7.
by @zeeykumurya
KOMAI NISAN DARE
page 7.
Zeey Kumurya
Cikin ikon Allah rayuwa ta fara warware wa su Inna, domin kuwa kamar yadda innar Ma'u ta faɗa ta yiwa Hajiya Talatu magana kuma ta ɗauki Inna, duk ranar juma'a tana samun 500 ɗinta sannan kuma ga abinci wanda za su ci su ƙoshi a ranar har dare, har washegari ma yake kai musu su d'umama su yi karin kumallo da shi. Ƴar Innar Ma'u ta fari ta kawo mata ɗanta mai suna Yusuf, ana kiransa da Malam ƙarami, ya dawo hannun Innar Ma'un gaba-d'aya da zama. Shine Innar Ma'u ta cewa Inna ta dinga yin aya mai sugar da Mai gishiri sai ya dinga fitar mata da ita idan ya dawo daga makaranta. Inna ta yi Na'am da wannan shawarar, ba tare da jinjiri ba ta siyo ayar ta fara soyawa. Alhamdulillah ana ciniki sosai, dan duk mutanen gari ɗaukar su Innar Ma'u ce take yi, ga kuma Nik'an kayan miyan shi ma ana kawowa ba laifi, Dai_dai gwargwado Inna sun samu rufin asiri, cikin abun da bai fi sati biyu ba ta biya Innar Ma'u duka bashin da take bin ta, sannan ta fara bankin ajiyar kuɗin kai A'isha asibitin Kano.
Yau juma'a, da yamma Inna suna ɓangaren su Innar Ma'u suna Nik'an kayan miyan wani biki da za'a yi anan unguwar ita da Innar Ma'un. A'isha da Ma'u suna gefe Ma'u tana ba ta labarin abubuwan da suke faruwa a makaranta. A'isha ta dubi saitin da take jin muryar su Inna ta ce. "Inna kin ji, Malam Buba kullum sai ya zo aji yana nema na, wai za'a mun passport ɗin zana jarabawar komen." Inna ta ce. "Me cece haka ita abun da zaki zana ɗin?" A'isha ta ce. "Jarrabar shiga Sakandire ce." Inna ta ce. "A'a, ba aji biyar kuke ba? Ina sai an zo aji Shida ake zanawa?" A'isha ta ce. "Ai zaɓar mu aka yi mumu uku a ajinmu aka ce zamu zana." Inna ta ce. "Toh, dama ana yin haka?" Innar Ma'u ta ce. "Eh mana, ƴar gidan gaji ma ai a aji biyar ta gama firamare, ita ma zaɓar su aka yi, masu ƙoƙari suke zaɓa ai." Inna ta ce. "Tab'dijan, to ke da ba lafiya ba ina kika ga ta wani zana jarrabawa? kawai ki bari sai wata shekarar, kafin nan kin samu lafiya da yardar Allah, sai ku zana tare da Ma'u." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ni dai Inna dan Allah ki bari in zana, an ce ma akai kuɗin jarrabawar 600 ko Ma'u?" Ma'u ta ce. "Eh, kullum sai ya ce in faɗa miki ma." Inna ta ce. "To da wanne idon zaki yi rubutun jarrabawar? Ki haqura kawai ki bari sai wata shekarar, sai ku zana tare da Ma'u." Innar Ma'u ta ce. "Ai ita ma Ma'un wannan shekarar zata zana, Kawunta ya ce ta isa shiga Sakandiren, Ranar Litinin zan bata kuɗin insha Allahu ta kai, tunda sun ce duk mai so zai iya biyan kuɗi ya zana." Inna ta ce. "To ai A'isha ita matsalar ba ta gani, amma sai mu je makarantar ranar Litinin ɗin mu ji ya za'a yi." Jin abun da Inna ta ce sai A'isha ta fara murna, dama ta gaji da zaman gidan, dan ko zaure Inna ba ta barin ta, ta je, sai dai in zata fita ne Innar Ma'u ba ta nan take tafiya da ita duk inda zata, idan kuma innar Ma'u tana nan sai ta bar ta a gurin ta. Washegari A'isha ta takurawa Inna sai ta je gidan Malama karatu, ita ta gaji da zaman gida har da kukanta. Inna ta ce to ta saka hijabinta Ma'u ta kama hannunta su tafi, Allah ya kiyaye. Zuciyar A'isha cike da zumud'i suka tafi. Idan ba sani ka yi ba ko an faɗa maka baza ka ce A'isha makauniya ba ce, domin idanunta a buɗe suke kuma babu alamar mara sa lafiya ne, ga ta tsaf fess da ita, Inna tana tsaftace ta yanda ya kamata, dan Inna akwai tsafta. Suna zuwa gidan Malama yara suka fara tsokanar A'isha suna cewa. "Ta zama makauniya!! Ta zama makauniya!!" Dama abun da Inna take gudu kenan shi yasa ba ta barin A'isha ta fita ko nan da can ba tare da ita ba. Ita kuwa A'isha ba ta kula su ba, guri kawai ta nema ta yi zamanta, Ma'u ce ma take yi musu magana. Sai da Malama ta fito ta tsawatar musu sannan suka bari. Hak'uri ta dinga bawa A'isha cikin tausayawa, sosai yarinyar take ba ta tausayi tun a daa, ga kuma jarrabawar da Ubangiji ya ƙara ɗora mata. Ko kaɗan abun da yaran suka yi bai damu A'isha ba, duk da ta ji zuciyarta ta karye kamar za ta yi kuka, amma dai ta daure ba ta yin ba. Bayan an tashi daga karatun suna hanya suka gamu da su Hindu. Hindu da ƙawayenta suka sha gaban su A'isha. A'isha da ba gani take ba jin tsayuwar mutane a gabanta yasa ta ƙara riƙe hannun Ma'u sosai tare da faɗin. "Ma'u su waye?" Dan a tunaninta Ɗan'juma ne. Kafin Ma'u ta yi magana Hindu ta riga ta da faɗin. "Su Uwarki ne, Shegiya Mayyar yarinya kawai." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ba dai Uwata ba wall...
..." Ai ba ta ƙarasa ba Hindu ta wanke ta da mari." Waro ido Ma'u ta yi ta ce. "Kai Hindu akan me zaki......" Kafin ta ƙarasa wata ƙawar Hindu ta janye ta tare da wancakalar da ita a gefe, cikin masifa ta ce mata. "Kama gabanki ki tafi kar mu haɗa da ke, yau sai mun ci kazakazar shegiyar yarinyar nan, saboda a kanta Ɗan_Juma yake mana rashin mutunci da wulaqanci." A'isha dake hawaye hannunta riƙe da kuncinta ta fara laluben iska tana cewa. "Kar ki tafi ki barni Ma'u dan Allah." Hindu ta dungure mata kai ta ce. "Sai ta tafi ɗin dan kan Ubanki, yau sai dai ki dinga tafiya kina fad'uwa a hanya." A'isha ta saka kuka ta fara kiran sunan Ma'u, ita ma Ma'un hawaye ta fara tare da ƙoƙarin kamo A'isha, amma saboda rashin tausayi su Hindu suka kora Ma'u, suka kuma daki A'isha son ransu. A'isha Tana durkushe a gurin tana kuka mai ban tausayi bayan su Hindu sun tafi Ma'u ta dawo ta ɗaga ta, dan dama ƙin tafiya ta yi ta b'uya a bayan wani gida. Cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haquri A'isha, kuma wallahi ba su daki banza ba, sai na je na faɗawa Sarki abun da suka yi miki." A'isha dai ba ta ce komai ba har suka ƙarasa gida. Ma'u ce ta zayyanewa inna duk abun da ya faru, sosai ran Inna ya ɓaci, amma ba ta ce komai ba, rarrashin A'isha kawai ta yi. Innar Ma'u kuwa Ma'u tana cikin ba ta labari ko gamawa ba ta yi ba ta zari hijabinta tay gidan Sarki ta kai ƙara. Babu ɓata lokaci Sarki ya saka aka kira su Hindu da iyayensu mata, sannan aka kira Inna da A'isha da Ma'u. Gargad'i sosai Sarki ya yiwa su Hindu akan A'isha bayan Ma'u ta ƙara zayyana masa yanda aka yi, ya kuma saka suka ba ta hak'uri, ya ce duk ranar da ko kallon da bai gamsar da A'isha suka yi mata ba idan ya samu labari sai ya saka dogarai sun zane masa su, ya kuma cewa iyayensu su ƙara ja musu kunne akan babu ruwansu da Aisha, sannan ya bawa Inna da A'isha haquri, daga nan ya sallami kowa. Suna tafe a hanya Inna ta dubi Innar Ma'u ta ce. "Me yasa kika kawo ƙarar su, da kin bar su ai." Innar Ma'u ta ce. "Su daki yarinyar sannan kuma a k'yale su? Sun ci bulus kenan, gobe ma su samu lasisin ƙara dukan ta kenan, yanzu kuwa da aka yiwa tufkar hanci ba shikenan ba. Ai ni wallahi yanzun ma na so kin bari an daddaki ƴan banza, amma kika wani dinga bayar da hak'uri kina ke kin hak'ura kin yafe." Inna ta ce. "Gwara dai da ba'a dake sun ba, me cece ita duniyar? Ai komai ɗan hak'uri ne." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne, Allah yasa mu dace." Saboda kuka da dukan da A'isha ta ci yau da ciwon kai ta kwanta.
Ranar Monday da safe Inna ta shirya A'isha cikin uniform suka tafi Makarantar su. Ta yi Sa'a suna shiga shi ma Malam Buba ya shigo, ganin Inna da A'isha ya gane mahaifiyarta ce, cikin girmamawa ya ce. "Sannunku da zuwa, Ina kwana Baaba?" Inna ta ce. "Lafiya ƙalau, ya ƙoƙari?" Malam Buba ya ce. "Alhamdulillah." Sannan ya dubi A'isha ya ce. "A'isha ba magana?" Murmurshi ta yi ta ce. "Ina kwana." Ya ce. "Lafiya ƙalau, ya jiki_jiki kuma? Asma'u ta ce kin sha jinya." A'isha ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "To Allah ya ƙara afuwa." Suka amsa da Amin, sannan ya ce da Inna su ƙarasa office ɗinsu bayan ta yi masa bayanin abun da yake tafe da ita. Bayan sun zauna Inna ta ce masa. "Dama akan maganar Jarrabawar da A'isha ta ce an zaɓe ta zata zana na zo, na ce ko za'a bari sai wata shekarar duba da lalurar da ta same ta, kafin nan insha Allahu an yi mata magani ta warke." Malam Buba ya ce. "Wai har yanzu ba ta gani? Na ɗauka ai idon ya buɗe." Inna ta ce. "Tukunna dai, muna nan muna ta addu'a." Malam Buba ya ce. "Subhanallahi, Sannu A'isha, Allah ya yaye miki." Inna ta ce. "Amin." Malam Buba ya ce. "To Baaba tunda ana saka rai idon zai buɗe ta zana jarrabawar a hakan kawai, zan yi mata registration da komai da sunanta da hotonta, akwai k'anwata Mairo sai ta zana mata, tunda jarrabawar ta rana ɗaya ce." Inna ta ce. "Kana ganin hakan zai yiyu?" Malam Buba ya ce. "Insha Allahu, ai nine exam officer, Ni nake yin komai na jarrabawar, shugaban makarantar ma bani da matsala da shi, ina yi masa magana zai yarda." Inna ta ce. "Toh shikenan Allah ya ba da sa'a, na gode sosai ɗana, Allah ya saka da Alkhairi." Malam Buba ya yi murmushi ya ce. "Babu komai Baaba, Allah ya ba ta lafiya ita kuma." Inna ta ce. "Amin." Malam Buba yana kallon A'isha ya ce. "Indodo kin daina magana ne? Na ji kin yi tsit kamar ba ke ce mai cika mana aji da surutu ba." Murmurshi A'isha ta yi, tare da saurin rufe fuskarta da hannunta. Inna ta ce. "Ko godiya ba ta iya ba." Cikin sanyin murya ta ce. "Mun gode Malam." Murmurshi kawai Malam Buba ya yi, haka kawai A'isha take burge shi, saboda nutsuwarta da hankalinta, ba shiru_shiru ba ce ita dan ba ta barin ta kwana, indai aka faɗa mata sai ta rama, amma ba ta da tsokana, in dai ka ji an yi faɗa da ita to tsokanarta aka yi. Yana jin tausayinta kuma a cikin ransa saboda tsangwamar da take fuskanta a gurin abokan karatunta. Abun da yake ƙara burge shi da ita tana da ƙoƙari dai_dai misali, indai an yi musu karatu tana fuskanta. Anan Inna ta bar ta bayan ta biya kuɗin jarrabawar da na passport ɗin da za'a yi mata. Yau A'isha murna fal ciki ta zo makaranta, duk da ba ta ganin komai amma dai ta ji daɗi, kuma babu wanda ya tsokane ta, saboda Malam Buba ne ya kai ta har aji ya kuma jawa yaran kunne akan kar wanda ya tsokane ta, duk wanda ya tsokane ta sai ya zane shi........
Rayuwa ta cigaba da tafiyar wa da su A'isha cikin godiyar Ubangiji, an zana common entrance ɗin har ma ta fito, A'isha da Ma'u duk sun ci makarantar sakandare dake cikin garin. Tare Kawunsu Ma'u ya yi musu komai kama daga kan uniform da su takalmi da jakar makaranta da littattafai. Har lokacin Inna ba ta gama tara kuɗin kai A'isha asibitin Kano ba saboda sha'anin rayuwa. Zuwa lokacin kowa na cikin garin ya san A'isha ta makance, labari ya gama baza ko'ina, Iya da Matan gidansu kullum cikin yiwa Inna gorin ƴarta ta makance amma ta kasa kai ta asibiti a yi mata magani saboda baƙin talauci, Inna dai ba ta kula su dan ba ta su take ba. A'isha kuwa zuwa yanzu har ta saba da rashin ganin. Da farko da aka kai su A'isha makaranta ƙin karɓar ta aka yi, Malaman suka ce ai kamata ya yi a kai ta makarantar makafi ba wai nan ba, Malam Buba ne ya yi ruwa ya yi tsaki daƙyar aka samu aka ɗauki A'isha, shi ma dan ya yi musu dabara ne da cewa, an kai ta asibiti sun ɗora ta akan magani tana kan shan maganin ne, sai ta gama shan maganin za'a yi mata aiki wanda idon zai buɗe. Ma'u ce take yi mata rubutu idan ta gama nata, ita dai kawai in ta je makarantar zama ne nata da saurare. Sai kuma wata sabuwar matsala da A'isha take fuskanta a garin, ba ta isa ta fito waje ba sai yara sun yi mata ihun Makauniya sun cinye idon wasu ya dawo kansu.
Yau Laraba, da daddare Inna ta ɗauko kuɗin da take tarawa na kai A'isha asibiti ta irga, ta ga kuɗin ya kai dubu shida da ƴan kai, zai isa su yi kuɗin Mota da kuma ɗan abun da take tunanin za'a buƙata a asibitin, dan haka ta yanke shawarar gobe za su je asibitin Kanon da yardar Allah......✍️