MISHAL

Page 24/25

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 24 / Page 25

Cikin sauri ta d’auke fuskarta , tana ‘bata rai, amma zuciyarta dukan uku uku take , sabida batasan wana irin hukunci Uncle zai yanke yanzu ba . 

Sake kallan fuskar Aya, Mamy tayi tana girgiza kanta cikin takaici “ Wallahi Mimi kin bani kunya , yanzu aushe zaki iya d’aukar hannu ki mari babba? Yaushe wuyanki yayi wannan kaurin? Ko da yake ba laifin ka bane , sangarta ki da ake ne yasa kike duk iskancin da kika ga dama , amma zanyi maganin  ki , kuma na gode Mimi, Nagode ! Nagode da kika nuna mun iyakata a kanki.

Kin riga kin gama naki ko? Toh kijira nima irin hukuncin da zanyi miki kinji.”

Da sauri Mimi ta nufi Mamy , amma Mamy tayi saurin dakatar da ita “ Wallahi kika matso kusa dani sai na sa’ba miki , mutuniyar banza mutuniyar hofi, sha sha sha kawai .” Sai kuma ta kalli Uncle Moh . 

“ Moh idan akan yarinyar nan ne ka kira ni , dan Allah ko me ka ga dama kayı mata , ni bani da lokacin ta , ko ‘ballata zakayi babu abunda ya dame ni, kuma ki bari na ganki a inda nake zaki gane kuren ki ne .”


“ Haba Mamy meyasa zaku dinga bin bayan bare akai na ? Duk yadda take takura mun bakwa gani amma laifi na kuke gani haba Mam 
.” 

“ Okay nima dawomun da magana zakiyi? Ina fad’a kina fad’a ?.”

Cikin sauri Mimi ta girgiza mata kai “ A’a Mamy kiyi ha’kuri .”


“ uhmmm” kawai Mamy tace , ta nufi inda Aya take a tsaye “ Kiyi ha’kuri Aya , bansan fuskar ki ta kumbura haka ba , zan kawo miki magani da zaki shafa a wajan , har kumburin ya sauka kinji?.

Amma yanzu ki soma rama maradin da tayi miki tunda ba tsoranta ake ji ba . 

Kuma karki wai muna tsaye a wajan , ki daddage ki wanka mata mari , idan ba zaki iya ba , ni ki bari zan rama miki.”


‘Dan ‘ka’kalo murmushi Aya tayi tana jinjina mata kai “ Na gode Mamy , amma ba sai na rama marin ba , tunda nima na mareta kuma shatin hannu na ya fito akan fuskarta.”


“ Duk da haka Aya , ai ni ta wula’kanta , tunda nice nace ta rakaki , ni ya kamata tazo ta mara tunda haushi take ji sabida nace ta rakaki
.”

Aya za tayi magana Mamy ta sake rigata magana “ Idan baki rama ba , toh ni zan rama miki da kai na .”

Kasa motsawa daga inda take Aya tayi, tana satar kallan Moh da kwata kwata babu wanda yake kalla a cikin falon, hannunsa ne kawai guda d’aya akan goshinsa yana d’an murzawa a hankali a hankali kamar besan abunda yake faruwa a cikin falon. 

‘Dan waigowa Mimi tayi tana kallan su Shukura.

Cikin sauri Shukura da Sadiq suka d’auke kansu akanta kamar basu san me take ba suka fice daga falon. 

Mayar da kallanta tayi kan Saleem, shima yayi fuska ya fice daga falon , yayi saura Uncle Abba da yayi mata murmushi, yana mata alamar ta kwantar da hankalinta , sannan yayi mata alamar kar tayi kuka , hakan yasa ta d’anyi masa murmushin ya’ke tana jinjina masa kai , kafin shima ya fita daga cikin falon. 

Falon yayi saura Moh, Aya , Mimi da kuma Mamy da take tsaye rai a ‘bace .

Falon ya d’au shiru na wasu mintuna babu me cewa uhm ko uhm uhm. 

Bayan kamar mintuna 2 da ‘yan seconds Moh ya sauke hannunsa daga kan goshinsa , yana gyara zamansa sosai .

Mamy ya soma kalla “ Babu damuwa Mamy ! Zanyi handling abun
”

‘Karamar ajiyar zuciya Mamy ta sauke tana jinjina masa kai alamar Toh , sannan ta ‘kara da “ Ka hukunta ta yadda ya kamata , tunda bata jin maganar kowa a cikin gidan nan , wuyanta ya isa yanka .” 

Baice mata komai ba sai kansa da ya d’an motsa, hakan yasa Mamy ta wuce part d’inta bayan ta d’anyi wa Aya murmushi , ta kuma harari Mimi da take kallanta. 

Lokacin da falon yayi saura su uku, da hannu yayi musu alamar su samu waje su zauna , ba tare da ya bud’e baki yayi magana. 

Ko wacce sim sim ta samu waje ta zauna. Kasantuwar 3 sitter da take gabansa ya nuna musu, yasa suka zauna waje d’aya amma kuma ba kusa da kusa ba . 

Sai da ya gama ‘karewa reaction d’in ko wacce daga cikin su , ya kuma karance su , ganin yadda suka sha jijin jikinsu , kamar ko d’an ya tsa aka saka musu a baki ba zasu tauna ba , sun wani nutsu kamar suna gaban baban su. 

“ So now ! Explain me ya had’a ku?” Suka ji saukar muryar sa daga sama , gashi babu wasa sam-sam a cikin muryarsa . 

Wani abu suka had’iye a zuciyar su , lokaci d’aya , dan Mimi kasa magana tayi sabida ‘kirjinta da yake wani masifar gudu ba tare da tasan dalilin gudan nasa ba . 

Aya ce ta samu courage d’in bud’e baki ta soma yi masa bayanı. 

Bata rage ko kalma d’aya ba , kuma bata ‘kara kalma d’aya daga cikin abunda ya faru ba , exactly sai da ta fad’awa Moh abunda ya faru tun daga shigowar gidan, maganar da sukai da Mimi, har abunda ya faru yau , marin ta da Mimi tayi , da kuma itama marin nata da tayi, har zuwa ha’kurin da tace Mimi sai ta bata , bata ‘boyewa Moh ba . 

Yana gama sauraran Aya ya kalli Mimi da take ‘ko’karin sai ta nutsuwarta , kuma ya riga ya gane she’s not comfortable yadda ya tsare ta da idanun. 

Tun kafin ma yayi magana ta furta “ Uncle Moh , ta kura mun tayi , bawai da gangan na d’aura hannu na mare ta ba , beside jawo ni tayi baya na fad’i , unexplained ne na mare ta da farko
”

“ And shi kuma marin na biyu fa ? Janyo ki tayi shima ?”. 

“ No mari na tayi nima nima na rama
.” Amma yanzu cikin silent turn ta ‘karasa magana ganin irin kallan da yake jefa mata . 

Tana kaiwa ‘karshen nan ya furta “ Mimi shekarar ki nawa ne ?”. 

Mimi ta d’anyi jimmm kad’an , cikin sanyin murya ta furta “ Going to 20..”

“ Okay going to 20 , ita wacce kika mara kinsan shekarar ta nawa?”.

A hankali ta furta “ A’a .”

“ Zaki iya marin Baby , Farida, Abba and Saleeem?”.

Cikin sauri ta furta “ A’a Uncle
”

“ Then who give you the audacity, ki d’auki hannu ki mare ta ? Sabida tana zaune a gidan ku? Ke d’in gidan kine ko kuma akwai kud’in ki a cikin gidan ?”

Mimi tayi shiru bata ce komai ba , sai ma sunkuyar da kanta ‘kasa da tayi dan ma ta rasa abun cewa 
.

Cikin kausash shiyar murya ya furta “ Karki bari na sake miki magana ki mun shiru baki bani amsa ba .”

“ Uncle Moh ba gida na bane .” Tayi maganar cikin sar’kewar murya
. 

Shiru Moh yayi na few seconds , kafin ya kalli Aya da tayi saurin sun kuyar da kanta ‘kasa . 

“ And you !Who the hell are you Aya da zaki d’auki hannu ki mare ta ? Are you mad?
”


“ Moh Moh wallahi ba da gangan na mareta ba , rai na ne ya d’an baci , ta’ki saurara na shiyasa na mare ta amma ba da wani manufa na mareta ba .”

“ Oh really
 Mari nawa kikai mata ?”

Cikin sauri Aya ta furta “ Just 1 Moh Moh 
.”

“ And ita kuma mari nawa tayi miki ?.”

Wani irin abu ta had’iye a ma’kogwaronta tana fad’in “ 2 Moh Moh 
” cikin sar’kewar nunfashi. 

“ Good ! Now slap her back
” ya fad’a babu wasa a muryarsa. 

Cikin sauri Mimi ta kallesa idanuwanta har sun soma tara ‘kwalla, kafin ta kalli Aya da itama take kallanta .
Itama Ayan idan ka kalli hannunta zaka ga yana rawa , kamar kuma batasan abunda take shirin yi . 

Hakan ta mi’ke ta matso kusa da Mimi. 
Mimi duk a tunaninta wasa ne Aya ba zata mare ta ba kamar yadda Moh yace . 

Sai dai bata kai ‘karshe cikin zancen taba , Aya ta wanka mata mari, kamar yadda Moh yace , tayi sauri kuma ta koma wajanta ta zauna ba tare da ta kalli Mimin ba .

Dafe kuncinta Mimi tayi, tana jin kamar almara yadda Aya ta d’aga hannu ta mareta . 
Taji zafin marin da Aya tayi mata , amma zafin Moh da yasa amaretan yafi marin yi mata ciwo. 

A hankali siraran ‘kwalla suka sauko akan kuncinta, tayi sauri ta saka hannu ta goge su , tana ‘ko’karin mayar da wanda yake san sake sakko mata .

Kallan yayi sau d’aya , ya d’auke kansa kuma “ And you too Mimi , ki bata ha’kuri akan abun kikai mata.”

“ Cab d’ijan , ga mari ga tsinka jaka ? Wallahi bazan bayar ba.” Ta fad’a a cikin zuciyarta , a fili kuwa ta d’auke kai kamar bata san me yace ba, har da rantsuwarta a cikin zuciya, baza ta bata ha’kuri ba sai dai yau ya kashe ta ya huta a cikin gidan nan .

“ Baki ji abunda nace ba?” Ya d’anyi maganar a zafafe, taji tsoran maganarsa dan har hannunta sai da ya soma rawa amma taurin kai irin na Mimi ta’ki ta bud’e baki , balantana ma ta bata ha’kurin .

“ Baki ji abunda nace ba?.”

“ Uncle Moh itama fa tana da laifi ,
kuma ka sata ta rama marin da nayi mata , ha’kurin me zan bata kuma?.”


“ Ni kike fad’a ma wannan maganar? Nace ni kike fad’awa wannan maganar?”. Yadda yayi magana a zafafe sai da Mimi da Aya suka mi’ke tsaye .


Shima d’in a yanzu mi’kewa yayi yana kallan Mimi , da hannu ya nunata ya nuna kansa yana fad’in “ Ni kike kalla kike fad’a ma wannan maganar? Are you mad sa’an ki ne ni?.” 

A d’an tsorace Aya ta furta “ Please Moh Moh kayi ha’kuri , ni banasan ha’kurin ma za
”

Kallo d’aya yayi mata, ta had’iye ragowar maganar da take yi, tana ja baya , dan ko kallan face d’insa kayi kasan ba ‘katar bacı yansa yayi ba a yanzu .

Mimi kuwa kasa ce masa komai tayi, da ta bud’e baki za tayi magana sai ta fasa sabida rawan za bakinta yake faman yi . 

Idanuwansa yana kanta , amma kuma umarnin da yake bayarwa a yanzu da Aya yake . “ Bar wajan nan Aya .”

Aya daman kamar jira take , tayi saurin ficewa daga part d’in ko waiwaye batayi. 

Hakan ya ‘kara tsananin tsoran da yake cikin zuciyar Mimi , ganin su biyu ne kad’ai a cikin falon. 

A hankali ya soma ta kowa inda yake , babu shiri ta had’a hannuwanta guda biyu alamar ro’ko , tana dai dai ta maganar da take cikin bakinta nata da yake fitowa a rarrabe “ Dan Allah kayi hakuri Uncle Moh , ka dena matsowa nan wajan.”

“Oh yanzu kina da baki kenan, na d’auka kurma ce ke..”

“No ina da baki na wallahi” Tayi maganar a tsorace. Ganin yana ‘ko’karin zuwa daf da ita, tayi saurin juyawa zata sa gudu , taku biyu ya ri’ko hannunta, kuma kamu ba na wasa ba , dan sosai ta soma jin zafin ri’kon da yayi mata . 

“ Uncle Moh dan Allah ka sakar mun hannuna , da zafi zaka tsinka mun hannu na .” 

A maimakon ya saki hannun, sai ya ‘kara kamasa yadda za tafi jin zafin. Wasu hawaye ne suka soma sauko mata cikin sauri sauri mai had’e da kuka , tana ‘ko’karin ’kwace hannun nata amma kuma ta kasa , ga zafi da take ji kamar a tsakiyar karta . 

Cikin kukan ta soma fad’in “ Dan Allah Uncle Moh kayi ha’kuri bazan sake ba zanje na bata ha’kuri , dan Allah ka sakar mun hannu na , karya tsinke.” 

Yayi ya sakar mata hannun , hakan yasa da iya ‘karfinta, ta sa d’ayan hannun nata tana dukansa dashi, shi kuma da ya tashi had’a hannayen yayi ya murd’e su, wanda murd’ewan da yayi mata sai da ta saka ihu me ‘karfi sabida a zabar zafi, ga kukanta da ya ‘karu. 

Yana sakin hannun ta tsugunna a dandariyar tiles tana kuka , duka hannuwanta ta kulle face d’inta dashi , tana kuka a haka, ga tiles d’in akwai sanyi sosai sabida Ac da suke a kunne. 

Yana tsaye a kanta ganin yadda take kuka kamar wacce aka halitta dan shi, kuka take da iya ‘karfinta muryarta har ya soma ‘ko’karin disashe wa .

“ Mimi tashi daga tiles d’in nan , akwai sanyi”.

Kamar yayi magana da dutse haka Mimi ta sharesa , tana cigaba da kukan da take , kuma itan ma tana jin sanyi Tiles d’in amma ta’ki tashi a wajan .

“ Mimi 
” ya kuma ambata , amma still ta’ki kulasa, sai kuka take abunta . 

A dai dai saitin kanta ya tsuguna yana ‘ko’karin mi’kar da ita , ta ‘kwace jikinta tana kuka “ Ni ka ‘kyale ni , bayan ka gama ‘ballamun hannu tukunna zaka mun magana , ga baki d’aya kun tsane ni sabida ka kawo budurwan ka gidan. 

Toh wallahi sai na tattara kayana na bar mata gidan tunda bakwasan gani na a cikinsa.”

‘Karamun murmushine ya su’buce masa a kusa , ita kuwa Mimi sakar baki tayi tana kallansa, ganin yadda yake murmushi akan abunda yayi mata . 

Tana gani ya sake kallanta , ta kuma saka wani kukan zata bar masa wajan ya ri’ko hannunta ya d’agata ga baki d’aya ya zaunar da ita akan kujera,  shima kuma ya zauna a kan kujerar, hannunsa guda d’aya yana cikin nata ba tare da ya saki hannun ba , ya d’auko handkerchief bari me kyau sai ‘kamshi yake , ya goge mata hawayen da yake kan fuskarta da ya’ki tsayawa . 

A hankali kamar wanda bayasan magana ya furta “ Idan kika bar mana gidan kuma mu me zamuyi dashi? Tunda me gida ta bar gidan ta , muma sai mu kwashe kayan mu , mu bar gidan.”

“ Nidai ka sake ni na tafi d’aki na tunda ka rama mata .” Tayi maganar zata mi’ke tsaye , ya sake mayar da ita ya zaunar, sannan ya d’ago da ha’barta yana kallan yadda ta ‘bata fuskarta da kuka .

“ Kinga ? Ki nutsu Mimi , karki sake ‘bata mun rai yanzu nan , now zamuje part d’ina ki bawa Aya ha’kuri , and wallahi kika sake mun taurin kai , you will regret knowing me in your life 
. 


Ki ajje duk iskancin nan a gefe , and face the reality or else zaki ga abunda zanyi miki.” Bada fad’a yayi maganar ba , infact cikin soft voice yayi maganar amma kuma tana d’auke da amo a cikinsa. 

Handkerchief d’in ya mi’ka mata, babu musu ta amsa ta goge hawayan fuskarta ga baki , amma kuma ta’ki kallan inda yake . 

Haka suka mi’ke suka fito daga part d’in nan hannunsa yana cikin nata kamar irin ‘yar baby da za’a tsallako da ita titi.


Allah sarki Aya tana waje sai faman kai wa da komowa take tunda yace ya fita daga falon . 

Ganin fitowar su a tare yasa ta d’an sauke ‘karamar ajiyar zuciya, tana bin Mimi da kallo. 
Cikin su babu wanda yayi magana har suka nufi part d’in Moh, Aya kuma tana bin su a baya. 

A tsakiyar falon ya saki hannun Mimi , ya wuce sama ba tare da ya ce dasu komai ba . 

Daga Mimi har Aya d’in suna tsaye , babu wanda yayi magana a cikin su, ita Mimi ba ita take kallo ba , Aya kuma ga baki d’aya hankalinta yana kan Mimi da kallo d’aya in kayiwa face d’inta zaka gane tayi kuka . 


“ Mimi ba nazo gidan nan dan na takura miki bane, nazo gidan nan sabida ke , ina sanki kuma ina ‘kaunar ganin ki cikin farin ciki, ina miki wannan abun ne ba dan wani abu ba. 

 I can never hate you , bazan ta’ba tsanar ki ba Mimi, infact kiyi ha’kuri marin ki da nayi , idan kinaso ki rama yanzu kafun Moh Moh ya sauko, idan kuma ya tanbaye ki ko kin bani ha’kuri kawai kice masa eh , dan ni ba sai kin bani ba , kinji?”.

Banza Mimi tayi mata , ta samu waje ta zauna akan kujera ta d’an kare fuskarta  da hannunta kamar me yin bacci .

Jiki a sanyaye Aya ta zauna a kujerar da take kallan ta Mimi , tana binta da idanu, kana kallan face d’inta zaka gane kamar tana cikin damuwa.

Moh sai da ya shafe hour d’aya dai dai a sama kafin ya sauko ‘kasa, ‘kamshin turaransa ne ya soma isar da shigowar sa, kafin shi mai gayyar. 

Mimi har ta soma jin bacci , jin ‘kamshin turaren sa da taji yasa ta bud’e ido tana kallan hanyar staircase d’in da yake . 

Fararan kaya ne a jikinsa riga da wando, sai boot da yake kafarsa black colour . 

Akan kujera ya zauna , ita kuma Mimi ta mi’ke , ganin ya kalle ta , yasa ta furta “ Ruwa zan sha .” Daga nan tayi hanyar kitchen. 

Ganin ta ‘bace ma ganin su Aya tayi saurin saukowa daga kan kujera tana tsugunnawa akan gwiwowinta “ Moh Moh wallahi is not my intention, ba da gangan na mari Mimi ba , trust me ..”

“ Okay kina jira tazo ta ganki a tsugun ne ne ko me? Uhm?”.

 â€œ No Moh Moh kawai , I just
.”

“ Then get lost from here Aya
”

Hakan yasa Aya ta koma kan kujerar da take ta zauna , kamar babu wani conversation da ya shiga tsakanin su yanzu , har Mimi ta fito daga kitchen d’in da cup a hannu ta zuba ruwa half cup cikinsa . 

Tana ajje cup d’in ta kalli Aya “ Kiyi ha’kuri .” Sai ta kalli Moh “ Uncle Moh zan tafi d’aki na ..” 

“Kika bar wajan nan sai na ‘ballaki a nan wajan Mimi , samu waje ki zauna my friend.” 
Ba shiri Mimi ta zauna a kan kujera .

“Now apologies properly !”. 
‘Karamun ajiyar zuciya Mimi ta sauke “ Kiyi ha’kuri 
” ta fad’a a hankali


“ Nima kiyi ha’kuri Mimi Dan Allah .”cewar Aya . 

Mimi bata yi magana ba , Moh ya kalleta tare da fad’in “ You can go now .” 

Babu musu ta tashi ta fita daga cikin falon , shi kuma ya mi’ke tsaye zai bar wajan , Aya tayi saurin mi’kewa tana fad’in “ Dan Allah ka saurareni Moh Moh wallahi ba dagan gan
.” 

Tasss taji saukar mari a kuncinta , babu shiri Aya ta dafe kumatun tana had’iye ragowar maganar da take bakin ki. 

“ Wannan akan marin fuskarta da kikai , yadda kika ‘bata komai da kanki kije ki gyara komai , kwana biyu kawai na baki , wannan ya zama karo na farko kuma da ‘karshe da zanga tabon hannun ki , ko wani abu a jikin Mimi 
.

Becareful 
.” Ta fad’a a tsawar ce . 

Kanta ta jinjina masa , alamar toh amma har lokacin hannunta yana dafe da kuncinta dan ba ‘karamun shigarta marin yayi ba . 

Da hannu yayi mata alama da ta fice masa daga part. 
Babu shiri itama ta fita daga part d’in ko wai waye bata yi . 


_*********

Mimi tana fita , d’akinta ta wuce kai tsaye , dan babu wanda yakesan yiwa magana ma a wannan lokacin . 

Tana duba wayarta sai ta missed call kusan guda 12 . 
‘Daya daga Uncle Abba , d’aya na Uncle Saleem , d’aya na Sadiq sai guda d’aya na Shukura kuma . Ragowar missed call d’in guda biyar na Zarah sai uku na Ameerah , babu wanda tabi kiransa , taja ‘karamun tsaki tana ajje wayar . 

A gaban madubi ta tsaya tana kallan shatin gefen da Aya ta mareta d’azu , da kuma ha’kurin da Moh ya sa ta bayar , duk da Cewar itama Aya d’in ta bata ha’kuri amma kuma sai take ji , ha’kurin bai yi mata ba sabida duka laifinta ne , da bata had’ata da family d’inta ba ko ta takura mata da duk Hakan bata faru ba . 

Tana tsakiya da kallan fuskar nata a gaban madubi ta tsinkayi muryar Joy a bayanta “ Kallan fuskar ya isa haka Mimi, kin tsaya a gaban madubi sai kallan fuskarki kike , me kike sa’kawa a cikin zuciya ?”.


“ Bakomai.” Shine kad’ai abunda Mimi ta furta , dan har Joy d’in yau batasan magana da ita. 
Joy kuma ta fahimci hakan, amaimakon ta barta a cikin d’akin ganin tana cikin damuwa, sai ta ja hannunta zuwa kan gado tana zaunar da ita , sannan ta saka hannu ta shafa marin da Aya tayi mata . 

“ Mimi me yasa kike da saurin hannu ne haka? Gashi kin janyo ran kowa ya ‘baci akan ki, yaushe zaki koyi danna zuciyar ki?”

“Joy kema abunda zaki ce mun kenan ? Ga baki d’aya kun fi supporting Aya akai na kenan? Idan har ita kukeso , me yasa ba zaku je wajanta ba kuke zuwa waje na ? Mai nayi musu da zaku tsane ni ga baki d’ayan ku daga zuwanta?.”


“ Sai kinyi ha’kuri Mimi, wani abun baya bu’katar bayanı, wani abun mutum da kansa yake ganowa bawai a ganar dashi ba . 

Lokaci yayi da zaki tsaya da kanki, kısan me kike , kisan abunda kike so da wanda ba kyaso bawai duk maganar da ta fito miki daga baki zaki fad’a ba . 

Wata maganar taunata ake a baki , a yar da nayarwa kafin a fito da na fitowa 
.

Ki d’auki maganar Moh kamar yadda ya fad’a miki face the reality Mimi, ki fito daga cikin duniyar tunanin da kika shiga , kisan abunda ya kama ce ki da ke , kinji ni ko?”.



‘Karamar ajiyar zuciya ta sauke , tana jin relief kad’an a ‘kasan zuciyarta kafin ta kalli Joy da itama take kallanta “ Yanzu Joy a cikin abun da nayi mene ne laifi na a ciki?.”

“ Kina da laifi mana Mimi, babu yadda za’ayi ki d’aga hannu ki mari Aya , wacce ta baki shekaru masu tazara . 

Kamar misali yanzu idan har ba zaki iya marin Baby ba , to babu yadda za’ayi ki mari Aya . 

Ko sabida bata da kowa anan shiyasa kike ganin abunda kikai dai dai ne ?.

Idan yau keçe a cikin yanayin da take ci zaki ji dad’i?. 

Ko so kike ki gina mata tabon da ba zata ta’ba mantawa ba sabida tazo gidan nan?

Wai ma na tanbaye ki Mimi mene ne asalin abunda Aya tayi miki kike faman d’aga jijiyar wuya ? 

Sabida Moh ya kawota gidan nan ? Toh gidan ki ne ? Ko yau idan yace zai aure ta zaki hanashi auran ta?. 

Ba zaki hana ba Mimi, idan yace yana santa babu abunda zaki iya yi dole ki girmamata kamar yadda kike girmama Uncle d’in ki. 

Ai abun alfahari ne ace Uncle d’in ki ya kawo wani cikin ku, kuma ku girmamasa kamar yadda zaku girmama Uncle d’in naku. 

Amma yanzu kinsan me kike nunawa ?” Ta dakata da maganar da take tana kallan Mimi da ta nutsu tana saurararta . 

Girgiza mata kai Mimi tayi alamar a’a , hakan yasa Joy ta cigaba 
“ Kin nuna cewa bakya respecting d’insa , kuma ko nan gaba ya kawo wani cikin gidan nan ba zakiyi respecting d’insa ba tunda bai isa ya saki abu ba , sai kinyi taurin kai , kin nuna babu wanda ya isa ya saki abu ko kuma ya hanaki, wannan rayuwar kike so ki ‘bullowa kan ki?. 

Kinsan wace ce ke kuwa? Mene ne yau dan wani yazo yaci arzi’kinka Mimi?.

Tabbas Mimi ki zauna kiyi tunani, ki gyara abunda kika gyara kafin komai yazo ya dame ki. 

Kije ki bawa Moh ha’kuri , ki bawa Mamy hakuri , sannan ki bawa Aya ha’kuri , duk cikin su babu sa’an ki , dan haka dole ki girmamasu kuma ki daraja su , idan ba haka ba zaki zo kina da na sani , a lokacin da dana sani bazai ta’ba yi miki komai ba Mimi.”da haka Joy ta ‘bace daga d’akin ba tare da ta bawa Mimi damar sake yi mata magana ba . 

‘Dan shiru Mimi tayi tana nazarin abunda Joy ta fad’a mata , da irin gardamar da tayiwa Moh , da kuma abunda ya had’asu da Aya , har zuwa yanzu da tasan Mamy ma tana fushi da ita . 

Sosai ta zauna tana tunani, har ta bawa kanta laifi, sai dai ta rasa ta yadda za’ai ta gyara abunda tayi , dan tasan tabbas shima Moh ransa a ‘bace yake a wannan lokacin kuma batasan yadda za’ai tayi masa magana ba har ya ha’kura . 

Tana cikin wannan tunanin ne aka ‘Kwan’kwasa ‘kofar d’akin sau biyu, a tunaninta Zarah ce , shiyasa ta nufi ‘kofar babu ‘bata lokaci tana bud’ewa , tana fad’in “ Zarah sai yanzu?.”

Ganin Aya a bakın ‘kofar yasa ta d’anyi sororo fuskarta cike da mamakin ganinta . 

Murmushi Aya ta sakar mata tana d’an nuna d’akin da idanuwanta “ Zan iya shigowa ?.” A hankali Mimi ta jinjina mata kanta, tana matsawa a hankali tare da bata hanyar shigowar . 

Wani murmushi Aya ta kumayi , tana shigowa d’akin. 
Binta da kallo Mimi tayi ganin ta zauna akan gefen gadon , tayi wa Mimi nuni da hannu akan itama ta zauna d’in. 

Still Mimi bata yi mata musu ba ta samu waje ta zauna amma kuma bata ce komai ba . 

Ajiyar zuciya Aya ta sauke tana facing Mimi da itama take kallanta .

“ Let’s talk now Mimi ! Naga kina mun kallo kamar wacce take san takura miki, ko kuma take ‘ko’karin dakatar dake akan abu. 

Banso haka ala’kata da ke ta kasance ba Mimi, but yes na yadda kuma nice na kai ki bango , but ki dinga controlling temper d’in ki, ki koya yadda ake danne fishi , da kuma yadda ake nunawa a lokacin da ya kamata . 

Ki koyi iya magana , ki koyi yadda zakiyi shiru akan wasu abubuwa. 

Ba komai idan akayi miki ba zaki ce zaki tanka , wani abun shiru ne ya kamata . 

A d’an saninki da nayi na ‘yan kwanakin nan na gane kina da saurin tunzura Mimi , kina da saurin fushi, kina saka tunanikan da ba haka suke ba a cikin zuciyar ki. 

Idan kina san sanin abu, ki bud’e baki ki fad’a da confidence d’in ki bawai ki dinga sakashi a zuciya ba . 

Yeah I admit , duk abubuwan da nayi miki ina sane nake yi miki su sabida naga halayen ki. 

Ki dena nunawa kamar kowa baya ‘kaunar ko ni ake so , wace ce ni? Duka yaushe nazo gidan na , kinsan wace ce ke ? Kinsan wane ne Moh Moh? A duniya babu mai yi masa musu kamar ke , babu mai saka shi doguwar magana kamar ke , kinsan sabida me ? Sabida ke d’in amana ce a wajan sa , al’kawari ne kuma a wajansa dan haka ki zama me kula akan abubuwa da yawa , bawai akan abu kad’an ba , ki koyi mu’alama sosai akan kowa da kowa , kuma kisan yadda zaki tafiyar da kowa ba tare da kin ‘bata ma kowa ba. 


Kiyi ha’kuri , kiyi ha’kuri , kiyi ha’kuri akan abunda nayi miki, and yes ki bawa Moh ha’kuri shima dan bazai ta’ba yafe mun marin da nayi miki ba idan har bake ce kika fad’a da kanki cewa kin yafe ba .

I have to go now .” Ta mi’ke tsaye . 
Itama Mimin mi’kewa tsaye tayi tana kallan Aya , cikin sanyin murya ta furta “ Wace ce ke?”

Hannunta Aya ta ri’ko tana murmushi kad’an , idan ka kalli idanuwanta zaka ga alamar taruwar ‘kwalla da suka kwanta a ciki . Cikin kulawa da taushin murya ta furta “ I promise you , zan fad’a miki amma ki bani sometime , kuma abunda kike tunani tsakani na da Moh ba haka bane , infact babu aure kwata kwata tsakani na dashi.” Da haka Aya tayi hugging Mimi ba tare da ta bata damar yin magana ba , kuma ta goge ‘kwallar da take idanuwanta ba tare da ta bari Mimi ta gan su ba , ya kuma fice daga cikin d’akin ta bar Mimi da sanyayan jiki. 

Lokaci d’aya Mimi taji nadamar abunda tayiwa Aya ya lullu’beta , wani irin warm kuma ya sake lullu’beta musamman lokacin da Aya tayi hugging d’inta . 

Duk wani ‘bacin ranta ya tafi ga baki d’aya ya maye gurbi da soyayyar Aya da ya shiga zuciyarta farat d’aya . 

Kwantawa tayi akan gado tana fad’in “ Ya Allahu yanzu ya zanyi na bata ha’kuri
?”.

**** Ragowar wunin ranar haka ya bar bar ‘bangarori da dama da tunanin abubuwa mabanbanta ciki kuma har da Mimi. 

Sai ‘karfe 3 da kusan kwata Mimi ta fito daga d’akinta , lokacin yunwar da take dannewa ta soma cin ‘karfinta , shiyasa tayi wanka shaf shaf ta sauko ‘kasa , tana san zuwa part d’in Mamy amma kuma batasan me zata tarar ba idan taje can d’in ba . 

Kitchen ta shiga ta tarar da an riga anyi abinci , suna cikin warmers , a plate d’aya ta zuba fried rice , da kuma dou-dou ( Dou- Dou mixed of plaintain ne da kuma nama da ake yankawa ‘kanana asaka musu pepper da maggi bayan an soya kamar sauce d’in plaintain da Nama yake .” Sai ta samu bowl ga zuba coslow d’inta a ciki , da kuma natural juice me sanyi a cup. Ta saka su a d’an tray ta fito daga kitchen zuwa living room. 

Akan carfet ta ajje komai, itama ta zauna a nan d’in tana cin abincin ta ahankali a hankali , har ta gama ta mayar dashi sauran kitchen babu wanda ya shigo . 
Sai da ta bari cikinta ya d’an lafa tukunna ta nufi part d’in Mamy . 

Mamy na zaune a kan kujera, ta saka plate d’in fruit a gabanta da yake a yayyanke tana sha, ga kuma sunna TV da take kalla. 

Shigowar Mimi ne yasa ta amsa sallamar nata amma kuma fuska a had’e, ta mayar da kallanta kan fruit d’inta da kuma kallan da take . 

Mimi tazo zata zauna a kujerar da Mamy take , Mamy tayi saurin dakatar da ita “ Kada ki kuskura na ganki a kusa dani, ki samu waje can ki zauna, amma kada na ganki
anan wajan.”

‘Dan marairaice mata murya Mimi tayi “ Haba Mamy kiyi ha’kuri mana , duba kiga fuska na ta rama marin da kika ce fa.”

“ Tamun dai dai ai , da bata rama ba ni da kai na zanzo na wawwanka miki marin ai Sha sha sha”. 

“ Yanzu Mamy idan aka ce ki mare da gaske marin nawa zaki yi Mimi ce fa?”. 

‘Dagowa Mamy tayi tana kallanta “ Wace ce ke d’in da baza’a mara ba ? Kika bari na ri’ke ki yanzu sai kin gane kuren ki tunda ke bakya jin maganar kowa sai abunda kika ga dama kike yi.”


“ Mamy toh dan Allah kiyi ha’kuri kar kice zakiyi fushi dani, kinji Mamy na please
” ta kuma marairaice fuska .

Harararta Mamy tayi “ ai kin fi kowa sanin wanda kikai wa laifi dan haka bani zaki bawa ha’kuri ba wacce kikai wa laifi zaki bawa ha’kuri idan kuma shima kin fi ‘karfin bada ha’kurin ne toh .” 

“ Mamy zan bata ha’kuri amma kema kiyi ha’kuri kinsan dai ina jin maganar ki ko?.”


“ Karki wani zo ki cika ni da surutu, idan kin gama fad’an abunda zaki fad’a ki fice mun daga waje , kina raba mun hankali akan abun da nake.”

“ MAMY
..”

“ Mimi tashi ki fice mun daga nan wajan kafin na sassa’ba miki. 
Idan kuma ba zaki iya tashi daga nan d’in ba ni sai na bar miki shi.”

“ No Mamy zan tashi
” cewar Mimin. 
Haka ta fita tana tafiya a hankali ko Mamyn zata dakatar da ita , amma har ta fice Mamy ko waiwayonta ba tayi ba shiyasa taji babu dad’i a ranta.  

****Tana ‘ko’karin hawa stairs taji sallamar Ameerah da Mimi, hakan yasa ta dakata tana waiwayowa wajan su. 

“ Ladies sai yanzu ake ganin ku?” Tayi maganar tana d’an kashe musu ido guda d’aya duk dan ta’boye abunda yake ranta. 

“ Ai babu abunda zaki ce mana , Kusan 3 missed call nayi miki baki d’aya ba , da zanzo sai nayi fushi amma kalle ni nan , gashi nan nazo wajan da kike .” Cewar Ameerah. 

Murmushi Mimi tayi mata tare da ‘karasowa wajanta tana d’an bata side hug “ Sorry Ameerah , ba dagangan nayi ba . My apologies please.” 

“ Kinci sa’a na ha’kuri.” Cewar Ameerah . 

Kallan Zarah , Mimi tayi , ganin yadda take d’auke kanta “ Mene ne kuma kike faman d’auke kanki?
Kema am sorry hakanan kusan ba zan ‘ki d’aga kiran ku ba ko ? Chills girl, kuzo mu zauna duk mun tsaya a tsaye kamar wasu sojiji.”

“Ai dole zaki ce mana Cills mana Mimi, Kira biyar nayi miki babu wanda kika d’aga har cewa Ameerah nayi ta kira ki , itama tace bata same ki ba , ko ‘yan wula’kancin suna kusa ne ?.”

“ Wana irin wula’kanci kuma Zarah ? Ai Kyamun uzuri yaushe raban da ki kirani ban d’aga kiran ki ba ? Yanzu ma kika sani ko wani dalilin ne yasa ban d’aga kiran naku ba?”.

“ Babu wani dalili da zai hana ki’ki d’aukar wayar mu sai dai kawai bakiyi niya ba , amma wana aiki kike apart from sleep , da cin abinci da kallan reels a waya , me kike har da ba zaki iya d’aukar calls d’in mu ba .”

“ Toh uwata Zarah , me kike so nace miki yanzu tunda kin riga kin yanke hukunci ?”.

“ Aaah mai da wu’kar Mimi bata kai da haka ba , so how far me ke going ?”.

“ Komai normal normal babu wani update 
” 

Tasowa Ameerah tayi daga kujerar da take , ta zauna a kusa da Mimi tana yin ‘kasa ‘kasa da murya “ Mimi wai wace ce jiya wanda Ameerah tace tazo ta tafi da ke da ‘karfi ? Da gaske ne ko dai wasa ne? Who is she?.” 

“ Kai Ameerah , gulma babu kyau .”

“ Babu wani gulma da nayi beside ni bansan wani friend d’inki da take sa kayan maza ma and Zarah tace kamar ba ‘yar nan bace , who is she please Mimi, wallahi ita nazo gani part d’in nan.”

“ Okay ba ni kika zo gani ba kenan?” Sai ta kalli Zarah “ Zarah maza maza fitar mun da wannan daga wajan nan .” 

“ Toh ai kusan tafiyar mu d’aya dan nima ita d’in nazo tanbayar ki Mimi, abun ya bani mamaki yadda jiya ta wani ja hannun ki ta fito dake daga part d’in mu , naso bin ku Mommy ta hanani , gashi ta ‘ki tsayawa tayi Hausa sai wani turanci take wa mutane kamar ance mata bama jin turancin.”


“ Uhm bata iya hausan bane shiyasa kika ga ta miki turancin ai , ko kinga ta miki kama da Hausa people like us?” Cewar Mimi.

“ Please Mimi mana wallahi am serious wace ce wannan ?  Iya sani na baki da friend irin wannan sai jiya unexpected da naga wannan ko daman kina da wasu friend ne bakya so mu sani?” Kafin Mimi ta bata amsa Ameerah ta rigaka .

“ Kinji ki da wani magana Zarah , daman dole sai kinsa duka friends d’inta ne ? Ke wane ne yasan friends d’inki ga baki d’aya ? Dole akwai wasu da aka sani akwai kuma wanda ba’a sani ba , toh kamar haka ne fa..”

“ No Ameerah kima dena had’ani da wannan misalin amma koma dai mene ne ya kamata nima nasan friend d’in da za tayi ko?”

“ Sabida wacece ke?” Cewar Ameerah tana kallanta baki asakake. 

Daman kuma Ameerah ba kanwar lasa bace kamar jira take , ta mayar da martani shiyasa tayi saurin mayar wa da Zarah martanin maganar da take ji me kama da wasan yara. 

“ Kunga abun duk ba na tashin tashin bane” cewar Mimi kafin ta cigaba da magana “ I think zan iya yin ‘kawance da duk wanda nake so ba wani babban abu bane and you Zarah kinsan ba dole bane ace idan zanyi friends sai na sanar da ke ba kema fa kina da wad’an da kika sani which I don’t know about
”


“ Tell her dai” cewar Ameerah. 

“ Yanzu dan na tanbaye ku wace ce shine kuke ‘ko’karin ku had’e mun kai? Mimi yanzu mene ne dan na tanbaye ki wace ce ita what are friends for ?”

“ Na yadda what are friends for , amma ai kuna cikin gidan zaku dinga ganin koda yaushe .”

“Kamar ya” cewar Zarah. 

“ Yeah tana cikin gidan nan ai , infact d’aki na ma yana kusa da nata koma wace ce zaku dinga ganin har ku gaji ma 
. Babu bu’katar sauri.”

“ Yanzu Mimi har friends d’inki kike kawowa cikin gidan nan da zummar kwana ? Yaushe kika soma haka wai kuma a kusa da d’akin ki. Toh Yaushe zata tafi?.”

Hannu biyu Mimi ta bud’ewa Zarah kafin ta furta “ Nima ban sani ba.”

“ Kamar ya baki sani ma , ki kawo ba’kuwa cikin gidan nan kuma kice baki san lokacin tafiyarta ba ?.” Yanzu Ameerah ce tayi magana.

Duka hannaye  Mimi ta d’aga musu “ Look ladies wad’an nan tanbayoyin naku sunyi yawa , kamar masu karantar journalist ? Let me be clear please bawai ‘kawa ta bace , and beside bani ce na kawo ta cikin gidan nan ba Uncle Moh ne ya kawo ta kuma yace zata zauna a cikin gidan nan so duk me wani dogon tanbaya I think bani ya kamata kuyi ba , it’s either Uncle Moh ko kuma ita , hope I make it clear for you now?”.


Lokaci d’aya suka had’a baki wajan fad’in “ UNCLE MOH?
..”.


_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***



***