THE THRONE OF THORNS

THE PROMISE TO RETURN

by @maryam730

Atti ce ke magana ita kaɗai cikin bacci tana cewa, “Leekah… Leekah… Leekah…” har bakinta na motsi, gaba ɗaya ta yaye bedsheet ɗin.
‎
‎Kafin kuma firgigit ta tashi zaune daga baccin.Jikinta duka ya jiƙe da gumi, numfashinta na fita da ƙarfi kamar wacce ta yi tseren mil goma. Zuciyarta na bugawa da irin wani ƙarfi kamar zai fasa ƙirjinta.
‎
‎Zazzare ido ta fara a duhun ɗakin.Dan ita kanta har yanzu taka sa gane a  mafarki take ba ko a zahirin gaskiya.
‎
‎Hannunta na rawa,ta riƙo kirjinta, tana ƙoƙarin daidaita numfashi.One,Two,Three,amma jikinta bai dai na rawa ba
‎
‎Muryar ta kamar wani abu ne ya riƙe maƙogwaronta daga ciki,ta fara magana kamar zararrayi tana cewa,“Ina nan… Ina nan a ɗakina,babu kowa,leekahh ta daɗe da mutuwa.”Ta maimaita hakan a ruɗe, tana ƙoƙarin shawo kan kanta.Amma zuciyarta ba ta amince da hakan cikin sauri ba.Fitilar wayarta ta kunna 3:07 a.m,ta kalli agogon na ƴan seconds,sai ta sauke wayar.
‎
‎Har yanzu sanyi gumin nata bai bushe ba. Sai da ta ɗauki dogon lokaci a zaune a kan katifar, gwiwarta biyu a riƙe da hannayenta, kanta a duƙunƙune, kafin bugun zuciyarta ya fara komawa yadda yake.
‎
‎Bayan wani ɗan lokaci, ta miƙe,ta ɗauki hijab ɗinta, ta fita ɗakin domin ɗauro alwala.Ruwan sanyi ya taɓa fuskarta, amma wannan karon ba ta ji shi kamar da,her mind was still somewhere else.Wani wuri da ita kanta bata sani ba.
‎
‎Bayan ta gama alwala, ɗakin ta ta komata shimfiɗa sallayar ta,ta fara sallah ita kanta ba yasan raka'a nawa take ba.sai da yaji ƙafafunta na ƙoƙarin yadda ita kafin ta zauna.
‎
‎Ɗaga hannun ta sama tayi duk wani guards ɗin ta breaking into pieces, wannan lokacin, babu wani tough face.
‎
‎Babu Atti wadda take nunawa mutane cewa komai yana ƙarƙashin control.Babu yarinyar da take ƙoƙarin kare kowa,a gaban Allah kawai take.Kafin ta fara da cewa.....
‎
‎“Ya Allah…”
‎
‎Muryarta ta fara rawa.
‎
‎“Ya Allah, kai ka san abin da ke cikin zuciyata.”
‎
‎Hawaye suka fara taruwa a idanunta.
‎
‎“Ka san abin da nake tsoro,Ka san abin da ban iya faɗa wa kowa ba,Ka san abin da nake ƙoƙarin ɗauka ni kaɗai.”
‎
‎Muryarta ta ƙara karyewa.
‎
‎“Ya Allah, idan wannan abu alheri ne a gare ni, ka sauƙaƙa min shi. Idan kuwa sharri ne, ka kare ni daga gare shi.”
‎
‎At that time tuni hawaye sun fara jiƙa eye lashes ɗin ta.
‎
‎“Ka kare Ummu,Ka kare iyalina,ka bani abinda zan musu duk abinda suke so,Ka ba ni ƙarfin da zan iya fuskantar abin da ke gabana.”
‎
‎Ta share hawayen, amma wasu suna rige-rigen sake fitowa.
‎
‎“Ya Rabb… kar ka bar ni ni kaɗai.”
‎
‎A ƙarshe ta fashe da kuka,ta yi kuka mai tsawo,ta bar duk wani ƙarfin da take nuna wa mutane ya zube a gaban wanda shika ɗai ne zai iya taimakon tam
‎
‎Sai da ta ji jikinta ya yi sanyi, zazzaɓi na ƙoƙarin kamata tukunna tayi shiru.A hankali, wani irin nutsuwa ya fara saukko mata.
‎
‎Ba wai saboda ta samu amsar abin da zai faru ba.A'a,saboda ta tuna cewa ba ita kaɗai take ɗauke da abin da ke gabanta ba,Allah yana tare da ita.
‎
‎
‎Wani dogon numfashi,tayi Sannan ya miƙe,ta ɗaukko Alƙur'aninta,saboda ta san komawa bacci ba mai yiwu bane yanzu.
‎
‎Karatu ta fara cikin ƙira'ar Sudanese mai daɗin ji da zaƙi, muryarta a hankali tana cika ɗakin,Aya bayan aya,shafi bayan shafi,har aka fara kiran sallar Asuba.
‎
‎Ta ajje Alƙur'anin, ta tada raka'atanul Fajr, sannan ta shirya domin sallar Asuba,a  lokacin ne ta fara jin motsin Ummu.
‎
‎Sallar Asuba a ɗakinta ta tayar saboda gudun Ummu ta ga yanayin ta.Amma tana cikin sallan ne sai aka turo ƙofar a hankali
‎
‎
‎Ummu ta leƙa,da ta ga Atti tana sallah, sai ta ja ƙofar ta koma ɗakinta domin yin tata sallar.
‎
‎Bayan sallar Asuba,su Ammar da Husna sun tashi har sun fara shirin makaranta suna ta ƴan ƙananun faɗansu.
‎
‎Amma a zuciyar Atti, wannan safiyar ta bambanta.
‎
‎Ta zauna a bakin gadonta tana kallon kayan da za ta tafi da su,ƙwanƙwasa ƙofar akayi muryar Ummu na cewa,“Atti?”,Atti daga ciki ta “Ummu Come in".
‎
‎
‎
‎Shigowa tana da sallama ɗauke a bakinta ,amsawa Atti tayi Ummu na zama a gefen katifar tana kallon ɗiyarta na ƴan seconds.kafin tace“Kin yi bacci?”,Atti ta yi murmushi kaɗan,“Eh… na yi.”Ummu ta kalle ta sosai,“Kar ki yi min ƙarya.”murmushin Atti ya ɗan gushe"Dagaske, Ummu.”
‎
‎Shiru ya sake shiga tsakaninsu,daga baya Ummu ta ce, "Atti kin san da cewa sometimes being strong doesn't mean you don't get scared.”
‎
‎Atti ta ɗaga idonta,Ummu ta yi saurin da katar da ita da cewa kar kice komai,kafin ta cigaba da cewa,
‎
‎“Kin dade kina ƙoƙarin zama strong for everybody. For me,for your siblings,for yourself. Kina ɗaukar komai kamar ke ce babba a gidan.”
‎
‎Atti ta yi murmushi mai rauni,“Someone has to.”“Ba dole sai ke ba,we are all family muma ya kamata muyi",maganar ta tsaya a zuciyar Atti.
‎
‎Ummu ta riƙe hannunta,“Ke ɗiyata ce before you became the girl everybody runs to. Before you became the one people depend on… you were simply my daughter.”
‎
‎Ummu ta matse hannunta.
‎
‎“Don haka idan kika ji tsoro, ki ji tsoro. Idan kika gaji, ki faɗa. Idan kika kasa, ki bari wani ya riƙe ki,You also a human .”
‎
‎Atti ta ce
‎
‎“Amma Ummu…I'm not scared.”
‎
‎Ummu ta kalli fuskarta,“Na sani,ba ƙaramin abu bane,na sani.”
‎
‎“Then why are you still letting me go?”
‎
‎Wannan tambayar ta sa Ummu ta yi shiru.
‎
‎Ta kalli ɗiyarta na dogon lokaci.
‎
‎“Saboda Ke ɗin MALEEKA ce jinin MUHAMMAD ne ke gudana ajinin ki,Kece wacce zata ƙara fito da sunan KANGIWA ,kece Maleeka Muhammad KANGIWA ta ƙarasa faɗa da wani proud smile akan face ɗinta"
‎
‎Atti ta runtse idanunta.
‎
‎Ummu ta cigaba da“Na san baki da tsoro, amma na san kina da zuciya. Na san ba za ki shiga wuri ki manta damu ba dan haka mun baki amanar kanki . Kuma na san idan Allah ya rubuta ki shiga, babu wanda zai iya hana abin da Ya rubuta.”
‎
‎Ta ɗan ja numfashi.
‎
‎“Amma kada ki taɓa tunanin cewa zan daina tsoro da fargaba .”
‎
‎Muryarta ta fara rawa.
‎
‎“Ni uwa ce.”
‎
‎Atti ta kalli Ummu.
‎
‎“Duk inda za ki je, wani ɓangare na zuciyata zai tafi tare da ke.”
‎
‎Ta yi murmushi cikin hawaye.
‎
‎“Ki dawo min.”
‎
‎Atti ta kasa riƙe kanta.
‎
‎Ta rungume Ummu.
‎
‎“Zan dawo.”
‎
‎Ummu ta rungume ta sosai.
‎
‎“Say it again.”
‎
‎“Zan dawo.”
‎
‎“Again.”
‎
‎“Zan dawo, Ummu.”
‎
‎“Allah ya sa.”
‎
‎A wajen ƙofae muryar Ammar ce yake cewa,"Ummu mun gama shiryawa",Atti da Ummu suka ɗan kalli juna.Sai Ammar ya sake cewa, “Za mu makara!”“Ku jira ni!” Ummu ta amsa.Ammar ya yi gunaguni daga waje,“Every morning the same thing.”
‎
‎Husna ta yi dariya,Atti ma ta kasa hana murmushi daga fuskar ta
‎
‎For a few seconds, komai ya koma kamar basu e ke cikin tsaka me wuya .Kamar babu wani sirri.Kamar Atti ba ta shirin shiga wani wuri da ba ta san abin da ke cikinsa ba.
‎
‎Bayan sun shirya, Ammar da Husna suka fito domin zuwa makaranta.
‎
‎“Adda” Husna ta ce tana kallonta, “ki kula da kanki.”ta faɗa kamar tasan wani abu zai faru Atti ta yi murmushi.“Ke dai ki kula da karatinki”,Husna ta yi dariya,“Okay, InshaAllah Adda ta",Ammar ya ɗaga hannunsa,“Bye,Bye.”
‎
‎Ummu ta tsaya a ƙofar tana kallonsu har suka fita.
‎
‎
‎Sai aka samu shiru.
‎
‎Wani shiru ne ya ratsa wanda ya dawo da komai da duk wani tension.
‎
‎Atti ta koma ɗakinta ta fara packing abubuwan da zata buƙata, shirya komai tayi cikin nutsuwa da tsari.
‎
‎Amma duk lokacin da hannunta ya taɓa wani abu, sai zuciyarta ta tuna mata inda za ta.
‎
‎Bayan ta gama, ta rufe bag ɗinta,ta ɗaga shi,Ummu ce ta shigo,ta kalli bag ɗin,sai ta kalli Atti,“Kin gama?,“Eh sauran abubuwa kaɗan .”
‎
‎Karɓa Ummu tayi tana cewa kawo in ƙarasa miki je kiyi wanka...end of chapter 11............
‎