Page 114
sunanki Tee-baby, amma zan fi sha'awar sanin ainihin sumanki, domin na tabbbatar zai fi. Tee-baby dadi". Tayi dan murrnushi, har jerin fararan hakoranta suka bayyana, tace "Sunan Tasleem". Muhseen ya maimaita sunan "Tasleem! Amma sunanki yana da dadi matuka, yakamata ki dinga alfahari da shi, ki daina amsa Tee-baby, domin Tasleem ya fi dadi» Tace "Zan yi ma shawararka kyakkyawan nazari Malam Muhseen" Ta fada, tana kokarin mikewa, ido kawai yasa mata, yana kallonta "Mu tafi, dare na yi, kuma ban yi da Hajiya zan kwana da wani ba". Muhseen ya numfasa yace "Wace ce Hajiya". "Wacce nake zama a hannunta".ta fada a takaice Muhseen yace "Ita ce take kayyade muku lokacin da za ku dawo gida? “ Ta gyada kai "Kwarai kuwa. Tunda a karkashinta muke sai abinda tace mu yi, zamu yi, ba ma ketare duk abinda ta gindaya a kanmu, ka'idarmu kuma in dai ba kwana za mu yi ba, to mu koma gida karfe tara, ga shi na tsaya jiranka, ban fita da kowa ba, yau ba wani abin kirki zan samu ba, don daga kanka, ina jin gida zan koma. Na san dai zan sha fada, idan na bada (Balance) kadan". Wannan karon kallon tausayi Muhseen ke yi ma Tasleem da takaici, yace yana kokarin gyara tsaiwarsa "Kada ki damu da batun balance, ba zan taba yarda ayi miki fada saboda haka ba, kuma ni kwana nake da bukatar ki yi aguna, don na dade ina nemanki, ba na jin awoyi za su ishemu. Ya za' ayi kenan?” Ya karasa magana yana kara zubama idanunta kallo wanda tunda ya zo su kadai ya ke kallo, Ita kanta Tee-baby, tana bukatar daukar lokaci tare da Muhseen, domin tana kwadayin kwasar ni'imar da take gani tare da Muhseen, ta san gwarzon namiji ne, wanda zai iya gamsar da ko wace ya mace. "Kin yi shiru Tasleem ko ba zai yuwu bane?" Ta girgiza kai cikin dan murmushi tace "Zai yuwu, amma bayan na sami amincewar Hajiya". Ya gyara tsaiwarsa yace "To ki kirata a waya mana, ki shaida mata." Tayi saurin kama baki ta rike tace "Ba mu isa mu gaya mata irin wannan maganar ta waya ba, sai mun koma gida." Muhseen ya maida bacin ransa yace "To mu je ki dauki izinin nata." Ta wuce gaba, yana bin ta a baya, har cikin motarsa, cikin kankanin lokaci ya ja motar. Tasleem na nuna masa hanyar da zai bi har gidan Hajiva me manyan mata, ita kam! Tee-baby gidan nasu me kyau ne, ba shi da makusa.