Page 104
juna Magana, wata rana ko kowa 'yan hayakin kansa in sun motsa, ba me kula wani, don haka ban san gidan da take ba". Kan Muhseen ya sara. Tashin hankalinsa ya karu. Ya kura ma Ummancy ido zuwa wani lokaci, sannan ya zaro Naira dubu goma, ya mika mata "Ungo wannan, ki taimaka min, ki zaga da ni gidajen karuwan da ki ka sani, domin mu nemeta". Ummancy ta amshi kudin da sauri tace "Gidajen karuwai ba za su kirgu ba, don ni kaina ba duka na sani ba, koma nace ko kwata ban sani ba, amma dal ina fatan ba cireta a harkar za ka yi ba? Domin ka san duk abinda mutum ya saba da shi, raba shi da shi abu ne me tsauri, balle irinsu Tee- Baby da duniyar ke yi da su." Muhseen yayi tsaki gami da duban Ummancy yace 'Wannan rayuwar ce kuke ganin a bar kwarai? Ba tayi magana ba, a fusace ya wuce zuwa wajen motarsa. Ummancy na binsa a baya har cikin motar, inda ya ja motar dauke da Ummancy. Haka Ummancy tayi ta shiga da shi gidajen karuwai, kai jama'a so makaho! So mahaukaci ne! In banda makanta irin ta so, ya za'ayi mutum kamar Muhseen me kamala da kwarjini, da ilimi, me tsananin son addini, ya dinga ketawa cikin karuwai yana neman Tee- baby, abinda bai taba yi ba, tunda ya zo duniya. Bai taba tsayawa gaba da gaba da karuwa ba, don babu abinda zai hada shi da karuwa, sai ga shi yau Muhseen a cikin gidajen karuwai saboda Tee-baby. Babbar magana! Wai karamar Magana, ta zama babba! Akalla sun shiga gidajen karuwai sama da goma, amma kome kama da Tee-baby ba su gani ba. Ummancy ta gaji, dan dole ta dubi Muhseen tace "Karfe goma da rabi ne yanzu na dare, na gaji, yau ka haramta min yin (Business) dina, ba kuma wai don dubu goman da ka ba ni bane yasa na bata lokacina wajen yi maka abinda kake so ba, kwarjini da kimarka yasa na yi maka, don haka ka kaini gida, ma hadu gobe". Muhseen ya dubeta cike da tashin hankali yace "Na gode Sakina, ina ne gidan naki? Daga nan ta yi ta nuna masa hanya har wani kazamin gida dake cikin unguwar Ajagule ko kwatar dake kofar gidan, ta isa ta sa mutum ciwo. Har ta zura kafarta za ta fita, ta