BIYU A ƊAYA

Chapter 25

by @barista

BIYU A ƊAYA 
    (Don't judge a book by its cover)


Page 25
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
The five ink legends


Magana ta ƙaƙare, ta kasa cewa komai, zuciyarta ta soma bugawa saboda ta tuna wahalar da tasha a hannun wannan azzalumin mutumin, sam bata yi wa Mamanta ƙarya, kuma bata ɓoye mata komai, duk abin da ya dame ta me kyau da mara kyau faɗa mata take yi mai tsaye, to amma kuma wannan lokacin taji ba zata iya faɗa mata abin da ya kusa faruwa da ita a wannan ranar ba, bata so Mamanta ta shiga damuwa ko ta kasa bacci...

"Bilqees tambayar ki nake yi kin yi min shiru, me yake faruwa ne? Me ya same ki a hannu da ƙafa? Ya aka yi kika ji ciwo?"

Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarfi, ta ƙwakulo murmushin dole ta ce 

"Mama ba komai ciwo kawai naji amma hakan ba zai sake faruwa ba"

"Bangane ciwo ki ka ji ba, menene ba zai sake faruwa ba?"

"Faɗuwa nayi"

Zuciyar Mamanta ta buga, da mamaki take bin Bilqees da kallo karon farko da ƴarta ta ɓoye mata abu, tun da ta taso bata taɓa yi mata ƙarya ko ɓoye nata komai ba, ko tusa ta yi sai ta faɗa mata, amma kuma jin abin da ta faɗa mata yasa sam Mamanta bata amince da cewa gaskiya bane, tasan ba wannan ne asalin abin da ya faru ba...

"Mama ki kwanta ki yi bacci, na sha magani bacci kawai zan yi"

Hankalin Mamanta ya tashi, me yasa Bilqees ta ɓoye mata abin da ya sameta, shin girma tayi ne? Ko kuma zurfin ciki ta fara. Ta sauke numfashi bata so ta takure ta sai ta faɗa mata, tun da ta ɓoye, Mama ta kwanta, bata sake cewa komai ba har bacci ya ɗauke Bilqees. Ta tashi jiki ba kwari ta shigo side na ALAJA, ta ci karo da Abida tana fitowa daga ɗakin, ko ci kanki basu cewa juna ba kowacce ta ɗauke kai Maman Bilqees ta shige ciki, ALAJA bata palour kai tsaye ta shigo cikin ɗakin, ta tadda tana kwance kan gado, ta iso ta zauna bakin gado suka kurawa juna idanun, ALAJA ta tashi ta zauna tasan me wannan kallon yake nufi, ta ce

"Menene?"

"Ke zan tambaya ai"

Murmushi ALAJA tayi ta ce

"Na gaji bacci nake ji, kin san irin aikin mu"

"Me ya sami Bilqees har taji ciwo a hannu da ƙafa?"

"Bata faɗa miki bane?"

"Cewa ta yi ciwo ta ji"

"To abin da ya faru kenan, ciwon ta ji shiyasa ta faɗa miki"

"Ba gaskiya bane, jiki yana bani abin da ta faɗa min ƙarya ne"

"Look Maman Bilqees, yanzu ƴarki ta girma, tayi wayo, tasan ciwon kanta, zata iya kulawa da kanta, me yasa sai kin matsa wa kanki sai kin san komai da ita, tun da ta ce miki ciwo taji sai ki amince da hakan"

"Shekaru ashirin da biyu take nema ina girma anan, har yanzu yarinya ce, bata yi hankalin da zata iya tsayawa rayuwarta ba"

"Kina baiwa kanki wahala, me yasa kika damu da rayuwarta fiye da taki? Me yasa akanta kika hakura da duk wani farin ciki kika bata, da yanzu kin zama wata aba, amma ina kin ɗauki tunanin ta kin ɗaurawa kanki"

"Dole na damu da ita, bani da wacce zan gani nayi farin ciki sai ita, ita ce farin ciki na, ita ce rayuwata, ita ce ta rage min a duniya, ita ce ahalina"

"To sai ki yi ai, ina me tabbatar miki za ki mutu a tsaye, ai ko ba za ku dawwama tare ba dole tayi aure"

"Na sani shi ne farin ciki na, naga Bilqees a ɗakinta"

"To ita da ko saurayi bata da shi ina wani, zancen aure, kin ga bacci nake ji"

"Ina so ki yi min wata alfarma"

"Oh my God! Menene kuma?"

"So nake Bilqees ta dinga dawowa da yamma kamar yadda take yi da, bana so ta kai dare"

Murmushin takaici Alaja tayi, ta ce

"Wai Maman Bilqees bangane ba, me kike nufi ne? Kina so ki ce min ni bana sonta, ko bana kulawa da ita, ni ina ganin ma na fi ki sonta"

"Na sani"

"To zan duba na gani"

"Na gode"

ALAJA ta kwanta, Maman Bilqees ta ce

"Me Abida ke yi da wannan lokacin anan"

Wani kallo ALAJA tayi mata na wani lokaci sannan kuma ta ƙwakulo murmushi, ta girgiza kai ta ce

"Kishi kike yi don tazo wajena?"

Maman Bilqees ta sauke numfashi ta ce

"Kin san me nake nufi, nasan ba za ta wuce ni a wajenki ba, amma kuma ai ta daina shigowa bangaren ki, me yasa yau ta yi?"

"Wani abu ne ya kawo ta"

"To sai da safe"

Maman Bilqees ta mik'e ta fice, ta dawo ɗakinsu ta kwanta.


*****

DR Waahab yana shigowa hotel ya tsaya a ƙofar ɗakin Dr Isma'il, ya murɗa ƙofar yaji a buɗe take hakan yasa kai tsaye ya kusa kai ya shiga ya tadda shi zaune daga shi sai gajeren wando ko vest babu yana kallon tv, ransa ya mugun ɓaci da ya ɗaura idanunsa akansa, kamar an ce Dr Isma'il ya ɗago, ganin Dr Waahab a tsaye yasa ya miƙe tsaye cike da mamaki da tsoro yayi tunanin ya rufe ƙofar ai, kan ya ankare Dr Waahab ya iso gare shi  ya kai masa naushi a baki nan take baki ya fashe jinin ya soma fitowa, ya shaƙosa sai da yaga ya kusa daina numfashi sannan ya kyale shi, ya nuna shi da yatsa tare da cewa 

"Da a lokacin ne, da na yi maka fiye da haka, mara tausayi kawai, ashe da ɓoyayyiyen hali gare ka, tirrrrr!"

Yana gama faɗin haka ya fice cikin zafin rai, Dr Isma'il sai da yaga Dr Waahab ya fice ya leƙo ya dinga ƙudunduna masa zagi, sai da ya yi me isar sa sannan ya dawo cikin ya rufe ƙofar ya yi treating kansa.

DR Waahab yana shiga, ya wuce ɗajinsa ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shower ya jima sannan ya fito, ya shirya cikin kayan bacci ya hau bed ya kwanta yana sauke numfashi. A hankali yake tuna yadda su kayi da me restaurant, to wacece wannan Bilqees ɗin? Me yasa matar take da iko da ita haka? Amma ta taɓa faɗa masa tana da Mama kuma tana gaida shi. Ya lumahe idanunsa baya so brain nasa ya yawaita tunani kawai ya kawar da komai daga cikin zuciyarsa har bacci ya sace shi.


**********************************

WASHEGARI 

Ta kammala shirin ta kamar yadda take yi, ta fito zuwa palour ta tadda Mamanta ta shirya musu abin karyawa, soyayyar doya ce me haɗe da fulawa, sai shayi da madara ta zauna tare da cewa 

"Mama kin san kuwa ina son doya"

"Na sani shi yasa ma jiya naje kasuwa na sayo da yawa"

"Mama kasuwa?"

"Eh kasuwa mana"

"A ina kika samu kuɗi?"

"Ragowar kuɗin dake wajena ne"

"Kai Mamana Allah ya bar min ke"

"Amin"

"Jiya Alaja ta bani dubu goma"

Ƙirjin Mamanta ya buga, jin abin da Bilqees ta ce, ta sauke numfashi ta ɓoye mamakinta da damuwarta ta ce

"Dubu goma akan meye?"

"Kawai ta bani ne"

Maman Bilqees ta san haka kurum ALAJA ba za ta yi kyautar kuɗi ba tare da ta sami riba ba, ...

"Mama ga ATM nawa ki cire kuɗin ki yi amfani da shi"

"Ai jiya na yi cefane sai dai ko bayan kwanaki biyu"

"To ga shi nan ki ajiye"

Ta ajiye ATM card nata kusa da Mama sannan ta ci gaba da cin abinci, sai da ta kammala ta yi wa Mama sai ta dawo ta fice zuwa ɗakin ALAJA a lokacin tana ƙoƙarin fitowa ta ce

"Bonjour Maa"

"Ah my Bilqees har kin shirya?"

"Eh ma"

"To ya ciwon naki?"

"Ya yi sauƙi"

"To mu je"

Suka fito zuwa bakin titi, mashin guda suka hau da Alaja zuwa restaurant, suna sauƙa ta biya suka shigo, ta ce Bilqees ta shirya wa Yallaɓai likita breakfast me rai ta kai masa, ta ce to, ta wuce kitchen ta haɗa masa, sai da ta kammala sannan ta dawo ɗakin ALAJA ta tadda tana lissafi ta zauna tare da cewa 

"Maa na kammala"

"Yawwa my Bilqees, shi yasa kike burgeni, to sai ki kai masa"

"To"

Ta tashi ta ɗauki rigar Yallaɓai likita, ta ce

"Zan kai masa rigar sa

"Yawwa hakan ya yi"

Ta fito ta ɗauki food carrier ta wuce international hotel.


*******

DR Waahab ya shirya cikin suit Ash color ya yi masa kyau, sai ƙamshi yake yi, yana tsaye gaban mirror wayarsa ta yi ringing yana dubawa yaga Daddyn Suhaima ne ya ɗauka tare da cewa 

"Barka da safiya Abbie?"

Daga cikin wayar Abbie ya amsa da 

"Barka dai Babangida, shiru kwana biyu"

Dr Waahab ya sosa keyarsa kamar yana gaban Abbie ya ce

"Ayyuka ne su ka yi min yawa, amma ina binka a raina"

"Ah to Allah ya taimaka tun da lafiya, daman haka aiki ya gada"

"Eh fah ya jikin Mommie?"

"Ai jiki Alhamdulillah yana sauƙi"

"Allah ya ƙara sauƙi"

"Amin"

Sun ɗan taɓa hira sannan su ka yi sallama, Dr Waahab ya kira Daddynsa suka gaisa sun jima suna tattaunawa, sannan su ka yi sallama, ya zauna a bakin bed yana danne danne a wayarsa kira ya sake shigowa ganin Ashfat ne yasa ya bari sai da ya katse sannan ya kirata bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa 

"Morning Ya Waahab"

"Morning A'isha, ya mutanen gida?"

"Kowa lafiya"

"To madallah"

"Ya Wahaab na samu aiki"

"Congrats na taya ki murna"

"Na gode, ba ka ce a ina na samu ba?"

"Oh! A ina kika samu?"

"A bank"

"Uhm banker"

Ta yi murmushi me sauti kamar yana ganinta ta ce

"Eh satin da za mu shiga ma zan fara fita"

"To ai result naki bai fita ba"

"Alhaji babba ne ya nema min ta hannun abokinsa a waiting results"

"Ikon Allah ya yi kyau"

"Na gode bye"

"Thanks"

Ya faɗa ya katse wayar, ya sauke numfashi tare da lumshe idanunsa, Ange ta faɗo masa cikin ransa, ya tuna kalamanta na ƙarshe

"Kana da kyakkyawar zuciya"

Ya sauke numfashi, ya ji an turo ƙofar, ya kalli bakin ƙofar yaga Bilqees ce, ta ƙarso tare da sallama ya amsa ta ce

"Yallaɓai barka da safiya"

A hankali ya kalleta tare da cewa 

"Yawwa, ya jikin naki?"

"Bana jin ciwo sosai"

"Ok ga magani akan dress mirror in kin gama sai ki ɗauka ki tafi da shi kina sha"

"To na gode Yallaɓai"

Ta iso tare da miƙa masa rigar sa ta ce

"Ga shi na gode sosai, Allah ya saka da gidan Aljanna"

Ya daɗi addu'ar ya sauke numfashi tare da cewa 

"Amin"

Ya ɗauki food carrier zuwa palour ya zuba abin karyawa ya soma ci, ita kuma ta maida hankalinta ta ci gaba da aikinta, har ya kammala bai fita ba sai da ta gama aiki ya taso ta gaba suka fito yana gani har ta fice, tausayi ta ba shi, yaso ya ce ta huta da kawo masa abinci to amma ya san wannan Madam ɗin zata tura ta wajen wani kuma ya cutar da ita...

"DR Waahab how fah?"

Ya kalli Dr Faisal tare da cewa 

"Normal fah, gari ya waye ko"

"Ai bana so gari ya waye a ce mu fita, na fi so na yi ta kulawa da Beb"

Murmushi Dr Waahab ya yi ya ce

"To sannu me Beb"

"Yawwa sannu gwauro"

"Zan baka mamaki"

Cewar Dr Waahab yana murmushi, Dr Faisal ya ce

"Ai an wuce wajen, mamaki na nawa gaka ba aure ashe ma tuzuru zan ce ba gwauro ba"

"Uhm lokaci ne bayyi ba"

"To Allah ya kawo lokacin kusa²"

"Amin"

Suna hira har suka shige mota suka fice ba ki ɗayansu.....


***********************************

Ta iso wajen kamar yadda ta saba, ta tadda duk sun yi tagumi, babu me magana ko ƴar wasan da suka saba yinta ma babu, tana isowa kusa dasu ta ce

"Abokaina"

Suna jin muryarta suka mik'e da sauri suka rungume ta, suna 

"Oyoyooooo kyakkyawar Aunty"

"To ku cika ni kada ku kadani"

Suka sake ta, ta zauna tare da cewa 

"Duk ku zauna"

Suka zauna, ta ce

"Aicha zo nan"

Ta iso ta zauna a cinyarta ta ce

"Yau babu gaisuwa?"

"Lah barka da safiya Aunty kyakkyawa"

Suka haɗa baki wajen faɗin hakan, ta amsa da 

"Yawwa barka dai, da fatan kuna lafiya?"

Suka amsa da 

"Lafiya kalau"

Ta raba musu alawa da biscuits kamar yadda ta saba, suna murna suna sha, yau ma su ka yi ta tambayar ta, uncle yaƙi zuwa haka ta yi ta lallaɓa su akan aiki ne ya riƙe sa, suna zaune tana jansu da hira sama sama kamar tambayar lafiyarsu da masu rainonsu, suna bata amsa da lafiya...

Kamar daga sama su ka ji muryarsa yana cewa

"Good morning friend's"

Aiko suna jin muryarsa suka mik'e ba shiri suna 

"Oyoyo"

Suka rungume shi, yana murmushi yana shafa kansu yana cewa

"I'm sorry friend's"

Ya kalli inda Ange take zaune yaga kanta a ƙasa ya sauke numfashi, ya iso inda take ya zauna tare da cewa 

"Friend's na kawo muku chocolate da BOBO"

Suna murna ya raba musu, nan take suka buɗe suna sha, da kansa ya buɗe wa Aicha ya bata tana sha...

"Ina kwana?"

Cewar Ange ya amsa yana kallonta

"Lafiya Angel ya hidima da marayu?"

"Sai godiya"

"Allah ya bada lada"

"Amin"

Ta faɗa cikin sanyin murya, ya kalleta kamar akwai sauyin yanayi a tare da ita, duk jikinta ya yi sanyi, bata da kuzari. Aicha ta zauna a cinyarsa tana wasa da sajensa da yasha gyara sosai, tana kallo, ya yi murmushi ya lakuci hancinta ya ce

"Haneef ka kaisu gida"

"To uncle"

Haneef ya sanya su gaba, suka tafi, ya juyo sosai yana kallon ganin taƙi su haɗa idanu yasa yaji wani iri kuma yake tunanin tabbas akwai abinda yake faruwa...

"Angel"

"I'm sorry uncle, zan faɗa maka wani abu, ina so ka fahimce ni"

Da mamaki ya dubeta, yana tunanin me take son sanar dashi?

"Menene?"

"Kai mutumin kirki ne, kana da kyakkyawar zuciya, kuma...


Ayi hakuri da typing errors, a ci gaba da haquri dani na rashin update akai akai abubuwane suka sha kaina amma in sha Allahu zan daidai komai da kuma lokacin update 



Ayi comments sannan ayi sharing fisabilillah