Chapter 14
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Ha蓷uwar rayuka da 茩addara ta tattara wuri guda.*馃敟馃挃}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*#WATTPAD: HAFNANCY01*
*#AREWAPEN:HAFNANCY*
*SADAUKARWA GA UWAR茒AKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 14.*
"Ya kuma kika tsaya? Meya faru?" In ji Muwaddah dake gabanta.
Hoton ta nuna mata da hannu tana fa蓷in"Shi ne me gidan abincin ko?"
Murmushi Muwaddah tayi bayan ta kai dubanta kan hoton, sannan tace"Eh, shi ne dai da nake ta baki labarinsa."
Huci me zafi Saffy ta sauke sannan ta ce"Wallahi ni kamar na ta蓳a ganin wannan fuskar a wani wuri amma ko dai kama ne?"
Gaba 蓷aya kanta ya yi murfi, ta manta cewa shine mijin Jidda. Kodayake ba haddace fuskarsa tayi ba, ganin sama-sama suka yiwa juna a wannan ranar.
"Babu mamaki kin ta蓳a ganinsa, amma na fi tunanin kama kawai yake miki da wani, kin san fa ance kowa na da wanda yake kama da shi."
"Hakane kam! Kuma shi wanda nake ganin yana kama da shi, wallahi ko wu茩a za asa min a wuya bazan iya tuna a inda na ta蓳a ganinsa ba."
Ita dai Muwaddah sai dariya take yi, haka suka fice Saffy na ci gaba da ko蓷a ha蓷uwarsa.
"Gaskiya my future boss ya wuce duk yadda ma nake tunani, kuma a hakan wai shi ya haifi Samha me gidan mata ko?"
"Of course Yes! Ga shi kamar be isa ya haifi irinta ba, yana da jiki me 蓳oye shekaru."
Saffy ta ce"Hmm gaskiya ni kaina mamakin hakan nake, duk da ban ta蓳a ganin 'yar tasa ba amma na san da cewa ita 蓷in babbar macece, sai dai ban yi tunanin zai haifi kamarta ba."
"Au! baki ta蓳a ganinta ko a hoto ba? To gaskiya ya kamata lallai ki halarci bikin nan namu saboda zai kasance tana wajen tun da kinga she's part of our family."
Gya蓷a kai kawai Saffy tayi tana sakin murmushin da ita ka蓷ai tasan dalilin yin sa.
Lokaci ya yi daya kamata ta san ko wacece _*SAMHA JALALUDDEN ALKALERI*_ domin tun data shiga gidan mata, tana neman wata na uku kenan amma ko a hanya basu ta蓳a jamewa ba. Za tayi amfani da opportunity ta je bikinsu Muwaddah domin samun damar ganin Samha.
***
*JIDDA.*
Bayan ta gama tsaftace jikinta, ta fito daga ban蓷aki, sai ta tsaya cak! a bakin 茩ofa ganin Samha kwance a kan doguwar sofa, tana jiran fitowarta.
Samha ta mi茩e zaune da sauri, idanunta kan Jidda cikin damuwa ta ce"Sannu Jidda, dama baki da lafiya ne?"
Shiru babu magana don ta rasa abin cewa sai bugawan da gabanta ke yi. Samha ta 茩are mata kallo daga sama har 茩asa ta ce"Mu je asibiti a duba lafiyarki."
Cikin dar-dar Jidda ta ce"A'a, ba sai an je asibiti ba. Zazzabi ne kawai, kuma ina kan shan magungunan da aka ha蓷a min."
Samha ta 蓷an yi shiru, kamar ba ta gamsu da amsar ba. Ta ce"To, Allah ya sawwa茩e amma shawarata gareki ki yi hankali da mutumin nan da ke yawon jan ki kuna yawoce-yawoce kar ki yi sakaci ya dirka miki ciki ya gudu."
Maganar Samha ya girgizata domin abin da take mata garga蓷i a kai tuni ya faru kuma ciki ne na wanda bata ta蓳a tunani ba.
A sanyaye ta ce"In sha Allahu zan kiyaye."
Samha ta ce "Tunda jikin da sauki, ki samu wuri ki zauna mu yi magana a gurguje don dama zuwan nan na yi shi ne na musamman domin ki."
Gabanta ya bada rass! A take wani irin fargaba ya mamaye ta.
'Ko dai asirinta ya tonu ne?'
'Samha ta ce zuwanta na musamman ne, to ko dai ta gano auren sirrin da ta yi da mahaifinta ne?'
Tunani ya sa zuciyarta bugawa da 茩arfi, har wani irin zufa mai 蓷umi ya fara keto mata a goshinta.
Samha bata damu da yanayin data ga ta shiga ba ta fara magana cikin 蓳acin rai.
"Wannan sabon 蓷an kwaltan da kika samu daya 蓷auke miki hankali, yake neman rabaki gaba 蓷aya da ni to wallahi ki garga蓷e shi ya kiyayi ha蓷uwata da shi domin naga yana nema ya wuce gona da iri."
Ta 蓷an dakata, sannan ta ci gaba da kakkausar murya.
"Baya bari ki tsaya ki gudanar min da aikinki yadda ya kamata kamar yadda kika saba. To wallahi, idan bai yi hankali ba, sai na sa an kama shi an nutsar min da shi, domin ba zamansa kike ba, zamana kike a garin nan. Ki ja masa kunne. Idan ba haka ba wallahi zan sa a 蓷aure shi. Kin dai ji garga蓷in da na miki ko?"
Jikin Jidda ya 蓷auki rawa kamar za ta saki kuka ta ce"I'm sorry ranki ya da蓷e in sha Allahu zan mishi magana, za a kiyaye Allah ya huci zuciyar Uwata."
A kufule Samha ta ce" Haka kike cewa za a kiyaye kuma ni sam bana ganin wani canji, abin naki sai da蓷a gaba kawai yake. Haba don Allah haka kawai kin bari mutum ya mayar da ke gantalalliya? Baki nan baki can, yasa kin san birni kin san 茩auye, kin san state kin san local gov't, kin san kasashe kuma kin san duk wani lungu da sako. Yanzu kina Nigeria anjima kina America, jim ka蓷an a jiki a mexico. Haba Alkhairina yaushe kika zamo totally loosed and classless ne haka? Wai waye shi wannan mutumin da ya canza min ke lokaci guda?"
Cikin 茩arfin hali Jidda ta 蓷aga kai ta kalleta ido cikin ido gabanta na harbawa ta ce"Shi 蓷in na musamman ne! Ya banbanta da sauran wa蓷anda na yi muamala dasu a baya. Ranki ya da蓷e kiyi hakuri ki bar fa蓷an nan a tsakanina dake, karki ta蓳o shi saboda baki san ko waye shi ba, kuma ki bar zaginsa, yin hakan zai iya yi wa rayuwarki illa."
"What? Jidda yau ni kike kallo kina nuna wani ya fi ni muhimmanci a rayuwarki? Kika ce kar in ta蓳o shi sbd ban san ko wanene shi ba ? Kuma kika ce in bar zaginsa domin yin hakan na iya illata rayuwata?"
Saurin saddar da kai 茩asa Jiddan tayi ganin irin kallon mamakin da Samha ke jifanta da shi.
"Hmmm! Hmmm!! Hmmm!!!"
Wannan shine sautin da kake ji ya na fitowa da ga bakin Samha don gaba 蓷aya ta ma rasa ta cewa.
Har Jidda ta bu蓷e baki za tayi magana, A tsananin fusace Samha tayi maza ta ce,"To shi 蓷in ubana ne da idan na zage shi zai illata rayuwata? Lallai Mummy tayi gaskiya data ce 蓷an adam butulu ne me manta alkhairi."
Da karyayyen murya ta ce"Yanzu Jidda har kin manta da duk irin dawainiyar da ni Samha na yi a kanki, har kika kai wannan matsayi na 蓷aukaka? Iyayenki suka gaza tsaya miki, amma ni Samha na tsaya miki. Ni ce na ri茩e hannunki, na taimake ki, na 蓷aga ki har kika zama wannan Jiddatulkhair da mutane suke gani a yau."
Ta nuna kanta da yatsa, hawaye suka fara taruwa a kwarmin idanunta.
"Shine har kin manta da komai a lokaci guda? Har za ki iya nuna min wani banza, 蓷an iska, 蓷an kwalta, ya fi ni matsayi a wajenki?"
Ta ida magana la蓳蓳anta na mugun rawa wanda hakan zai tabbatar maka da sosai abin ya mata ciwo.
"Kiyi hakuri ba haka nake nufi ba, babu wanda ya isa ya ture matsayinki a wajena. Amma don Allah kamar yadda na fa蓷a ki bar zaginsa, sam bana so kiyi nadamar hakan."
Jidda ta sake jaddadawa zuciyarta na mugun azalzala tam茩ar wanda ake roasting 蓷insa kan pan.
Cikin zafin rai Samha ta ce"Jidda waye shi da har zan yi nadama don na zage shi? Ina son saninsa domin na ga kamar mugun tsoronsa kike ji, sanin kanki ne babu wani mahaluki da nake tsoro tunda ina da 蓷aurin gindin jami'an tsaro, to shi 蓷in wanene da bazan iya taka shi in zauna lafiya ba?"
Kafin Jidda ta kai ga bada amsa, Mummy ta doko wa Samha kira a waya tana kuka. sosai hankalinta ya yi masifar dagawa tace "Mummy meya faru kike kuka?"
"Samha duk inda kike don girman Allah kiyi gaggawar zuwa gida yanzun nan ki sameni ina jiran ki."
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun! Don Allah Mummy ki gaggauta fa蓷a min abin da ke faruwa kar a nemi zuciyata a gurbinta a rasa."
Samha ta furta hakan a ru蓷e gami da fashewa da kuka.
"Samha magana ne daya shafi daddynki."
"Wani abin ne ya sami daddyn?"
"Ba tsayawa za ki yi kina jefo min tambayoyi daga inda kike ba, ki hanzarta kawo kafarki inda nake."
Ta fa蓷i hakan azafafe.
"To mummy gani nan tafe."
Tana gama furta hakan ta kashe wayar tana kuka.
A matukar razane Jidda ta dubeta muryarta na bala'in rawa ta ce"Meya sami daddyn? don Allah meya sameshi? Allah dai yasa ba wani mummunar abin ne ya same shi ba."
Kuka ya ci 茩arfinta wanda hakan ba 茩aramin mamaki yaba Samha ba. Taku uku kacal tayi ta matso inda Jiddan ke tsaye, kallo 蓷aya zaka mata ka fahimci cewa tafi ita Samhar shiga wani hali.
Kamo hannunta tayi idanunta na zubar hawaye, muryarta har ta fara dishewa ta ce "Don Allah ki fa蓷a min abin da ya faru da daddy."
"Nima ban san abin da ya faru da shi ba, ko baki ji Mummy ta ce in hanzarta samunta a gida ba? bari in je sai munyi magana, nagode da damuwar da kika fito kika nuna 蓳aro-蓳aro kan mahaifina."
Jakarta ta 蓷auka tayi 茩ofa sai ta ji Jidda ta ce,
"Ai ni ma ubana ne! fatarmu dai Allah yasa lafiya."
Juyowa tayi ta jefeta da murmushi na 茩arfin hali don sosai zancen nata ya yi bala'in da蓷a蓷a mata.
"Amin Alkhairina, nagode."
Tana gama fa蓷ar hakan tayi gaba. Fitarta ke da wuya Jidda ta fashe da kuka.
A ru蓷e take fa蓷in"Jalal bana son wani mummunar abin ya sameka saboda idan na rasaka tamkar duniyata ce ta rushe a gaban idanuna."
Layinsa ta nemo ta sanya kiransa domin idan ba ji duriyarsa tayi ba sam hankalinta ba zai ta蓳a kwanciya ba.
Kwata-kwata ba ta damu da tsayawa tunanin ko ya dace ta kira shi a daidai wannan lokacin ko rashin dacewar hakan ba. Burinta kawai ta dai ji sautin muryarsa koda a wani hali ne yake ciki domin ta 蓷an samu natsuwarta.
A daidai wannan lokacin kuma Yallabai na tsaka da tattaunawa da bakinsa na Japan, bayan dogon jawabi da akayi, aka dam茩a masa takardar tayin yin partnership business da su a 茩asarsu wanda kai tsaye yasa hannu.
To, ana cikin jawabin godiya ne sai ga kiran Jidda ya shigo wayarsa, jikinsa na rawa ya nemi izini ya fita domin amsa kiran Alkhairinsa.
"Alkhairi sorry yanzu na kar蓳i offer 蓷in, A very big congratulations to us."
Ya furta yana kyakyata dariya na tsantsar farin ciki.
Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tana fa蓷in "Alhamdulillah! Ashe babu abin da ya sameka, jin sautin muryarka ka蓷ai ya tabbatar min da cewa kana cikin 茩oshin lafiya."
Ta ida magana tana zubda hawayen farin ciki.
Cike da mamaki ya ce "Dama wani abin ne aka ce miki ya same ni?"
"A'a kawai mummunar mafarki na yi a kanka amma nayi addu'a. Allah ya tsare min kai, Congratulations Allah ya tabbatar da alheri."
Da sauri ta datse gudun kar ya fahimci karya ta lafta masa ko ya tsareta da tambayoyi.
'Daddy dai lafiyarsa lau, to meyasa Mummy take neman Samha ido rufe a kansa?'
'To ko kuma shine dai yake 蓳oye mata wani abun?'
Wa蓷annan tambayoyin su keta kai komo a cikin ranta wanda ba ta da wanda zai iya ba ta amsoshin tambayoyin nata sai dai ta yi hakuri ta 蓷an jira ka蓷an, koma menene idan tayi wari za a ji.
Haka dai ta lallaba ta koma ofis domin taimakon SALA a ci gaba da harha蓷a dukiyar samha amma tunaninta na wajen iyalin Yallabai da kuma Saffy da ta rasa inda ta shiga.
Azagwai da ke ta jiran fitowar Samha, ganin tayi waje yasa ta yi wuff ta mi茩e daga inda take zaune ta mara mata baya. Har za ta bu蓷e murfin mota kawai ta tsinkayi muryarta daga sama kamar an yi wa wada 茩wace.
"Ranki ya da蓷e tafiya zaki yi ne?"
Ta furta tana 蓷an sosa 茩eya, 蓷an guntun gulmar da ta kwaso na mugun cizon ranta.
Samha ta juyo ta kwasheta da wani irin kallo tun daga samanta har zuwa 茩asanta, sannan ta ce"Ga zahiri nan kin gani ko baki da ido ne? Ko hana ni tafiyar zaki yi ne?"
"Wa! Ni na isa in hana ki tafiya? Dama dama dai...."
Sai kuma ta ja bakinta ta gumtse.
"Dama me? Yi magana mana kin yi shiru sauri nake ban da lokacin 蓳atarwa kan shirmenki, ina da muhimmin wajen zuwa."
"Wani magana nake son na tsegunta miki domin kisa ido sosai a kan mutanen da ke 茩ewaye da ke musamman wa蓷anda kika fi basu muhimmanci a rayuwarki."
Cike da rashin gamsuwa da maganarta Samha ta ce"ke! ni sam ban fahimci wannan zancen soki burutsun naki ba fa, dama ina da labarin ke munafirci kamar a 茩o茩on ranki yake, idan baki yi ba sam bakya samun natsuwa. To, idan zaki bar zagaye ki fito a mutum ki gaya min abin da ke faruwa ki yi da hanzari idan ba haka ba zaki jawo in sa a 蓷aure min ke domin ni 蓷in ba sa'ar wasarki ba ce, ehe."
Azagwai ta waro ido waje jin an sako batun 蓷auri amma kafin ta kai ga cewa wani abin Mummy ta sake dokowa Samha kira kan ta hanzarta.
"Kamar yadda na fa蓷a miki sauri nake, bazan iya biye ta shirmenki ba amma Idan na samu lokaci zan nemeki da kaina amma ki sani idan zance mara kan gado ne, to wallahi kisa a ranki muddin na kau da matsalar gabana sai nasa an 蓷aure ki kamar yadda na 蓷au alkawari."
"Babu matsala na amince da shara蓷inki amma ki sani na tabbata kina da bukatar jin abin da nake tafe miki da shi, idan kin shirya jin koma menene sai ki tuntu蓳e ni."
Tana gama fa蓷an hakan tasa kai ta yi gaba, ta bar Samha da jin wani irin tsananin fa蓷iwar gaba.
Har Azagwai ta kusa shige gida ta ji Samha ta ce"Tuna min da sunanki."
"Shafa'atu nake, amma nafi son ki kira ni da Azagwai domin akwai iya zazzago bayanai."
Samha ta girgiza kai cike da mamakin yarinyar, kana ta fa蓷a mota ta bar unguwar don ta lura idan ta kuskura ta biye wa Azagwai tsaf za ta mantar da ita tashin hankalin da ke jiranta.
Azagwai ta bi bayan motar da ido tana girgiza kai ta ce"Allah sarki Samha bata san wa拼anda ke zaune gidanta ba da kuma abin da ake yi a bayan idonta."
Tafiyar Samha da kamar minti 5 sai ga motarsu Muwaddah ta sauke Saffy nan junction. Ta jawo 茩atuwar ledar kayan da Muwaddan ta ba ta, ashe abin ma hadda wani arnen designer bag me masifar 茩yau da takalminsa ta ha蓷a mata, sai kuma head tie na kayan, komai ready ranar kawai za a jira.
Har ta bu蓷e murfin mota za ta fice sai kuma ta ga dacewar sake jaddada bukatarta ga Muwaddah.
"茦awata nagode Allah ya saka miki da alkhairi, in sha Allahu zan yi 茩o茩ari na halarci bikin naku, sannan don Allah kar ki manta da maganar da muka yi da ke wallahi da gaske nake, ina sha'awar aiki a _Jay. Alkaleri's kitchen_."
Dafa kafa蓷arta Muwaddah ta yi tana murmushi ta ce"Kar ki damu ki kwantar da hankalinki zan yi 茩o茩arin ganin na cika miki burinki."
Daga haka suka rabu, farin ciki fal ran Saffy gani take kamar babu ta yadda za ayi Chef Jalal ma yaki amsar bukatar Muwaddah idan aka yi duba da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.
"In sha Allahu zan bari har sai burina ya cika na samun wannan aikin kafin na fa蓷awa Yaya Jidda, kawai surpise zan mata kuma na san tabbas za tayi farin ciki sosai da hakan."
Ta furta tana murmushi, da haka har ta karasa cikin gidan matan. Ga mamakinta sai ta tarar da Jidda a gidan Ashe har ta bada sanarwa a group ita duk bata sani ba sbd tunda suka fita da Muwaddah ko bin ta kan wayarta ba tayi ba balle ta hau kan WhatsApp, Gaba 蓷aya _Jay.Alkaleri's Kitchen_ ya gama tafiya da imaninta.
Jidda bata bari wani hira ya shiga tsakaninta da Saffy ba saboda sa ido amma ta kudira a rai fitan nan da Saffyn tayi sai sun yi magana a kai.
Jidda na cikin ofis suna shirin tashi aka kirata a waya wai Samha ta samu accident, yanzu haka anyi da ita asibiti da gaggawa amma dai an tabbatar mata da sauki.
Hankali a matukar tashe ita da SALA suka fito sai kuka gaba 蓷aya har 'yan gida. Masu tausayi kamar Jidda ne suka mara mata baya domin zuwa ganin halin da Samhar take ciki, masu raunin zuciya na kukan tsoro kar su rasa gatansu domin Samha gata ce a garesu.
Mutum fiye da ashirin suka mara mata baya, ciki hadda Azagwai wacce bayan Jidda kusan ita tafi sauran shiga tashin hankali har da kukanta.
"Don Allah Hajiya kar ki mutu ki bar mu."
Sosai abun ya ba wa mutane mamaki don abu ne mawuyaci aga Azagwai na zubar da hawaye kan abu koda kuwa abun tausayi ne.
Shatar adaidaita sama da biyar suka yi, wasu ma saman cinyoyi suka zauna. Halin ko in kula da Saffy ta nuna kan Samha ba 茩aramin ciwo ya yi ma Jidda ba. Bai kamata ta nuna rashin tausayi kan wacce ta bata mafaka ta zauna kyauta ba, duk da tasan zaman gidan Samha na da disadvantage amma idan za ayi mata adalci tana taimaka wa da wajen zama, kula da ci, da sha hatta pad Samha ba ta bari su yi kukansa. Amma shine don rashin tausayi wasu daga cikinsu masu busasshen zuciya suka nuna halin ko in kula.
Bayan hannu tasa ta share zafafun hawayen da suka zubo mata. Adaidai lokacin suka karaso asibitin. Sun tarar already Samha na emergency room ashe har miscarriage ta samu sanadin hatsarin domin a cikin jini ma aka kwasota.
A reception suka riske Haj. Nafeesa mahaifiyar Samha da kawarta Haj.Haire, ashe ita ce aka fara kira aka sanar da ita mummunar labarin kasancewar ita ce wacce Samha tayi waya da ita a 茩arshe kafin layin Jidda dake biye da nata.
Haka ta nemo Haj.Haire a waya hankali tashe suka nufo asibitin. Suna zaune anan reception suna jiran ikon Allah, Haj. Haire sai tausarta take tayi, ita ce ma tayi 茩arfin halin karban wayar Nafeesan ta kira Yallabai da Haseeb mijin Samha take sanar da su halin da ake ciki.
Haj. Nafeesa na ganin zugar 'yan gidan mata ta mike a fusace ganin alhairin Samha ita ce jagoransu, wato Jiddatulkhair Kabir, _Shugabar gidan mata_. Dama can ta santa, ba sanin yau ba ne, amma dai ta ji ma bata sakata a ido ba ne.
Jidda na ha蓷a idanu da ita sai da ta ji gabanta ya yi wani irin mummunar bugawa, irin kallon da take jifanta da shi ka蓷ai ma ya tabbatar mata da lallai za a tada hazo na rikici yau amma kuma a inda sam be dace ba.....
*Me kuke tunanin zai faru?*