THE AFTERMATH 🫡
JA DA BAYA...
Book 1
Page 34 ✍️
***
Bacci ne ya dauki Inarah, wanda har lokacin tana kwance a jikin Innah, cikin sanyin jiki da gajiyawar kukan da tayi. Numfashi take sauke wa a hankali tana ajiyar zuciya, fuskarta tayi wasai, sai dai alamun marin da aka mata har yanzu suna bayyane radau akan fuskar ta ta.
Innah ta gyara mata kwanciyar sosai, tana kallonta cikin tausayawa tare da shafa fuskar ta ta cikin rashin Jin dadin Marin na ta da akayi. rufe mata jikinta ta sake yi da mayafi, sannan ta cigaba da zama kusa da ita tana kallonta,ita Kadai tasan tinanin da takeyi akan yarinyar.
***********
Bangaren Ayzaan kuwa...
Tun bayan shigewarsa dakinsa, zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa. Yana zaune akan sofa hannayensa biyu hade ya dunkulesu, kansa a sunkuye. Amma duk lokacin da ya tuna yadda fuskar Inarah ta koma bayan marinta da mammah tayi, sai ransa ya kara baci.
Ya dago kansa a hankali, ya kalli bango kamar yana magana da wani.
“Me yasa zata taba ta? Me yasa?marin chuchu tayi fa”
Ya furta cikin takaici, kafin ya mike ya fara kai-komo a cikin dakin.
Idanuwansa haryanzu suna ganin Inarah tana kankame jikinta tana kuka, tana kiran sunansa cikin tsoro. Abin yana kara masa ciwo a zuciyar sa.
“Wallahi idan aka sake taba ta...”
Ya dakata, ya sauke numfashi mai nauyi.
“Ba zan iya barin hakan ya sake faruwa ba,abinda akayi mata abaya ya isa.”
Haka ya gama sake saken sa da fushin sa adaki yayin da ita wacce aka daka dinma tana can tana baccin ta.
Shirin da zaiyi na meeting da za'ayi ma koma wa yayi ya kwanta a kan gado.
************
A bangaren Hajja kuwa, abin bai wuce haka kawai ba.
Domin kuwa bayan fitarsu kuka
Farhah take kamar wacce aka ce mammah ta mutu,ga azabar da fuskar ta take mata,ga bakin cikin yadda Ayzaan ya bige ta agaban kowa,Kuma akan inarah,ji take kamar ta hada wuta ta tsoma inarah aciki.
yayin da Mammah take ta fada cikin tsananin fushi kamar zata cinye kanta.
“Kin ga abinda wannan tambadadden yayi? A gaban idona ya mare farhah hajja! ban taba tunanin Ayzaan zai daga hannu ya mare farhah agaba na ba saboda wannan yarinyar me kama da shaidanu ba.”
Farhah ta share hawayenta, muryarta tana rawa tace.
“Mammah, wallahi bana son ta,na tsane ta se na kashe ta. Tun daga ranar da na shigo gidan nan nake jin haushinta. Kullum sai ta zo ta dauke min komai,duk abinda ya kamata ace nawa ne se naga itace Mai shi,mammah ni Yaya Ayzaan kawai nakeso auren shi nakeso inyi.”ta fada tana kuka yayin da zuciyar muhibba ta buga sabida abinda farhah tace.
Mammah ta girgiza kai tana kallonta.
“Ki barni da wannan yarinyar,nasan maganin ta. Ni dai na gaji da ganin yadda kowa yake Wani nan Nan da ita,yarinya sauran lalura da cuta,abarta taji da ciwon haukar da ke damun ta ma,Amma se rashin kunya fal cikinta,zanyi maganin ta ai. Har Ayzaan din ma bazan bari Dan iskan yaro mara mutunci,nagaya Miki auren ku ba zai yuwuba sabida bazan kaiki inda Zaki cutu ba Dan Babu abunda zai iya tsina na Miki,kyan Dan maciji ne".haka mamah ta cigaba da fadan ta Wanda kowa ke sauraran ta zuciyar da yawansu abun Bai musu dadi ba.
Hajja wacce take zaune tana sauraren su, ta sauke ajiyar zuciya tace.
“halimatu, kiyi shiru mana. Abin da ya faru ya Riga ya faru. Ke kika fara yi mata fada, Farhah kuma ta tasa da niyyar marin ta,inarah bazata yadda ba,Banda kwana biyu ma tayi sanyi ba Wanda ya Isa ya nuna mata yatsa bata karya ba . Ai ba haka ake son a gyara abu ba, farhah bata kyau ta ba Sam,kema Kuma be kamata ki mare ta ba,kinma ci daraja yan mutuncin nasa suna kusa yau da ya daga hankalin kowa a gidannan.”
Mammah ta waigo tana kallon Hajja tace.
“Amma Hajja, ai ba dole ne kowa ya rika daukar Inarah kamar wata sarauniya ba,Babu Dan datafi da zaa ce abinda take so shi zaayi ma ta ba.”
Farhah ta sake fashewa da kuka tana fadin.
“Ni fa Mammah, ban taba son ganinta ba Kuma ni Ina son Yaya Ayzaan inban aureshi ba mutuwa zanyi, se na kashe kaina...”
“Ki daina kuka,” Mammah ta katse ta, tana kara tsuke fuska. “Ki bar komai a hannuna,nasan matakin da zan dauka Maza share hawayenki kije kiyi wanka kafun anjima mu fita kinji ko,duk abinda kikeso tabbas se kin same shi indai Ina duniya.” mammah ta fada cikin rarrashi tana bubbuga bayan farhah kamar karamar yarinya.
A gefe kuwa, su hibba sunyi tsuru tsuru yayin da hibba da zaitoon suka ji dadin dukan da Ayzaan yayi wa farhah din,Kowa yana sane da cewa fushin Ayzaan ba irin wanda ake wasa da shi bane,domin Shima ba tayar baya bane asalin arrogant ne.
Hafiz kuwa har yanzu yana cike da haushi, yana zaune yana goge gefen fuskarsa,bakin sa har ya kumbura sabida Marin da Ayzaan ya zafga masa.
Umair da ke kusa da shi, yana kallonsa wata irin dariya ce ta kubce masa ganin yadda bakin sa ya kumbura gashi Yana ta huci kamar mayunwacin zaki.da kyar ya danne dariyar yace.
“Kai Hafiz, ka bari mana Abin ya wuce kake ta huci kamar kumurci.”
Hafiz ya kalli Umair cikin matukar bacin rai yace.
“Ya wuce fa kace? Ka ga yadda ya mare ni kuwa?He was wondering who he thought he was to do that to me? He will regret it!”
Umair ya girgiza kai yace.
“Amma kai ne Mai laifi Hafiz,Ka bar abin ya tsaya nan,domin bazakayi nasara ba kasan waye Ayzaan,sannan maganganun da ka fada Sam basu Dace ba,Babu Wanda ya wuce kaddara”umair Yana gama magana6sa ya mike ya fice a bangaren.
Hafiz bai sake cewa komai ba.
Shima ya mike ya fice asashin ya tafi bangarensu tare da muna Nan kuduri aransa.
Haka dai aka watse kowa zuciyar sa ba dadi yayin da can bangaren ummee tana ta jiran ta ga dawowar su inarah daga bangaren hajja sabida suzo suyi shiri sabida lokacin meeting Yana ta yi,Amma ta jisu shiru,Kuma tasan Ayzaan bazai taba Dade wa har haka a bangaren hajja ba hakan yasa ta dakko wayar ta tana so ta kira su.
Can kuwa Bayan kusan awa biyu da baccin wahala ya dauki Inarah, ta bude idanuwanta a hankali. Da farko ta dan kalli wajen da take, kafin ta tuna abinda ya faru a falon Hajja.
Hannunta ta kai a hankali zuwa gefen fuskarta ta shafa tana marairaice fuska.
“Wayyo…”
Ta furta a hankali cikin muryar ta Mai dadi, sannan ta tabe fuska saboda har yanzu tana jin radadin marin.
Innah wacce ta fito yanzu daga bedroom dinta,ta karaso ta zauna ganin ta farka yasa tayi murmushi tace.
“Kin tashi gimbiya iyayen daru?”
Inarah ta kalli Innah, sannan ta turo baki tace
“Innah, har yanzu fuska ta tana min zafi,kalla ki gani fuska na taji ciwo ko?.”inarah ta fada tana karyar da Kai Gefe like karamar yarinya
“Na sani mana takwara. Ki yi hakuri, zai daina kinji,aike jaruma ce.”
Inarah ta dan yi shiru, kafin ta Bude Baki a hankali tace,
“Ina Zaki innah?”
“yana daki ko?
“Nasan yana fushi ne ko?”
Innah tayi murmushi sannan tace.
“Ke dai kin san halinshi
shi ai. Tun da aka mare yar gwalo dinsa ai yau ba Mai Gane kansa,nace yatashi yaje yayi wanka ya shirya ko Dan zaman meeting dinnan Amma ko kallo ban isheshiba kamar ni ce na mareki🤔.”
Inarah ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta gyara mayafinta ta mike tace.
“Zan je in gan shi innah.”
“Inarah!”
Ta tsaya tana kallon Innah.
“Karki shiga wajensa yanzu. Bari ya kara sauka daga wannan fushin nasa,inya gama zai sauko.”
Inarah ta dan yi murmushi sannan tace.
“Ni kadai ce zan iya sauke masa fushin innah bari namai magana.”inarah ta fada tana yin hanyar dakin da tasan yana ciki.
Innah ta girgiza kai tana dariya.
************************
A can kuma ana ta shirye-shiryen babban taron iyalan gidan Mai Rabo Estate din wato meeting da suka Saba yi.
A tsakiyar Estate din kuwa dama akwai wani babban hall da suke amfani da shi wajen manyan taruka na family din.
An shirya wurin tun da wuri.
An jera kujeru cikin tsari, akwai babban teburi a gaba inda manyan gidan zasu zauna, sannan a tsakiyar hall din aka bar fili mai kyau domin kowa ya samu damar zama cikin sauki.
A gefen gaba kuma an tanadi wasu kujeru na musamman domin Hajja, Innah da sauran manyan iyalan gidan.
Duk wasu ma'aikatan Estate din a wannan ranar suna cikin aiki ne suna ta shiga da fita suna duba komai, yayin da ake tabbatar da cewa komai ya kasance cikin tsari kafin lokacin taron.
Inarah ta isa kofar dakin Ayzaan.
Ta tsaya na wasu dakiku tana kallon kofar.
Wanda inda da ne zata shiga ne Amma yanzu tana bukatar izini kafin ta shiga.
Tsayawa tayi ajikin kofar ta manna fuskar ta ajiki kamar Mai yin rada tace.
“Zaki na….
Shiru Bai bata amsa ba,hakan yasa ta sake Bude Baki cikin shagwaba tace.
“Zaki, ni ce,inshigo?.”
A ciki, Ayzaan wanda yake zaune cikin shiru ya dago kai Jin muryarta azuciyar sa yace"stubborn 👌"yasan inbai amsa ba haka zata ta Kiran sunansa, sauke ajiyar zuciya yayi, fushin da yake zuciyarsa yana raguwa a hankali Jin muryar ta Babu alamar kukan,dakyar ya Bude Baki cikin husky voice dinsa yace.
“Shigo.”
A hankali ta bude kofar ta shiga.
Tana kallon sa, sannan ta turo baki.
Shi kuwa kallon fuskarta yake yi ko kyafta idanu baiyi ba tsawon wasu dakiku Yana kallon ta.
Alamun marin har yanzu suna nan.
zuciyarsa ta sake cika da bacin rai.
Amma wannan karon bai nuna fushin ba.
Sai dai ya mike ya nufi inda take sannan ya shafa fuskar tata ahankali yace.
“yana Miki ciwo?”
Inarah ta gyada kai.
“Kad'an.”
Ya kalleta cikin nutsuwa sannan yace.
“Kin ci abinci?”
Ta girgiza kai cikin shagwaba alamar a'a tace" Kuma inajin yunwa.
Ya lumshe idanuwansa na dan lokaci kafin yace.
“Kin tashi daga bacci kenan kika zo nan ba tare da kin ci komai ba?,banson rigima oya muje"ya fada Yana Jan hannunta suka fito.
Alokacin ma Abbie ya shigo bangaren na innah domin tafiya can gurin meeting din.
Kasantuwar bazata iya tafiyar kafa ba Kuma kusan kowa ya Riga ya halarta wurin, shiyasa yazo sabida su tafi da innah.
Abbah sun Riga sun tafi,tunda ummee tayi ta jiran dawowarsa basu dawo ba.
Kuma ta kira Ayzaan din wayar sa bata shiga ba,hakan yasa suka wuce kawai.
Abbie da ke gyarwa innah mayafin ta Yana tambayar Ina yan rigimar nata kokuwa wannan karon halin nasu na zuwa a makare ma zasuyi.
Sedai innah bata Kai ga bashi amsa ba yaga fitowar inarah da Ayzaan din Wanda idonsa ya sauka akan fuskar ta da sauri ya furta"subhanallah,mamana me yafaru, meyasamu fuskarki haka?bobo na lafiya naga fuskar ka ba annuri me yasame ne?". tambayoyin dayake ta jero musu kenan cikin damuwa Yana karasowa gurinsu.
Innah ce tace"Kai Babu komai rabu da su,tsakanin su da uwar su,halimatu ce ta mare ta,shi Kuma wannan barden yake ta bacin Rai haryanzu na gaza Gane kansa.
Ai ta Isa tayi musu hukuncine shiyasa".hajja ta karasa maganar ta tare da gyara mayafin ta sosai.
Abbie jikinsa yayi sanyi duk da baice komai ba Amma har zuciyar sa baiji dadi ba.
Amma haka ya boye yace"Hala kinyi kiriniya ko mama na,kiyi hakuri kinji kuzo mutafi ko bobo na,kayi hakuri karkaji komai kaji Dan albarkana.
"Abbie ku tafi kawai ni asibiti zan kaita aduba fuskar ta".ya fada Shima Yana turo Baki kamar yaro,domin in agaban Abbie yake ji yake kamar yaro ne shi Dan shekara daya.
"Haba Bobo na Wani irin asibiti yanzu kayi hakuri kaji mutafi fuskar na ta zai washe kaji,mama na ai Babu zafi ko?"ya fada Yana kallon inarah da fatan ko zata ce Babu zafi.
Aikuwa cikin iKon Allah tace"Zaki na ni banson zuwa asibiti mutafi kawai kaji".
"Shikenan Abbie kuje yanzu zamu tawo canza kaya itama haka"Ayzaan ya fada Yana kallon Abbie.
"Kaini tawo mu tafi kyale wadannan bazan iya da rikicinsu ba bokararrun yara haka".innah ta fada tana wuce wa tayi gaba,yayin da Abbie yake ce musu suyi sauri to suzo yanzu.
Ayzaan ya kalli Inarah, kafin ya ce cikin nutsuwa,
“ chuchu muje ki canza kaya, ni ma zan canza sai mu tafi.”
Inarah ta ɗan yi shiru tana kallonsa, sannan ta gyara mayafinta tace.
“To Zaki ni bazanyi wanka ba kawai zancaja kaya ne.”
Abbie kuwa ya girgiza kai yana murmushi ya yiwa yafi innah Yana cewa.
“Bobo na, sarkin rigima.”
Ayzaan ya kalle shi da gefen ido Yana fadin.
“Abbie, yau fa bana son wasa Allah.”
“Na sani, tunda antaba zuciyar ka,bayan itama ta iya tsokana,ka sassauta zuciyarka. Ranar Meeting ne yau, ba ranar yaƙi ba kaji dai.”
Bai jira amsar Ayzaan ba suka fice daga dakin lokacin suma su Ayzaan sunfito daga bangaren innah lokacin babah adama kawai suka bari a sashin.
Lokacin kusan kowa ya hallara shigar su innah yasa ya zama su Ayzaan ne kawai basu shigo ba,kasantuwar basu da yawan kananan yara sosai yasa duk manyan ne se yan matasan se yara kananan da basu fi biyar ba.
Bangaren inda Hajja zasu zauna ita da innah daban.
Haka bangaren su ummee, Ammie,mommy mammah duk dai Suma gurin zaman nasu daban.
Haka bangaren su Hibba da su Zaitoon su Muhibba kuma tana kusa da Najlah da Khairah,duk dai wasu yanmata Suma suna guri daya ne.
Haka Suma bangaren mazan gurin irinsu Yaya Khalid, Umair, Hafiz duk dai Suma sun hallara,Ayzaan ne kawai Babu agurin.
Bangaren su Ummee kuwa tana cikin damuwa saboda har yanzu Inarah da Ayzaan ba su bayyana ba,tasan dole se anyi magana Kuma wayarsu duk bata shiga ba,hakan yasa matsa kusa da Ammie da itama irin tunanin takeyi,tace mata, Ammien Ayzaan kinga abinda yayanki sukayi ko?Ayzaan kullin yafi so ya dinga samu magana.
Inba sa'a ba yanzu se kinji ana magana." Ta karasa maganar jikin rashin Jin dadi.
Ammie ma cewa tayi"Kuma nayi musu gargadi fa,Amma kinga se da dai suka ki zuwa akan lokaci...
Ammie bata rufe bakin ta ba kuwa suka tsinyaki maganar baba Umar cikin fushi Yana fadin"wai Ina wannan yaron ne,shi kullin se ya samu jira kokuwa shine gaba damu da zamu zauna anan muna jiransa! Kullin iskancin sa Kara karuwa yakeyi ba ."haka yacigaba da fada yayinda wasu daga cikin iyayen Suma suka sa Baki cikin maganr kowa da manufar sa.
Haka itama mammah acan bangaren taita kananun magana "su da sukafi kowa ne Yaya zane ai sayi hakan yara sun Raina kowa ba Wanda suke gani da da daraja marasa tarbiya kawai."haka take ci gaba da maganar Wanda Babu Wanda ya tankata acikinsu.
Abbah Yana kokarin Kiran wayar Ayzaan din suka ji sallamar su acikin hall din.
Kowa ya waiga ya zuba musu Ido kowa da tunaninsa akansu.
Ayzaan ne ya fara shigowa.
Sanye yake cikin jallabiya navy blue Mai matukar taushi, fuskarsa babu murmushi ko kaɗan, sedai yayi Wani irin kyau na fitar hankali kansa kamar ko yaushe daure gashinsa cikin band navy blue Wanda ba'a hangowa sabida yadda gashin ya kwanto a gadon bayansa.
Bayan shi kuma Inarah ce takebin sa a hankali kamar zata shige jikinsa,dogon hijab ne jalbab ajikin ta navy blue Wanda yayi matukar yimata kyau.
suna shigowa, idanuwan mutane da dama suka sauka a kansu.
Inarah wacce tafito abayansa Jin fadan da baba Umar yakeyi ne yasa ta fito ahankali kamar mara gaskiya ummee da idonta ya sauka akan fuskar inarah lokaci daya da yadda Ammie ma idonta yakai fuskar ta ta Amma bata motsa ba.
Ummee kuwa wacce ta mike cikin sauri daga inda take tayi gurin inarah tana fadin"me ya same ki Rabin Raina,lafiya fuskar ki tayi haka? Kai Ayzaan me yasamu fuskar ta....
Innah ce ta katse maganar ganin anfara kananun magana tace"Babu komai maleekah je ki zauna lokaci yana tafiya,Maza zakin Mai rabo je ka zauna kaji Dan albarkana."inda idanuwan wasu yake kansu kamar zasu mutu tsabar bakin ciki.
Kamo hannunta Ayzaan yayi agaban kowa, se da ya kaita har gurin zamanta,sannan ya rada mata wata magana a kunne ya juya ya wuce gurin zaman sa batare da ya Kalli kowa agurin ba,fuskar sa a tsuke Dan yau Kam abokin mutuwa yake nema.
Haka kowa ya rakasa da idanu shi kuwa Bai Kalli kowa ba.
Ita kanta inarah sakon harara take amsa daga bangarori da dama.
A hankali hall ɗin ya sake daukar shiru.
Adduo'i aka fara za'a fara gudanar da meeting ,bayan angama adduo'i anbude taro da addu'a hajja amatsayin ta na babba itace wacce zata fara magana,hakan yasa
Hajja ta ɗaga kai tana kallon kowa da kowa Sannan tace.
“Da farko, ina godiya da Allah da ya sake haɗa mu baki ɗaya bayan wani lokaci. Inayiwa kowa gaisuwa da fatan alkhairi,sannan wannan meeting ɗin ba wai kawai domin mu zauna mu gaisa bane.....
Ta yi ɗan shiru na Wani lokaci sannan ta cigaba.
“Mun haɗu ne saboda akwai wasu abubuwa da suka shafi wannan ahali namu gaba daya hakan yasa muka zauna domin mu tattauna akan wasu abubuwan sannan mu fahimci juna.
Saboda haka, ina so kowa ya saurare ni kafin wani ya fara magana,sannan ya zamana duk abinda zakuji kowa ya dauke sa da muhimmanci Babu ja'inja,Babu fada,haka Kuma Babu isgili,Ina fatan yadda muka fara lafiya Allah yasa mu tashi lafiya.”
Ameen sauran mutanen suka amsa.
Sannan ita ma inna tayi magana tace"Babu abunda zance domin hajja ta Fadi komai se dai Ina Kara jimanta mana tare da alhini na rasuwar alhaji baba,tare da fatan Yana cikin rahamar ubangiji,da Kuma Kara Jan hankali agaremu Baki daya gurin Yi masa addu'a.
Haka Ina Kara Yi mana gaisuwar rashin hauwa'u da mukayi(ameerah)Allah ya jikanta.
Ameen aka amsa gaba daya sannan
Daddy sulaiman Wanda shine babba zaiyi magana yace to alhmdlh kamar yadda hajja tayi magana Ina fatan kowa zai saurari abinda zamu tattauna sannan Kuma fatan zaku bamu hadin Kai.