KOMAI NISAN DARE

13.

by @zeeykumurya

KOMAI NISAN DARE 


Page 13


Zeey Kumurya 






Cikin gigita A'isha ta ƙwalla ƙara tare da sakin kuka, hankali a tashe Umar ya riƙo ta kafin su kai cikin ruwan ya rungume ta da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya dafa wani dutse dake bakin ruwan, amma duk da haka sai da ƙafafuwansu suka shige cikin ruwan ya kawo har gwiwoyinsu. Mutanen gurin gaba-d'aya suka yo kansu suna salati tare da kallon Ɗan'juma wanda shine ya hand'aka sun. Cikin sauri aka zaro su daga cikin ruwan, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un kawai Umar yake maimaitawa cikin kid'ima, dan shi ba ma ta kansa yake yi ba ta A'isha yake ita da ba ta gani. Ita kuwa ta ƙi sakin shi sai kuka take, dan ta tsorata ba kaɗan ba. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umar ya saki ya yiwa mutanen da suka ciro su godiya. Sannan ya juya ya kalli Ɗan'juma dake tsaye yana ta muzurai shi kaɗai, ji ya yi kamar ya damk'o shi ya naɗa masa na jaki, amma darajar Mahaifinsa yasa ba zai iya aikata hakan ba. Ɗauke idonsa ya yi daga kansa ya zare A'isha daga jikinsa a hankali sannan ya tsugunna dai_dai tsayinta ya shiga share mata hawayen fuskarta, so cool ya ce. "Sorry Dear, ki bar kukan nan haka Please, ko kina jin wani ciwon a jikinki ne?" Hannunsa ta riƙe gam cikin kuka ta ce. "Mu tafi gida ni dai ka kai ni gurin Inna."  Gabad'ayanta a tsorace take, sai ajiyar zuciya take saki akai_akai. Cikin lallashi ya ce. "Yanzu za mu tafi, amma Please ki bar kukan kin ji?" Gyaɗa mata kai kawai ta yi amma ba ta bar kukan ba. Miƙewa ya yi ya kama hannunta suka tafi bayan ya ɗauko mata takalmanta ta saka. Kafin su shiga gida sai ya rararrashe ta, ta bar kukan da take yi gudun kar hankalin Inna ya tashi. Suna shiga tana jin muryar ta tafi ta faɗa jikinta ta fara hawaye. Inna dake kallon su cikin mamaki ganin duk rabin jikinsu a jik'e ta ce. "Lafiya kuwa?" Cikin son kwantar mata da hankali Umar ya ce. "Lafiya lau Mama, a bakin ruwa muka zauna muka zira ƙafafuwanmu a ciki." Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Na san ita ta takura maka kuka shiga, dan na san ta da maitar hakan, to kuma me aka yi mata take wannan kukan?" Shafa kai Umar ya yi ya ce. "Wai dan mun taho gida yanzu ne." Tsaki Inna ta yi ta ture ta daga jikinta ta shige ɗaki tana faɗin. "Ki rufe mun baki ko jikinki ya faɗa miki, idan ba ku taho ba kwana kike son ku yi a can?" Kama hannunta ya yi ya zaunar da ita akan kujera ya shiga share mata hawaye, a hankali ya ce. "Dan Allah ki bar kukan nan Humairah ko kina so nima in yi?" Girgiza kai ta yi. Ya ce. "To ki daina, ba ki san yanda nake ji ba ne a cikin raina idan na ga kina kuka." Barin kukan ta yi cikin sanyin murya ta ce. "Na tsorata sosai Yaya Umar, na ɗauka za mu faɗa cikin ruwan ne, kuma na san da mun faɗa mutuwa za mu yi." Yana goge mata hancinta da handkerchief ɗinsa ya ce. "Ki bar zancen nan kar Mama ta ji, kuma ko na tafi kar ki faɗa mata ki ce mun kusa faɗawa ruwa." Ta ce. "Me yasa?" Ya ce. "faɗa zata yi miki mana, kuma ba za ta ƙara barin ki ki fita ko nan da soro ba, kin sani." Gyaɗa masa kai ta yi a hankali. Ya shafi kuncinta ya ce. "Good Girl, bari na tafi Magriba ta kusa." Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba. Murmurshi ya yi ya ya miƙe ya yiwa Inna sallama ya tafi. Bayan Fitar sa A'isha ta cewa Inna za ta yi wanka dan wari iri take jin jikinta, sai da ta yi Sallah ta ci abincin da Inna ta matsa mata ta ci kaɗan sannan ta yi wankan ta kwanta. Bayan Sallar isha'i Umar ya je shop ya yiwa A'isha siyayyar kayansu Biscuits da choculates da sweets masu yawa. Lokacin da ya je kai mata ta yi bacci sai Inna ya bawa ta ajiye mata. Inna tana duban ledar da aka zubo kayan cikin mamaki ta ce. "Umar wannan fa na mene ne?" Kansa a ƙasa ya ce. "Na A'isha ne Mama." Inna ta ce. "Haba Umar, wannan siyayyar ai ta yi yawa." Bai ce komai ba. Inna ta ce. "Toh an gode, Allah ya saka da Alkhairi ya biya ka da gidan aljannah, amma ba dan ba da na baka ka mayar da kayan nan inda ka siyo su ko ragewa ne a yi, wahalar ai ta yi yawa." Murmurshi ya yi ya amsa da Amin sannan ya yi mata sallama ya tafi. Ita kam Inna har cikin ranta ba ta son kashe_kashen kuɗin da Umar da yake yiwa A'isha, dan kwanaki haka ya kawo mata sabulan wanka masu ƙamshi da na wanki da toothpaste da man wanke gashi. A ganin ta d'awainiyar da yake yi da su ta yi yawa.






Wajen ƙarfe goma na dare Umar yana kwance yana operating system kira ya shigo cikin wayarsa, ɗaukar wayar ya yi ya duba, Abbansa ne yake kiran, d'agawa ya yi ya kara a kunnensa tare da yin sallama. Daga ɗaya ɓangaren bayan Abban ya amsa ya ce. "Umar ya aikin? Da fatan komai lafiya babu matsalar komai?" Umar ya ce. "Alhamdulillah Abba komai lafiya." Abba ya ce. "To Masha Allahu, Allah ya taimaka.... ɗazu Mamanka take sanar mun wai ka ce a cikin satin nan zaka dawo? Har ka gama abun da ka je yi ne?" Ɗan jimm Umar ya yi sannan ya ce. "Ban gama ba Abba da ɗan saura, ita ce dai ta ce sai na dawo ɗin." Abba ya ce. "Me yake damun Amina ne? Ni ban san mene matsalarta da zamanka a garin nan ba, ta bi duk ta damu kanta kullum cikin zancen take yi, na faɗa mata ba inda za'a cutar da kai na tura ka ba, dan na san halin abokina mutumin kirki ne." Umar ya ce. "Ka yi hak'uri Abba, amma zan taho cikin satin nan ɗin Insha Allah tunda haka take so." Abba ya ce. "Ba zai yiyu ba, ka tsaya ka yi abin da ka je yi a tsanake, idan ka gama sai ka dawo, ita kuma ka barni da ita." Umar ya ce. "Tom shikenan Abba Na gode, Allah ya ƙara girma." Abba ya ce. "Yawwa, ka ci gaba da kula dai, Allah ya taimaka ya yi Albarka." Umar ya ce. "Amin Abba." Daga nan suka yi sallama Abba ya katse kiran. Wani kiran ne ya ƙara shigowa cikin wayarsa, kallon wayar ya tsaya yana yi, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya d'aga tana gaf da katsewa ya kara a kunnensa bai ce komai ba. Ɗaga ɗaya ɓangaren aka ce. "Ya Faruq me na yi maka ne duk ka canza mun?" Umar ya ce. "Chanji kuma? Wanne iri Khausar?" Cikin damuwa ta ce. "When last rabon da ka kira ni ko ka mun magana a chat? Ina ga tun kafin ka yi tafiyar nan fa." Numfashi Umar ya sauke ya ce. "Toh shikenan ki yi hak'uri abubuwa ne suka shamun kai, Ya kike ya su Mommy?" Khausar ta ce. "Kowa lafiya ƙalau, amma ban da ni da nake cikin kewar ka, yaushe zaka dawo?" Umar ya ce. "Nan da 1 month insha Allah." A sanyaye ta ce. "Allah ya kai mu, amma kamar ya yi yawa ya Faruq, har 1 month zan ƙara ban gan ka ba, bayan kwanakin da na yi a baya?" Umar ya ce. "Ba wani yawa, kamar yau ne zaki ga kwanakin sun wuce har na dawo." Khausar ta ce. "To, Allah ya kai mu, baka ji daɗi da farincikin da nake ji ba yau na ji muryarka." Umar ya ce. "Haka ake so, yanzu ina ɗan yin wani aiki ne, I will call you later." Bai jira cewarta ba ya katse wayar ya cigaba da abun da yake yi. Washegari Umar ya je gidansu A'isha kamar yadda ya saba zuwa, ya tarar Inna tana yiwa A'isha tsifar kai. Bayan sun gaisa da Inna ta tufkewa A'isha gashin da aka tsefe ta ce mata ta ɗaure kanta idan Umar ya tafi ta cigaban mata, sannan ta tashi ta shige ɗaki.







A hankali A'isha ta ɗago kanta ta ce. "Ina kwana?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?" Ta ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah." ƙarasawa inda take ya yi ya kama hannunta ya ce. "Haka kike da gashi Humairah?" Rufe fuskarta ta yi da hannunta tana murmurshi ƙasa ƙasa ba ta ce komai ba. Ya ce. "A ina ake saloon a garin nan mu je a yi miki? Na san idan aka yi gashin naki zai ƙara kyau." A'isha ta ce. "Mene shi ɗin?" Ya ce. "Gyaran gashi mana." Girgiza kai ta yi ta ce. "Babu masu yi a garin nan." Ya ce. "Shikenan, watarana zan kai ki inda ake yi ayi miki." Cikin murna ta ce. "To Yayana na gode." Daga nan suka ɗora karatunsu daga inda suka tsaya. Kafin ya tafi ya yiwa Inna tambayar da ta dad'e tana yawo a cikin zuciyarsa. "Mama matsalar idon A'isha dashi aka haife ta ne?" Inna ta ce. "A'a, daga zazzaɓi kawai Ubangiji ya ɗoro mata, ko shekara biyu ba'a yi ba." Umar ya ce. "To me yasa baku je asibiti an duba idon ba?" Inna ta ce. "Na kai ta nan asibitin Rano suka ce sai dai mu je can Kano a duba ta, su ba su da k'wararrun likitan ido, mun gwada magungunan gida su ma ba'a dace ba." Umar ya ce. "To me yasa ba ku je can ɗin ba?" Shiru Inna ta yi ta rasa me zata ce masa. Numfashi ya sauke ya ce. "Shikenan Mama, Allah ya ba ta lafiya, bari na wuce gida." Sallama ya yi musu ya tafi. Wunin yau gaba-d'aya Umar cikin tunanin yanda zai yiwa A'isha magani ta warke yake yi, tunda ba da ciwon aka haife ta ba da yiyuwar zata warke da yardar Allah. Ya san da zai faɗawa Mahaifinsa ya nemi taimakonsa zai taimaka mata, ko da ƙasar waje ta kama akai A'isha akan ta samu lafiya zai iya kai ta, inda matsalar take baya son mahaifiyarsa ta sani, amma ya san matuƙar ya faɗawa Abbansa to sai Mom ɗinsa ta samu labari, dan Abba idan zai yi abu ba zai b'oye mata ba wai dan gudun ɓacin ranta ba. Idan kuma ya ce shi zai yiwa A'isha magani da kuɗinsa bai zama lallai kuɗaɗen dake cikin account ɗinsa su isa ba, sai dai idan Motarsa zai sayar, idan kuma ya siyar da Motar ina zai cewa Abbansa da Mom ɗinsa ya kai Motar? Haka dai ya kwana yana sak'e_sak'e shi kaɗai da neman mafita, dan babban burinsa a yanzu A'isha ta samu lafiya idanunta su buɗe.





Rayuwa ta cigaba da tafiyarwa su Inna cikin farinciki da kwanciyar hankalin da ba su taɓa riskar kansu a cikin  kamar sa ba, sanadiyyar zuwan Umar cikin rayuwarsu. Umar ya zame musu wani bango da yake ba su kariya ta ko'ina a cikin rayuwarsu, dan hatta k'warzabar da mutanen gari da ƴan gidan suke yi musu sun samu sauƙin ta, domin Umar duk ya taka musu birki akan hakan. A gefe guda kuma shak'uwa mai ƙarfi tana ƙara shiga tsakanin Umar da A'isha, kodayaushe suna tare yana koya mata karatu, idan sun gama ya yi mata waƙa ko ya kunna mata kallo a wayarsa tana saurara, wani lokacin kuma ta ce ya kira mata Ma'u su yi hira da Numbern Innar Ma'u da ƙaninta ya tura musu. Da hutunsu na makaranta ya ƙare aka koma shi yake kai ta ya ɗauko ta. Wani irin wasai A'isha take jin zuciyarta a yanzu babu damuwar komai, ta samu abokin hira mai ɗebe mata kewa da nuna mata k'auna. Idan dare ya yi suka rabu da Umar Allah_Allah take gari ya waye su haɗu su ɗora daga inda suka tsaya. Umar ya ɗaukewa Inna komai tun daga kan abinci har komai na buk'atun rayuwa, duk da ita har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba, ko dan yawon da ake yi da su a cikin gari ana sun mallake bak'o daga zuwansa garin suna ta tatse shi yana d'awainiya da su. Har nuna masa ɓacin ranta take yi akan siyayyar kayan da yake yiwa A'isha amma bai fasa ba. Bayan watanni ukun da ya ce zai yi a garin sun ƙare sai ya cewa Abbansa shukar da suka yi ba ta yi kyau ba sai sun sake wata, dan haka sai ya ƙara a ƙalla wasu watannin biyu kafin ya koma gida. Cikin rashin damuwa Abban nasa ya amince masa, Mom ɗinsa ce dai ta dinga yi masa masifa kamar zata ari baki, shi kam ya yi hakan ne saboda bai san tafiya ya bar A'isha. 





Yau Litinin, da yamma ɗaya daga cikin ƴaƴan Sarki mai suna Haulatu ta dawo daga makaranta ta zauna a ɗaki ba tare da ta nemi abinci ba ta rafka tagumi da hannu bibbiyu, kallo ɗaya mahaifiyarta ta yi mata ta gane tana tattare da damuwa. Cikin kulawa ta dube ta, ta ce. "Ke lafiya kuwa kike?" Kamar Haulatu zata yi kuka ta ce. "Uwa wallahi wani abu ne yake damuna." Da mamaki Uwa ta ce mata. "Mene shi?" Ƙasa ta yi da kanta ta ce. "Uwa Umar ne idan na gaishe shi cikin rashin kulawa yake amsa mun, ba ya sakar mun fuska, ko na je gurinsa da niyyar mu yi hira sai ya haɗe mun rai, kuma ni gaskiya son shi nake yi." Uwa ta ce. "Wanne Umar kenan?" Haulatu ta ce. "Wanda yake zaune a cikin gidan nan ɗan abokin Sarki." Kama hab'a Uwa ta yi ta ce. "Kin san wa kike faɗa kuwa Haulatu? Lallai ba ki da hankali, to bari ki ji in faɗa miki, tun wuri ma ki cire shi daga cikin ranki dan ba'a ajinki ba ne shi, ato." Cikin damuwa Haulatu ta ce. "Saboda me?" Uwa ta ce. "Mahaifiyarsa! Matar nan ba ta kirki ko na sisin kwabo, mun taɓa zuwa gidanta sau ɗaya lokacin da mahaifin shi Mijin nata ya rasu, kakansu Umar ɗin kenan, Sarki ya kwashe mu muka je muka yi masa gaisuwa, yanda Matar nan ta wulaqanta mu abun ba zai faɗu ba, da muka gaishe ta daƙyar ta amsa kamar an yi mata dole, ƙarshe ma tashi ta yi ta bar mu yashe a falo sai masu aiki ne suka yi hidima da mu. Sai dai Mahaifinsa shi mutumin kirki ne, mutumin nan shi idan mutunci yana yin yawa to nasa ya yi, dan shi ba ki ga yanda ya mutunta mu ba wallahi." Haulatu ta ce. "Toh tunda Babansa yana da kirki ba shikenan ba, ni dai gaskiya Uwa ki yiwa Sarki zancen, dan shi kaɗai nake son na aura." Uwa ta ce. "Abun fa da ba zai taɓa yiyu ba ne Haulatu, idan zaki hak'ura ki hak'ura." Kuka Haulatu ta saka ta ce. "Wallahi Uwa zai yiyu, idan ya san ba za'a bar shi ya auri ƴar ƙauye ba me yasa yake kula waccan makauniyar Yarinyar, son ta fa yake yi kuma kowa a cikin garin nan ya sani." Shiru Uwa ta yi na wasu sakanni tana kallon ƴartata, tabbas abun da ta faɗa gaskiya ne, da Umar ya san ba za'a bar shi ya auri ƴar ƙauye ba da ba zai fara soyayya da A'isha ba, idan kuwa har haka ne Ƴarta ce tafi dacewa da auren ɗan gidan mai kuɗi ɗan birni ba ƴar talakawa mara asali ba. Idan Haulatu ta auri Umar za su zamo abun alfahari a garin nan, ko a cikin kishiyoyinta za ta yi musu zarra ƴarta ta auri Mijin da kaf ƴaƴansu babu wadda ta auri ko wanda ya kama ƙafarsa ne a komai da komai, dan yanda take jin Sarki yana faɗar kuɗin mahaifin Umar ba ƙaramin mai kuɗi ba ne. Wani murmushi ta saki tare da miƙewa cikin sauri ta ɗauko kuɗi a cikin jakarta Naira ɗari biyu ta bawa Haulatu ta ce. "Share hawayenki ki kwantar da hankalin ƴata, na samo mana mafita wadda nake da tabbacin zata raba Umar da waccan yarinyar cikin sauƙi, idan hakan ta kasance ke kuma na san yadda zan yi mu janyo hankalinsa gare ki." Haulatu ta ce. "Ta yaya? Me zaki yi?" Uwa ta yi murmurshi ta ce. "Ke dai je ki siyo mun katin MTN da wannan kuɗin, idan kika dawo a gabanki komai zai faru, za ki ga abun da zan yi." Ajiyar zuciya Haulatu ta sauke ta miƙe tana share hawayen fuskartata ta fice daga ɗakin...........✍️