The Unwanted Daughter

Page 15: A Cry No One Heard

by @hauwajaywrites

Zahra ce ke waya da iyayenta a Kaduna. Hira suke yi cikin annashuwa har babanta ya ce zai shiga ciki ya ɗan huta, ya bar su ita da mahaifiyarta suna ci gaba da tattaunawa.


Can Zahra ta ce “Yauwa dear mother, ina son na turo muku yaran nan su yi holiday a can Kaduna, su ƙarasa hutunsu tare da ku”


Mahaifiyarta ta ɗan yi shiru kafin ta ce “Da Dua ma kike nufi?”


Zahra ta amsa “Yeah Mama, it’s a plan kin san Dua ta fi Amrah kyau Sultan kuma a made for Amrah, amma kullum ina ganin idanunsa na kan Dua, kamar yana nuna interest a kanta, jiya haka na Kama su a garden”


Mahaifiyarta ta yi ɗan dariya mai cike da mugunta “Ke dai ki kwantar da hankalinki, mun gama da ubanta balle ita, yaushe za su zo?”


“Next week, In shaa Allah”, Mama ta ce “Alright then, sai sun zo” suka yi sallama daga haka


Tun daga lokacin Zahra take cikin farin ciki, tana ganin komai zai tafi yadda take so


A gefe guda kuma…


Daddy da Alhaji Tukur sun samu gagarumar nasara a meeting ɗinsu ta international trade. Sun kulla yarjejeniya mai amfani, wacce ta kawo musu riba mai yawa Murna sosai suke yi


Daddy ya ce “Alhamdulillah! Wannan abin farin ciki ne”


Alhaji Tukur ya amsa “Hakane, ya kamata mu yi celebration yadda familyn zasu ji dadi”


Da suka dawo gida suka sanar da iyalansu labarin, nan take aka yanke shawarar shirya dinner party domin godiya ga Allah da kuma murnar nasarar


Aka fara gayyatar ’yan uwa da abokan arziki domin liyafar da za a yi washegari da daddare


Lokacin lunch… kowa yana dining room yana cin abinci sai dai ba a ga Dua ba


Abidah ta lura da hakan. Wannan ba shi ne karo na farko ba da ta lura yarinyar tana yawan rasa zama tare da iyalanta lokacin cin abinci


Ta ɗaga kai ta tambaya

“Where is Dua? Ban ga tana nan ba”


Zahra ta amsa cikin rashin damuwa “She’s full, ta riga ta ci ai”


Abidah ba ta ce komai ba, ta ja kujera ta miƙe a hankali ta nufi sama, kai tsaye ɗakin Dua ta shiga


Tun daga bakin ƙofa ta ji sautin shessheƙar kuka, ta tura ƙofar a hankali


Dua na jin an buɗe ƙofar ta yi saurin goge hawayenta ta juya baya, Abidah ta ƙarasa kusa da ita, ta riƙo hannunta cikin tausayawa “What is it, Dua?”


Ta ɗan shafa kanta “Tell me… I’m your mother too”


Dua ta girgiza kai “Nothing, Ummi”


Abidah ta ce cikin sanyin murya

“Why are you hiding it from me? Open up. Don’t be scared, I promise, duk abin da za ki faɗa zai tsaya tsakanina da ke”


Da jin waɗannan kalamai, Dua ta tuna da marigayiya mahaifiyarta, Ita ma haka take rungumarta idan tana kuka


Nan take ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Abidah ta rungume ta tana lallashinta har ta ɗan natsu.


Daga bisani ta ce,m “If you’re not happy here… sai na tafi da ke tunda ni Ina son ki”


Dua ta girgiza kai cikin sauri “No, Ummi…” Ta haɗiye kukan da ke maƙalewa a maƙoshi “I just miss my mummy… Ina da abubuwa da yawa da nake son na gaya mata… but she’s no more”


Zuciyar Abidah ta cika da tausayin yarinyar a ranta tana ayyana 

“Ya Allah… wane irin rayuwa ce wannan yarinyar take ciki?”


A ɗaya ɓangaren kuma

Amrah na fitowa daga wanka kenan sai wayarta ta fara ringing. Da ta duba, sai ta ga sunan Jackson, ta ɗaga cikin murmushi “Hello, Jackson”


Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce

“I’ve been trying your number, but it wasn’t reachable, Hope everything is okay?”


Amrah ta yi dariya “I’m perfectly fine. Kada ka ɗauka wai na bugu ne. No… it’s just my first time sipping alcohol, shi ya sa na ɗan ji wani iri but I’m okay now”


Jackson ya sake sauke numfashi

“Thank God. I was really worried”


Suka ɗan yi hira na wasu mintuna, kafin Amrah ta gayyace shi zuwa dinner party da Daddy zai shirya washegari


Daga nan ta haɗa su a conference call ita, Firdausi da Rumaisa, ta ba su labarin abin da ya sa ta bar birthday party da wuri,m


Su ma suka yi mata alkawarin za su halarci dinner party ɗin


Da yammacin wannan ranan  Daddy ya kira Dua da Amrah zuwa parlour.


Da suka zauna, ya ce

“After this dinner party, zaku tafi Kaduna domin holiday”


Da jin haka, zuciyar Dua ta tsinke, nan take ta tuna da dangin Zahra…


Ta tuna yadda suke nuna mata ƙyama, da yadda suka saba zaginta tare da marigayiya mahaifiyarta


Ta ɗan ɗaga kanta cikin ladabi

“Daddy… I don’t want to go”


Daddy ya ɗago ya kalle ta “Why?”


Ta haɗiye yawu kafin ta ce

“Besides… ba ma mu fara holiday a Islamiyyah ba”


Fuskar Daddy ta sauya

“Are you arguing with me?”


“No, Daddy” Ta girgiza kai da sauri “I’m not arguing… I just…”


Kafin ta ƙarasa maganar… Paa! Mari ya sauka a kumatunta


Ta dafe wajen cikin firgici Daddy ya nuna mata ƙofa “Get out of my sight shegiya!”


Hawaye suka cika idanunta, ba tare da ta sake cewa komai ba, ta juya ta fita da gudu


Abidah tana zaune a parlour tana kallon televisio, Jin ƙarar marin ya sa ta ɗago kai


Sai ta ga Dua ta fito a dakin ta ruga sama tana kuka, ta bi ta da kallo har ta ɓace.


Tun daga wannan lokacin hankalinta ya kasa kwanciya, fiye da mintuna goma sha biyar tana zaune, amma zuciyarta na ci gaba da gaya mata cewa akwai wani abu da ba daidai ba


A ƙarshe ta miƙe “I need to check on her”


A ɗayan ɓangaren kuma… Dua ta faɗa kan gadonta tana kuka kamar zuciyarta za ta fito


Ta rasa me ya sa duk lokacin da ta yi ƙoƙarin faɗar abin da ke zuciyarta, sai ta ƙare da hukunci can kuma ta tuna da wani movie da ta taɓa kallo


A cikin movie ɗin, wata yarinya da ta gaji da wahala ta kashe kanta ta hanyar rataya ta share hawayenta


A hankali ta furta “Maybe… this is the only way”


Ta fita zuwa store ta ɗauko wata doguwar igiya, da ta dawo ɗakin, ta haɗa stool biyu, ta jawo su ƙarƙashin ceiling fan


A hankali ta ɗaure igiyar, hawaye na ci gaba da zuba a idanunta “If I die…” Ta yi murmushi mai cike da ciwo “…I’ll see my mummy again”


Ta saka igiyar a wuyanta, wanda ta daure da fan din, lokacin da take shirin ture stool ɗin…


Sai ƙofar ɗakin aka buɗe, Amrah ce, ta tsaya tana kallonta na wasu mins sai ta ce cikin raini,


“Finally… I’ll be the only daughter” Ta juya ta fita kamar ba ta ga wani abu mai hatsari ba


Dua ta rufe idanuwanta ta ƙara riƙe igiyar…


A daidai lokacin… Abidah tana hawa stairs ne sai ta yi karo da Amrah tana saukowa


Amrah ta yi murmushi ta ce

“Ummi, sannu”


Sai dai Abidah ko kallonta sosai ba ta yi ba. Wani irin rashin kwanciyar hankali ne ya mamaye zuciyarta kai tsaye ta nufi ɗakin.


Da ta tura ƙofar… abin da idanunta suka gani ya sa numfashinta kusan ɗaukewa “Dua!!” Ta yi wani irin ƙara mai firgitarwa


A lokacin ne Dua ta ture stool ɗin da ƙafarta, nan take igiyar ta matse mata wuya


Da gudu Abidah ta ƙarasa, ta rungume ƙafafunta domin rage nauyin da igiyar ke yi a wuyanta “Ya Allah! Dua! No… no!”


Ta yi ta ƙoƙarin ɗagata sama, tana kuka tana neman taimako, Ihun Abidah ya cika gidan


Kusan duk mutanen gidan suka ruga zuwa sama, Aryan ne ya fara isa


Da ya ga Dua rataye, jinin jikinsa ya daskare nan take “DUA!”


Ya yi saurin hawa kan stool ɗin, ya ɗago ta sama yayin da Sultan ya shiga da sauri ya riƙe jikinta


Abbah ya ɗauko wuƙa ya yanke igiyar nan take suka kwantar da ita a ƙasa.


Dua ba ta motsi, Idanunta a lumshe

Numfashinta yana fita da ƙyar


Aryan ya durƙusa yana jijjigata

“Dua! Open your eyes… please!” Shiru  ko motsi ba ta yi ba.


Abidah kuwa ta rungume ta tana kuka

“My daughter… please don’t do this”


Sultan ya tsaya cak yana kallon abin da ke faruwa, ko a mafarkinsa bai taɓa tunanin wata yarinya za ta kai ga yunƙurin kashe kanta ba.


Abbah ya ɗaga murya “Me ake jira? Mu kai ta asibiti yanzu!” Aryan ya ɗauke ta cak kamar ƙaramar yarinya, da gudu suka fita zuwa mota


Bayan kusan mintuna arba’in…


Kowa yana zaune a reception na asibitin cikin tashin hankali, Abbah na ta kai da kawo, Sultan ya kasa zama wuri ɗaya


Aryan kuwa idanunsa sun yi ja Duk da ba kuka yake ba, Abidah na zaune tana jan tasbihi tare da yi wa Dua addu’a


Sai Zahra… tana zaune gefe ɗaya ba tare da wani atom na damuwa a fuskarta ba


Doctor ya fito daga Emergency Room

Ya kalli waɗanda suke wajen kafin ya ce

“I need to speak with the girl’s parents”


Sultan ya yi saurin cewa “Bari na kira Mahaifinta”, Sai dai Abidah ta dakatar da shi “A’a” Ta kalli Aryan “Zo mu je”


Su biyun suka bi bayan doctor zuwa office ɗinsa, da sun shiga, doctor ya zauna sannan ya ce “The good news is… we’ve stabilized her”


Abidah ta sauke numfashi “Alhamdulillah…”


Doctor ya ci gaba da magana.“But…” Kalmar ta sa zuciyoyinsu sake bugawa


“She didn’t just try to end her life because of today” Ya haɗa hannayensa a kan tebur “This is a child who has been carrying emotional pain for a very long time”


Aryan ya runtse idanunsa, Doctor ya ci gaba “Please… protect her, she doesn’t just need medication”


Ya kalli Abidah “She needs love”, Ƙwallar hawaye ta zubo daga idon Abidah, ta yi ƙasa da murya ta ce “In Shaa Allah…”


A zuciyarta kuwa ta yi alƙawari guda, ba za ta ƙara barin Dua ta yi rayuwa cikin wannan azabar ba


Following dina dai kar a manta ayi