MAKAUNIYYAR SOYAYYA
Wannan labarin kerariya ne, kama daga suna, waje da kuma Guri
Idan labarin nan yayi kama da labarin ka/ki toa a yafe min kafin alkalami ne.
BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM
MAKAUNIYYAR SOYAYYA
Written
By
Mukaramat Yusuf
Page 3
Dariya sofeeya tayi sannan tace: a'a,ba fyade yake kokarin ya min ba,Ni da kaina na jima kaina ciwo ,sannan na daura masa lai'fin ,yana so ya ci min zarafi ,kuma haka dukkanin ku kuka yarda da gaske nike, ilham tace: amma mesa kike masa haka? sofeeya tace:saboda ke,na aikata hakan,na sa ya haukace sosai a kaina,kuma ban daba yin nadama a rayuwa ta ba.tana kai wa nan ta mike ta fice daga dakin.
FLASH BACK
ABUJA
Ameer Bude mana files din da mama ta bamu,fadin Yash,Ameer ya tashi ya dauko files bag da mahaifiyar su ta basu lokaci guda yana buɗe bag din, hoton mahaifin su ya gani tsakale a wani diary da alamu wannan littafin sirrin mahaifiyar su ne,kwanta wa Ameer yayi akan gadon su lokaci daya yana buɗe littafin, Yash ka zo karanta mana,fadin Ameer,daman shi bai iya karatu ba,ya qware ne wajan zane,shi kuma Yash ya qware wajan rubutu da karatu,da sauri Yash ya gyara kwanciyar shi,ya soma karantawa kamar haka:
Ni sunana Hafsah, haifaffiyar yar Yobe da Maiduguri,mamata shuwa Arab ce,babana kanuri ne,mamata nada yara 4,mata 3 namiji 1,ta farko itace A'isha,ta biyu itace Fatima ta uku itace Hafsah watoa Ni kenan,sunnan namijin mu kuma Sultan ,munyi makarantu da yawa a Kano,duk da mu masu masa kaicin karfi ne , amma hakan bai hana mu muyi karatu ba,ina shekara 12 mamar mu ta rasu,a nan baban mu ya soma rashin lafiya a saisai har ya kwanta,sosai yaya na tayi aiki Tukuru ta na dawainiyya da gidan mu,tana biya mana school fees, we are not lack in every thing,har mahaifin mu ya rasu ya bar mu,anan ne duniya ta soma mana zafi,mun rasa daga ina zamu fara, a duk lokacin da na tambaye A'isha tayi min abu,zata ce bata da kudi,duka kuɗaɗen ta tana biya school fees din sultan ne,wanda yake eropian yana karanta d.s.s.,a nan ne na samu wani dan mai kudi ,mai sona,muka soma soyayya,da soyayya ya kai soyayya har kaina na bashi,don ya min alkawarin zai bani kudi,gida da abubuwan jin dadi tare da cewa zamu yi aure,Ni kuma sai na yarda tsar idanuwan ta wa sun rufe da soyayya ma'ana MAKAUNIYYAR SOYAYYA.
Bayan wasu watanni , na soma lau layi,a nan ne aisha,Fatima,da Kani na Sultan wanda ya soma aiki kenan a dss in department of binciken sirri, muka nufi asibiti aka min test, anan ne nakura ta tabbatar da ina dauke da cikin watan Ni,yaya A'isha ta kale Ni tace:Sultan bana gaya maka ba , ciki gare ta,yaya Fatima tace:ashe karatun da ki kayi na likitan ci ba a banza ba,Bama wannan ba,yanzun likita me za'a yi,zan baku wasu magunguna sai tasha,nan Sultan ya biya kudin maganin.
Bayan wasu shekaru abubuwa da yawa sun faru,na alkairi mana,ciki hadda haihuwar ku, auran yaya A'isha,duk muna zaune ne a gidan mijinta,ta auri wani dan kabilar yar'bawa ne,a chan Oyo state,mijin ta shi yayi dawai niyyar sunan ku,shi kuma Kani na Sultan ya na bincike akan waye uban ku,kuma ya samo,shi da kanshi ya zabar maku suna,a nan ne Adebayo mijin yaya A'isha yace:ya aure Ni wannan shine zaman lafiyar mu,shi kuwa mahaifin ku yace:ba zai auri mace wanda take cikin MAKAUNIYYAR SOYAYYA da shi ba domin kuwa ko babu shi zata iya yi da wata,yana kai wannan ya fice,yaya A'isha tace:Kinga illar MAKAUNIYYAR SOYAYYA,gashi har kin haifi shega,shin uban su amer da Yash yace:yana son ki? a'a ko,toa ki sani yayi amfani da soyayyar gaskiya da kike masa,shike nan zan lalabe miji na sai yaje ya bashi hakuri dan kuyi aure,a hankali Hafsah tace :toa.
Mashaallah,Adebayo ,da yaya Fatima sun je har gidan baban ku ,kuma ya yarda da aure,washe gari aka kawo sadaki na ,da abubuwan al'adu sannan aka sa rana, alhamdullilah an daura auren lafiya lau,har an min shiri na tafiya Kano,a karo na biyu zan shiga Kano,a yammacin ranar na bi jirgin sama nan da nan muka iso,a takaice a ranar ya sake Ni,sannan yace shi zai na ciyar da Ni da ku,mu zauna a matsayin marayu,muyi rayuwar tamkar ba Muda shi, wannan shine kwanciyar hankaln shi da nawa,abun da bansaniba shine ashe yayi aure , sannan umurnin sa take bi Ali da yauce.
CIGABAN LABARIN
Washe gari,da Misalin karfe 8 da rabi na safe secetariya ta iso,a lokacin ko wani dalibi na nan a class,yasa ba wanda ya ga fita warta da kayanta,sai filin jirgi,karfe 9 daidai jirgin su ya tashi,sai dai ince Allah sauke su lafiya.
BAYAN WASU SHEKARU
Kai masoyi , dubu dari uku ka mika min tamkar ka shillar da pepopi(papper') fadin wata matashiyar budurwa ,wanda ganin ta daya tak sai ka su suce,tsabar ken ta,ga
Ko ina sun ciko,ta kara wani freash da ita, murmushi wannan saurayin yayi sannan yace :haba Beb , it's my pleasure, murmushi sofeeya ta yi, sannan tace:time for launch, Nan suka mike suka fita,hira kasa kasa suke yi abun gwanin burgewa , Hashim yaushe zaka turo kudin gaisuwa, kasan babu lokaci, fadin sofeeya tana kallon wannan matarshi mai suna Hashim ,murmushi Hashim yayi sannan yace: sofeeya ta,gobe yayi?ya tambaye ta lokaci guda yana daura hannun sa a' waist dinta, e'h Hakan yayi, ya furta a hankali, mutumin da ke zaune a table 7 ,sanye da face mask,sai kallon su ya ke, wannan idanuwan sa yana nan yadda suke a lokacin baya,watoa lumsasu, Fara re,mai gwanin burgewa,da taga ido ya masu yawa kwai sai ta sanya bakin ta cikin na sa,a fisa ce mutumin dake table 7 ya mike ya fita,motarshi ya shiga ya tayar ya bar harabar gurin ,a nan ne maganar mahaifin ilham ke dawo masa : sofeeya Bara san ka,amfani da kai take don ta cinma burin ta,mtwwww ya ja saki sakanin lips dinsa .
Washe gari da Misalin karfe biyu na rana a ke kokarin a hadda ma sofeeya baiko, ita da Hashim,sosai hole din ya cika da jama'a tare da dangi,kafin a fara da ko wani kalan shiri, i will like you to wach
this video from Mr smile,fadin wata matashiyar budurwa wace akayi hayar ta a matsayin kawar amarya, nan ta sanya carset dake hannun ta,sai ga hotunan Hashim da sofeeya, yana kaiwa karshe wani video ya soma play, kamar haka : kai aboki muna baka shawarar kada ka aure ta,don ta kwana da Ni sau 23,wani kuma yace:ai dazun a restaurant kaga halin ta,indai batun kudi ne toa tana
gaba,ko batun iskan ci,nan aka sanya wani video din ta,babu kaya a jikin ta ,ita da isham ,suna yin abun da Allah ya hana watoa zina,sanda video din ya kai karce aka nuna producer by smile in emoji line.
A take a wajan mahaifiyan ta ,Ade -kunle,ya yanke jiki ya fadi,kanwar sofeeya,Dele da mahaifiyar ta temi tope su suka tallafo mahaifiyan su, lokaci guda suna neman taimako, Amma Babu Wanda ya taimaka Masa,suna cikin wannan halin motar asibity ta kariso da alammu an kira su ne,da sauri sofeeya zata shiga motar maman ta daka tar da ita,ta hanyar cewa dan Allah ki barmu hakan. Da na saurari zuciya ta,toa na na zubar da cikin ki,tun da jima.
FLASH BACK
Angwan folaye illorin road
Temi tope”dakun mo binu, Moda Inu yin nu,so to bi”temi tope kar ki zubar da cikin nan , kinji wata kila alkairi ne a garemu,temi tope tace: a'a ita ba alkairi bace ba,da alkairi ne da baza kayi asarar a wannan shekarar ba, murmushi Ade-kunle ya yi sannan yace:na yarda da qaddara,ki saka hakan a matsayin qaddara.
CIGABAN LABARIN
A gidan ƙaruwai sofeeya ta kwana,sosai tasha kayan maye kafin ta kwanta,washe gari, wayan tane yaso ma kara,da alamu ana kiran tane,kara wayar tayi a kunni,” aka fada miki shaye shaye shine mafita ko tushin bil adam,toa karya ne , mudun baki zo asibiti ba ,toa rayuwar baban ki na hatsari”, aka gaya a dayan bangaren,dA sauri tafita daga ita sai kayan jiya, asibi daret ta nufa ,jiya da yau sosai ta fice a hayacinta,yadda ta fito a yau toa ba marabar ta da mahaukaciyar kan titi.
FLASH BACK
KANO
Tun lokacin da na dawo zama a Kano,bani da wani abokin sai ku,da laila , ina gida naji rasuwar Adebayo,na yi kokarin naje amma mahaifin ku ya hanani,a haka muke rayuwa , mutuwa na gobara ce,amma set up ne,laila itace wace ta kuna ashana a palo, don dana fito daga wanka,naji warin petrol,sai ban dauke shi a komai ba,ina daki na soma jin zafi na fito palo , anan ne naga cewa wuta na ci,kuma na kira laila Amman bata daga min waya ba,sai kuma na kira mahaifin ku,shine yace:gashi nan zuwa,kada ku yarda da duk abubuwan da zai baku,don Lokacin da nake yi masa gaskiyan soyayya ya kasa nuna min,sai akan ku ne zai nuna? amsar shine a'a,ba ya san ku,kada ku rayu da soyayyar mahaifin ku.sannan kada ku shiga MAKAUNIYYAR SOYAYYA ,wanda zai kai ku ya baro ku kamar Ni dai mahaifiyar ku. CIGABAN LABARIN
Fumilayo hospital Lagos
Idan ka isa ka fito in ganka,don na tabbatar da cewa yash ne, a lokaci
Guda ya sa aka fasa baiko naa , mahaifiya ta ta yaye Ni,na koma tamkar mara hankali,dariya yayi sannan yace:a lokacin da kika daura min sharin zan ke da maki hadin ki,shin kin yi tunanin yaya rayuwa ta zata changer, a'a toa nima ban yi tunanin hakan ba,sannan gani a bayan ki,yana kai wannan ya kace wayar shi ,bindigar dake jakarta ta fito dashi ta juya ji kukeyi tas…..tas…..tas da alamu ta halbe sa .