5
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
BAYA TA HAIHU
Ummu Maher (Mrs green)
Kuyi haƙuri na koma Mrs SHU'AIBU to amma da dama basu gane ni ba zan koma Mrs green ɗin domin ku masoyana.
5
Na tsugunna a gaban Baffa na ce "Wallahi Baffanmu na haƙura da Hammah Habibu don Allah kai da Ammi ko koma kamar da Wallahi ban san hakan za ta kasance tsakaninku ba da duk irin son da nake masa zan haƙura".
Baffah ya miƙe bai ce min komi ba, ina kuka na bishi da ido har ya isa wajen Ammi wacce take haɗa kaya a cikin ɗakinta, ya fara magana "Kin ga abin da kika janyo ko? Kin gwammaci ƴarki ta haƙura da abin da take so ko? Shin kin san abin da hakan zai janyo? To wallahi in har ni ne mahaifinta wallahi babu wanda ya isa yasa a fasa wannan auren in har kika ga an fasa to Allah ya ƙadarta dama can dole ne sai an fasa dama kuma ba matarsa ba ce".
Ammi ta ce "To sai me? Dama ka ji na ce a fasa ne, ita munafukar da ta haɗa komi ita ce da kanta ta ce ta fasa saboda haka ga ka ga tanan na bar maka ita, kuma ba zan canja maganata ba in Allah ya yarda wannan auren sai ya sanya ku kai da ita a cikin bala'i da masifa in sha Allah sai ta yi danasanin yin wannan auren".
Tana kaiwa nan ta ɗauke akwatin ta tayi waje, tana sababi na bita da sauri ta juyo ta cire min hannuna daga na ta da ƙarfi har sai da hannuna suka riƙe saboda azaba, ina kuka na ce "Don girman Allah Ammi ki dawo wallahi na haƙura da auren ki yafe mun".
Bata saurare ni ba ta yi tafiyarta, na durƙushe a wajen na saki wani irin kuka me zafi sai na ji na fara tsanar kai na domin duk ni ce na janyo komi, yau wai Baffanmu ne ya saki Ammi saboda aurena? Anya kuwa na yi wa kaina adalci? Anya kuwa auren nan ba zai zama ajalina ba kuwa? Duk ba ni da amsar waɗannan tambayoyin saboda Allah ne kaɗai yasan gobe.
Baffanmu yana tsaye, sai na ga ya yi saurin juyawa alamar ƙwalla ya fara a idonsa amma baya son na gani. Addah Hafsah da Humairah duk sun bi Ammi, daga ni sai Baffanmu a gidan haka na dinga rayuwa ni kaɗai tamkar munafuka ga shi ni kuma ba ni da wata ƙawa ballantana ma na faɗa mata abin da yake damuna, ga shi Baffah ya dakatar da zuwan Hammah Habibu gudun tashin hankali ya ce ya bari kawai a kawo masa ɗakinsa idan an ɗaura aure. Muna dai yin waya amma na kasa faɗa masa matsalar da nake ciki, duk da ya fuskanci da matsala amma na kasa faɗa masa abin da ban yarda da shi na faɗa wa wani komi kusancin da muke da shi sirrin gidanmu domin kuwa ba a yi ciki kaɗai domin cin tuwo ba an yi sa ne domin ɓoye wasu sirrikan.
Rannan na shirya na tafi gidansu Ammi, da yake Babu nisa tsakanin gidanmu da na su titi ne kawai ya raba mu. Ina shigowa gidan na hango Ammi tana wanki Addah Hafsah da Humairah suna tsere kansu da yake sati me zuwa ne bikinmu. Addah Hafsah ta wani haɗe rai kamar dai ba ita ce ta ce na bijire akan auren Hammah Hamzah ba, na yi mamaki sosai saboda ganin yadda ta haɗe girar sama da ta ƙasa Humairah ta haɗe min rai duk suka haɗu suka yi kamar basu sanni ba kowa yaƙi kula ni, nan da nan na fara kuka ina cikin kukan ne Goggo mahaifiyar Ammi ta shigo da fara'ar ta tace "Tsohuwa yau kece a gidan na mu"... Ganin ina kuka duk sai ta damu tunda ita ma tasan me yake faruwa a tsakanina da Ammina.
"Fatima kina azabtar da yarinyar, akan mi Allah ya baki ƴa kike wulaƙantawa akan ta zaɓi sunnar ma'aiki kuma wallahi da arziƙi da talauci duka na Allah, saboda haka ina me gargaɗinki da ki janye kalaman ki akan wannan yarinyar saboda shi Allah da kike ganinsa shi yasan gobe, saboda mijin da za ta aura ba shi da kuɗi shi kenan sai a guje shi? To a gaskiya baki kyauta ba, ke naga ai mahaifinta ba shi da komi kuka yi aure uban wa ya hana ki aure da?.
Ammi ta magantu "To Goggo idan na auri mahaifinta ba shi da komi shi kenan mu a haka zamu ƙare? Sannan ni duk ma ba wannan ne damuwata shan giya da mahaifinsa yake, sannan ga caca shi kenan shima wannan ba abun dubawa bane?.
"Abun dubawa ne mana, amma ke kin jahilci abun ne saboda ba yaron ne yake yi ba, sannan don girman Allah ki bar wannan maganar yarinyar nan ta samu ta auri wanda take so ina ganin hakan zai fi mana baki ɗayanmu, sannan kuma ni ba ki da wajen zama a gidana inda kika fito cen za ki koma to idan ma banda abin kunya ya za a yi wai kamar ke ace kin dawo gida a mata a ɗakina kece babba ƙannenki mata uku ne duk suna ɗakin mazajensu babu ko ɗaya a gabana, sannan banda abin kunya ke kizo kice za ki zauna Ni kuma ga ni uwar mata tunda mahaifinku ya rasu sai kizo ki zauna min, bari Yayanku Sale ya zo da daddare ya maida ki ɗakinki ba anan za a yi min sakalci ba".
Ammi ta ce "Don girman Allah Goggo ki yi haƙuri, kina ganin wulaƙancin da Jaɓɓama ya yi min saboda ƴarsa ya sake ni ke duk hakan bai miki zafi ba Goggo?. Ta yi rau-rau da idonta alamar tana son yin kuka.
"Ai kinsan Allah ko saki uku ne sai kin koma kin yi zaman ƴaƴanki, uban waye ya ce kice a sake ki? Kin ga kada ki zo min da maganar banza Allah kisan yadda za kiyi domin ni yau za ki koma".
Tana faɗar hakan ta yi shigewarta ɗakinta tana me jin haushin ƴarta, muna nan zaune Yaya Hamza ya shigo yayanmu uwa ɗaya uba ɗaya sunansa ɗaya da wanda Addah Hafsah za ta aura wato Hammah Hamzah, sunan kakanmu suka ci wanda ya haifi su Baffanmu.
Shima sai nasiha yake ta yiwa Ammi, domin har ga Allah yana son auren ƙanwarsa da Habibu saboda yasan halayyarsa me kyau ce, zai riƙe masa ita da amana ya yi ta lallaɓa Ammi daga ƙarshe na ji tana faɗa masa wai dani da shi dama halin Baffanmu ne damu, ba mu damu da damuwarta ba da Baffanmu ne yake cikin damuwa da yanzu mun cire sa.
Wannan maganar ta ta tana ƙona min rai, amma babu yadda zan yi dole na yi mata biyayya mahaifiyata ce, amma batun ban damu da ita ba duk bai taso ba na ga saboda ita ne zan rabu da muradin zuciyata tabbas nasan da za a buɗe zuciyata da anga irin so da ƙaunar da nake yiwa Hammah Habibu amma saboda na faranta mata na ce na haƙura, banda ma Baffanmu ya ƙi yarda dana haƙura ko don mummunan furucin da ta yiwa auren, tunawa da wannan yasa na durƙusa a gabanta na riƙe ƙafafunta na ce" Ammi don girman Allah ki janye kalaman ki da ga kan aurena bansan me zai faru dani ba a gaba, ina tsoron na fuskanci mummunan ƙalubale a gaba".
Ta janye ni sannan ta ce" kinsan za ki shiga ƙalubalen kika nuna ni banda mutunci, tunda nake da mahaifinki duk da yana da zafi da faɗa amma ba a taɓa jin mun yi cacar baki bama balle muyi faɗa har ya sake ni ba, shi yasa na bar muku gidan ki aura masa wata mata..."
Tsawa Goggo ta daka mata sannan ta ce "Wai ke Fatsima wacce kalar macece? Waɗannan maganganun sun yiwa wannan yarinyar girma kina faɗa mata abin da ya girmi zuciyarta Wallahi idan baki yi da wasa ba nima akan yarinyar nan zan yi mugun ɓata miki, za kice an ya kuwa ni na haife ki? Ai ita ma rai ne a jikinta kuma ai kin ɓata min rai nima sosai, amma hakan na danne saboda kasan kema zuciyarki cike take da haushi, da ina son ƙuntata miki ko gidan nan wallahi ba za ki zauna ba".
Ta saki baki tana kallon Goggo, yarinyar da ta haifa a cikinta tana son haɗa ta da mutane mafi kusanci a rayuwarta. Hafsah ta dafa kafaɗar Ammi sannan ta ce "Dama ina yawan faɗa miki son da kika nunawa Mero ya yi yawa ga shi nan tun ba a kai ko'ina ba tana haɗa ki da mutanen da suka fi kowa muhimmanci a rayuwarki".
Yaya Hamzah ya kawo mata hannu zai dake ta Ammi ta ce "Kada ka sake ka dake ta ai ba ƙarya ta yi ba, balle ka dake ta kawai akan aurenta ne to na tsame hannuna bama zan yi faɗan ba balle ace na yi mugun fata gwara na yi shiru".
A ranar Ammi ta koma gidanmu, na yi murna sosai duk da bana ganin fara'ar Ammi amma a hakan ma na godewa Allah haka dai aka cigaba da shagalin biki amma ni tamkar ba amarya ba ba ni da wanda zai kula ni wai duk domin na auri talaka.
************
"Ammi wallahi bana son auren yarinyar nan kawai dai domin anfi ƙarfina ne sannan kuma ina kunyar Baffah ba zan ƙi auren ƴarsa ba, ke kanki Ammi kin san ba ita na so ba ƙanwarta na so amma yarinyar nan ta dage sai ni, ko da wasa ban taɓa son ta ba sannan bana so muyi aure na cutar da ita ko da ban san ta ba bazan cutar da ita ba balle na santa jinina ce".
Ammi ta dafa kafaɗarsa sannan ta ce "To ina so ka fara sonta ita ma, ita fa Maryam da kanta ta ce bata sonka to ni a ganina tunda Hafsah tana son ka ai za ku zauna lafiya".
Hamzah ya kasa cewa komi, domin yasan Amminsa ba za ta taɓa goya masa ba amma shi yasan dole sai BAYA TA HAIHU, tunda ba ita yake so ba ƙanwarta yake so shi dai yasan zama da wanda ba ka so akwai wuya.
A satin ɗaurin aurenmu Baffanmu yasa aka kira mu ni da Addah Hafsah, ya sanya mu a gaba ya yi ta mana nasiha me ratsa zuciya dukkanmu jikinmu ya yi sanyi, sannan ya ce wa Hafsah ta tashi ta tafi ni kuma na zauna.
Har a zuciyarta ba ji daɗi ba, ta yi abin da yake so ɗin.
Tana zuwa ɗaki ta fashe da kuka ta kalli Ammi, sannan ta ce "Wai Ammi me yasa Baffanmu ya fi son Mero ne? Yanzu fa tare ya kira mu ba sai ya sallame mu tare ba, amma ni ya kore ni ita ta zauna tsakani da Allah ya yi min adalci?.
Ammi ranta ya ɓaci sosai ta ce "Na faɗa masa ya rage son da yake wa yarinyar nan, amma ya ƙi saboda haka ne yasa nima nake nuna masa bana sonta domin ya ji haushi, saboda sunan babarsa ne to ai kema sunan babata ne dake ashe abun son kai ne".
Yaya Hamzah ya shigo, duk ya ji tattaunawar su ya yi gyaran murya haɗi da sallama sannan ya shigo ya zauna a bakin gado ya ce "Ammi kin ga wannan banbantawar da kike nan gaba ke zai dinga yiwa ciwo, kuma maganar Mero da kuke yi tsakani da Allah tun da ke kin nuna baki sonta shi sai yaƙi sonta, kar fa ki manta Ammi ke fa kika haifi Mero kika ɗauki cikinta har kika haife ta kika shayar da ita, to duk son da Baffah zai mata ai ba zai kai naki ba domin kuwa kin santa tun tana karama kin san abin da za ta yi da wanda ma ba za ta yi ba, to meye abin damuwa anan?.
Jikin Ammi ya ɗan yi sanyi, amma fa har yanzu ba ta sakko ba da dai Baffah zai ce ya janye auren Mero da wancan matsiyacin yaron da ta ji daɗi, da kuma ta yafewa Mero amma tunda sun nuna mata shi da Mero ƴan taurin kai ne za ta nuna musu ta fisu.
Baffah ya ce "Mamana".
Na ce
"Na'sam"
"Ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, abin da yasa na ce Hafsah ta tashi akwai abin da ba zan faɗa a gabanta domin za ta ɗauka ai nima bana son auren ki ne, amma har ga Allah bana so Uwata saboda ke kanki kin san duk wanda bai da sana'a bai dace ka bashi ƴarka ba amma ganin kina sonsa sannan shima bai da wata matsala yasa na yarda ki aure shi, ba don komi ba saboda raya sunnar ma'aiki ne amma ki faɗa masa ina nemansa da daddare".
Kai na yana ƙasa na amsa masa, ya bani umarni dana tashi sannan na ta shi. Ina ganin Baffanmu yana ta yi min kallon tausayi saboda irin rayuwar da zan shiga, saboda shi ya kasance ɗan kasuwa duk da ba wani me kuɗi bane amma kusan mun fi ƙarfin komi na rayuwa, amma yanzu zan koma rayuwar da tufafi ma sai ya gagare ni saboda kana ganin Habibu kasan tufafi ya musu ƙaranci a gidansu duk da mutum ne shi ne tsafta amma kana ganinsa kasan babu ta baibaye su.
Na faɗawa Hamma Habibu a waya nan da nan kuwa ya zo ya samu Baffanmu, ko da ya shigo gidan na mu Ammi tana tsakar gida tana tuwon dare, ko da ya gaishe ta ba ta amsa ba sai ce wa ta yi "Uban waye ya ce ka shigowa mutane gida? Ko kuwa an faɗa maka gidan ƴan caca ne nan? To maza ka ficewa mutane daga gidan tunda ba gidan ƴan giya ba..."
Tsawa Baffanmu ya daka mata sannan ya ce "Ni na ce ya zo, kuma wallahi Fatsima idan kika ƙara zaginsa ranki zai yi mummunan ɓaci". Yana faɗar hakan ya shige ɗakinsa ya bar Ammi a tsaye tana mamakin yadda aka yi Habibu ya samu shiga a wajen Baffah har yake da fifita Habibu akan ta, ta yi ƙwafa ta cigaba da aikinta tana yi tana sababi.
"Habibu"
Ya amsa.
"Na'am Baffah".
Baffah ya ɗan nisa sannan ya ce "Dama na kira ka ne domin na yi maka nasiha sannan na damƙa maka amanar ƴata, sannan kuma na baka jari ko da dubu ɗari ne ka ha jari saboda aure babu sana'a ba zai yiwu ba".
"Haka ne Baffah, amma bana son ɗora maka nauyi dama ina so na dinga zuwa ko da dako ne saboda na samu abin da zan kula da Mero".
Baffah ya ce "Duk da haka ba zan barka ba, a da nima ba ni da shi da dakon na fara har na samu na ciyar da mahaifiyarsu dama su kansu kuma ka ga yanzu Allah ya rufa min asiri, ina da nufin asiri dai-dai gwargwado to ka ga babu abin da zan cewa Allah sai godiya, tunda Allah ya hore mun ni kuma zan taimake ka in sha Allah, fatan mu dai Allah ya taimake mu baki ɗaya Allah ya baku zaman lafiya me ɗorewa". Habibu ya amsa da Amin, Sannan Baffah ya ba shi kuɗi dubu ɗari ya ce yaje ya nemi sana'a kafin biki, ya dinga godiya sosai ya tashi ya yiwa Baffah sallama sai me kuma? Ammi ya gani a bakin ƙofa tana masa wani irin kallon tsana, ya sauke kyawawan idanuwansa ƙasa saboda ba ya son kallonta tana masa wannan irin kallon, ya sanya kansa domin fita daga gidan Ammi ta fara magana wacce ta yi sanadin saurin juyowar Habibu.
Mrs green ce✍🏾