The Unwanted Daughter

Page 17: The Unexpected Chance

by @hauwajaywrites



Da sassafe Dua ta tashi kamar yadda ta saba, ta fara aikinta ba tare da bata lokaci ba. Ta yi ta kai-komo cikin gidan, tana gyara komai cikin nutsuwa har ta gama dukkan ayyukanta kafin ƙarfe bakwai na safe. Bayan ta gama, ta zauna ta yi breakfast, sannan ta haura sama, ta shiga bathroom ta yi wanka. Bayan ta shirya, ta fito cikin jilbab, ta ɗauki kayanta ta nufi ƙasa domin tafiya


A lokacin babu kowa da ya sauko ƙasa, domin ba kasafai suke fita da sassafe ba a weekend, Dua kuwa ba ta ɓata lokaci ba, kai tsaye gidan Ayesha ta wuce


Da ta isa, sai ta tarar Ayesha ma yanzu-yanzu take, tashinta daga barci knn, Da ta ga Dua tsaye a gabanta da sassafe, Ayesha ta kama baki tana kallonta da mamaki, sannan ta ƙarasa da zolaya tana dariya “Who am I seeing?”


Dua ta yi murmushi ta girgiza kai

“Get up jhoor, common I want some advice”


Ayesha ta gyara zamanta Akan king size bed nata, sannan ta kalle ta da ɗan damuwa “Hope all is well?”


“Not at all”


Nan take Ayesha ta zauna sosai, ta mayar da hankalinta gare ta “What’s up BFF? I’m all ears”


Dua ta sauke ajiyar zuciya kafin ta furta

“I’m going to Kaduna to spend my holiday there”


Ayesha ta zaro ido “Don’t tell me you’re going to Amrah’s grandmother’s house?”


“Sure”, Ayesha ta zaro ido “Then ya za ki yi?”, Dua ta ce “I don’t know too”


Ayesha ta kalle ta da mamaki, kamar ba ta yarda da amsar da ta samu ba


“You’re mad Dua, Don’t tell me you don’t know what to do, kawai za ki yarda ki bi su bini-bini, ga ki me biyayya. Ke da dangin Mummy ba sa sonki, kowa kyama yake nuna miki”


Dua ta sunkuyar da kai, muryarta ta yi sanyi “I’m out of words. Ban san ya zan yi ba”


Ayesha ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar tana tunanin mafita, sai kuma ta ɗago yatsarta da sauri“I find one way. I think it would help”


Dua ta ɗago kai “Say it please, in shaa Allah it would help”


“The only solution kawai mu je wajen Mu’allim mu gaya masa duk abin da ke faruwa. Abin da muke so ya mana shi ne kawai ya zo ya samu Daddy, ya ce an saka ki cikin musabaqa, kuma ke za ki represent school ɗinmu. Shi kenan, ba sai kin tafi ba”


Farin ciki ya bayyana a fuskar Dua. Nan take ta tashi ta rungume Ayesha “You’re such a darling”


Dukansu suka haɗa baki “What are friends for?” Suka sake fashewa da dariya


Daga nan Dua da Ayesha suka tafi Islamiyya, suka samu Mu’allim suka gaya masa duk abin da suke son ya taimaka musu da shi. Da ya ji labarin, musamman yadda lamarin yake damun Dua, tausayi ya kama shi. Ya yi mata alƙawarin cewa zai je ya samu Daddy ya yi masa magana


A gidan kuwa, Ummi ta lura cewa lokacin breakfast Dua ba ta nan. Bayan ta gama breakfast, sai ta nufi ɗakin su Dua domin ta duba ta. Amma da ta shiga, ba ta same ta ba.


Hankalinta ya fara tashi.


Kwanaki biyu kenan tana lura da yadda Dua take cikin wani irin yanayi na damuwa. Wani mummunan tunani ya fado mata rai


Allah Allah, kar ace Dua ta gudu


Da sauri ta girgiza kai, tana kawar da tunanin


A’a, wannan ba zai faru ba. Dua ba irin wadda za ta aikata hakan ba ce


Ta fita daga ɗakin ta nufi kitchen, inda ta tarar da Fatima tana aiki


“Fatima, Dua tana ina ?”


Fatima ta ɗago kai “Ta tafi Islamiyya ne. Ai kullum tana zuwa idan ba hutu suke ba”


Ummi ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta koma cikin parlour


A wannan lokacin Amrah ta fito domin yin lunch. Da ta fito sai ta hango Sultan a zaune, wayarsa a hannunsa yana ta latsawa. Da ya ɗago ya gan ta, sai ya yi mata murmushi “Hey you”


“Hey Yaya”


Nan suka fara hira, cikin ɗan lokaci suka shiga dining area suka yi lunch tare. Bayan sun gama, Amrah ta roƙi Sultan ya kai ta unguwa, shi kuma bai ƙi ba


Da yammancin ranar, Daddy da Mummy suna zaune suna ɗan hira, sai wani maid ya shigo “Ana sallama da Daddy a waje”


Mummy ta kalli Daddy “Je ka ce baya nan”


Amma Daddy ya yi saurin cewa

“Noo, ce masa ina zuwa”


Mummy ta ɗaga gira

“Yanzu sai ka samu ’yan maula ne?”


Daddy ya yi mata kallon gefe

“Whatever dai, bari in fita in gan shi. Ko speculation ɗin da kika saba yi ne”


“Toh, a dawo lafiya”


Daddy ya fita. Da ya isa wajen, sai ya ga sabon fuska, in fact, bai taɓa ganin mutumin ba a baya


Ya yi masa maraba zuwa guest room, suka gaisa, sannan Daddy ya kalle shi “Amma ban gane kai ba”


Bakon ya yi murmushi

“Eh ba ka san ni ba, Ni ne Mu’allim ɗin genius daughter ɗinka”


“Oh, okay”


Mu’allim ya gyara zamansa sannan ya fara bayani


“Daman akwai wani musabaqa da za a yi na inter-school, so your daughter is among them. Mun zaɓe ta ne akan za ta represent school ɗinmu. An kira parents ɗin yaran da za su yi musabaqar meeting, amma mun san yadda commitment ɗinka ya yi yawa, shi ya sa ba mu yi inviting ɗinka zuwa school ba. Shine a ƙarshe muka yanke shawarar in zo in same ka da kaina. Ana son yarinyar ta samu more time na tilawa a gida, sannan ana son su riƙa zuwa school da wuri dan rehearsal kafin lokacin”


Daddy ya gyada kai “Okay bakomai daman za su yi tafiya ne, amma yanzu it will be cancelled. Na gode”


Mu’allim ya yi murmushi “Thank you, sir”, Bayan sun yi sallama, Mu’allim ya tafi


Ba daɗewa ba, Abba da Ummi suka shigo gidan cike da gajiyar ziyarar da suka yi. Parlour ɗin babu kowa sosai sai Mummy, yayin da Sultan da Aryan suke dining area, kowa yana kan abin da yake yi. Mummy ta gaishe da Abba, ya amsa mata, sannan suka gaisa da Ummi. Suka zauna kenan sai ga Daddy ya shigo.


Bayan sun gaisa, Abba ya kalle shi

“Yau tun safe muka rabu sai yanzu”


Daddy ya yi murmushi

“Wallahi, yau kam ma ko gate da niyyar fita wani waje ban yi ba, in ba zuwa masallaci ba. Yanzu ma daga guest room nake”


Nan ya ba su labarin zuwan Mu’allim da abin da ya kawo shi


Mummy kuwa tana kallonsa da wani irin kallo, amma Daddy bai fahimci abin da take nufi ba. Abba da Ummi suka sa albarka, har cikin ransu suka ji daɗin labarin. Aryan da Sultan da suke dining area suma suka zo parlour, suka nuna farin cikinsu, musamman Aryan


Fatima ma, wadda take ta aikin yamma, da ta ji labarin ta yi murna wa Dua har cikin ranta ita ma


Mummy kuwa kamar za ta fashe, ta miƙe ta haura sama abinta


Daddy ya lura da yadda ta bar wajen, sai kawai ya bita


Ummi ta kalle su suna haura sama, ta yi murmushi a ranta. Ta san yau za su haura sama, kuma da ƙyar za su sauko


Aryan kuwa ya nufi ɗakin su Dua, da ya shiga, ya tarar da ita ita kaɗai, tana karatu, ko dagowa ba ta yi ba. A ranta ma tana tunanin Amrah ce, har sai da ta ji an gyara murya


Da sauri ta juyo, Aryan ya yi mata murmushi


“Congratulations our little baby, the talented girl”


Dua ta kalle shi cikin mamaki

“Ya Aryan, for what?”


Nan ya gaya mata abin da ya faru


Dua ta yi shiru na ɗan lokaci. Ba ta taɓa tsammanin Mu’allim zai zo ba, balle har ya samu Daddy. Wani irin farin ciki ya cika zuciyarta, farin cikin da ta daɗe ba ta ji irinsa ba


Kenan Daddy ya yarda ba za ta Kaduna ba

Kuma har Daddy ya gaya wa mutanen gidan, ta kalli Aryan da murmushi “Thank you, Ya Aryan”


“Shiiits mention not, little”


“Toh”


“Bye, kar na dameki” Aryan ya fita, ya bar Dua cikin farin ciki


A ɗakin Daddy kuwa, Mummy ta fara masifa. Magana take ta inda ta shiga ba nan take fita ba


“Kaban mamaki! Imagine har ka amince masa without my consent? Bama wannan ba, ka je kana wani fada a parlour, kowa da kowa yana nan, har wasu munafukai suna murna. Toh ina ruwana? Dan wulakanci, ina ta magana da ido amma kai ko a jikinka sai zuba kake kamar wani sabon taɓaɓɓe”


Daddy ya daka mata tsawa, muryarsa cike da fushi “Dua is my daughter. Remember this always. So duk yadda take so, hakan zan mata, kamar yadda zan yi wa Aryan and Amrah. So don’t push me. Dan wallahi ranki sai ya baci. Ji yadda kike min kamar wani ɗanki. Do you really think zan zuba miki ido kina min magana yadda kika ga dama ne? So mind your own tone, okay?”


Ya juya ya fita, ya bugo mata ƙofar dakin


Zahra ta tsaya cak, ta ɗaga hannu ta mare fuskarta sau uku, kamar tana son tabbatar wa kanta cewa ba mafarki take ba, Is this really so?


Wannan shi ne karo na farko a rayuwarta da ta ga Daddy cikin irin wannan fushi. Ba wai kawai ya fusata ba, har ya mata tsawa da magana cikin irin wannan yanayi.


Ta daura hannu a kai, ta sa ihu kamar wadda aka sikara. Daga nan ta ɗauki wayarta ta kira Nuwairah


Bayan sun gama magana, ta kashe wayar ta kwanta, amma zuciyarta cike take da fushi da tunani


Da daddare, bayan kowa ya tafi ya kwanta. Nuwairah ce ta kira Mummy a waya “Kin iso?”


“Gani fitowa”


Daddy, saboda fadan da suka yi, bai shiga ɗakin Mummy ba. Hakan ya ba Mummy damar cika kudirinta


Ta leƙa parlour ta tabbatar babu kowa. Sai ta fito tana tafiya a hankali, sannu a hankali har ta isa bakin gate


Gate man ya buɗe mata ƙofa, ta fita ta nufi motar Nuwairah. Ta shiga, sannan suka bar unguwar


Duk abin da ke faruwa, Aryan yana kallonta daga nesa. Mamakin mahaifiyarsa kawai yake yi a ransa


Toh ina za ta cikin dare?


Bayan kwana biyu, Daddy ya shigo ya kalli Mummy “Gobe ne tafiyarsu Amrah?”


“Eh”


Dama Mummy ta ɗaga tafiyar su Amrah saboda abin da ke ranta. A ranar ta je ta gaya wa Amrah da Dua su gama haɗa kayansu, domin gobe za su tafi Kaduna


Dua kuwa banda kuka babu abin da take yi, ta nufi wajen Aryan tana kuka “Ya Aryan, bana son zuwa. Ka ba Mummy haƙuri”


Aryan ma ya tausaya mata sosai. Ya kasa jure ganin yadda take kuka, sai ya nufi wajen Ummi ya gaya mata abin da ke faruwa


Ummi ta yi mamaki

“Je ka, zan yi wani abu a kai”


Nan take Ummi ta nufi ɗakin su Dua. Da ta shiga, ta tarar da idonta ya yi ja saboda kuka


“Dua, Aryan ya ce min wai za ki Kaduna, ba za ki yi musabaqa ba, hakane?”


“Eh, Ummi”


“Kin son zuwa?”


“Noo Ummi, Please do something”


Ummi ta zauna kusa da ita, tana patting dinta sai kuma ta tuna da Hibbah, ta mike


“Alright, Kar ki sa damuwa a ranki”


Ummi na shiga dakinta, ta zauna tana lissafin lokacin London da Nigeria a ranta. Lokacin bai yi daidai da kiran Hibbah ba tukuna


Amma daga baya za ta kira ta


Kuma wannan karon, Ummi ta kuduri aniyar yin wani abu domin Dua.


Have this, sorry for waiting 🤍 In shaa Allah gobe ma za ku ji ni. Good night, my loves 🤍


Please kuna liking na book din, hadi da following acc Dina for more updates