CHAPTER 12
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 12.*
*SAMHA.*
"What?? Yanzu Jidda bata son min aiki yadda ya kamata. Amma bari in ɗauki kafa inje in sameta tun kafin lokaci ya buga ta sa kai tabar gidan tunda ga dukkan alamu ta koma aiki kamar agogo sannan ta zama kuɗi masu baƙar wahalar samu."
Samha ta furta da zafinta bayan ta gama karance saƙon Jidda na sanarwar da ta bayar a group. A gurguje ta shirya, duk da laulayin daya ɗan tasata gaba a cikin 'yan kwanakin nan wanda fita ma ya zamar mata dole amma haka ta ɗaure ta nufi gidan mata.
***
Saffy na fita gida ta tsaya daidai junction tana waige-waige amma bata hango ko mai kama da Muwaddah ba, duk napep ɗin daya gifta sai ta leka ko zata hangota ciki amma bata. Hakan yasa ta nemeta a waya, hakuri ta bata tace gata nan karasowa. Matsawa daga gefen titin tayi, ta tsaya tsayuwan jiranta.
Wata toyota yaris fara kal ce taga ta tsaya gabanta, har zata matsa gefe taga an sauke glasses kasa, idanunta yayi arba da wasu wayayyun mata biyu. Wacce ke tuki ta makala wani kafcecen baby pink glasses a idanunta me ɗaukar ido wanda ya rufe mata rabin fuska, ita me zaune a kujerar me zaman banza kai tsaye ake kallon cikin ƙwayar idanunta don ita bata sa madubi ba.
Kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kai sannan ta nemi barin wajen.
"Ke! Where are you going? Come back, kamar dai baki shaida wacce kike ta tsayuwan jira ba ko? Kodayake ba laifinki bane baki yi tsammanin ganinta cikin me ƙafa huɗu ba, a ranar da kuka fara haɗuwa cikin tricycle ne shiyasa."
Budurwar dake zaune a kujerar me zaman banza ta faɗi hakan tare da tunsirewa da dariya.
Cak! Saffy ta tsaya a waje ɗaya gabanta na mugun harbawa jin irin cin fuskar da aka yi mata.
'Kan uba! wacce me ƙarfin halin ce wannan ɗin da take ƙoƙarin ci mata mutunci?'
Ta ayyana aranta.
Kafin ta ce wani abu sai ga ɗayan yarinyar me gilashin ta fito hankalinta a mugun tashe, ta zare glasses hakan yaba Saffy damar shaidata.
"Muwaddah!"
Ta ambaci sunanta, sannan ta girgiza kai ta kuma cewa "Ashe dai yau tafiyar ta manya ce bata yaku bayi ba, shiyasa naga wata har tana ci min fuska, hakan na nufin kin bada labarin haɗuwata dake kenan. Dama Saƙon kenan? cin mutunci? ba damuwa nagode."
Tayi niyyar barin wajen don muddin ta tsaya ci gaba da jin abin da zai sosa ranta to kuwa zuciya na iya ɗibanta ta kakkarya 'yar mutane a kan titi.
Da sauri Muwaddah ta riko hannunta ta marairaice ta ce"Don girman Allah ƙawata kiyi hakuri, dana san haka zai faru da ban taho da Raihan ba, pls karki biye mata ita haka halinta yake, cin mutuncin wani ba komai bane a wajenta, ina zuwa bari na ɗauko miki saƙon naki a cikin mota."
Bata ce da ita komai ba, Allah sarki Muwadda a rikice ta koma mota don dakkowa saffyn sakonta, tatass tayi ma Raihan kan abin da tayi wa Saffy sam bata kyauta ba kuma bata ji daɗinsa ba. Hakika ta kunyatar da ita, ta tabbata Saffy za tayi tunanin ko haka itama halinta yake. Hakan da tayi ya fusata Raihan ainun!
Babu shiri ta banko kofar motar ta fito tana kuka, ta ce" Muwaddah don kin yi sabuwar ƙawa shine zaki wulakantani? a kan wata 'yar ghetto kike zagina? Nagode, amma wallahi ki sani ba zan taɓa sonta ba tunda ta nemi shiga tsakanina dake kuma ki sani sai su Ammi sun ji zancen nan."
Tana gama faɗin haka ta fara ƙoƙarin tsai da abin hawa, Muwaddah duk tabi ta ruɗe sai rokonta take.
"Raihan don girman Allah kiyi hakuri in maidake gida, kema kin san baki kyauta ba be kamata ki ci mutuncinta ba. Na tabbata idan nayi ma wata ƙawarki kwatankwacin abin da kikai ma Safiyya sam ba zaki ji daɗi ba."
Ko bin ta kan jawabinta ba tayi ba ta tsai da wani ɗan sahu ta afka ciki, tare da masa kwatancen inda zai kaita. Mai babur yaja suka yi gaba ko sake kallon ɓarin da Muwaddah take ba tayi ba, balle ta saurareta.
Juyowar da za tayi sai gani tayi wayam! babu saffy, tuni kanta ya kara ɗaukar zafi. Can ta hangota har ta mika layin cikin unguwarsu tana lafta uban sauri kamar zata kifa kasa.
Sauri-sauri, gudu-gudu haka ta bi bayanta tana ƙwalla mata ƙira, Saffy sai ƙara uban sauri take don kar ta cimmata. Tana shan kwanar layin, taga wani gida me gate ba tare da tunanin komai ba ta afka cikin gidan mutane, ita ce harda tura ƙofar ta rufe da sakata.
"Ke! Kehhh! tsaya daga nan! Ya zaki faɗo cikin gidan mutane hadda rufe ƙofa? wannan ƙarfin hali da me yayi kama?"
Me gadin gidan ya furta da zafinsa daga inda yake zaune, ya daka wani uban tsalle rike da sandarsa sai gabanta ya dira. Hakan kuwa ba ƙaramin tsoratar da Saffy yayi ba.
Ja da baya tayi ta ce a rikice"Don Allah kuyi hakuri biyoni a kayi."
"Uban wa ya biyoki? barayin waya ko 'yan bindiga?"
Ya watsa mata tambaya yana ƙoƙarin kai hannu domin ya zare sakatar, shi a dole ga jarumi kuma takamarsa me gidan jami'i ne.
"Don girman Allah karka buɗe, wallahi kwata-kwata bana so ta kusanto inda nake, ta takura wa rayuwata ni wallahi."
Wani irin kukan shagwaɓa ne ya kufce mata, a sanyaye me gadi ya komo da baya yana me kwantar da murya ya ce"Wacece take bibiyar ki? Ko dai ƙwacen saurayi kika mata ne? Don 'yan matan wannan zamanin baku da wani aiki sai rigima kan samari a ƙarshe kuma a yaudareku."
Wani kallo ta watsa masa wanda yasa dole ya shiga taitayinsa.
Kafin ta kai ga bada amsa suka ji daga bayansu an ce"Wai kai Iliya meyasa bakinka sam baya da control ne? Ka tasa mace gaba ka tsareta da tambayoyi sai kace ɗan jarida, maimakon kayi abin da ya dace ka tsaya shirme, ina ganin lokaci yayi daya kamata na sauyaka da wani."
Jin haka yasa Iliya yayi saurin kamewa tun kafin uban gidan nasa ya karaso ya ce" Mon sir! don Allah kayi hakuri na tuba zan gyara."
Ko sake bin ta kansa Abuturab be yi ba ya kalleta, ita ma ɗin kallonsa take tare da yin tasbihi ga Allah da irin halittan daya ƙera a nan. Har ya buɗe ƙaramin bakinsa zai mata magana sai suka ji Muwadda daga waje tana tambayar wani almajiri inda Saffy ta shige. Abinka da yaro ba wayo sai kawai ya nuna mata gidan. Godiya ta masa sannan ta isa gate ɗin ta fara bubbugawa har tana kuka.
"Safiyya don Allah kiyi hakuri karki guje min akan abin da Raihan ta miki."
Hakan ba ƙaramin kashewa Abuturab jiki yayi ba, da sauri ya kai hannu zai zare sakatar kofa, Saffy tayi ƙoƙarin dakatar dashi.
Karon farko da yayi mata magana ya ce" Kiyi hakuri ba a haka, komai na rayuwan nan hakuri ake kin ji ko?"
Jikinta ne yayi sanyi, sai kuma ta tsinci kanta da daga masa kai alamun ta saduda, ya sakar mata kayataccen murmushinsa don sosai ta birgeshi.
Abuturab yayi matukar ƙoƙari na ganin ya sulhunta tsakanin sabbin ƙawayen biyu, sannan ya musu fatan alheri kana ya koma ciki tare da rufo ƙofar gidansa a kan idanunsu.
"Na zaci nan ɗin gidanku ne ai, kuma shi ɗin yayanki."
Muwaddah ta jefo mata tambaya bayan sun kama hanya.
"No, ba gidanmu bane kuma kamar ke, nima yau ɗin na fara sakashi a ido, kawai dai na afka cikin gidansu ne domin na kauracewa ganinki."
Muwaddah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Na fahimta, amma dai ya kamata yau ki min izini in fara sanin gidanku kafin daga baya nima ki ziyarci gidanmu don muamala ta tsakani da Allah nake son mu kulla ni dake Safiyya bata ƙarya ba."
"Gaskiya wanda nake zaune wajensa baya so ana kawo masa mutane gida amma kiyi hakuri zan nemi alfarma a baki damar zuwa wajena."
Muwaddah ta saukar da wata kalar ajiyar zuciya don ta fahimci Saffy ba gaban iyayenta take ba, riƙonta ake kuma ga dukkan alamu ana takurata.
"Ba damuwa, mu je ki karɓi saƙon da nake ta ja miki rai."
Saffy ta ce"Na fito karɓan saƙo aka ci mutunci na. Ko karyawa ban yi ba amma na karya da takaicin wata."
Muwaddah ta tuntsire da dariya ta ce"Au! Dama baki karya ba? This is to 10 fa?"
"Serious ban karya ba."
Muwaddah tayi mata tayin karbo koda takeaway ne a wani restaurant da ke kusa. A farko taso bijirewa saboda outfit dake jikinta amma sai taga babu wani aibu tattare da ita tunda ta rufe jikinta har ƙasa da dogon hijab. Alkaleri's kitchen suka nufa saboda shine gidan abincin daya fi tashe a garin.
***
*YALLABAI.*
Manyan baƙi yayi daga ƙasar Japan waɗanda suka wanko kafa na musamman domin jarraba kalolin girke-girkensa don tantance ɗanɗanonsu da ake ganin babu kamarsa kaf Africa.
A kwanakin baya sun gayyaceshi ƙasarsu a inda ya samu shiga wata gasa da suka shirya na kwararrun masana sanin sirrin girke-girke. Duka Nahiyoyin duniya bakwai aka gayyata, a inda Executive Chef Jalaludden Alkaleri ya wakilci nahiyar Afrika.
Cikin ikon Allah shi yayi nasarar lashe gasar ya samu maɗaukakiyar nasara domin ya bige sauran abokanan fafatawar tasa ne da abinciccikanmu na Afrika masu ɗanɗano me daɗin gaske. Ya samu lambar yabo tare da wasu manyan ƙyaututtuka na kayan aiki na girke-girke, sai kuma damar daya samu ta kafa gidan abincinsa a ƙasarsu wanda su ne zasu ɗauki nauyinsa domin so suke su haɗa partnership business dashi.
Tun jiya da suka sauka gari ya kai su branch ɗinsa biyu na nan Kaduna for thorough inspection domin ganin yadda abubuwansa ke tafiya kuma sosai suka yabawa ƙoƙarinsa har suke ganin tabbas ya cancanci a bashi damar kafa shahararren gidan abinci a ƙasarsu wanda za a dinga siyar da abincin afrika ne zallah.
Farin ciki yake sosai ganin wata dama ta sake samu bayan wanda ya samu daga kasar birtaniya.
Gaban madubi yake yana naɗa navy blue neck tie akan farar long sleeves ɗinsa, hannunsa ya kai wajen jerin turarukansa masu musulman ƙamshi me sanyaya rai.
Hannunsa ya kai kan 'OudTouch' wanda a duk cikin turarukan da yake sawa Jidda tafi son ƙamshinsa. Wayarsa ya ɗauka ya sanya kiranta.
A daidai wannan lokacin tana zaune tana yagar kazarta data karɓo daga gidan abincinsa, tana haɗawa da shayi da bread. Zuwa yanzu ta kwashi 15mins babu wacce ta shigo ganinta.
Tana shirin neman Saffy a waya ta ji inda take, sai ga kiran Yallabai ya shigo ta ɗaga.
"Sai yanzu ka tuna dani?" Ta faɗa cikin wasa.
"Alkhairi kiyi hakuri ni ban isa in manta dake ba. kodayaushe kina nan makale a raina, kawai dai mutanen Japan ne suka shiga hakkinki."
Ta ce"To, Jay Allah ya tabbatar da alheri."
"Ameen, Ki tayani da addu'a yanzu nake shirin zuwa in ƙarbi offer ɗina a wajen baƙin nawa sannan in sallamesu don yau za su koma ƙasarsu. Jidda shiyasa na ce ke alkhairina ce, tun daga lokacin da kika shigo rayuwata nake ta samun ɗaukaka da ci gaba a harkar kasuwanci na. Bayan haka kuma ga natsuwar da nake samu idan ina tare dake. Jiddatulkhair I love you so much, indeed you're the rahma that Allah sent to me, alhamdulillah!"
Sosai kalamansa suka ida gigitar da ita, sai murmushi kawai take tayi abinta har ya bukaci su yi vidiyo call domin taga shirin da yayi na fita.
Nan fa suka shiga vidiyo ya ga ashe har tana gidan mata.
Girgiza kai ya yi ya ce"Jidda, wannan gidan matan dai na kusa rabaki da shi amma komai lokaci ne. Ina nan ina shirin da baki san da shi ba amma na tabbata za kiyi farin ciki."
Bata ce komai ba sai murmushin da tayi da yake iya jiyo sautinsa.
"Idan na ƙarbi offer ɗinmu zan zo mu yi celebrating."
"To shikenan sai na ganka, Allah ya tabbatar da alheri.."
Daga haka suka yi sallama, Bayan Yallabai ya sauke waya ya ce kasa-kasa,
"Jidda! In sha Allahu na kusa rabaki da GIDAN MATA na har abada, dama zuba idanu kawai nayi domin in ga iya gudun ruwanki. Ni ya dace ki bauta wa ba 'yar cikina ba."
Ya ida magana yana kallon cikin madubi yana me ƙarewa kansa kallo. Girgiza kai yayi alamun something is missing, ya tafi wajen jerin gilasai na idanu, hannunsa ya kai kan wani farin eyeshade me farin kwalba, me shegen kyau, ya ɗakko ya makala kana ya koma gaban madubi, sosai ya yi masifar haɗuwa ta ko'ina. Sai daya gamsu cewa tabbas ya fito sannan a gurguje ya jawo navy blue suit ɗinsa ya aza saman farar rigarsa sai kuma cover shoes baki da safa, sannan ya fice a hanzarce ɗauke da briefcase yana waya da baƙinsa dake zaman jiransa.
Kafin ya tafi sai daya shiga side ɗin Haj. Nafeesa ya sallameta. Sai dai kuma ya fahimci kamar tana cikin damuwa don ya nuna a fuskarta. Koda ya tambayeta ta nuna masa babu komai ɗan zazzabi ne take ji kawai. Ya mata Allah ya sawwake sannan ya bar gidan zuwa inda za su gana da baƙinsa.
Tuni mutane suka yi ma Jidda caaa! akai a cikin ofis, ana biyan kuɗin haraji. Wasu kuma kayan abincin wata suke bin bashi, amma ba fanninta bane dole sai sun jira dattijan matan da suke incharge a wannan ɓangaren sun zo.
Korasu waje tayi tace dasu zata nemi officials a waya sannan ta maida hankali kan masu biyan kuɗin haraji, a yayin da SALA ke tayata shigar da bayanai.
Azagwai ce ta gaba da zata biya kuɗi, Nan take Jidda ta tuno abin da tayi mata.
Tsaki ta ja ta maida dubanta kan wacce take bayan Azagwai ɗin ta ce"Don Allah next person please."
Azagwai ta tattare wuri taki ba ta bayan nata hanya.
"Ki bani guri mana ko baki ji tace in matso kusa ba?" Yarinyar ta furta tana hararan Azagwai.
Azagwai ta ce"Wallahi kin ma raina wa kanki hankali da har kike tsammanin zan bari ki matsa kusa da wannan tebirin bayan kin san da cewa bana bari a ci min layi. To ki sani sai ta gama sauraron bukatuna kafin azo kan ki."
Cikin zafin rai Jidda ta ce "Azagwai ba zan saurareki ba! Kin ji ko? Ina so in ga ƙarshen rashin kunyarki, idan yaso ni kuma zan nuna miki ƙarfin isa da ikona a gidan nan."
Jidda ta ida magana da zafinta, har da miƙewa tsaye da buga tebirin gabanta wanda shi ya mata tsakani da matan dake tsastsaye gabanta.
Duk da cewar Azagwai ta matukar kaɗuwa da yanayin Jiddan, amma sai ta fuske ta ce,
"Jidda ina so ki ture duk wani personal issues dake tsakanina dake, yanzu a kan aikinki kike don haka ya zame miki wajibi ki saurare ni idan ba haka ba zanyi kararki wajen uwarɗaki."
Jidda ta nuna kanta da 'yar yatsa ta ce"Are you threatening me? Shafa'atu bismillah je ki kai ƙarar tawa yau ina so inga iya gudun ruwanki."
Kafin ta kai ga bata amsa suka tsinkayi muryar Samha ta faɗo gidan tana tambayar matan dake zube a waje abin da suke zaman jira shanye a rana haka. Galibinsu 'Yan yara-yara ne waɗanda basu fi irin sha takwas zuwa ashirin ba.
"Shugaba ce tace mu ɗan jira kaɗan za tayi waya da masu ba da kayan abinci za su zo nan bada jimawa ba su sallamemu."
A cewar wata a cikin matan kenan.
Wata kuma ta ce cike da gajiyawa " Akalla mun shafe sama da awa ɗaya da rabi muna jira amma har yanzu shiru kuma bana tsammanin ta kirasu awayan ma kamar dai ta manta da batunmu ne."
Ta ida magana kamar zata saki ɗan marayan kuka. Hakan kuwa ba ƙaramin motsa tsokar ran Samha yayi ba don ita ɗin me tausayi ce, bata ƙaunar ganin ana hora koda dabba ne da abinci balle kuma ɗan mutum. Duk wanda kaga an masa horon kayan abinci a wannan gidan to lallai ya kaita bango ne, ya karya wani doka, to shine zaka ga ya fuskanci hukunci na ɗan lokaci.
Gaban Jidda ne ya bada rass! Jin abin da yarinyar ta faɗa don tabbas ta sha'afa da batunsu. Da sauri ta daga waya zata kira Baaba Rabi wacce ita ce head incharge kuma gidanta na nan kusa cikin unguwa ne ma.
Sai ganin Samha tayi ta faɗo ofishin ranta a matuƙar ɓace. 'Yan matan dake ciki ma na gaisheta hannu kawai ta daga musu idanunta kyam! a kan Jidda wacce ta sha jinin jikinta.
Duk iskancinka duk iya shegenka duk cika bakinka sam baka iya yin shi gaban Samha. 'Yar yarinya ce amma kwarjini take da shi na ban mamaki.
"Yanzu kike shirin kiran Baaba Rabi da kika ga zahirina a gabanki, haka ne?"
Ta furta cikin bayyana fushinta, shiru Jidda ta mata kanta a ƙasa.
"Sauke wayar kuma kiyi ending call ɗin tunda dama bakiyi niyya ba."
Ta bata umarni, da sauri ta dago kai ta dubeta don already har Baaba Rabin ta daga kiran nata.
Jin muryata tana ta rangada sallama sai kuma Samha taga rashin dacewar a datse kiran, ta ce"Yi mata magana."
Kamar dama jira take ta ce a ɗan rikice"Amm...Ammm. Baaba Rabi....dama...dama....akwai masu jiran ki ne kizo ki bada kayan abinci."
"To! To! To! shikenan gani nan tafe."
Ta sauke wayar daga kunneta tana "Ranki ya daɗe barka da zuwa don Allah ki gafarce ni."
Ko kallonta Samha bata yi ba don wani irin bala'in zogi take jin ƙirjinta na mata tamkar wacce ake sossokawa mashi.
"'Yan mata ayi hakuri a ɗan bamu wuri zan gana da Shugabarku."
Cike da girmamawa aka watse aka barsu iya su biyu a cikin ofishin. Matsowar Samha kusa yasa zuciyar Jidda mugun tashi sakamakon ƙamshin turarenta da tayi masa kyayyawan shaƙa, nan take taji wani irin abu ya taso ya tsaya mata a makoshi ya tokare.
Samha na "Lafiya kuwa?me yake damunki?"
Kakarin amai ta shiga yi, da sauri ta runtuma waje da gudu rike da wuya da hannu biyunta. Tun a bakin ƙofar ofishin ta fara kelaye amai har zuwa tafkeken famfon dake tsakar gidan. Mutane suka rufu a kanta ana mata sannu, Ita kanta Samhar hankalinta ne yayi mugun dagawa. Da hanzari ta rufa mata baya ɗauke da wayar Jidda da ake ta nacin kira...