HARAMTACCIYAR GADA

Chapter 13

by @hafnancy

*HARAMTACCIYAR GADA.*


_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_


*NA*


*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*


*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*


*BOOK 1*

    

 *Page 13.*


Sosai Jidda ta fita hayyacinta sakamakon amayar da 'yan hanjin cikinta data kusan yi nan duƙe, jama'a duk sun rufu a kanta ana mata sannu. Da ƙyar Samha ta ƙaraso wajen don ita ma ji tayi jiri na neman ɗibanta ya makata ƙasa ga wayar Jiddan da take rike dashi da aketa nacin ƙira wanda ta rasa ko wanene.  

   

"Don Allah Ku matsa min na ganta." 


Ta furta tana ƙoƙarin ture waɗanda ke gabanta. Da sauri suka bata damar kusantar inda Jiddan take. Tsugunnawa tayi tana leƙen fuskarta, sosai tayi kalar tausayi ganin yadda kamannin Jiddan ya sauya a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. 


"Sannu Jidda dama baki da lafiya ne?"


Kai kawai ta daga mata alamun eh'

 

"A kawo mata ruwa ta tsaftace jikinta." Samha ta bada umarni. 


Da sauri Jidda tace,

"A barshi kawai zanje na canza kayan jikina a ciki."


Miƙewa tayi ta nufi ɗakinta jiki duk a mace, aka rakata da sannu. Da hanzari Samha ta take mata baya ita ma nan ji take kamar zata kifa kasa kawai ƙarfin hali take. 


Azagwai da ta lura da yanayinta ta ce"Uwarɗaki ke kanki naga kamar baki da cikakkiyar lafiya." 


Murmushin yaƙe kawai Samha ta sakar sannan ta waigo ta sauke idanunta a kanta ta furta a hankali,


" Tawa rashin lafiyar ta laulayin ciki ne."


Wani irin sowa 'yan matan suka saki daya ɗan firgita Samha har yasa tayi danasanin faɗa musu. 


Wata ta kada baki tace,


"Congratulations Uwarɗakinmu, ashe an kusa samun magaji ko magajiya, Allah ya raba lafiya." 


Ko kula su ba tayi ba don magana na neman gagararta. Bin bayan Jidda tayi wacce sai mamakin Samhar take data kasa ɓoye sirrinta. 


Idan mace tana da juna biyu be kamata ace ta maidashi waƙa har sai kowa ya gama ji ba. Mace me alkunya shiru take har sai ya bayyana da kansa a gani da ido. Ita gata da juna biyu amma babu wanda ya sani, sai dai dayake nata akwai dalilin ɓoye shi.


Jidda na shiga ɗaki direct banɗaki ta shiga don tsaftace jiki. Samha kuma ta shigo ta kwanta kan doguwar sofa saboda yanayin da take ji a jikinta.


***

Bayan barin Yallabai gida, hankali a tsananin tashe Haj. Nafeesa ta nemi ta hannun damarta Haj.Haire a waya.


"Hairatu ina cikin matsala babba, Malam Shagala ya yi gaskiya, ta tabbata Jalal ya kafa wata ƙarfaffiyar rayuwar sirri da wata macen bayan ni." 


kuka ya kufce wa mata, hannun data rike wayar sai mugun rawa yake sosai kamar zai saɓule ya faɗi.


Daga ɗaya ɓangaren Haire ta kai hannu ta buga ƙirjinta, ta ce" Mun shiga uku! ke ya akayi kika sani?" 


 "Dazu dana je tayashi shiryawa ne naji yana magana ƙasa-ƙasa da wata a waya, nan dai na laɓe bakin ƙofa ina sauraransu. Na ji yana bayyana mata irin tarin ƙaunar da yake mata har yake sanar da ita cewa da zarar ya karɓi offer ɗinsa daga mutanen Japan zai je su sha shagalinsu."


Wani sabon kuka yaci ƙarfinta, Haire ta ce"Nafeesa ba fa kuka zaki tsaya yi ba, shin kin haddace sunanta a ƙwanyarki? don shi ne abu mafi muhimmanci a yanzu."


"Ni fa tsintar maganar nayi sama-sama, kuma kamar zan afka cikin ɗakin in tada hazo ayi rikici amma sai na tuna sharaɗin Malam Shagala daya ce kada na kuskura na nuna masa nasan komai. Ko naji in nuna ban ji ba, ko na gani in nuna ban gani ba, hakan yasa na ɗanne zuciyata sannan nayi watsi da matakin da naso ɗaukawa."


Tagwayen Ajiyar zuciya Haire ta saukar sannan ta ce"Yanzu shi Malam Shagala babu abin da zai iya taimaka miki dashi ne daga inda yake har sai ya dawo? Ni fa wallahi ban ki ya aika da mugayen aljannun da za su haukata shegiya ba, ko kuma su dasa mata wani cutar me wahalar warkewa."


Haj. Nafeesa ta ce"Ni ma zan so hakan amma da muka yi waya a ƙarshe kafin ya tafi garin Agadez yace dani in kwantar da hankalina abi komai a sannu."


"Yanzu haka zakiyi ta zaman jiransa har sai ya dawo? Me zai hana kiyi wa Aljani Labari kiran gaggawa ki aike shi ga uban gidan nasa? Me yiwuwa yana iya bashi wani saƙo ya kawo miki, amma ya kika gani?"


Cike da damuwa ta ce"Tun jiya nake ta kiransa amma yaki bayyana har dai na gaji da kiranyen na hakura ban san menene matsalar ba."


 "Tohh! Ko dai laifi kika masa ne? don ko jiyan nan ma sai dana neme shi ya karɓo min saƙo wajen Malam a game da nawa matsalolin. Kin san shi fa Aljani Labari muddin ba ka kyautata masa to fa sai yaki bayyana a duk lokacin da kake da bukatarsa. Kai idan ma ka taki sa'a ya bayyanan to fa sai dai yata maka iskanci da shirme. Amma dai ki ƙara gwada yin hayaƙin nasa dakyau yabi ko'ina a jikinki sannan ki hanzarta bada sadakarsa a miƙawa musaki, sannan mu zuba idanu nasan tabbas zai bayyana."


Daga haka suka yi sallama, Haj. Nafeesa ta miƙe da hanzari ta murza makullin ƙofar ɗakin ta rufe, sannan ta nufi wani wadrope ɗinta ta fara birkita kayan cikinsa don bata gangancin ajje duk wani maganin da Malam Shagala ya bata a fili. A tsakiyar tulin kayanta na wadrop ta zaro wani ƙaramin ƙullin turaren hayaki dake ƙunshe cikin baƙin zani wanda akayi wa kyayyawan ɗauri.


Da sauri ta nufi banɗaki rike da ƙullin hayakin, lighter, kasko, charcoal, sai kuma wani baƙin zanin da take rufa ayayin hayaƙin kasancewar komai na shi baƙi yakeso, kuma a tsarin Aljani Labari a wajen kazanta ake samunsa kuma baƙi me baƙar aniya.


Shi ma ƙofar banɗakin sai da ta rufe shi sannan ta dire kaskonta ta zuba gawayi a ciki sannan ta kyasta lighter nan take ya kama ci, sai data ɗan jira na wasu 'yan daƙiƙu bayan yayi rushi sannan ta sance ɗaurin kullin turaren. 


Nan tasa 'yan yatsunta biyu ta ɗebi garin turaren wanda yake bakikirin sai tashin wani wari yake mara daɗi ta watsa cikin rushin sannan ta jawo baƙin zaninta ta rufa akai. Sai ƙirari kawai kake ji yana tashi, anan wai ƙiran gaggawa take yi ma Aljani.


Tana gamawa ta nemi baƙin tantabara tasa a kai ma musaki.


A ɓangaren Haj. Haire kuwa, faɗin kalar tashin hankalin data tsinci kanta ciki abun ba a cewa komai, don suna gama waya tayi cilli da wayar saman gado, ta ɗora hannayenta akai tana jero salati tace"Na shiga uku ni Hairatu! Wankin hula yana neman kai ni dare. Wacce 'yar kutumar uba ce haka ta min shigar sauri a wajen Executive chef Jalal?"


Ta furta tana me cizon ɗan yatsa, babu zato babu tsammani wasu zafafun hawaye masu raɗaɗi suka ziraro suka malale saman kuncinta.


"Malam Shagala gaskiya ya kamata kayi wani abu a kan al'amari na, lokaci nata ƙurewa kar zuciyata tayi bindiga a kan soyayyar da na daɗe ina dakonsa kan Jalal. Shekaru mikakku har ashirin da uku ai ba zancen yau ba ne."


Kuka yaci mugun ƙarfinta, da gudu ta nufi gaban dressing mirror ta ɗauki wani kwallin gargajiya ta mallaka wanda aka kawata shi da fatar damisa. Wannan shine saƙon da Aljani Labari ya karbo mata a wajen Malam Shagala.


Ta kwashi shekaru tana dakon soyayyar mijin kawarta Jalal. Ta bi duk hanyoyi mafi sauki da tasan zai gane tana ƙaunarsa amma bata ci nasara ba. Shi ɗin ya daɗe da karantar halin da take ciki a kansa amma fuskewa kawai yayi sannan ya bar sakar mata fuska. Ita Haj. Nafeesan ce kawai kanta a doɗe da bata fahimci komai ba har kawo wannan lokacin.


Shekarun Haj. Haire 48 a duniya amma bata taɓa aure ba, Jami'a ɗaya suka yi tare da Haj. Nafeesa da Jalal, kuma tun bashi da komai take ƙaunarsa kawai dai alkunya ta 'ya mace ne ya hana ta bayyana masa. Shi kuma kawarta Nafeesa ya so, ita kuma Nafeesan a lokacin bata sonsa sai daga baya data ga ya kuɗance ya kuma samu daukaka a sannan ta dawo gareshi, duk da yazo baya yinta amma sai da tayi shige da fice ta samo kansa har ya aureta.


Ba ƙaramin hali Haire ta shiga ba da jin bayanin da Nafeesa tayi mata. Sai dai kuma tayi koƙarin kai zuciyarta nesa ko kaɗan bata fito ta nuna ba. Ta ci alwashin auren Jalal amma har yau buri bai cika ba.


Kwallin za ta fara amfani dashi wajen jawo hankalin Jalal gareta, idan har aka ci nasara to tabbas sauran aikin zai zo da sauki.


Yanzu ta wacce hanya ya kamata ta bi don ganin ta cimma wannan nasara a sauƙaƙe duba da yadda ko kaɗan Jalal baya ƙaunar ganinta kusa dashi?

 

Zama tayi a kan tiles rike da kwallin tana tunanin mafita.


***

*JAY. ALKALERI'S KITCHEN.*


Tun daga bakin gate Saffy ta sake baki tana ƙarewa katafaran gidan abincin kallo saboda haɗuwar wajen ma wani abin tsayawa kallo ne. 


Ga ma'aikata nan kowa cikin shiga me ɗaukar hankali very neat da su, kowanne sanye da rigar kuku wanda ta gabansa an rubuta da manya haruffa da kalar ja 'JAY. ALKALERI'S KITCHEN' a bayan rigar kowanne kuma an rubuta sunan ma'aikaci, wani kaga 'Chef Sam', 'Chef Zarah', 'Chef Rufa'i', da sauransu. 


Ma'aikata Sai up and down suke suna attending ma customers, sam ba harkar wasa a lamarinsu. They look quiet serious and disciplined. Sosai abin ya matukar birgeta har sai data kasa hakuri tayi magana don ita Saffy ko kaɗan bata cutar kanta muddin abu ya birgeta ko akasin hakan sai ta nuna.


"A Gaskiya an tashi kaina, koda gani ba sai an faɗa maka ba, me gidan abincin nan shi ɗin professional ne, be fito ba sai daya shirya." 


Murmushi Muwaddah tayi, bayan tayi parking a harabar gidan abincin ta ce.


"Ai duk yadda kake jin labarin Executive Chef Jalal to wallahi ya zarce tunanin mutum, sai ma ka gansa a zahiri zaka raina kanka."


"Really?" 


Saffy ta watsa mata tambaya fuskarta shimfiɗe da tsananin mamaki. 


Muwaddah ta ce"Duk abin da kika ji na faɗa akansa to lallai babu karya a cikin zancen. Shi ɗin mahaifi ne ga Samha me gidan mata, kuma ita ɗin matar yayana ce, Dr. Haseeb Aliyu Gamawa."


"What? Ita Samha ɗin?"


"Ita fa, na san dole zaki santa tunda Gidan matan ai anan cikin unguwar da kike zaune yake. Kuma bayan haka ma ina kyautata zaton mafi yawan mutane sun san da zamanta, don ina da labarin cewa gidan nata ya fara karɓan bakuncin mata daga kasashe daban-daban na yankin Afrika. Amma na tabbata duk wannan shaharar tata sai ta jira mahaifinta saboda shi fa har ƙasashen ketare sun san da zamansa."


Nan tayi ta bata labarin irin shaharar da Chef Jalal yayi a idon duniya da tarin nasarorin daya samu har suka isa VIP section sai hirar kawai take mata. 


Saffy kam gaba ɗaya ta tattara hankalinta zuwa ga Muwaddan ne don sosai hirar ke mata daɗi, nan take kawai ta ji Chef Jalal ya kai makura wajen birgeta. 


VIP section, waje na musamman ne da aka kebance na muhimman mutane irinsu Muwaddah. 


Duk wani irin cima da suke marmarin ci daga ita har 'yan gidansu ko ƙwandala Chef Jalal be yarda a ƙarba a hannunsu ba kasancewar su ɗin ai sirikansa ne. Shiyasa Muwaddah a kowane lokaci ita da Raihan suke iya zuwa gidan abincin kai tsaye su kwashi girki. 


Raihan ma ta mayar da gidan abincin kamar madafin gidansu. Son banzarta ya yi yawa har abin ma ya koma bawa Muwaddah haushi amma babu yadda ta iya da ita, dole ta zuba mata ido.


Sai santi kawai Saffy ke yi na abincin da suka yi oda kasancewar bata taɓa ci ba sai yau, Muwaddah nata ƙyaƙyalar dariya abinta.


"Ƙawata anya ba zaki min hanya a ɗaukeni aiki a gidan abincin nan ba? gaskiya ni dai wallahi ban taɓa shiga gidan abincin daya birgeni kamar wannan ba, wannan shine ake kira da capacity iya capacity."


 Cike da mamaki Muwaddah ta ce,


"Executive Chef Jalal fa baya kwasan anyhow chefs, duk wanda kika gani a cikin gidan abincinsa to professional chef ne, ai shiyasa gidan abincin nasa yasha banban da sauran da kika sani. Tukunna ma meyasa a tashin farko kika nuna sha'awar aiki da Jay.Alkaleri's kitchen? Ko don birgeki da chefs ɗinsa suka yi ne?" 


Kai tsaye ta ce "Ba zanyi karya ba tabbas an birgeni, bayan haka kuma dama na daɗe ina sha'awar zama professional chef damar hakan ne da ban samu ba, amma ina kyautata zaton a yanzu zaki taimaka min wajen ganin na samu cikar burina. Muwaddah Ina ji a jikina cewa shigowarki rayuwata alkhairi ne, don girman Allah ki min wannan alfarman sbd in samu abin dogaro da kaina ni ɗin marainiya ce."


Hawayen da suka cika kwarmin idanunta suka gangaro kan fuskarta. Sosai Muwaddah ta tausaya mata har take jin a ranta kome zai faru sai ta taimaka mata.


Ta kwana da sanin cewa abu ne mai matukar wahala ta samu karɓuwa a wajen Chef Jalal idan akayi duba da tarin ma'aikatan dake karkashinsa, kaf ɗinsu ƙwararru ne, sam baya ɗaukan 'yan koye-koye.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace,

"Na ji zan taimaka miki amma me kika iya daya danganci girki don hakan zai zo mana da sauki. Kin ga koda ace baki ƙware ba, Chef Jalal zai iya sa ayi training ɗinki har ki zamo ƙwararriya amma hakan bazai samu ba har sai ya tabbatar da cewa lallai kina da ɗan skills na iya girki a tattare dake."


"Ina da ƙwarewa a ɓangaren dangin snacks, kamar _Occasional cakes_ like birthday cakes, wedding cakes, da sauransu. Sai kuma _All-Occasional cakes_ kamarsu; Carrot cakes, red velvet cakes, da sauransu. Muwaddah na iya sarrafa filawa ta hanyoyi daban-daban fiye da tunaninki wanda saina sa kin tabbatarwa kanki da lallai kowa da baiwar da Allah yayi masa. Sai dai ban sani ba ko zan iya kasancewa ƙwararriya a wajensa idan akayi la'akari da yadda kike ta zuzuta min ƙwarewarsa."


 Cike da gamsuwa Muwaddah tace

" In sha Allahu Safiyya zan taimaka miki, idan ki kayi beating expectations ɗinsa ma na tabbata yana iya rubuta sunanki cikin waɗanda zai kwasa zuwa sabon katafaren branch ɗinsa ta ƙasar birtaniya da ake kan kafawa a halin yanzu....."


 "....ke! ƙawata don Allah are you serious? Waya ga su Safiyya a ƙasar masu jajayen kunne? Oh my God! Wallahi I can't wait." 


Ta furta tana me bushewa da dariyar farin ciki har da bubbuga kafafunta a ƙasa yadda kasan an tabbatar mata da cewa already ta riga ta samu karɓuwa ne. 


"Wallahi Muwaddah ba zan baki kunya ba don Allah tashi muje ki musu magana, I can't wait any longer." 


Ta miƙe tsaye tana jan hannunta, ta tilas mata dire kofin madarar tufan da take sha. Hakan kuwa ya ɗan sosa ran Muwaddah amma sai ta shanye ta ce" Don Allah meye haka? Shi fa matattakalar nasara a sannu ake binsa ana takawa, a natse kuma cikin hikima. Sam ba'a masa gaggawa idan ba haka ba ina me tabbatar miki da cewa tun a takun farko kina iya zamewa ki faɗi."


Sosai ta fahimci abin da take nufi, ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Kuma fa haka ne! Am so sorry wallahi ni ɗin na kasance me gaggawa da kuma bala'in naci akan duk abin da raina keso shiyasa kika ga ina neman rasa duk wata natsuwata. To, yanzu ta ina ya kamata mu fara?"


Tayi mata tambaya bayan ta koma mazauninta, sosai ta tsareta da dara-daran idanunta masu ɗauke da zallar burin abin da tasa a gaba.


"Kamar yadda na faɗa miki inaso mubi komai a sannu don ganin kin cika burinki. Haɗuwa da Executive Chef Jalal ba abu ne mai sauki ba, dole sai an haɗa da strong connection shiyasa nake tunanin in yi ma Yaya Haseeb magana. Zan zayyane masa bukatarki tunda ai kin ga shi sirikinsa ne, kai tsaye zai iya ganawa dashi, so please ki ɗan ara mana lokaci I will get back to you in sha Allah." Acewar Muwaddah kenan.


Ajiyar zuciya Saffy ta saukar, fuska cike da murmushi ta ce"Allah yasa in ji alkhairi daga gareki ƙawata."


"Ameen...yauwa tashi muje mota na baki sakon naki tunda yanzu dai tumbinki ya cika, dama kayan dinner ne da aka ɗinka ma sister ɗina sai kuma tafiya ya kamata wanda zai hana mata samun damar halartar bikin, to shine dana ga yanayin jikinku ɗaya sai nayi tunanin kawai na kawo miki kayan kema ki saka mana anko."


Saffy har kasa magana tayi tsabar mamakin daya cikata, dakyar ta iya cewa " Anya ina da kuɗin biya kuwa ? Da kayan da kuɗin ɗinkin idan aka haɗa nawa zai kama?"


"Dubu ɗari da ashirin ne kacal.."


Hannu takai ta buga ƙirji ta ce

"A kira ni da 'yar wa ? Wallahi bazan iya siya ba kiyi hakuri abin na manya ne bana YA-KU-BAYI ba, kar ki dami kanki zan saka duk abin da Allah ya hore min. Idan na samu atampa ta 'yar leda da aka bazawa ɗinkin fita kunya na saka ai an gama ko? sai dai idan korata zaku yi."


Muwaddah ta fashe da dariya tace,

" Wallahi kina da ban dariya, to ai ni kyauta zan miki bance ki bani ko sisi ba, Allah ya sawwake in zo da wata sutura tawa wai kisa kuɗi ki siya, ni dake fa an riga an zama ɗaya."


Mutuwar zaune Saffy tayi da jin wannan zance, lallai kirkin Muwaddah ya wuce duk yadda take zato. Godiya tayi mata sosai kamar zata goyata sannan suka tashi don tafiya.


Sai da suka fito ne a lokacin idanun Saffy ya kai saman wall na kofar shigowa, katon picture frame na  Yallabai ta gani an manna a bango, sanye cikin cikakken shirinsu na 'yan kuku masu capacity. 


Sosai yayi masifar kyau, a kasan hoton an rubuta boldly _*'Executive Chef Jalaluddeen Alkaleri'*_ a ƙarƙashinsa kuma aka rubuta da ƙananan haruffa _*'Head chef & founder/owner of Jay.Alkaleri's kitchen.'*_


Cak! Ta tsaya ta kasa gaba, gabanta ya shiga harbawa da sauri-sauri, ta fara tunanin inda ta taɓa ganin wannan fuskar.....


*Mu je next page.*🤣


NAGODE ALL❤️