7
*BAYA TA HAIHU*
7
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
Ummu Maher (Mrs green)🍀
Ammi ta É—an nutsu sosai saboda tana son ta fuskanci matsalar sannan ta ce"Hamzah meye laifin Hafsah? Ita ba mummuna ba ita ba mara kunya ba sannan kuma ga ta Ć´ar uwarka".
Ya ja iska sannan ya ce "Duk nasan da haka Ammi, amma tun a farko ai na ce miki bana son ta kuma bana son cutar da ita saboda zaman aure ba wai zama ne da za a yi gobe a fito ba, ana nan tare mutu ka raba".
"Duk nasan da haka Hamzah, amma kai kasan me hankali ne kuma nasan komi zai wuce don girman Allah komi ya wuce".
Hafsah jikinta ya gama yin sanyi, wai roƙonsa ma ake ya so ta sai kace wacce ta rasa mijin aure? Ta biyewa kuɗi ga shi tun ba a kai ko'ina ba yana wulaƙantata, ita kuwa tasan ko karen hauka ne ya kamata tasan ba za ta fita daga gidan Hamzah ba, in sha Allah mutuwa ce za ta raba su".
Bayan fita Ammi ta ce "Hafsah zo nan".
Nan Ammi ta shiga koya mata dabarun ƙwace miji da saye zuciyarsa ya so ta fiye da yadda ya so Mero.
***
Bayan wata biyar.
A yanzu haka ina É—auke da ciki wata uku, duk abin da nake so shi Habibu yake kawai inda aka samu matsalar shi ne, kuÉ—in da Baffanmu ya ba shi yana jari duk ya sanya su a gaba ya cinye, maimakon ya kama shagon kamar yadda Baffah ya ce a a sai ya biyewa zuciyarsa ganin kuÉ—in ba zasu isa ba, idan da ya juya ai ko Ć´an uwansu sa taimaka masa.
Yau ma kamar kullum ina zaune akan gadona, duniya duk ta yi min zafi saboda yadda ƴaƴan hanji na suke haɗewa saboda yunwa ina tuna rabona da abinci tun jiya da daddare ga shi yanzu har yamma ta yi babu abinci ba labarinsa, ga shi kwana biyun nan mahaifiyarsa ce take ciyar damu sau da dama haƙura take ita ta bamu idan girkin bai isa ba, sai ta siyo garin kwakwi ita ta sha. Rayuwar dai ta yi zafi, amma son Habibu har yanzu bai goge a raina ba jinsa nake tamkar yau ne muka yi aure.
A halin yanzu kuma lokacin awo ya yi, amma saboda talauci na kasa zuwa asibitin cikina wata na biyar kenan sai dai a haka za ka É—auka cikin bai fi wata 2 ba, saboda rashin abinci.
Ina cikin tunanin ya shigo, ya ƙwanta akan gadon shima da alama dai yau ma babu sa a, saboda banga alamar fara'a a fuskarsa ba.
Cike da son jin abin da ya samo na ce"Habibi, ya naga fuskarka haka"?.
Cike da haushin tambayar ta wa ya ce"To me kike son gani Maryam".
Sosai na wari ido, saboda baya kira na da sunana Khadijah yake ce min saboda sunan wata ƙanwarsa ce wacce ta rasu ƙawata ce sosai, kai kusan ma ba ni da aminiyar da ta kaita sanadin ta ne ma muka haɗu da shi, yana son ƙanwar ta sa sosai sai kuma mutuwa ta yi masa yankan ƙauna da ita saboda kamar su ɗaya kamar an tsara kara.
Da mamaki na ce"Habibi yau sunana kake kira"?.
Ta shi ya yi ya zauna, ya janyo ni jikinsa sannan ya ɗago haɓata ya zamana muna kallon juna sannan ya ce"Yi haƙuri kin ji Hubby, ki kalli idona kiga zufa, yunwa, rana, duk yau sai dana sha su amma ban samu ko sisi ba wallahi ko ruwa na kasa sha saboda baƙin ciki, kuma bana son na dawo ban taho da komi ba".
Kuka na fashe da shi, sannan na ce"Ka yi haƙuri Habibi ni nasan Allah ne ya jarabce mu kuma ina sha Allah komi zai wuce, kawai dai mu dage da addu'ah".
Haka muka gama hirar ba daɗi, muna ɗakin na jiyo Muryar mahaifinsa yana kiransa da ƙarfi alamar dai akwai matsala a kiran, ko kuma wani abun mamaki zai kira sa ya faɗa masa.
Ya fita da sauri, ya durƙusa a gabansa sannan ya ce"Baffah Am, ga ni".
Shima ya amsa sannan ya ce"Dama wani Company ne na shinkafa suke neman matasa shi ne na ce bari na faÉ—a maka tunda ni kaga na girma ko naje ba lallai ne su É—auke Ni ba".
Habibu ya yi murna sosai sannan ya shaidawa Baffansu, gobe da sassafe zai tafi ko Allah zai sa a dace.
Ina É—aki murna ta cika min ciki, saboda ko ba komi shima zai samu farin ciki sannan kuma rayuwarmu za ta canja.
Allah ya taimake sa kuwa da wuri ya shirya ya tafi tun da asussuba na azalzale sa, ai kuwa tun safe ya je sai rana tsaka ya dawo duk hasken fatarsa ranar sai da ya yi ɗan baƙi saboda yunwa ga rana. Daga yadda za kaga fuskarsa kana kallonta kasan da matsala ba a samu abin da ake so ba, jikina duk ya gama yin sanyi.
Rannan na shirya, na tafi gidan Addah Hafsah kai tsaya tun daga bakin get ɗin gidan na fara cin karo da baƙin ciki, saboda mai gadin ne ya hana ni shiga zuciya ta ɗebe ni na dinga faɗa masa magana saboda irin mutanan nanne waɗanda basu iya magana ba ko kaɗan.
Jin na ƙi tafiya yasa ya shiga ciki, ya shaida mata abin da yake faruwa ta ce"Kwatanta min ita ko zan gane ta".
Tas ya kwatanta ni, jin hakan yasa ta gane ni ce ta bashi umarni da ya barni na shigo.
Ni kuwa ina ƙofar bakin tamfatsetsen get ɗin na su, na ce a zuciyata Addah Hafsah tana cikin daula saboda tun daga bakin get ɗin gidan za ka gane me gidan me kuɗi ne sosai. Amma duk da haka banji ko na raya dama ni ce na auri Hammah Hamzah ba, saboda ba shi ne muradin raina ba.
Bayan na shiga anan ne na ƙara shaida tsaruwar gidan ga shi da girma da kuma kyau, ƙofar babban falon ta buɗe da kanta na nutsa kai na cikin babban falonta na nutsa ƙafata, wani irin sanyi ya ziyarce ni na ji wani irin sanyi da nutsuwar zuciya.
A babban falon na same ta, ga wata wangaleliyar Tv yadda kasan ka ciro mutum a ciki. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ga wani sanyayyan lemon juice a hannunta kana ganinta kasan tana jin daɗi, duk da ba ta yi ƙiba ba amma ta ƙara fari sosai fatarta ta ƙwanta luwai-luwai.
Tuni na ji daɗin ganinta tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa, ranar dai haka muka yini muna ta hirar mu gwanin sha'awa. Anan ne ta sanyo min hirar halin da take ciki da mijinta, na yi shiru duk da dama nasan hakan zai iya faruwa na ce"Addah Hafsah kiyi haƙuri kowa da irin ƙaddararsa, ni wallahi sau da dama har gajiya nake da Habibu saboda yana da naci sosai sai na rasa yadda zan yi".
Jikin Hafsah ya yi laƙwas, ikon Allah ita ga ta mabuƙaciya amma ta samu mijin da ko ta ita baya yi, ƙanwarta kuma ba mabuƙaciya ba amma ga shi ta samu miji wanda yake irin ta. Tuni ta fara hasaso wani abu amma gudun shaiɗan sai ta share ta yi a uzi biyya.
Bayan tafiyata Hafsah ya fara wani tunani, sau da dama idan buƙata ta taso mata sai dai ta yi ta kuka ga shi yanzu suna da kusan wata shida amma mijinta bai santa a mace ba, ga ta ita kuma me buƙata a take shaiɗan ya gina wa Hafsah gini me kyau a cikin zuciyarta ta fara wani mummunan tunani ta fara fara'a.
Mrsgreen ce✍🏾