19
by @mahmazee1
Fuskar shi a kame sosai, wannan Karon ma yana cikin tsadaddiyar jallabiya mai daukar ido tun daga nesa, sai sunglasses din gucci mai dan haske kadan da ya kawata fuskar shi.
Ba tare da damuwa da wanzuwar mutum a gurin ba, ya nufi lift ya latsa button tare da dan ja baya kadan yana rungume hannayen sa duka baya, da alama hakan dabi'ar sa ce, yana jiran isowar lift din.
Tun da ya tunkaro gurin tayi saurin dauke kan ta daga kallon shi, A sanyaye tayi kasa da idanun ta har ya latsa lift din ya ja baya.
Rungume hannayen ta tayi a kirji tana Jin yanda wani irin kwarjinin sa ya cika ta musamman da su biyu ne kawai a gurin, hakanan tana shakar daddadan kamshin patchouli da ta tabbatar daga turaren sa ya ke fitowa, ta kasa iya ko waiwayowa bare ta ko gaishe shi.
Har lift din ta iso, sai da mutanen da ke ciki suka gama fita kafin ya shiga, dan janyewa tayi ta bashi hanya domin ta fishi kusa da elevator din, bata Jin zata iya hada lift da shi, saboda haka sai tayi deciding jiran next one.
A hankali ya zare sun shades din idanun shi, ba tare da ya dago kai sashen ta ba ya dan fizgar da iska, kafin ya mika hannu ya tsayar da lift din da ke kokarin hayewa sama, wanda hakan ya bayyanar da kwantacciyar gargasarar da ke farar fatar sa da agogon frederique constant da yayi amfani da shi.
Kamar daga sama ta jiyo kamilalliyar muryar sa wacce ke fita cikin bada umarni, wanda hakan har ya zamo dabi'ar sa wato commanding
"Do come in" ya fada cikin kakkausar muryar sa mai cike da kwarjini.
Tayi dan jim Tana squeezing jilbab din jikin ta, kafin ta taka a sanyaye ta shiga, ba bata lokacin elavator din ya daga, yana daukar wani irin shiru.
Duk fadin elevatorn sai ta ji mere presence din sa ya cike gurin gabakidaya, ko don tsayin sa mai ban mamaki da kuma kwarjinin sa mai intimidating, da ya sanya ta yin kasa da kanta kawai, ta zurawa flat shoes din kafar ta ido.
Sai lokacin ne ta iya gaishe shi ba tare da ta dago da kanta ba
"Ina yini" ta furta a sanyaye
Da lafiya ya amsa gaisuwar, yana gyara tsayuwar sa tare da crossing kafafun shi, dayan hannun shi rike da shades din sa da bai mayar ba.
Har elevator din ya kawo su lobby floor, shi ya riga ta ficewa da hanzari, yayin da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tare da shakar iskan da tayi mata wuyar Shaka tun dazu, sai kamshin shi na Gucci Guilty da ya cike ta.
Tuni ya bacewa ganin ta, ta janyo wayar ta da ke cikin siririyar jakar da ta rataya ta kira Adam, wanda ya nemi ta bashi minti biyu yana saukowa daga dakin Najib da yake suna tare tun dazu.
Kan daya daga cikin kujerun lobby din ta zauna jiran sa har ya sauko suka fice.
Gobe suke komawa Nigeria, saboda haka tun a yau suka tattare komai na su, washegari jirgin su ya daga a Jidda.
Tunda suka dawo tayi resuming school saboda academic activities da aka soma tuni, she got busy da karatu da project din ta, wanda ya dauke mata hankali sosai, Adam ma ya cigaba da aikin sa cikin tarin nasarori.
********
Karfe shida ta shigo gidan yau daga school a mugun gajiye, haka kawai ta ke Jin wata irin kasala kwanakin nan, bata iya tabuka komai, shiyasa lectures din yau suka bata wahala domin tun 10am ta shiga school.
Kai tsaye bedroom din ta ta nufa tana jefar da handbag din hannun ta kan gado, da kuma folder na project din ta da har ta fara submitting Ana yi mata gyara.
Duk da yammaci da yayi, da magrib da ya dosa, sai da ta dan kwanta kan gadon, ta dan huta for a while kafin ta fada bandaki.
Tayi wanka ta fito daure da madaidaicin towel ta nufi dresser, tayi shirin ta cikin sassaukar boubou ta tayar da sallar magrib, tayi evening azkar din ta wanda sai yanzu ta samu damar yi kana ta nufi kitchen.
Cornflakes ta hada ta sha sosai kafin ta hada simple dinner, stir fried pasta tayi, wacce tana yi tana yatsine fuska saboda warin abincin da ke bugun ta.
Hakan ya sanya ko da ya dawo shikadai yayi dinner Sam sai taji bata son cin pasta din.
Washegari ya riga ta tashi, yayi mamaki ganin har ya gama shirin shi bata tashi ba, bare tayi shirin fita school.
A hankali kamar mai tashin karamin yaro ya soma daddaba ta a karo na uku kan ta tashi ta shirya.
Manyan idanun ta da suka yi laushi sosai alamar mai bacci ta ware kan shi, daga kwancen da ta ke ba tare da ta mike ba, ta dan yatsine fuska kadan tare da dafa goshi.
"bana Jin zan fita yau, kai na ya na dan ciwo"
Take damuwa ta bayyana kan fuskar sa, cikin nuna kulawa ya zauna gefen ta yana dafa goshin ta "are you okay, me yasa ba ki gayamin ba"
"Hmmm ba wani sosai ba ne, tun da nayi sallah me nake dan Jin headache din" ta ansa shi
Kallon yanayin ta yayi da kyau kafin ya gyara mata lullubi yace "okay ki koma bacci, zan kira ki later in ji ya jikin"
Ya mike bayan kissing hannun ta da ke cikin na shi yana fadin "Allah ya sawwaka"
Bayan fitar shi ta koma baccin ta, ko da ta tashi sosai ciwon kan ya tsanan ta mata har ma ta kasa yin chores din gidan, Adam ma bai fasa kiran ta ba jimi jimi domin Jin lafiyar ta.
Karfe biyar da rabi ya shigo gidan, zuwa lokacin tana kan sofar falo, ko daga yanayin kwanciyar ta zaka fahimci ba lafiya ba.
Da hanzari ya karaso yana zama kan center table da ke gaban ta.
"Wifey jikin ne" ya fada yana kama hannun ta cikin na shi.
Da kyar ta iya bude idanun ta da suka yi mata nauyi ta dora su kan shi, tare da gyada mishi kai alamar eh.
"Ayyah sorry, sannu, kin ci abinci, kin sha maganin"
Nan ma da kai ta amsa shi ta hanyar girgiza mishi kan ta, gabakidaya ba abinda ta iya ci yinin yau, sai ruwa kawai, maganin ma da ya matsa ta sha dazu bata iya sha ba.
"No haba, fahima, kina son janyowa kan ki babban ciwo ne, ina zuwa" ya mike ya nufi kitchen kai tsaye, indomie ya hado mata da orange juice a glass cup ya kawo wanda spoon daya kawai tayi ta ji abincin na tayar mata da zuciya.
Cikin damuwa ya kalle ta "toh me zaki iya ci"
"Cornflakes" tayi saurin fada
Kitchen ya sake komawa ya hado cornflakes a bowl ya kawo mata, wanda ta sha sosai fiye da na jiya, har tana mamakin yawan da ta sha.
Ya ballo mata paracetamol biyu ta sha, kafin ya fice masallaci cikin sauri saboda sallar magrib da aka tayar.
Ta dan samu karfin jikin ta domin sai da ta watso ruwa ma kafin tayi sallah, sai dai ko da dare ya raba headache din ya dawo mata wannan Karon har da zazzabi.
Zuwa safe jikin ta yayi zafi sosai, cornflakes din ma tana sha yau ta amaryar da shi duka, ganin jikin na ta yayi tsanani har zuwa zuhr ba sauki ya dauke ta kawai suka fice asibiti.
Kai tsaye Dr da suke gani ya shiga duba ta, wanda ya ba ta gado tare da running tests.
Yana zaune gefen ta kan kujerar roba rike da hannun ta da ke cikin na shi, yayin da ta ke kwance ba bacci ta ke yi ba, sai dai ta ji dadin jikin ta sosai tun bayan drip din da suka dora ta kai.
Da sallama likitan ya karaso dauke da madaukakiyar fara'a kan fuskar sa
"Na zo da kaina domin sharing good news din da ku" ya nisa
"congratulations Mr and Mrs Adam, you're pregnant" likitan ya karashe da fara'a, shi kan shi zaka fahimci how delighted he is da wannan news.