RU'UYAA (The dreams we never lived)
6. ...Jay D...🖊️
by @autum17
zaune muke a class ana shakaka ruwa kowa sai ƙoƙarin rufe jikinshi yake banda ni sanyin daɗi yake min ba kaɗan ba...ƙanƙame ni a kayi daga baya .tun kafin na juyo nasan ko wace ce...Jadeedah,babbar ƙawata, banyi muku magana akanta ba saboda mun samu saɓani da ita,aganina duk wanda ke ƙoƙarin shiga tsakani na da Asma'u to ya zama dole in rabu dashi... abinda take ƙoƙarin yi kenan tace wai, Asma'u tana kishi dani bayan ni nasan cewa ba haka bane..toh me zaisa ma tayi kishi dani bayan tana da duk wani abinda banda shi? shine yasa nida Jay D mukayi farraƙ.. '' kiyi haƙuri Bee...bazan sake ba kinji '' ƙin magana nayi hakan yasa ta ƙara ƙanƙame ni '' pls Bee..'' '' naji!" na faɗa mata batareda na kalleta ba sai kuma na juyo muna kallon juna riƙe hannunta nayi cikin nawa ina kallon kyakkyawar fuskar ta nace '' Jay D Ina matuƙar son ki,kinsan cewa bana abota da masu kuɗi amma ƙawance na dake daga Allah ne...kada ki shiga tsakani na da Asma'u..Ina matuƙar son ƙanwata!"
gyaɗa kanta Jay D tayi tana sakar min murmushin ta me kyau har dimple ɗinta ya fito murmushi nima nayi '' kina Min kama da wani a wurin aiki...sunan shi Abeed '' na faɗa mata har yanzu hannu na cikin nata '' ai yau zan zo wurin aiki nima''
kallon ta nake ina tunani a raina meyasa suna da kuɗi amma suke aiki a restaurant? kasa haƙuri nayi saida na tambaye ta '' saboda kuɗin baban mune ba namu ba,baban mu baida matsala fa,har faɗa mana yake kowa yayi kuɗi da kanshi,kuɗinshi nashi ne ba namu ba..bla bla bla '' nikam na kasa Dena kallon Jay d ta ƙara da faɗin '' nima nafison haka bana so in dinga dogaro da kowa gara insan kuɗin nawa ne!" murmushi nayi na ja dogon hancin ta
. daidai nan IRS ya shigo macijin sari ka noƙe ido muka haɗa yayi min wani banzan kallo
yan matan ajin mu suka fara gyare gyare... irin nason ɗaukar hankalin mutum nan ya fara zagayen aji yana magana akan topics ɗin daya koyar kwanaki,komai ban tuna ba wallahi
'' ke!" ya nuna ni bazato ba tsammani ɗagowa nayi na kalle shi '' meye janaba kuma meke kawo janaba?!" yayi maganar fuska a matuƙar tsuke waishi kada akawo mashi raini,ni kuwa nasan iskancin shine ya motsa shine yake tambaya ta wannan tambayar kuma wallahi bazan amsa ba kai tsaye nace '' ban sani ba!"
tsawa ya daka min ya fara zagina yana aibata ni,yan ajin mu sukayi shiru wasu suna dariya abun yamin zafi ba kaɗan ba kasa magana nayi sai hawaye da suka jiƙe min fuska '' babu abinda ke cikin kanki sai iskanci daƙiƙiya kawai... Fuskar ki mummuna kiyi ƙoƙari kisa wani abu a wannan jakar ƙwaƙwalwar taki!" ya ƙarashe maganar yana nuna ni da yatsanshi... idona sukayi jawur ga yan ajin mu sai dariya suke kawai dan yace inada jakar ƙwaƙwalwa...'' haba Malam,a tunani na kai Malami kake koyar damu shin baka karanta acikin Alkur'ani ba inda Allah yace,
Al-Hujurat 49:11
يَآأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمࣱ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرࣰا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءࣱ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرࣰا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
";Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai.";
Shiru dukan su sukayi harda malamin sari ka noƙe,wankin babban bargo Jay D tayi musu ba tsoro...fita yayi daga ajin a fusace yan ajin mu suka zo suka fara bani haƙuri...harda jana sukayi wurin rumfar mama yam lokacin break suka siyama na kayan ƙwalama....nayi farin ciki sosai sannan nace na yafe musu,daga nan muka fara wasanni daban daban dama nikam ina son wasa ba kaɗan ba...
a gurguje na shirya na wuce wurin aiki cike da farin ciki...amma bayan naba Mama labarin abinda ya faru a makaranta, Asma'u daga gefe batace uffan ba,nayi kewarta kuma nasan itama tayi kewata...
Fuska a sake nake karɓar order '' ..da alamu yau kina cikin farin ciki?" Abeed dake gefe na ya faɗa, murmushi na me kyau nayi cike da nishaɗi nace '' yau Jay D zata zo aiki!" ''uhmm...Yau dai zanga wannan Jay D ɗin'' ya furta,yar ƙaramar dariya nayi daga ƙasan zuciya ta nace '' nifa mamaki nake wai baku taɓa haɗuwa ba duk da muna aiki tare!" Murmushi kawai yayi baice komai ba ya fara amsar table ɗin dake gaban shi
nima ina kallon table ɗin dake gabana na haɗe fuska, wannan mutumin ne mema sunan shi..ɗan iskan nan daya taɓa rutsani a ɗaki? yawwa..wai Ibrahim...kamar koda yaushe ya kafe Ni da shegun idonshi kamar na akuya yana murmushi
gefen shi kuma wannan mutumin ne wanda na jefa da gora saye da facemask yake kamar wani mai korona Virus, wayar shi a hannun yana latse latse, sai wani mai farin gashi,dukan su shigar su iri ɗaya ƙananan kaya riga da wando jeans baƙaƙe..gayen Nan me saye da face mask yasa p cap ƙamshin turaren sa se shiga hancina yake..
... har zan wuce table ɗin su yace '' Pretty deejah baki karɓi order table ɗin muba ai!" dariya ya bani daya kirani da wannan sunan...wai firijin deejah...dakewa nayi nace '' ba hakane sunana ba!"wannan gayen mai farin kai ya ɗago ya kalleni kafin ya mayarda kanshi ƙasa,mai facemask kuma kamar bai san da mutane a wurin ba..
'' to meye sunan ki?" yayi tambayar da zolaya (flirtatiously) yana min kallon ƙasan ido.. naji kamar in shaƙo shi
'' Malam nan wurin aiki nane ba wurin faɗar suna ba...idan ba abinci zaka ci ba ina da abun yi!" na faɗa a ƙule takaici na kawo min har maƙoshi
farin gaye mai farin gashi ya fara magana da turanci yana kallo na...nayi tsaye ƙiƙam ina binshi kamar kurmar da bata ji kuma bata iya magana ba...ina fa nake ji?suyi magana da Hausa ala dole sai sun ba ƙwaƙwalwata wahala...
juya hannu na nayi littafin riƙe da ɗayan hannun '' English no! Hausa Yes!" na faɗa ina zaro ido...yayi shiru, Ibrahim ɗin nan kuwa ya gimtse dariya..ban kalli sashen Shiba...nayi ƙoƙarin barin wurin sai kuma na dakata na sake tambaya
'' me za'a kawo muku?"
'' Shine kika ban wrong number ko?" ya jefo tambayar batareda ya amsa tawa ba...wai shi me yake damun shine? ga abinda na tambaye shi ga wanda yake magana akai...
'' oh...ashe wrong number ne? ina fatan dai mijin wacce ka kira ya maka dukan tsiya!" na ƙarashe ina hararar shi''lumshe idonshi yayi ya sake buɗesu tare da faɗin '' sorry to burst your bubble,ai budurwa ce... besides Bruno anan...'' ya nuna min mai farin gashi
'' zai shigar min!" ɗage kafaɗa nayi dan ban fahimci mai sentence ɗin shi na farko ke nufi ba..wannan sunan bruno yayi kama da sunan kare amma dai ban faɗi hakan a fili ba
nayi tafiya ta, araina kuwa har naga abinda zan kawo musu,shi wannan ɗan wulaƙancin kamar bai san da mutane a wurin ba,ko ɗagowa bai yiba
kitchen na shiga nace a haɗa tuwon dawa miyar kuka..duk da sunyi mamaki hakan bai hanasu haɗawa ba,plates uku kuwa..zama nayi har suka gama aka haɗo min tuwon dawa miyar kuka da ruwa...ɗaukar tray ɗin nayi ina tafiya a hankali tun daga nesa nake jin idonshi akaina...na rasa Uwar me yake nema
na kawo wurin su ina tsaka da ajiye tray ɗin ta rugo da gudu '' Beeeee!!!! ''tayi tsalle ta haye ni trayn ya faɗi daga hannu na abincin ya juye musu a jiki nida Jay D muka faɗi ƙasa...suma da sauri suka miƙe saboda yanda miyar kukan ke basu ƙyama.... wurin kowa ya dawo da kallon shi akan mu...Jay D ta fara miƙewa tayi hiri hiri da ido kafin nima na miƙe
Gayen nan mai farin gashi yake magana da Yaren da ban taɓa jiba...fuskarsa ba kyaun gani tsabar ɓacin rai...
mai facemask kuwa kamar wanda ya shiga shock sai kallon kayan jikinshi yake... Khalil babu abinda ya samu nashi kayan..in wani abu sai gimtse dariya yake...nima nawa idon kamar zasu fito,harda yar zufa naji tana sauka a gadon baya na..na haɗiye yawu sanda mai saye da facemask ya watsa min wani shegen kallo har cikin ƙasusuwana.. ƙirjinsa na sama da ƙasa..kamar zai ƙona ni da idonshi...Jay D ta riƙe hannuna muka yi taku ɗaya baya ..
wurin yayi shiru kowa mu yake kallo, ƙafafuna babu abinda suke sai rawa..zagayowa mai facemask yayi zai damƙo ni,da sauri Ibrahim da ɗayan gayen suka tare shi
" Calmati Di caprio (kwantar da hankalin ka Di caprio)!"mai farin gashi ya furta da yaren da ban sani ba, Ibrahim na shafa ƙirjin gayen..ture su biyun yayi a tsananin fusace ya nuna ni da muryar shi kamar ana tuƙa tsohuwar mota yace
''Come faccio a calmarmi?! Ma è pazza?! Mi ha rovinato i vestiti, maledetta!(taya zan kwantar da hankalina? bata da hankali ne? ta ɓata min kaya..damn girl!)
" Calmati! calmati!" kawai gayen mai farin kaya yake maimaitawa...shima Ibrahim yana taya bada haƙuri... ido na ya haɗu dana mai face mask...naga idon shi ya ƙara duhu..can kuma ya dunƙule hannunshi..sama da ƙasan ƙirjinshi na ƙaruwa kamar kallona kawai na ƙara kunna shi...da sauri na cire idona daga nashi na kalli Ibrahim da shima ni yake kallo..murya ba amo nace
'' dan Allah kayi...''
'' SHUT UP!!!!" Mai facemask ya daka min tsawa sai dana kusa faɗuwa,Jay d ma ta tsorata da alamu ta ƙara ƙame ni...
'' calm down Ro..''
da wani irin yanayin magana(accent )wanda bai yi kama da yanda masu turanci ke magana ba yace '' this is all your darn fault BRAHAM!'' Ibrahim ya gyaɗa kanshi da ban haƙuri a fuskar shi...
nifa gayen ya fara ban haushi tuntuni sai haƙuri ake bashi amma yaƙi ya sake harara ta
'' Abeedah mubar wurin nan...'' jay d ta raɗa min a kunne...gyaɗa kaina nayi muka fara ja baya a tare..mai facemask sai banbamin bala'i yake da shegen yaren su mara daɗin ji
ido na sake haɗawa da Ibrahim '' in kawo maku wani sabon tuwon?" na waro mashi idona,dama ace abincin kan shi ya zube..amma naji daɗi daya zuba kan wannan mara mutuncin...ɗan zaro ido yayi sai ya girgiza kai yana nuna min gayen nan da idon shi...wata irin dariya na kwashe da ita ba shiri...kowa yake kallona a wurin kamar na haukace
gane hakan yasa na miƙe da kyau tare da haɗa hannayena wuri guda '' yi haƙ...''
'' if you open that your dirty mouth again,I will slap you hard across the face!" yayi maganar a mugun fusace.. jim nayi ina ƙoƙarin fahimtar abinda yake nufi can ƙwaƙwalwata,ta tattaro bayanai da ƙyar...haɗe fuska nayi cin mutuncin yayi yawa'' baƙin ciki kake min ko? Allah ya bani baki wanda bai wari ba saina sa fes mas ba shi...'' kafin in gama naga ya wani harzuƙo mun bansan sanda na warto hannun Jay D muka kwasa da gudu ba sai kitchen
bayan mun gama haki sai kuma muka rungume juna muna dariya '' ke Bee, wannan gabjejen mutumin idan ya same ki ai shemar dake zaiyi da bugu ɗaya!"
'' yoni hauka nake da zan bari ya same ni?" na bata amsa mu biyun muna miƙewa tsaye ganin manager, fuskar shi a murtuke...kafin ya fara magana na fara kukan ƙarya '' Jay D bayana ji nake kamar ƙashin bayana ya karye!" nayi maganar ina juya mata baya da ƙifta ido '' yi haƙuri Bee laifi nane..'' ganin dramar mu manager ya ɗauka da gaske ne ya shiga bamu haƙuri daga nan ya bamu dubu biyar yace Jay D ta kaini kyamis
yana fita muka ƙara rungume juna muna dariya sannan muka fita ta baya, a parking lot na hango Asma'u... da sauri muka isa wurin datake '' me kike yi anan?" Jay D ta tambaya nabi ta da ido,faɗawa jikina tayi murya kamar zatayi kuka '' dan Allah Tuwo kiyi haƙuri...'' kallon kallo mukayi nida Jay D shafa kanta nayi '' ba komai!" na faɗa ina ɗagota murmushin ta me kyau tayi min
'' Mutafi mu hole da dubu biyar ɗin manager!" Jay D ta faɗa tana riƙo hannu na,har zamu bar wurin saiga Malam samin macijin sari ka noƙe ya shigo shida wata yarinya, hannun shi riƙe da ƙugunta,yana mata raɗa a kunne kafin kuma suka haɗe baki wuri guda kis,zaro ido mukayi mu biyu kafin mukalli Asma'u dake hawaye, lallashinta muka fara yi amma ina kukanta ƙara sauti yayi da ya jawo hankalin su akan mu... tsaye yayi wuri guda shima yana kallon mu idonshi kamar zasu faɗo firgici bayyane a fuskar shi musamman dayaga yanda Asma'u ke risgar kuka
. takowa ya fara zai zo wurin mu ta tsere tabar wurin ,bin bayanta Jay D tayi kallon sama da ƙasa nayi mashi '' Sheɗanin banza ɗan iska!" na faɗa a fuskar shi kafin nima nabar wurin
Asma'u kuka take kamar ranta zai fita lallashinta ba ƙaramin aiki bane, jan mu Jay D tayi zuwa wani wuri inda ake sayarda su abincin gefen hanya,irin su suya,ice cream da sauran su,wasu dubu biyar ta ƙara akan wanda manager ya bamu muka kwashi Gara
suya ta siya mana ta dubu biyu da ice cream na dubu ɗaya da ɗari biyar kowa ɗaya, duk wani kayan maƙulashe saida Jay D ta siya mana daga ƙarshe sai wurin maghrib muka bar wurin bayan mun ƙara sayen suya ta dubu biyu muka wuce da ita gida.... Jadeedah ma ta wuce gida bayan ta bamu dubu biyu mu riƙe
munyi mata godiya sosai...
'' Tuwo kiyi haƙuri akan duk abinda na maki bazan sake ba insha Allah '' Asma'u ta faɗa tana shafa min ruwan shinkafa akai,yau akwai wuta, Mama tana tsakar gida tana kalkamta kaya dan akwai hadari..
'' nayi farin ciki..yanzu dai nasan kinga Abinda nake faɗi ko? Wannan yarinyar ba itace ta farko ba,ya kawo mata da yawa...bai dace dake ba!" gyaɗa kanta tayi hawayen ta na faɗowa a fuska ta da sauri ta goge su kada Mama ta gani...
washegari jumu'a yasa Mama bata bamu ko kwabo ba,ina ta ture turen baki kamar ƙaramar yarinya taɓe baki Mama ta ɗauke ido
'' Mama abincin jiya ya rage?" Asma'u ta tambaya '' a'a, shinkafar ma ta ƙare yau idan kun dawo sai dai ku sha garin kwaki'' Mama ta bata amsa jida nayi ance babu shinkafa yasa naji wani iri a zuciya ta '' yanzu tuwo zamu dinga kilma ko?" wani kallo Mama tayi min '' ai shima tuwon babu .. abincin ya ƙare duka!" kallon kallo mukayi nida Asma'u kuma fa wata baiyi nisa ba balle ince an kusa biyan mu albashi...
'' kuyi sauri kada ku makara har rana ta fito '' Mama ta faɗa tana miƙo mana kunun mu karɓa nayi raina a cunkushe yanzu ya zamuyi?
nasan buba me kayan masarufi bazai bamu bashi ba dan har yanzu akwai sauran bashin shi a kan mu..har na shanye kunun bansan na shanye ba tsabar yanda nayi nisa cikin tunani, ajiye cup ɗin nayi na goge baki itama Asma'u ta ajiye nata muka saka hijaban mu dake rataye a igiya jakunkunan mu a hannu '' mun tafi..'' miƙewa Mama tayi ta biyo mu da nasiha da addu'oi har bakin ƙofa '' a dawo lafiya.."
yau Ban hawo bishiyar mangoro ba makaranta muka wuce daret babu wanda ke magana cikin mu,sanda muka isa an kusa gama assembly bada daɗewa ba muka shiga aji...abin da ya ƙara min baƙin ciki..Jay D bata zoba! dama ita doja ce ta bugawa a jarida
lokacin break na cigaba da tunanin ya zanyi da abincin da babu a gida? shawara na yanke zan karɓi rabin albashi na hakan ya ɗan sanyaya min ruhi
da gaske da muka dawo garin kwaki muka sha ba suga ba giɗa babu ƙuli... Kamar inyi kuka,muna gamawa muka ɗauki bucket gidan wani Alhaji babba muka tafi ɗibar ruwa, akwai layi dayawa dan haka muka shashance da wasa...sai wurin ƙarfe uku muka kawo bokiti guda guda Mama tana tayi mana faɗa...da muka koma layi ya rage da sauri muka ɗibi ruwan muka cika komai kafin na shirya na wuce wurin aiki bayan nayi wanka
Sai dai me? an kore ni daga aikin ba bayani ba komai kuma an canja manager,duk yanda naso in ji dalilin korata babu wani takamammen bayani... albashin ma an hanani...a dai dai wannan gaɓar ji nayi rayuwa tayi min zafi, duk yanda naso in daure na kasa na fara surfa masifa....sabon manager'n yasa securities su fitar dani daga wurin wai ina damun customer ɗinsu... haka wa'yannan gaɓa gaɓan abubuwan suka saɓani a kafaɗa suka jefar dani waje kamar buhun shinkafa...
zagi da Allah ya isa sai wanda na manta kafin na duƙe a wurin ina sharɓar kuka...ban ankara ba ashe har dare yayi miƙewa nayi na fara tafiya gani nayi kamar akwai wata mota a baya na amma ban kawo komai a raina ba har Saida na sha wata corner inda babu mutane sosai motar nan tasha gabana....
PAGE 7 A AREWA PEN
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️