KOMAI NISAN DARE

8.

by @zeeykumurya

KOMAI NISAN DARE 


Zeey Kumurya 


Page 8.



Washegari tun sassafe suka shirya, A'isha tana zaune tana karyawa, Inna kuma tana duban kuɗin da za su yi amfani da shi a inda ta ajiye jiya da daddare amma kuɗi ya ce ɗauke ni inda kika ajiye. A cikin wata jaka dama ta ajiye su, ta duba jakar ya fi sau goma ta zazzage ta amma ba ta ga kuɗin ba. Wasu guraren ta shiga dubawa ko ta manta ta canza musu guri ne, sai da ta birkice duka ɗakin amma ba ta gan su ba. A'isha da take sauraren b'uruntun da Inna take ta yi ta ce. "Inna wai me kike dubawa tun ɗazu?" Cikin damuwa Inna ta ce. "Kuɗin da zan kai ki asibitin A'isha, ban gan su ba." A'isha ta ce. "Ko dai kin manta inda kika ajiye ne?" Inna ta ce. "Amma ko  mantawar na yi yanda na birkice ɗakin nan ya ci ace na gan su, sai dai in ba ya cikin ɗakin." A'isha ta ce. "Allah yasa dai ki gan su Inna." Inna ta ce. "Amin." Dai-dai nan innar Ma'u ta shigo zagayen nasu, bayan ta yi sallama sun amsa mata ta ɗaga labulen ɗakin tana faɗin. "Har yanzu ba ku tafi ba? Idan takwas ta wuce fa ba za ku samu ganin likita ba." Inna dake maimaita kalmar innalillahi a cikin zuciyarta ta dubi Innar Ma'u cikin sanyin murya ta ce. "Ladidi kuɗaɗen na nema na rasa." Innar Ma'u ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kamar ya kin neme su kin rasa? A ina kika ajiye?" Inna ta ɗauko jakar da ta ajiye kuɗin ta ce. "A cikin jakar nan na saka, kuma ko kafin na yi bacci na duba na ga suna ciki, Jakar kuma a gabana ta kwana a k'ark'ashin shimfid'ata." Innar Ma'u ta ce. "Bari dai na shigo mu ƙara duba ɗakin sosai, ko wani gurin kika cilla su kika manta." Inna ba ta ce komai ba har Innar Ma'u ta ƙaraso cikin ɗakin ta fara dubawa. A'isha dake ta murna yau za'a kai ta asibiti a yi mata magani sai murnar ta koma ciki, kana kallon fuskarta ka san tana cikin damuwa. Sai da innar Ma'u ta ƙara duba ko'ina a cikin ɗakin amma babu kuɗin babu alamar su. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, baiwar Allah har gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta na rud'ani. Duban Innar Ma'u ta yi wadda ita ma take cike da tararrabin abun ta ce. "Kuɗin nan fa ba ya cikin ɗakin nan." Innar Ma'u ta ce. "An shigo an ɗauke su kenan?" Inna ta ce. "Amma da na yi matuƙar mamaki, saboda babu yanda za'a yi a ɗaga shimfid'ar da nake kwance har a zare jakar nan ban ji na farka ba." Innar Ma'u ta ce. "Hmmm, Asabe bar mutum kawai, maso abun ka ya fi ka dabara, amma ko tantanma bana yi in dai shigowa aka yi aka ɗauki kuɗin nan to da sandar nan da suke amfani da ita suka zo, wadda idan aka ajiye ko idonka biyu baza ka iya motsawa ba har sai sun gama ɗaukar abun da za su ɗauka sun ɗauke ta." Inna ta sauke numfashi tare da zama dab'as a ƙasa cikin raunin murya ta ce. "Allah kai ka san me kake nufi da wannan al'amari, kuma kai ka bani wannan kuɗin Allah ka ƙara bani wasu." Cikin tausayawa Innar Ma'u ta ce. "Amin ya Allah, insha Allahu Asabe kuɗin ki sai ya fito, Allah ya dawo miki da su, ya toni asirin duk wanda ya ɗauka." Kamar A'isha zata yi kuka ta ce. "Inna shikenan yanzu baza mu je asibitin ba an sace kuɗin?" Inna ta ce. "Ki yi hak'uri A'isha, haka Allah ya Ƙaddaro mana, babu yanda zamu yi." Tsugunnawa Innar Ma'u ta yi ta dafa kafadun A'isha cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Insha Allahu A'isha Ubangiji zai kawo hanyar da za'a kai ki asibiti, ki kwantar da hankalinki insha Allahu zaki warke." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. miƙewa Innar Ma'u ta yi ta fice bayan ta ce musu tana zuwa. Hawaye ne yake ƙoƙarin zubowa daga idon Inna amma ta ƙi ba su damar hakan, wani irin zafi take ji a cikin zuciyarta, kuɗin da ta hana kanta ci, ta hana kanta sha, da goma da ishirin ta tara su kusan watanni goma amma wani mara imanin ya raba ta da su a dare ɗaya, ita yanzu ina ta ga hanyar da zata kuma samun wasu kuɗaɗen? Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yanzu shikenan Inna ni ban zan kuma gani ba tunda an sace kuɗin da zaki kai ni asibitin? Allah ya isanmu wallahi, ba mu yafe ba, Allah ya kumbura cikin duk wanda ya ɗaukar mana kuɗinmu."  Inna ta ce. "In Allah ya yarda A'isha zaki warke." A'isha ta ce. "To Inna wa zai ƙara baki wani kuɗin ki kai Ni?" Inna ta ce. "Allah, shi ya bamu wannan ɗin kuma shi zai ƙara bamu wasu."





Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa da rashin walwala A'isha da Inna suka yi su, dan Inna ko abinci kasa ci ta yi. Abun da yake bata mamaki game da ɗaukar kuɗin da aka yi, ita dai a iya saninta babu wanda ya san da batun kuɗin kaf cikin gidan balle kuma a waje, daga ita sai Innar Ma'u suka sani, kuma ta san Innar Ma'u baza ta yiwa kowa zancen kuɗin ba, tunda ba wani shiga sabgar matan gidan take yi sosai ba. Amma babu komai ta bar wa Allah, shi kaɗai ya san me yake nufi da hakan ta faru, fatanta Allah ya musanya musu da mafi Alkhairi. Innar Ma'u ta yi iyarka ƙoƙarinta wajen ganin ta samu kuɗi ta bawa Inna ta je asibiti a cikin satin amma hakan bai samu ba saboda halin rayuwa. Haka A'isha ta cigaba da rayuwa cikin makanta, ga tsangwama da tsanar da suke fuskanta daga mutanen garin, babu abun da ya ragu sai ma ƙaruwa da ya yi.






Yau ta kama ranar Talata, da safe k'anin Innar Ma'u dake Kano ya zo. Bayan sun gama gaisawa da ita sun sha hirar yaushe gamo ya gyara zama ya ce mata. "Yaya ni fa abun da ya kawo ni na zo ɗaukar ku ne ku koma can Kano da zama tunda Allah ya nufa na kammala ginina." Cikin mamaki innar Ma'u ta ce. "Mu koma can kamar ya? Ina kake nufi? Ba dai Kano ba?" Ya ce. "Can mana gidana, sai ku fara shiri jibi za mu wuce tare." Innar Ma'u ta ce. "Haba Muntari, ya za'a yi mu koma gidanka mu ɗora maka nauyi bayan wanda yake kanka? Kuma ita Rakiyan ai kamar zamu takura ta idan muka koma gidanka gaba-d'aya da zama." Muntari ya ce. "Babu wani nauyi Yaya, ni fa na ce ku koma kuma na san zan iya ne, Rukayya kuwa ba ki da matsala da ita, da na faɗa mata ma murna tay ta yi." Shiru kawai Innar Ma'u ta yi ba ta ce komai ba, amma ko kaɗan ba ta so komawarta Kano ta bar garin da aka haife ta a ciki ba, gashi kuma ba ta son barin su Inna, amma saboda kar Muntari ya ga ta gwale shi sai ta amince, ta dinga yi masa godiya tare da tarin addu'oi. Jiki a sanyaye Innar Ma'u ta shiga ta sanar da inna batun tafiyarsu. Inna ta ce. "Jibi_jibin nan kuma? Ikon Allah" Innar Ma'u ta ce. "Wallahi Nima na ga abun ya yi kusa sosai, yaushe na gama zaga ƴan'uwa da abokan arzik'i na yi musu sallama? ga gari na damuna wataran ma sai ruwa ya hana ka fita. Amma ya zan yi tunda Muntari ya dage." Inna ta yi murmushi ta ce. "Ai da gaskiyarsa, ya san in ya tafi baza ki koma da wuri ba, Allah ya kai mu Jibin ya sanya Alkhairi." Innar Ma'u ta ce. "Amin, amma ko kaɗan ban so barinmu garin nan ba ko dan ku Asabe." Inna ta ce. "To ya za'a yi? Haka Allah ya yi, kar ki saka komai a ranki na damuwa saboda ni, Ubangiji yana tare da mu ai." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne kam." Inna ta ce. "Zan shigo anjima mu yi wata magana idan na gama abun da nake yi" innar Ma'u ta ce. "To sai kin zo."......... Kwana biyun nan zuciyoyinsu Inna babu daɗi saboda tashin da su Ma'u za su yi, ita kanta innar Ma'u ta shiga cikin damuwa, ga tunanin halin da za ta bar su Inna ga kuma kewarsu da za ta yi. A'isha ma sosai ta damu saboda rabuwa da Ma'unta, ita kaɗai ce ƙawarta duk cikin garin, idan ta tafi shikenan ba ta da kowa. Ranar Alhamis da safe wanda ya kama ranar tafiyar su Ma'u, Inna tana wankin uniform ɗin A'isha Hansai ta shigo zagayen nasu babu ko sallama, ta tsaya akan Inna cikin izgilanci ta ce. "Yau koma wasu sai kwanan baƙin ciki, wadda aka yi nasarar lashewa kurwa zata bar gari, sai mu ga kuma da wa za'a dinga yin mu'amala yanzu." Inna ta yi murmushi ta ɗago ta kalle ta ba ta ce komai ba. Hansai ta cigaba da yadawa Inna habaici cikin shewa, yau duk matan gidan zuciyarsu fari k'al suke jin ta, a ganinsu tunda innar Ma'u za ta bar gidan watan tagayyarar su Inna ya kama. Har ƙofar gida aka kawo Motar da su Ma'u za su tafi a cikinta, bayan an gama saka kayansu a ciki suna bakin Motar a tsaye matan gida duk sun fito yi musu rakiya. Inna tana tsaye hannunta riƙe da na A'isha wadda ke ta gunjin kuka ita da Ma'u, ita kanta innar dauriya kawai take yi amma yanda take jin zuciyarta kamar ta fashe da kukan, ganin abun take tamkar a mafarki, kamar za'a ce wasa ne su Innar Ma'un sun fasa tafiya. Innar Ma'u ta rungume A'isha tana hawaye ta ce. "Ki yi shiru A'isha ki bar kukan nan haka, kin ga idanunki dama ba lafiya ce da shi ba, ai zamu na zuwa muna ganin ku, kuma za ku na kawo mana ziyara, na bawa Innarki Lambar Muntari, idan kun tashi zuwa sai ta kira shi ya ba ta adreshin inda muke, ki yi hak'uri kin ji." A'isha dai tamkar ƙara zuga ta innar Ma'u ta yi, maimakon ta yi shirun sai ma ƙara volume ɗin kukan ta yi. Janye ta Inna ta yi, ta dubi Innar Ma'u tana murmurshin da ya fi kuka ciwo ta ce. "Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya, Na gode sosai da irin taimakon da kika ba ni a zamantakewarmu, Allah ya saka da miki da mafaficin Alkhairin sa, tabbas ke wani bango ce a cikin rayuwarmu." Ba ta jira cewar Innar Ma'un ba saboda wani kuka dake neman kufce mata ta shafa kan Ma'u ta ce. "To Asma'u, Allah ya tsare sai mun zo ko kuma ku kun zo." Ma'u ta riƙe Inna ta ce. "Ni na fasa tafiyar anan zan zauna tare da A'ishata, ni ba zan iya tafiya in bar ta ba." Inna ta ce. "Haba Asma'u, kar ki ce haka kin ji yarinyar kirki na, ki yi hak'uri." Ma'u ta saki Inna ta rungume A'isha suka fashe da kuka mai ban tausayi, hakan ya karya zuciyar innar Ma'u ta fara hawaye sosai ita ma, abun tausayi. Sabo da shak'uwa ba k'arya ba ne, tunda su A'isha suka taso tare suke yin komai da Ma'u, yau rana tsaka kuma Ubangiji ya raba su, abun da babu wanda ya yi tunanin faruwarsa nan kusa. Sosai suka bawa wasu daga cikin mutanen gari tausayi, shi kanshi Muntari dake tsaye yana kallon su sai da ya ji kamar ya fasa tafiya da su Ma'un, Malam ƙarami kuwa Mutumin Inna shi ma sai kuka yake yi. Dauriyar Inna ta ƙare, hawaye masu ɗumi ne suka shiga kwaranyowa daga cikin idonta, cikin matuƙar sanyin jiki ta d'agawa su Inna hannu sannan ta ɗaga ƙafafuwanta daƙyar ta yi cikin gida da sauri. Matan gidan suka bi ta da kallo suna sakin murmurshin mugunta. Daƙyar aka iya raba Ma'u da A'isha, ƴar Innar Ma'u ta shigar da A'isha gida Ma'u kuma aka tusa ta cikin Mota. Kuka sosai A'isha ta yi a yau, ko makaranta ba ta je ba, sai bayan Azhar bayan Inna ta saka ta, ta yi Sallah bacci ya ɗauke ta. Ita kanta Inna ta ci kukanta ta gode Allah. Sai yamma A'isha ta farka daga baccin, ta tashi da ciwon kai saboda kukan da ta sha. Tana farkawa abun da ta fara cewa shine. "Shikenan su Ma'u sun tafi sun bar mu, yanzu ba mu da kowa, ba ni da mai kama hannuna mu je makaranta, ba ni da mai yi mun rubutu." Inna ta ce. "Mu na da Allah A'isha, kuma shi zai yi mana maganin komai ya ba mu yanda za mu yi." 





Sosai kewar su Ma'u take damun su Inna, gashi ita ba waya ba bare ta kira lambar Muntari su yi magana da su ko sa ɗan ji daɗi. Duniyar duk sai ta yi musu wani iri babu daɗi. Gaba-d'aya A'isha ta daina walwala, komai cikin sanyin jiki take yin sa, ta rage yawan magana, kamar ba ita ce a daa idan ta fara yiwa Inna surutu sai ta ce ta rufe mata baki ba. Satin da su Ma'u suka tafi gaba-d'aya ƙin zuwa makaranta ta yi, Inna ba ta takura mata ba akan hakan ta bar ta, ta huta. Ranar Lahadi da daddare suna cin tuwon masarar da Inna ta yi musu Inna ta cewa A'isha. "A'isha ki daure gobe ki koma makaranta, dan babu Ma'u kuma sai ki daina karatu? Ko ba kya son ki zama likitar ne yanzu?" A'isha ta ɓata fuska ta ce. "To Inna da wa za mu dinga tafiya tare?" Inna ta ce. "Ni zan dinga kai ki in na ɗauko ki." A'isha ta ce. "To wa zai dinga mun rubutu? Idan an fita Sallah wa zai na kama hannuna mu je mu yi?" Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Mu je makarantar dai sai mu ji yanda za'a yi." Washegari ba dan A'isha ta so ba ta shirya suka tafi Makarantar tare da Inna. Allah ya haɗa su da wata Malama mai kirki mai suna Malama Hajara, Inna ta yi mata bayanin abun da yake tafe da ita, ta kwantarwa da Inna hankali ta ce, insha Allahu zata na kula da A'isha yanda ya kamata, ko da ranar da ba za ta zo makarantar ba zata yi waya ta faɗa a kula da A'ishan. Inna ta yi mata godiya sosai sannan ta dawo gida.







Cikin satin nan rayuwa ta fara yiwa su Inna tsanani, saboda yanzu ba ta sana'ar komai, sai aikin abincin sadakar nan, 500 kuwa a sati mai zata yiwa rai biyu, ga abubuwan da yawa, bayan abinci ga sabulun wanka da na wanki, ga man shafawa, ga omon wanke_wanke, ga siyan ruwan amfanin gida, ban da sauran abubuwan buƙata na yau da kullum. Jarin ayar da ɗan guntun kuɗin dake hannunta duk sun ƙare. Sai suka koma irin rayuwar daa, sai su farka ba su da ko ƙwayar hatsin da za su ci a cikinsu. Yau Alhamis, wanda ya kama sati biyu cif da tafiyar su Ma'u. Da rana A'isha ta gama shirin tafiya makaranta kasancewar ta yamma suke yi tunda su ƴan junior section ne. Jakar makarantarta ta laluba ta ɗauka, cikin sanyin murya ta ce. "Inna na gama mu tafi." Inna ta sauke tagumin da ta rafka ta ce. "Haka zaki je makarantar ba ki ci komai ba A'isha, da hak'ura kika yi na fita na dawo ko Allah zai sa in dace in samo miki wani abun ki ci, sai ki tafin." A'isha ta ce. "Toh Inna a ina zaki samu?" Inna ta ce. "Sabon Gari zan je gurin Hajiya mai k'uli_k'uli, idan da aiki in yi mata ta biya Ni, na san ma ba'a rasa aikin ba tunda gobe ne cin kasuwa za'a zo a sissiya." A'isha ta ce. "To mu je makarantar, idan kin samu sai ki kai mun can ɗin." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Kin kawo shawara kuma, tashi mu je kar ki makara, daga can sai na wuce." Miƙewa A'isha ta yi, Inna ta kama hannunta suka fice.






Tun bayan da Inna ta tafi  ba jimawa A'isha take saka ran dawowarta, domin wata irin yunwa take ji ba kaɗan ba, ɗan kokon Naira goman da ta sha da safe shi kaɗai ne a cikinta. Har aka fita Sallar la'asar Inna ba ta zo ba, gashi yau Malama Hajara ba ta zo ba, sai wata yarinya ta roƙa ta fitar da ita waje ta yi ta Sallah ta dawo da ita. Bayan an dawo aji tana ta jin yara na ta ciye_ciye abunsu, suka bar ta da jin ƙamshi. Har aka tashi Inna ba ta zo ba, zuwa lokacin yunwa ta fara galabaitar da A'isha, dauriyar ta ƙare ta fara hawaye. Gashi yara duk sun tafi gida sai ita kaɗai a bakin aji a tsugunne. Wani Malami ne ya hango ta ya taho inda take, da mamaki yake duban ta ya ce. "Ke lafiya kike zaune anan ke ɗaya?" A'isha ta ce. "Innata nake jira ta zo ta ɗauke ni." Malamin ya ce. "Ayya ke ce mai ciwon idon nan ko?" Gyaɗa masa kai A'isha ta yi. Ya ce. "To yanzu zama zaki yi ki ta jiran ta kuma? Yamma ta yi ga garin hadari ya haɗo sosai, mu ma duk tafiya za mu yi, amma abun da za'a yi bari na saka a raka ki gida, ina ne gidan naku?" A'isha ta ce. "A Ƙofar fada ne." Malamin ya ce. "To mu je a raka ki, wannan hadarin ai ba zai yiyu ki zauna ke kaɗai anan ba, gashi ba gani kike ba." Sai da suka fita daga cikin makarantar yana riƙe da hannunta sannan ya samu wani yaro ya ce ya raka ta gidan Sarki, daga nan sai ta samu wani ya kai ta gida, tunda shi yaron bai san gidansu ba. Kafin su ƙarasa, garin ya ƙara duhu, an fara iska mai ƙarfi haɗe da yayyafi. Yaran sai jan A'isha yake, duk ta ƙara galabaita, tafiya kawai take yi amma jin ta take kamar zata faɗi. Yaron yana kai ta ƙofar gidan Sarki ya juya ya yi tafiyarsa, saboda zuwa lokacin ruwa ya fara ƙarfi. Ɗan_juma suna zaune a soro akan benci shi da Hamza da wani abokinsa suna karta, kamar a mafarki ya hango A'isha tsaye ta rakub'e a jikin bango, ƙura mata ido ya yi yana tuna when last da ya gan ta, ya jima bai gan ta ba gaskiya. Sai ya ga ta ƙara girma ta fara zama ƴar budurwa. A'isha tana shekaru goma sha uku a yanzu, amma saboda tana da garin jiki da ɗan tsayi idan ka gan ta zaka yi tunanin shekarun ta sun fi haka. Ruwan da ya fara dukanta ya saka uniform ɗin jikinta duk ya mammanne mata a jiki. Ɗan_juma ya ƙurawa ƙirjinta da ya ɗan fara tasawa da irgen dangi ido, nan fa shed'an ya fara buga masa ganga akan mummunan k'udirinsa akan A'isha. Wani murmushi ya yi tare da lasar leb'ensa ya ce da su Hamza. "Tsuntsu daga sama gashashshe." Bai jira cewar su ba ya miƙe ya fita ya janyo A'isha cikin zauren ta ƙarfin tsiya, bayan ya duba gabas da yamma kudu da arewa ya ga babu kowa a wajen. A'isha ta ƙanƙame Jakarta a jikinta cikin rudu ta ce. "Waye wannan? Me na yi maka? Ni ka cika ni? Mene ne haka?" Ɗan_juma ya cika ta yana murmurshin mugunta, abokansa da sai yanzu suka gane mai yake nufi suna taya shi murmurshin. Laluben Hanya A'isha ta fara yi cikin hawaye, jikinta gaba-d'aya rawa yake yi saboda tsabar tsoratar da ta yi da janyon tan da Ɗan_juma ya yi, gashi ba ta san ko wanene ba. Garin neman hanyar fita ta ƙume goshinta da garu, kuka ta saka tare da kiran sunan Inna. Cikin rashin Imani ɗan_juma ya fizgo ta tare da fizge jakar hannunta ya cillar a ƙasa, wani uban ihu A'isha ta ƙwala ta fara tittirjewa, amma saboda ruwan da ake yi mai ƙarfi ne yasa babu wanda zai jiyo ihun nata balle ya kawo mata ɗauki, cak Ɗan'juma ya ɗaga ta ya shige da ita wani ɗaki dake cikin zauren ya kullo ƙofa. Ihu sosai A'isha take yi tare da ƙoƙarin k'wace kanta daga hannun Ɗan'juma amma ta kasa. Mara masa baya su Hamza suka yi zuwa cikin ɗakin, a ƙasa Ɗan'juma ya jefar da ita sannan ya saka ƙafa ya take ƙafafuwanta da take haurin sa da su, da ido ya yiwa su Hamza alamar su danne masa A'isha. Hamza ya ƙaraso ya saka hannunsa ya toshe bakin A'isha da ƙarfi saboda da ihun kukan da take, ɗayan kuma ya daddanne mata hannayenta da iyakacin ƙarfinsa. Cikin tsantsar zalunci Ɗan'juma ya cire Hijabin jikinta ya cillar, yana wani irin murmushin zallar iskanci da duniyanci ya fara cire kayan jikinsa...........✍️