5.
by @zeeykumurya
KOMAI NISAN DARE
Page 5.
Zeey Kumurya
Innar Ma'u ce ta ƙaraso ta riƙe hannun A'isha, ganin yanda Inna take ƙoƙarin rikicewa yasa ta dube ta cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Karki tayar da hankalinki Asabe, na fi tunanin sumbatun ciwo take yi, kin san zafin zazzaɓi yana saka haka." Inna ta ce. "A'a Ladidi, taɓa jikinta ki ji babu wani zafi sosai, jikin nata ma fa ya yi sauƙi, gaskiya zazzaɓin jikinta bai yi yawan da zai saka ta sumbatu haka ba." Innar Ma'u ta ce. "To ko yunwa ce ta saka bata gani sosai? Kuma ga gari ya fara duhu shi yasa baza ta ga komai ba." A'isha dake sauraren su ta ce. "Innar Ma'u ba yunwa ba ce, gani ne bana yi, kuma idon ya mun nauyi." A rikice Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan wanne irin ciwo ne haka? Daga zazzaɓi sai ki daina gani? Kuma ga idon naki nan babu alamar wani abu ya same shi, dan ko sauya kala bai yi ba." Innar Ma'u ta ja hannun Aisha suka fara tafiya ta ce, "Ina zuwa, bari na gwada wani abu." Mara mata baya Inna ta yi cikin tashin hankali. Kasancewar Innar Ma'u tana k'wan wutar sola a ɓangarenta sai ɓangaren ya samu wadatuwar haske sosai. Bayan sun shiga ɗaki ta cewa A'isha. "Kina gani yanzu?" Girgiza mata kai ta yi alamar a'a, fitila Innar Ma'u ta ɗauko ta haske idon A'isha, amma nan ma ta ce babu abun da ta gani. Hankalin Inna fa ya ƙara dugunzuma ta fara hawaye, jan A'isha ta yi jikinta tana ta duba idon nata kamar me neman abun da ya hana A'ishan gani. Ita ma A'ishan kuka ta fara tana faɗin. "Inna ki kai Ni a bani magani idona ya buɗe in cigaba da ganin ku." Rungume ta Inna ta yi ta ce. "Insha Allahu Idonki zai buɗe A'isha, ki cigaba da ganinmu." A'isha ta ce. "To Inna, raka ni in yi fitsarin." Innar Ma'u wadda hankalinta ya fara tashi ita ma da al'amarin ta kama hannun A'isha cikin sanyin jiki ta raka ta, ta yi fitsarin, dan sosai hankalin Inna ya tashi, kuka take yi ba kaɗan ba, jikinta gaba-d'aya ya yi sanyi, ga wata irin fad'uwa da gabanta yake yi. Cikin tausayawa Innar Ma'u ta dube ta bayan A'isha ta yo fitsarin ta ce. "Ki yi hak'uri Asabe, in Allah ya yarda ba wata matsalar ba ce, yanzu abun da za'a yi ki shirya mu je gidan Malam Ilyasu mai magani ya duba idon nata, ina da wasu yan canji za su ishe mu insha Allahu, tunda Ma'un ba ta dawo ba." Inna tana goge hawayen idonta ta ce. "Toh." Gidan Malam Ilyasu da ɗan nisa daga nan, dan haka Innar Ma'u ta ce bari ta yiwa Adamu ɗaya daga cikin yaran gidan magana tunda ranar Kasuwa ce duk suna nan ya kai su a babur ɗinsa, saboda kafin su samu na haya ɓata lokaci ne, dare ma ya yi duk sun tafi zai yi wahala su samu. Inna shiru kawai ta yi mata, amma ta san zai yi wahala ya je in ya ji su zai ɗauka. Suna soro suna jiran Innar Ma'u sai ga ta ita da Adamun, mamaki ne ya cika Inna ba kaɗan ba, amma dai ta shanye ta kama hannun A'isha da nufin su fara tafiya sai ta ji Adamu ya ce. "Aaa, Innar Ma'u ya na ga wannan Matar kuma? Da ita za mu tafi ne?" Cikin tausasa harshe Innar Ma'u ta ce. "Ita ma zaka ɗauka tare da Aisha ai, saboda A'ishan ma na kira ka, ka san ba ta da lafiya ba za ta iya doguwar tafiya ba." Adamu ya haɗe rai yana wani gyaɗa kai irin na wulak'anci ya ce. "Wallahi ba zan ɗauki Mayun nan a babur ɗina ba gaskiya, Innar Ma'u sai dai ki nemi wani." Innar Ma'u ta ce. "Haba Adamu, taimako fa zaka yi, kai ma watarana Ubangiji sai ya baka abun da ba ka yi tsammani ba sanadiyyar taimakon nan da zaka yi, dan Allah ka taimaka ka ɗauke su, ni sai in baka ɗan kuɗin Man babur ɗin ma." "Sai dai fa ki yi hak'uri gaskiya, dan baza ni ba." Adamu ya faɗi haka tare da juyawa ya yi tafiyarsa. Inna ta share hawayen idonta ta ce. "Mu je da ƙafa kawai Ladidi." Innar Ma'u ta ce. "Ya za'a yi mu je da ƙafa, ai mu in zamu iya zuwa A'isha baza ta iya ba." Inna ta ce. "Sai in goya ta." Innar Ma'u zata kuma magana, Inna ta katse ta da faɗin. "Karki damu zan iya, Ni dai burina mu yi mu je gurin mai maganin nan." Innar Ma'u ta ce. " To Allah ya kai mu lafiya." A hankali Inna ta zare A'isha wadda ta yi lamo a jikinta, sannan ta tsugunna ta ce ta hau bayanta. A'isha bata yi musu ba ta hau, Inna ta miƙe daƙyar har ta yi kamar zata tintsira saboda babu laifi A'isha tana da ɗan nauyi. Innar Ma'u ta ce. "Yi a hankali dai." Duk da Inna ta ji a jikinta da ta ɗauki A'isha amma haka ta daure ta jure suka je har gurin mai maganin, bayanta har sagewa ya yi, tana sauke A'isha ta shiga numfarfashi kuwa. Daƙyar suka samu ganin mai maganin, dan da farko cewa ya yi sai dai su dawo da safe yanzu dare ya yi. Innar Ma'u dai ta roƙe shi akan ya taimaka musu, ta faɗa masa daga ɗan nesa suke kuma da ƙafa suka zo. Tofi mai ganin ya yiwa A'isha a ido, bayan Inna ta yi masa bayanin abun da ya faru. Ya kuma ba su wani magani ya ce a haɗa mata da farin kwalli ana saka mata a cikin idon, indai jinnu ne kamar yadda suke tunani to idanun za su buɗe da yardar Allah, idan kuma har bayan kwana uku idon bai buɗe ba kuma an yi mata amfani da maganin to sai dai su je asibiti a duba mata idon. Godiya sosai suka yi masa sannan suka ba shi abun sadaka suka dawo gida, a dawowar ma haka Inna ta ƙara goye Aisha. Ai kuwa da jan ƙafa ta dawo gida, dan ba ƙaramin ciwo bayanta yake yi mata ba, gashi Innar Ma'u ta ce ta kawo ta taya ta da goyon A'ishan amma ta ƙi bata. Dan a ganinta hakan bai dace ba, ta ja ta sun yi tafiyar ƙafa kuma sannan ta ƙara mata da goyon ƴa. Duk da gajiyar dake addabar ta suna dawowa ta hau dakan maganin da suka karb'o, dan ita kawai burinta Allah ya buɗar mata da idon yarinyarta.
A'isha kuwa jin ta take wani iri kamar ba ita ba, kamar a mafarki haka take gani abun. Duk inda Inna ta yi tana biye da ita, gani take kamar in ta zauna ita kaɗai wani abun zai faru da ita saboda ba ta gani. Duk bayan wasu mintuna sai ta shafi idon nata ta ji dai a buɗe yake, ko kuma ta yi ta kifkifta shi wai ta ji ko ya daina motsi. A daren Inna ta haɗa maganin da farin kwalli ta shafa mata a idon tare da addu'ar neman dacewa, ba jimawa da shafa matan ta yi bacci bayan ta ci tuwon da Innar Ma'u ta kawo mata. Inna kuwa daren yau ko runtsawa ba ta iya yi ba, tasa A'isha ta yi a gabanta ta rabka uban tagumi tana hawaye, da dare ya tsala kuma ta miƙe daƙyar ta yo alwala ta hau yin nafila akan Allah ya buɗi idon ƴarta. Washegari a makancen Aisha ta tashi, Inna ta yi mata wanka da duk abun da ya kamata sannan ta ƙara saka mata maganin, kamar yadda mai ganin ya ce tana saka mata sau biyu a rana, safe da dare. Wuraren ƙarfe tara na safe Inna tana zaune a tsakar gida tana gyangyad'in da ba ta san lokacin da yake ɗaukarta ba ta ji maganganun mutane a cikin kanta. Buɗe idonta ta yi ta ga su Ramatu ne da wasu daga cikin matan gidan. Hansai na duban ta, tana tafa hannuwa ta ce. "Ashe haka abu ya faru kuma? An cinye idanuwan wasu abun ya dawo kanku, an yi k'aik'ayi koma kan masheki'ya kenan? To Allah ya tsare mu ya tsare mana ƴaƴanmu, wannan masifa har ina ta lashe_lashe da cinye_cinyen naman mutane." Sai kuma suka saki shewa haɗe da dariya gaba-d'ayansu suka cigaba da yarwa Inna habaici, ita dai ko kanzil ba ta ce musu ba. Ana cikin haka sai ga wata tsohuwa tana tafiya daƙyar ta zo ita ma, tana shigowa ta fashe da kuka ta fara faɗin. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan wanne irin bala'i ne Isuhu ya kawo mana cikin zuri'a, gashi ya mutu ya bar mu da jalala, a ce a cikin gidan nan Mayya ta cinye idon wani abun ya dawo kanta? Wannan ai abun kunya aka ja mana a cikin zuri'a." Sai ta ƙara fashewa da kuka kamar wadda aka ce wani shak'ik'in nata ya mutu, cikin kukan ta ce. "Ba irin yanda ban yi da Yaron nan ba akan ya saki tsinanniyar matar nan amma ya ƙi, saboda ba ni na haife shi ba bai ɗauke ni a bakin komai ba duk da ina matsayin k'anwar Ubansa, to ga irin ranar da nake guje mana nan ta zo ai, Isuhu ka cuce mu ka ɓata mana sunan babban gida irin wannan a cikin garin nan." Innar Ma'u tun tijarar da su Hansai sukewa Inna take jiyowa, amma bata yi yunk'urin zuwa ba sai yanzu da ta ji yo Muryar Iya. Mayafinta ta zara ta yafa ta shiga zagayen su A'ishan cikin sauri, dan duk maganganun da Iya ta yi a cikin kunnanta, hakan yasa tana zuwa ta ce mata. "Haba Iya, wai don Allah me yasa kuke haka ne? Wannan abun da ya faru da A'isha Allah ne fa ya ɗora mata, cuta ce daga Allah, amma........." Cikin masifa Iya ta katse ta da faɗin. "Ke Ladidi bana son shishshigi a al'amurana fa kin sani, tunda ke an riga da an gama shanye miki kurwa ai dama baza ki taɓa ganin abun da take yi ba, dan haka ki mun shiru kafin na saɓa miki a gidan nan billahillazi." Innar Ma'u ta tausasa harshe ta ce. "Allah ya baki hak'uri Iya, amma dan Allah ku bar ta haka ta ji da abun da yake damun ta." Cikin son ƙara tunzura Iya Ramatu ta ce. "Iyee, lallai Ladidi wuyanki ya isa yanka, Iyan tana magana kina mayar mata akan wannan tsintacciyar magen?" Ta ƙarasa Maganar tana riƙe haɓa tare da jinjina kai kamar wadda ta ga an yi wani babban sab'on Ubangiji." Iya ta ce. "K'yale ta Ramatu ta zage ni, ai dama ba yau ta saba ba, amma yanzu ba ta ita nake ba tukuna." Ba ta jira amsar kowa ba ta dubi Inna ta ce. "Wallahi yau sai kin bar gidan nan ko da uban kike yawo a cikin garin nan, duk wani ma wanda yake ɗaure miki gindi kike cigaba da zama a gidan nan yau zan iya da shi, komai zai faru sai dai ya faru amma yau sai kin bar mana gida, baza ki cuce mu ki shafa mana baƙin fenti a cikin zuri'a ba, tunda yanzu kin fara cinye idanun mutane nan gaba kayan cikin mutane zaki fara ci, tunda dai k'asurgumar k'ungurnar MAYYA ce ke. Ato gara ki tattara ki yi gaba, maza_maza a haɗa tsummokarai a bar mana gida, yau ba mai_garin Kumurya ba, ko Mai_Kano ne gaba-d'aya wallahi bai isa ya saka na janye na bar ki kin cigaba da zama a gidan nan ba, ehe." Inna dai kanta na ƙasa ko d'agowa ba ta yi ba, wasu irin hawaye masu ɗumi ne suka zubo akan kuncinta, a hankali ta yi saurin saka hannu ta goge su." Sauran matan gida dake gurin farinciki fal zuk'atansu, ji suke kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha, yau ranar tonan asirin Inna ta zo, domin sun san ba ta da gurin zuwa kuma ba ta da mai ba ta gurin zama, wannan tozarci da Inna ta yi mata ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba." Cikin tsawa kamar Iya za ta kai mata duka ta ce. "Asabe ba kya jina ne? dake fa nake, ki tashi ki yi ki bar mana gida, idan kuma ba so kike in saka a fitar mun dake ba, tunda na bi miki ta mutunci amma ba ki gani ba." A hankali Inna ta miƙe cikin sanyin jiki, murya a sanyaye ta ce. "Ki yi hak'uri Iya, yanzu za mu tafi insha Allahu." Iya tana gyara ɗaurin zani ta ce. "Yawwa, yi maza_maza da Allah, ayi_ayi a zo a ƙara mai, umma ta gai da Ashsha." Ba tare da Inna ta kalli kowa ba ta juya ta shige ɗaki dan haɗa kayansu............✍️