HARAMTACCIYAR GADA

CHAPTER 11

by @hafnancy

*HARAMTACCIYAR GADA.*

_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}*_

*NA*

*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*


*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*

*BOOK 1*
    
 *Page 11.*

"ku ji min 'yar ballaja'u, daga taimako sai abu ya koma na cin mutunci?" Azagwai ta furta bayan sun gama waya da Jidda.

"Sai kace idan aka tashi gwangwajeta da mazajen kuɗaɗe za ta tuna dani ne da take wani manna min hauka mtswww ai wallahi tayi kai, kin yi maganin gobe."

Ita fa nan a tunaninta gani take Anty Hadizan ta karɓi hoton Jiddan ne don ta haɗata da wani mai maikon.

"Azagwai ke kuma da wa? Na ji kina faɗin tayi kai?"

Wata me suna Zeenatu da ta faɗo ɗakin ne ta jefo mata tambaya. Sai taunar cingam take na rashin ɗa'a irin tasu ta 'yan bariki.
   
Azagwai da ta yi wani fuu! da ita kamar za ta fashe tsabar takaici, tasa hannu tana gyara zaman kallabinta wanda ta karyo shi har gaban goshi, sannan ta ce"Shugaba ce take neman raina min wayau kuma wallahi ni ba zan ɗauka ba, idan tayi min ramawa zan yi. Don ana shiru ana kyaleta tana murza mulki son ranta, hakan ba yana nufin tsoronta ake ji ba, matsayinta kawai ake dubawa yasa ake ɗaga mata kafa."

Nan ta kwashe labarin komai ta fesawa Zeenatu.

Kama baki Zeenatu tayi ta ce"Ke fa Azagwai ba zan ɓoye miki ba, son kuɗin nan naki na neman wuce gona da iri. Na lura ke komai ma zaki iya yi akan kuɗi, abin takaici ma kin maida gulma sana'a, sai kice ba zaki faɗi zance ba sai an biyaki kuɗi koda kuwa mutum na bakin ramin mutuwa ne. Gaskiya muna ganin different character's a gidan mata, amma wallahi Azagwai ki canza hali wannan sam ba ɗabi'a mai kyau ba ne."

Wani irin tsalle Azagwai ta daka saman katifarta hannunta rike da tsukakken kugunta ta ce" Ni kuwa nake ganin ribarsa, gara dani gulma ce sana'ata amma karyarka kace ka taɓa kama ni ina iskanci."

Zeenatu ta sha jinin jikinta don ta san ba karya Azagwai ta sharara ba. Ita bata harka da maza, ita dai ka barta da gulma da tsugudidi sune sana'ar data kama a hannu, muddin ta gano wani ɗan liki na sirrinka to ka gama yawo, sai ta samu na cin abinci a jikinka idan ba haka ba ta fallasaka. 

Kai koda ace ka rufe bakinta da shegun, sai ta fesawa ire-irenta masu son jin gulma amma suma ɗin sai ka bada ɗan wani abu kafin kasha zance. Kafin ka ankara, ta gama rarrabawa kowa sirrinka har ya dawo kunnenka. Yanzu da aka ganota, masu hankalin sun shata layi tsakaninsu da ita, marasa wayon ne dai har yanzu suka kasa hankalta da ita har suke bari take nasara a kansu. Sai kuma waƴanda basu san halinta ba suke faɗawa tarkonta kamar Hadiza wacce tayi kuskuren kai kanta ramin mutuwa.

Zeenatu ta ce"Allah ya kyauta, dama ni zuwa nayi ki bani rancen dubu biyar idan na dawo anjima zan mayar miki da abarki."

Wani irin kallo ta watsa mata ta ce"Gaskiya ba zan baki ba saboda baki da cika alkawari. Anjimanki yana nufin gobenki ne, sannan idan kin tashi mayar da kuɗi bakya son saka riba bayan kin san da cewa kuɗin sana'a ne."

"Ke dai komai a wajenki kin maishe dashi sana'a, kwata-kwata baki taɓa bari a moreki a banza."

Azagwai ta ce"Ku ji min 'ya fa? ban da na rike abin da kike Allah wadai dashi a matsayin sana'a zaki zo neman rance wajena? Kakaf! Gidan mata wacece ake samun rancen kuɗi wajenta idan aka cire Shugaba bayan ni? Ai kuwa kin ga ina da amfani."

Tabbas Idan magana ake na ba da rancen kuɗin bashi da ruwa to Azagwai ce kat! A gidan.

"Hakane! yanzu dai ba sai kin goranta min ba, zan samu ko ba zan samu ba?"

Susa kai tayi kan ta ce"Zaki samu mana amma gaskiya sai kin ɗau alkawarin dawo min da kuɗina a kan lokaci tare da 'yar ribata, idan kuma kin ƙiya to a sauka lafiya."

Sai da ta amince da tsarin nata sannan ta kirgo kuɗi ta bata, ita ce har da ɗakko wani long note inda take rubuta sunayen 'yan bashi da kuma ribar da za su bada, sai kuma ranar da suka ƙarbi kuɗin da lokacin da suka yi alkawarin dawowa dashi. 

Haka ta rubuta sunan Zeenatu da amount na kuɗin da ta ƙarba, sai kuma ribar ɗari biyar da za ta bayar tunda kuɗin ba kwana a hannunta zai yi ba, idan kuma ta kuskura ta ƙara kwanaki to tabbas ribarta ƙaruwa zai dinga yi. Abin ma har ba wa Zeenatu dariya yayi ganin abin nata lallai azimun ne.

"Kina wani dariya, to bari kiji duk wanda ya ɗauki sana'arsa serious, irin haka yake yi, zai kasance yana da record book na musamman domin lissafa abubuwa, idan kuma kina da ja da abin da na faɗa ko kuma tunanin karya nake, to ki tambayi Uwarɗaki za ta faɗa miki sirrin da yasa GIDAN MATAN TA sai ci gaba da ɗaukaka kawai yake."

Zeenatu uffan ba ta sake cewa ba ta karɓe kuɗi tayi gaba don ta lura muddin ta biyewa surutun Azagwai to fa fitarta zai yi wuya don kuwa idan ta kama zance tayi ta jansa kenan kamar zaren ɗinki.

***

Jidda na isa gidan abincin, ba ta shiga ciki ba ta tsaya a waje. Aliyu ya fito ya miƙa mata abin da ta yi oda. Tana karɓa ta juya za ta tari napep da zai kaita gidan mata, sai kiran Abba Habibu ya shigo mata.

Da sauri ta koma gefen wani shago sannan ta ɗaga wayar bakinta ɗauke da sallama.

Abba Habibu ya amsa da fara'arsa, yana cewa, "Maijidda, kuna lafiya? Ya maigidan naki?"

Cikin kunya ta ce, "Muna nan lafiya, Abba. Ya Saude da Yaya Naziru?"

"Kowa ƙalau! Dama kan batun Saude ya sa na kiraki."

Da sauri ta ce"Amma lafiya ko?"

Saude da Yaya Naziru duk ya'yansa ne.

Abba Habibu ya ce"To, da sauƙi dai amma wallahi Maijidda rayuwar ce sai a hankali. Idan baka kai zuciyarka nesa ba kana iya kashe kanka a kan rashi."

"Subhanallah Abba ka bar faɗin haka, Allah dai yasa mu fi ƙarfin zukatanmu. Yanzu dai kayi min bayanin abin da ke faruwa."

Ya yi shiru na wasu 'yan daƙiƙu, kafin ya fara magana.

"Kin san dai rayuwa ba kullum take tafiya yadda mutum yake so ba. Wani lokaci kana ganin yau ka samu, gobe kuma babu. Shi yasa tun da na ga Allah Ya sauya miki rayuwa, na fara tunanin Saude."

Cikin rashin fahimta ta ce"Meya faru da saude?"

"Maijidda, idan ba za ki ga kamar ina neman ɗora miki nauyi ba... ko za ki iya amsar Saude ta zo ta zauna wurinki?"

Jidda ta yi shiru.

Kalaman nasa sun zo mata da bazata.

"Saude?"

"Eh, Saude fa...Idan kika ɗauke mana nauyinta kin gama mana komai. Ko da mai aikin gida ne ko ki sama mata wani aiki na daban, Maijidda ki taimaka mana don Allah. Ina tunanin Wataƙila kasancewarta a wurinki zai buɗe ƙofofin da zamu samu sauƙin rayuwa."

Ta fahimci damuwar Abba Habibu, so yake ya samu kyakkyawar rayuwa shine yake neman tura 'yarsa don su sha inuwarta.

"Abba," ta kira shi cikin sanyin murya.

"Na'am, Maijidda."

"Na fahimci abin da kake so. Kuma wallahi bana ƙin Saude. Ba zan taɓa ƙin ta ba don ƙanwata ce amma..." Ta dakata.

"Amma me?"

"Ba na ganin ya kamata a yi gaggawar bani ita. Ya kamata a bani lokaci ni ma in fara sanin yadda rayuwata za ta kasance kafin in ɗauki nauyin wani."

"Gaskiya ne!" 

Abba Habibu ya furta cikin jin kunya.

Jidda ta samu ƙwarin gwiwa ta ci gaba"Kuma bai kamata na amsa bukatarka kai tsaye ban nemi amincewar wanda nake karkashinsa ba."

Ya ce"Eh...To...haka ne kuma fa."

Jidda ta ce "To ka gani? Dole sai da amincewarsa. Kawai Abba ka bari Idan na ga cewa ya dace Saude ta zo wajena, zan sanar da kai. Taimako dai zan rika bada duk abin da Allah ya hore min insha Allah."

Jin batun taimako ya washe hakora yana zuba godiya da sa mata albarka.

Har sun yi sallama za ta kashe waya ta ji ya ce"Yauwa, Maijidda ji mana..ban gama magana ba."

Ta dakata tana "Abba ina jinka."

Ya ce"Magana nake so mu yi kan mahafinki."

Nan take fuskar Jidda ta sauya. A lokaci guda wani irin zafi ya taso daga cikin ƙirjinta.

"Wane mahaifi?" ta tari numfashinsa cikin ɓacin rai.

"Mutumin da ya yi sanadin shigata duniya? To, me zan masa?"

"Maijidda, mahaifinki ne. Na san bai kyauta ba, amma bai kamata ki watsar da shi ba."

Jidda ta runtse idanunta. Hawaye suka cika su kafin su fara gangarowa a kumatunta.

"Abba, wai ka manta ne? Mahaifina shi ne ya sa na shiga duniya, Kuma shi ne ya sa na guje kowa nawa. Domin muddin ya gano inda nake, zai je ya ƙwace ni sannan ya cika burinsa na aurar da ni domin biyan bashin da ake binsa."

Ta share hawayen da suka kasa tsayawa.

"Ko ka manta ne?"

Abba Habibu ya yi shiru don ya san gaskiya ta faɗa.

Ta ci gaba da magana da rawar murya"Ya yi alƙawarin ba da aurena ga wani tantirin mashayi da yake binsa bashi na miliyoyin kuɗi. Da ya gagara biyan bashin, sai mutumin ya ce babu abin da zai karɓa daga hannunsa face ni. Ya dage cewa ko dai ya ba shi ni a madadin kuɗinsa, ko kuma ya sa a kawo masa ni har inda yake ya min fyaɗe."

Tana kai wa nan ta fashe da kuka.

Cikin ƙasa da murya ta ce,

"Sanin ko wanene shi ne ya sa mahaifina ya tsorata. Ya san ba zai iya biyan kuɗin ba, shi ya sa ya nuna zai ba shi aurena a madadin kuɗinsa."

Ta ja numfashi mai nauyi.

"Ni kuma, da na san halin Sani Kasko, sai na bijire da maganar auren. Amma Abie ya nuna ko mutuwa zan yi, sai na auri Sani Kasko."

Hawayen suka sake zubo mata.

"Wannan shi ne dalilin da ya sa aka wayi gari aka ga babu ni a gida. Na toshe duk wata hanya da na san za a iya samun labarina. Sai da na tashi yin aure sannan na nemeka, don na san kai mutum ne mai amana."

"Abba..." Ta ambaci sunansa cikin jin zafi.

"Na'am, Maijidda," ya amsa cikin rauni.

"An ɗaura aurena ba tare da an yi shela ba, saboda tsoron kada Abie ya sani ya yi ƙoƙarin dakatar da shi. Ni da nake da dangi, amma a ranar aurena, bare ne kawai suka kasance shaidu."

Kuka ya ci karfinta, Abba habibu duk dauriyarsa sai daya zubar da ƙwalla.

"Abba, me kake so in kira mutumin nan? Mahaifi?" Ta furta cikin raɗaɗi.

"Mutumin da ya kamata ya zama garkuwata shi ne ya so sayar da ni. Mutumin da ya kamata ya kare ni shi ne ya sanya rayuwata cikin haɗari."

Abba Habibu bai ce komai ba.

Jidda ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya, hawaye na ci gaba da zubowa.

"Wannan dalilin yasa bana son komawa gida. Mahaifina ba mutumin da za a so ba ne. Mai sayar da kayan maye, kai kanka ka san ba alfahari za ayi da shi ba."

Ta yi shiru na wasu daƙiƙu sannan ta ci gaba da magana cikin rauni.

"Ni dai abin da nake so shi ne ya bar ni da rayuwata. Na gudu daga gare shi ne saboda in ceci rayuwata."

Abba Habibu na so ya jata da magana ta ga lokaci na tafiya, ta ce"Abba kayi hakuri idan na samu lokaci za muyi magana da kyau."

Daga haka suka yi sallama. Sai sun sake waya za ta faɗa masa har Safiyya ma yanzu suna tare. Ta ciro hankici daga jaka ta share fuskarta sannan ta je ta tari napep drop da zai kaita gidan mata.

****
**SAFFY**

Muwaddah ce ta bi ta addabeta da kira a waya da wannan safiya kuma tana gani ta share don ta tsani naci. Daga haɗuwa jiya-jiya ta wani liƙe mata.

Ganin nacin ya yi yawa yasa ta ja tsaki ta ce"Me zan mata to? Ni fa gaskiya ba zuwa bikinku zan yi ba abu sai kace dole? Daga haɗuwa jiya-jiya kuma shikenan sai a nemi shisshigewa mutum?"

Saffy ta furta a hasale kamar ita Muwaddan na gabanta, sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ta daga. Ta kasa furta komai saboda ɓacin rai.

Daga ɓangaren Muwaddah ajiyar zuciya ta sauke na ganin an daga kiranta, ta ce"kawata kiyi hakuri na takuraki da kira ko bacci kike ne?"

"Eh wallahi amma karki damu, yakike? Ya kuma shirye-shirye?"

"Ina son ganinki pls gani a junction ɗinku, sako zan baki."

"Sakon me fa?"

Saffy tayi tambaya cike da mamaki.

Muwadda tayi murmushin da har ake iya jiyo sautinsa sannan ta ce"Ke dai ki fito ki sameni, idan kin zo kya ga ko menene and please don Allah karki ɓata lokaci sauri nake."

 "Ok, gani nan tafe."

Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar sannan ta mike tana mamakin ko saƙon me take son ta bata. 

Dogon hijabi ta jawo ta ɗora saman gajeran wandon dake jikinta da riga 'yar shara-shara ta shan iska, hijabin kuwa ya rufe ko'ina na jikinta. Wayarta ta ɗauka sannan ta fice da sauri bayan ta rufe ɗakin nata.

Fitar ta da kamar 5 mins Jidda ta sauka daga napep amma dayake ta bayan layi ta biyo shiyasa basu haɗe da Saffy a hanya ba.

"Shugaba! Maraba da zuwa!"

Shi ne abin da matan da ta riska a tsakar gida suke ta ce mata, ta amsa musu cikin sakin fuska. Tasa wata ta anso mata makullin ofis daga wajen SALA, ta buɗe ta shiga. 

Shigar ta ke da wuya bayan ta zauna ta jawo wayarta ta bada sanarwa a group.

_"Duk wacce ke da bukatar ganawa dani to a yanzu ina ofis. Ina nan daga yanzu har zuwa ƙarfe 1:00 na rana, daga 1:30 kuma na tashi babu wanda zan sake saurara sai wani lokaci."_

_Muna fatar samun haɗin kai daga gareku kamar kodayaushe._

_Mungode._

_*Jiddatulkhair Kabir (SHUGABAR GIDAN MATA.)*_

_*Salamatu Abdulrasheed (Mataimakiya).*_

Wannan shine sanarwar da Jidda ta bayar a cikin WhatsApp platform ɗinsu. Tana gama aike saƙon ta kashe datan sannan ta mike tayi cikin gida, a inda ta tsaya gaisawa a tsanake da wasu matan dake harkokin gabansu, tana gaisuwan ne amma idanunta a kan ƙofar ɗakin Saffy da taga an garkame shi da kwaɗo. Ta tabbatarwa kanta da lallai bata gidan.

"Safiyya! Allah yasa dai ba kwanan waje kika fara yi ba."

Ta ayyana wannan zance a ranta, haka kawai taji ranta ya ɓaci da hakan. Kai tsaye ɗakinta ta nufa wanda a yanzu take masa kallon wajen hutawa.

Masu jin haushinta suka fara tseguminta bayan ɓacewarta daga gabansu. Wata data gama karance saƙon Jiddan a wayarta, ta ce da sauran dake zazzaune kusa da ita,

"Yarinya sai shegen iyayi da ganin kanta kamar tafi kowa, hadda wani daga 1:30 duk wanda yaje ofis ba zata saurare shi ba yadda kasan ita keda Gidan matan, mtssw! aikin banza wai zane a mazaunai."

Wata ta kada baki ta ce" Ai kuma duk abin da tace ya zaunu kenan, babu wanda ya isa ya ja da ita idan ba so kake ka gamu da mugun ɓacin ran uwarɗaki ba."

"Ni sai nake ganin ma kamar mugun shakkar Jiddan take, sai ka rasa ma a cikinsu ko wacece uwarɗakin ? idan akayi duba da yadda kowacce take gudun ɓacin ran ɗaya " acewar wata daban kenan.

Tsit! Suka yi ganin tana fitowa da kofin shayi a hannu dake fitar da tururi, a electric cooker ta tafasa ruwa kasancewar akwai wutar lantarki. Giftawa gabansu tayi, cike da sanyinta ta ce" Sannunku fa! A ci gaba da bada himma, kuma zan sake faɗa da zarar 1:30 ya buga wallahi ko minti ɗaya ba zan ƙara ba zan rufe ofis."

Tana gama magana tayi gaba, ta barsu nan lulluɓe cikin kunya, hakan na nufin ta ji gulmarta da suke yi kenan tunda kusa da ɗakinta duk suka yi zaman kashe wandon.

Sake waiwayowa tayi ta sauke kallonta a kan ɗaya daga ciki, ta ce" Hajara na san dai kina da bukatar gani na akan kuɗin harajinki na watanni biyu da muke binki bashinsa. Wannan shine karon ƙarshe da zan sake tuntubarki akansa ko kuma ki jira hukuncin da zai biyo baya."

 A fusace Hajara ta mike tsaye kamar za tai kanta ta bugeta, ta ce" Haba don Allah shine sai kin fito kin tona min asiri a gaban mutane? Ki je don Allah zan sameki a ofis."

"Ai na zaci tasowar da ki kai rufe ni da duka zakiyi, ashe a jerin 'yan iskan ma ke ɗin ta goye da zani ce. To ki sani ina jiranki don wallahi yau bazan bar gidan nan ba har sai kin bada kuɗin harajinki."

Cike da izza da takama ta shige ofis ko sake bin ta kan haukarta ba tayi ba.

Zama tayi a kan kujera ta mike kafafunta saman teburin gabanta, sannan ta jawo ledar kazarta da biredin data siya a kan hanya ta fara aikawa cikinta, lokaci zuwa lokaci tana kurban ruwan shayi. A yayin data zubawa ƙofar shigowa idanu tana jiran masu bukatar ganinta.