dan tasan halin kayarta, yanzu za ta iya cewa, "Malam, lafiya." Hajiya Falmata ce tace, "Tun yanzu? To, bari in ɗauko miki saƙon." Ɗaki ta shiga, ta ɗauko mata wata leda, ta ba ta. Sallama suka yi mata, suka fita.
Tafiya suke a compound, Fatima sai tsokanar Atti take, tana cewa, "Ohh, su bestie ma, an yi goshi! Ke, kinga yadda ya dinga kallon ki kuwa, kamar ya samu TV. Ko ɗaya ke ba, laifin shi ne ba — gwanda ya baiwa idonsa abinci" — ta ƙarasa faɗa, tana ƙyalƙyalewa da dariya a karo na ba adadi. Atti, da ta gama ƙulawa, ce ta mata banza.
Sun kusa kaiwa bakin gate, kawai suka ji wata siririyar murya ta ce, "LEEKAH..." Dakatawa Atti tayi, amma ta kasa juyowa. Wani abu ta ji ya taso mata a wannan — zuciyarta ta fara bugawa da sauri, da sauri. Wani ɗinki a zuciyarta na ƙoƙarin farkewa... wannan muryar ce, dan bazata taɓa mantawa ba...
...end of chapter 8... written by Muraimaa Naabba.....