MATAR GIDA PAGE 56
* MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P56
Da ido Ɗalha ya bi bayan Unaisa,bayan wasu ƴan sakanni ya tashi ta bar parlourn ya shiga ɓangaren Unaisa,bayan shigarsa ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya shirya kansa cikin wata jallabiya kalar toka daga haka ya fita daga ɗakin,bakin gado ya tadda Unaisa ta buga tagumi,bakinsa dauke da sallama ya shiga ɗakin Unaisa bata amsa sallamar sa ba kawai ta ɗago ta kafe sa da ido,waje Ɗalha ya samu ya zauna kafin ya yi gyarar murya ya ce ''in Allah ya kaimu gobe Lahadi za ki fara zuwa islamiyya'' shiru ya yi yana jiran amsarta,da fari Unaisa ta so ta yi masa gardama sai kuma ta tuna da batun koyan mota da ta biya ƙudi shekaran jira kawar da idonta ta yi daga garesa kafin ta ce ''kenan jahila ce ni?" ta yi magana tare da harɗe hannayenta a kirji, murmushi mai sauti Ɗalha ya yi kafin ya ce ''a'a ke ba jahila ba ce sai dai kina buƙatar komawa islamiyya'' a takaice Unaisa ta ce ''na fa yi sauka ko baka sani bane?" Ɗalha ya gyara zama kafin ya ce ''na sani wannan islamiyyar ba iya Kur'ani suke koyarwa ba har zamantakewar aure suna koyar da sauran littattafai na addini'' taɓe baki Unaisa ta yi kafin ta ce ''shikenan Allah ya kaimu'' yunƙurawa Ɗalha ya yi tare da miƙewa tsaye idanunsa kanta kafin ya ce ''karfe goma ake zuwa a tashi ɗaya na rana'' kwanciya Unaisa ta yi kafin ta ce ''Allah ya kaimu'' Ɗalha dake zaune ya ce ''ameen'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''ni zan wuce ɓangaren Amirah sai da safe'' ɗago kai Unaisa ta yi daga kwanciyar da ta yi ta ce ''daman kana yi min sai da safe ne,daga ni sai kai a gidan nan baka taɓa yi min sai da safe ba sai yau dan kawai kana son ɗaga min hankali" murmushi mai sauti Ɗalha ya yi, cikin zuciyarsa yana mamaki ashe daman tana da kishi har sannan fuskarsa dauke da murmushi ya ce ''kwanta ki yi bacci kada ki makara,kar ki manta karfe goma za ki tafi islamiyya'' daga haka ya yunƙura tare da miƙewa tsaye yana shirin barin ɗakin Unaisa ta ce ''kenan saboda yau zata dawo yasa ɗazu ka bar ni a kwance kamar wata shashasha alƙawari ka yi mata?cewar ba zaka taɓa ni ba?" Unaisa ta ƙare magana cike da ɓacin rai tana kallon fuskar Ɗalha ganin yadda yanayin ta ya sauya lokaci guda ya sa Ɗalha sauke wata doguwar ajiyar zuciya bai san ta yadda zai faɗa mata yanayin da ya shiga ɗazu ba,kawai ya yi shiru na wasu ƴan sakanni can ya ɗago ya kalle ta yaga shi take kallo kawai ya ce ''sai da safe'' ya faɗa tare da fita daga ɗakin yana ja mata kofa,bakin ciki kamar ya kashe Unaisa duk yadda ta kai ga jurewa sai da ta yi kuka wannan daren ta dauki sama da mintina goma tana kuka kafin daga bisani ta kwanta tana mayar da numfashi
A can wajen Amirah kuwa bayan komawar ta ɓangarenta ta gyarawa yara wajen kwanciya ta yi kafin ta wuce ɗakinta tare da Fauziyya,bayan shigarta ɗaki kwantar da Fauziyya ta yi daga haka ta canza kayan jikinta daga doguwar riga atamfa zuwa wata riga bacci mai tsamsi kalar hoda da kaɗan rigar ta wuce gwaiwarta,ta rufe kanta da wata baƙar hula daga haka ta wuce wajen madubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo cikin madubi ita kanta ta san ta ƙara kyau, sabulun da Ammi ta haɗa mata ya ƙarawa fatarta kyau da haske kaɗan,turaren humra da Ammi ta bata ta dauko ta shafe jikinta tana nan tsaye wajen madubi Ɗalha ya buɗe kofa ya shigo ɗakin bakin sa dauke da sallama Amirah na tsaye gaban madubi ta mayar da dubanta ga kofar tana cire ƴan kunne dake kunnenta tana kallon Ɗalha kafin ta amsa sallamar fuskarta dauke da murmushi a hankali Ɗalha ya ƙaraso har inda take yana buɗe hannayensa alamar ta zo,murmushi kawai Amirah tare da kawar da kai ta mayar da dubanta ga madubi tana ƙara kallon kanta cikin madubi,tana tsaye Ɗalha ya shiga gabanta ya tsaya yana kallonta langwaɓar da kai Amirah ta yi tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, hannu ya kai ya riƙe hannuwanta duka biyu har sannan idonsa kanta ya ce ''ba ki yi kewata bane wata guda fa bama tare,na zaci kina ɗaki kina jirana''..shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya daura da ''tun da ke ba ki biyoni ba to gani na zo'' ya kare magana yana haɗata da jikinsa wani irin riƙo ya yi mata kamar za a kwace masa ita,yana sauki ajiyar zuciya ko ba a faɗa ba ta fahimci Ɗalha ya yi kewarta sosai,gyara murya Amirah ta yi kafin ta ce ''kar ka ƙarya ni'' ta faɗa da kyar murmushi mai sauti Ɗalha ya yi kafin ya sassauta riƙon da ya yi mata ya ce ''haba dai kara ce ke?'' ya faɗa yana kokarin haɗa bakinsa da nata Amirah ta shiga kawar da fuskarta daga garesa gudun kar ya haɗa bakinsa da nata shi kuwa yana ta ƙokarin haɗa fuskarta da nasa ''nan fa ɗakina ne,ga Fauziyya can kwance tana bacci'' da wani irin sauri Ɗalha ya haɗa bakinsa da nata ya haɗa lips ɗinta gaba ɗaya ya tsusa,raba bakin ta da nasa ta yi ta daura da ''wutan ɗakin fa a kunne yake'' tana shirin sake magana Ɗalha ya kama bakinta da nasa ya mata wani irin kiss kamar zai cinye lips ɗinta,daga haka ya sake lips ɗinta da kyar ya iya furta ''wa ya hanaki kashe wutar?" Amirah ta shiga kokarin raba jikinta da nasa tana faɗin ''dan Allah ka bari,ka tafi zan zo shirya wa nake ban gama ba'' cak Ɗalha ya dauki Amirah kamar jaririya zaro idanuwa waje ta yi ta shiga mutsu mutsu tana son sauka daga jikinsa ta ce ''put me down Please..put me down'' ganin tana son yi masa gardama yasa haɗa bakinsa da nata ya shiga kissing ɗinta passionetly a haka ya shiga ɗakinsa yana riƙe da ita bai diri ta ko ina ba sai kan bed ɗinsa,ya dauki sama da mintina biyar yana kissing ɗinta,zuwa yanzu jikin Amirah ya yi sanyi,sosai jikinta ke amsar saƙon da Ɗalha ke aiko mata magungunan da Ammi ta bata sun fara aiki gaba ɗaya Amirah ta rasa nitsuwarta tun da take bata taɓa shiga yanayin da take jin kanta yanzu ba, idanunta sun yi ja sosai da kyar take iya buɗe su,a hankali Ɗalha ya raba jikinsa da nata ya sauka daga kan gado ya je ya kashe wutar ɗakin, lokaci guda duhu ya mamaye ɗakin haske wata dake shiga ta taga yasa ɗakin yin haske kaɗan a hankali Ɗalha ya dawo ya kwanta gefen Amirah hannu ya kai ya ɗago ta kafin ya daura ta kan cinyoyinsa ya zamana yana ƙasa ita kuma tana samansa a hankali Amirah ta kai bakin goshinsa ta manna masa kiss
A wannan dare Amirah ta ajiye kunya da kishi a gefe ta mora mijinta da kyau,shi kanshi mamakin Amirah ya rinƙa yi tsawon zaman sa da ita bata taɓa masa irin abinda ta yi a wannan daren ba,kusan raba dare suka yi suna abu guda,duk yadda Ɗalha ya kai ga jureya ya ƙasa,tabbas Unaisa ta riƙe mutuncinta ta basa kyautar budurcinta sai dai yadda ya ji jikin Amirah a wannan daren banbancin ta da budurwa kaɗan ne dan dai ba a haɗa budurwa da wacce ta haihu ne da zai ce Amirah ta fi Unaisa ɗanɗano da ni'ima,da ya san Amirah zata dawo haka da bai ɓata kuɗi ya aure Unaisa ba ina ma zai iya koma da hannu agogo baya,karfe uku da mintina goma na dare Ɗalha ne kwance gefe Amirah yana kallon ta cikin hasken wata dake shiga ta tagar ɗaki, baccin ta take hankali kwance,kananan kitso dake kanta Ɗalha ya kai hannu a hankali yana shafawa har sannan idonsa kanta kamar yau ya fara ganinta,a hankali Amirah ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta sauke su kan Ɗalha wata ƙawatacciyar murmushi ya sake mata mata,ɓata fuska Amirah ta yi tare turo baki gaba ta wani kwaɓe fuska hannu Ɗalha ya kai ya janyo ta kusa da shi ya daura kanta a kafardarsa ya ce ''ya aka yi ne me ke damun ki?" shiru Amirah ta yi kamar bata ji abinda ya faɗa ba kiss Ɗalha ya manna mata a kai kafin ya ce ''kin gaji ne?" a shagwaɓe Amirah ta ce ''umm..lokacin sallah ya yi?" Ɗalha yana shafa bayanta ya ce ''a'a da saura yanzu karfe uku" ƙara shigewa jikinsa ta sake yi kafin ta ce ''ya kamata mu yi wanka kafin lokacin sallah'' shiru Ɗalha ya yi bai ce mata komai ba ganin haka yasa Amirah ƙokarin tashi da wani irin sauri Ɗalha ya janyo ta tare da kwantar da ita ya haɗe goshinsa da nata murya can ƙasa ya shiga jero mata addu'oi' yana sa mata albarka,washe gari karfe tara da wasu ƴan mintina Amirah ta gama haɗa abin kari alale da kunu ta yi masu,bayan ta sawa yara ne ta dauki na Ɗalha ta kai masa ɗaki,bakin ta dauke da sallama ta shigo ɗakin har sannan Ɗalha na kwance bai tashi ba,a hankali Amirah ya shiga kiran sunan sa tare da buga ƙafarsa,a hankali ya buɗe idanuwansa ya sauke su kan Amirah a hankali ya buɗe baki tare da tashi zaune ya ce ''karfe nawa?" Amirah dake shirin barin ɗakin ta waigo tana dubansa ta ce ''karfe tara'' daga haka ta fita daƙin zuwa kitchen bayan fitar Amirah,bathroom Ɗalha ya shiga ya yi wanka tare da brush daga haka ya fita ya shirya kansa wata farar shadda ɗinki zariyya riga da wando,lokacin karfe tara da mintina arba'in Ɗalha bai tsaya yin breakfast ba ya fita,bayan fitarsa ɓangaren Unaisa ya wuce,Amirah dake kitchen tana wanke wanke ta ji motsin fitarsa hakan yasa ta wuce ɗakinsa dan ta duba taga ko ya yi breakfast bayan ta buɗe wormer turus ta tsaya tana ƙarewa alale kallo ko taɓa bai yi ba,rufe wormer ta yi ta fita daga ɗakin,wayarta dake daure kan daining ta dauko ta kira layin Ɗalha bugu ɗaya ya ɗaga kiran shiru Amirah ta yi na wasu ƴan sakanni Ɗalha yana ta cewa hello hello Amirah ta yi shiru bata amsa ba bayan wasu ƴan sakanni ta ce ''ka fita baka ci abinci ba'' murmushi Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ba fita na yi ba ina ɓangaren kanwarki,fita zamu yi yanzu,da na dawo zan ci'' wani irin ƙatoton kishi ya taso wa Amirah duk surutai da albarka da ya rinƙa sa mata daren jiya,abu na farko da zai yi yau shine zuwa bangaren kishiya? ba tare da ya ci abinci ba, wani irin zafi zuciyar Amirah ya fara mata anya kowa ba yaudarar ta Ɗalha ke yi ba,wani irin ciwo kanta ya fara mata lokaci guda,da sauri ta kai hannu ta dafe kujerar daining dalilin jiri da ya fara ɗibarta,nan take ta fara karanto duk addu'a da ya zo bakin ta tana sauke ajiyar zuciya cike da karfin hali ta saita nitsuwarta kafin ta ce ''ok Allah ya tsare hanya sai ka dawo,pls ka dawo da wuri zama da yunwa babu kyau ka gaida amarya ka ce ina gaishita'' washe baki Ɗalha ya yi kafin ya ce ''an gama ranki shi dade islamiyya zan kaita da na dawo za ki gan ni''lokaci guda Amirah ta nemi ɓacin rai da kishi dake cinta ta rasa, nan take ta ji zuciyarta ta yi sanyi,miƙawa Unaisa wayar Ɗalha ya yi yana faɗin ''gashi ku gaisa'' Unaisa ta haɗa gira ta yi wa Ɗalha banza ganin da gaske baza ta ƙarɓi wayar ba Ɗalha ya mayar da wayar kunne ya ce ''zata ji'' daga haka ya kashe wayar,mayar da dubansa ya yi ga Unaisa ya ce ''Allah ya shirye ki'' Unaisa bata tanka sa ba ta fita waje,inda yake parking mota cike da ɓacin rai ta buɗe mota ta zauna kujerar gaba,da ido Ɗalha ya bita,bayan fitar ta ya ƙulle kofar bangarenta
SHUUKRAN