AMATULLAH

Chapter 3

by @ameerahfarouk

Haka muKa Kama hanya muKa tafi, baba naruke da hannuna muKa cigaba da tafiya muna tafe munata labarinmu har muKa isa maKarantar . aKa hadani da wata mata tadauki sunana awani Karamin littafi Kuma ta dauka measurement dina aKace sai next week uniform din zaizama ready . baba yayi masu godiya wani yaro yazo wucewa aKa Kirashi aKa cemashi ya raKani Nursery one , har munjuya sai baba yatuna da bai bani Kudin break ba . naira dari ya fiddo yabani na amsa nayi godiya .


"Kiyi hakuri Amatullah nazaci zamu zo nan amachine gashi Kuma Kudin break dinki Kawai nadauKo Kisiya wani abun kici Koda na naira saba''in ne sai Ki hawo express KiKoma gida da sauran chanjin , amman ya sauKeKi aKan corner Kada ya isa daKe aKofar gida " baba yacemani tare da cewa "Allah yabada sa'a " na amsa mashi " Ameen baba in sha Allah ni zani rukayin na daya a ajinmu " baba yace "Allah ya yadda Amatullah Kedai Ki dage da addu'a da Karatu Kinji Koh " 


dagama shi Kai nayi muKa tafi ina biye abayan yaron da zaya raKani zuwa class din namu har mika isa .

 
 Shiga mukayi cikin ajin sai naga classmates din nawa duK nafisu girma Kuma sai na lura da duKansu Kallona suKeyi suna dariya.


"yaya sunanKi ? teacher n da na iskece ta tambayeni . amsa nabata da cewa "sunana Amatullah" 


kara nunama classmates din nawa ni tayi takara da cemasu "yau nafara zuwa " sannan tace Kowa yatashi ya fadamani Sunanshi ta yanda zamu zama friends ni dasu , suka tashi sunata gayamani sunansu one by one suna hadawa da dariya cike da rainin hankali . 


nikuwa banda binsu da idanu babu abunda nakeyi . teacher tace mani insamu extra seat inzauna saboda Kowa da seat dinshi .


samun seat nayi nazauna ta cigaba da yin lesson,time din da  tagama Koyawa ne tayi tambayar "Kowa yagane?" Sauran suKace sungane tasako mani lesson din tun daga farko saboda ba dani aKa fara shi ba . 


 Time din breaK yayi aKayi, breaK time din tashi yayi aKa tashemu kowa yatafi gida . 


tun ranar da nafara zuwa school dinmu classmates dina suKa dauKi Karan tsana suKa dauramani , suKa wareni basuyin Komai dani , niKuma abun sai yaruka damuna duK da tsanar da suKa yimani bai sa nadena Karatun ba .

 
 Inna Kande Kuma babu abunda tafasa saKani a ayyuKan da taKe sani .daa duK asuba taKe tadani bacci amman da nashiga school tabillo da wani sabon salon tashina tun Kafin asuba . 


idan nafiddo Assignment zaniyi sai ta Kwace littafin sannan Kuma ta KirKiro mani wani aiKin tace sai nayimata shi aloKacin . haKa zani Kuma tashi inyishi babu yanda na iya . 
 

Dibar ruwa Kuma shima ban fasa yinshi ba haKa zani bi hanyar deboshi ga nisa ga Kuma uban layin da naKe isKewa agurin . haKa naKe haKura har sai layin yazo Kaina sannan . idan Kuma zalumcin manyan ciKinmu yatashi sai su tattare gaban layin su tutturemu suce wai sun rugamu zuwa gurin . haKa zamuyi haKuri har sai sun gama diba sannan mu diba . 


ahaKa naKe dibar ruwan ina Kaiwa gida sannan ingama inKama hanyar school intafi akasa . shiyasa Kullum cikin maKara naKeyi babu Kudin breaK, ba yin breaKfast babu Komai . wanKa daman sai idan nadawo daga talla naKe yinshi shima ba Kullin ba idan yan abun inna Kande  yatashi sai tace bazaniyi wanKa ba in Karar mata da ruwan gida Kuma bafita naKeyi ba . baKuma tabari baba yabani Kudin break . 


har schoolbag dita inna Kande Ke bi taduba taga Ko baba yasaKa mani Kudi aciKi . baKuma ta barina muzauna da baba mu Kadai atsakar gida saboda Kar ma yasamu damar bani Kudin break asace ba tare da tasani ba . 


 Tallar fanke shima ba denawa nayi ba saima abunda yayi gaba . Kullum idan nadawo daga school abunda nake cin Karo dashi Kenan Katon plastic bucket din fanKe da yaKe jirana . abinci Kuma bazani  cishi ba har sai na saido fanken tas sannan . ga Kuma bulalar da zani sha idan ban saido shi duKa ba . 


 Bani taba manta ranar da inna Kande tafara dauramani tallar fanke . ranar baba ne yadawo daga Kasuwa agajiye . sallama yayi muKa amsa mashi atare . babu inda idanuwan baba suKa Kai sai Kaina da naKe durKushe gaban inna Kande da taKe Kokarin daura mani katon plastic bucket aKaina .


 "aiKenta zakiyi ne ?" baba ya tambayi inna Kande . 


"wane aiKe? fanKene zata ruka Kaimani chan baKin Kasuwa saboda nafara gajiya da zaman banzan da taKeyi aciKin gidannan"amsar da inna kande taba baba kenan. 


"Kiyi hakuri sai naga boKitin nan Kamar yayi ma Amatullah girma gata Kuma mace sai naga Kamar yafi asamu almajirin da zaya ruka KaimaKi shi Koh?" Baba yafada  atsorace muryarshi kasa kasa . 


afusace inna Kande tace daKata malam ba shawararKa naKe nema ba fanKe Kuma ta runka Kai shi Kenan har sai sanda da Kaina naga damar ta dena sannan!" 


ciKe da tausayi na da baba keyi yajuyo ya Kalleni ya girgiza Kanshi ya karasa dakin shi ya daga labule ya shiga ciki . 


ni dai tsaye naKe dafe da bucket din da ya runjayeni "zonan munafuka tsayawama KiKayi Kina Kallona Koh ? ana magana Kina Kallona munafuKa Kawai wuce Ki Kama hanya Kitafi !" inna Kande tafada mani tare da Kwatsa mani tsawar da tayi . 


Kalmar munafuKa Kuwa sai da ya zauna mani akwalwata. kokarin juyawa in nufi hanyar  fita nayi ban anKara ba sai naji inna Kande ta fizgoni har sai da bucket din da yake Kaina yadan yi tangadi Kamar zai fado . hannu dayan da bansa na dafe bucket din bane nayi sauri nasa na taroshi dashi . 


matsowa tayi da fusKarta Kusa da tawa tare da cemani  "Kibar ganin ubanKi yayi magana kinsan shi Kanshi bai isa ba ballantana Ke koh !?" sannan tahada da yimani concrete warning " wlh Amatullah KiKa bari KiKa dawomani da Koda fanKe guda dayane sai jikinki ya gayamaKi sai Kin kwammace daman baKi dawo gidannan ba, wuce Ki Kama hanya Kitafi munafuKa Kawai" najuya nafice da saurina saboda nasan sauran idan na tsaya .


 HaKa naje nayita yawona da fanKen babu wanda yasaya, wasu ma Ko Kallona basuyi Ko nayimasu magana ma basu Kulani . ga maganganun inna Kande da sukayita dawomani akwalwata. 


wata majalissa da nawuce sai naji wani aciKin su yana cewa "wlh wasu iyayen basu san ciwon yayansu ba , yanzu Ku Kalli waccen yar karamar yarinyar har anfara aiKen ta da marKade mai uban yawa haKa aKanta !" sannan yaja dogon tsaKi  tare da cewa"Allah ya Kyauta" shi dauKarshi aiKena aKayi da marKade saman Kaina . 


nacigaba da wucesu  naKuma yita tafiya har nagaji ba'a saya fanKen ba . haKa na nufi hanyar gidanmu inata sake saken ta yanda zanKoma ma inna Kande da fanKen da Ko daya ba'a saya ba . wata zuciyar tana rayamani insamu Kwata in watsar dashi inKoma incema inna Kande Kudin ciniKin sunfadi wata Kuma nacemani inKoma dashi Kawai . 


gajiyar da nayine da yunwar da ta isheni ce yasa nayi deciding Komawa gidan da fanKen Kawai . haKa nayita bata loKaci har sai da duhu yafarayi sannan har aKayi sallar magrib aKa gama banKoma gida ba saboda fargabar  irin haduwar da zanyi da inna Kande. 


Har nagaji dai nakoma gidan shigata Kenan na isKe inna kande tsaye abaKin Kofa tana ruke da katuwar dorunarta da alamu dai ni take jira indawo . 


dandanan gabana yafara cewa "DARARAM !" saboda kwata kwata banyi expecting ganin inna Kande agurin ba . 


Kallona tayi from head to toe tareda kara Kallon hannuna da yaKe dafe da bucKet din fanKen da ya runjayeni "Amatullah maimaKon inga Kin dawomani da boKiti ahannu alamun Kin saido tallar da nadaura maki sai inga Kin dawomani da shi yanda na dauramaKi shi ?"


karasowa tayi dai dai inda naKe daKanta , taKai hannunta ta sauKe bucKet din ta ajiyeshi gefe sannan tabuga kirji tare da cewa " ni zaKi yima asara Amatullah !?" 

Nikuwa banda KuKa babu abunda naKeyi ga jiKina da yaKeta rawa . dakyar nasamu nabude bakina lips dina na rawa tareda cewa" Kiyi.. hakuri.. inna.. wlh.. naje.. basu.. si..ya.. ba!" toh wlh yau sai namaKi abunda Koda da Kudi gobe bazaKi Kara yarda Kidawoman da talla ba !" inna Kande tafada afusace .