The Unwanted Daughter

Page 18: The call that changed the plan

by @hauwajaywrites

Wayar ta yi ringing na kusan seconds talatin da ɗaya kafin ta yanke. Yarinyar ta ɗago kai ta kalli Dada, sannan ta ce

“Dada, yanzu ma wayan har ya yanke bai ɗauka ba”

Dada ta yi murmushi, ta ɗan gyara zamanta “Ki ƙyale shi, ai ya san ya yi min laifi ne, ba zai iya ɗauka ba ai”

Ba su gama maganar ba sai ga wayar ta fara ringing, Dada ta kalli wayar, sannan ta kalli yarinyar “Duba, ko dai shi ne?”

“Eh, shine Dada”

“Allah sarki Ɗan albarka, nasan baya kusa ne shi ya sa bai ɗauka ba”

Ta karɓi wayar, sannan ta sa a hands-free ta miƙa wa Dada, daga ɗayan ɓangaren aka ji muryarsa cike take da fara’a “Assalamu Alaikum, Dada na”

Dada ta ɗan harari wayar, kamar wanda ya samu damar faɗa masa duk abin da ke ranta “Sai da na kira sannan za ka san da ni? In ce ka manta da kakarka ko Ayman? Yanzu har za ka zo kasan nan amma ka gagara zuwa ganina, sai dai in ji labarin komawarka ko? Halan ma shekarun da ka saba yi a can ma za ka yi. Toh ai yayi muku kyau, kai da iyayen naka”

Muryarsa ta fito da dariya a hankali
“Calm down Dada na, Kin san ba za ki ce ban kira ki ba, kuma kin san ban da kamarki. Toh Hajiya, ko hutawa ban yi ba, Abba ya tura ni in duba wani abu a ƙasar waje, amma har na sa ranar da zan zo Kaduna gurinki fa. Na kusa zuwa ƙasar, ina zuwa Kaduna zan zo na ɗan huta a gurinki”

Dada ta yi dariya “Ayyo, toh ai na ɗauka mantani ka yi ai”

“Na’isa ni Aymanu” Dukansu suka yi dariya, sannan suka ci gaba da hirarsu ta kaka da jika

A wani bangaren, wata mata na kwance a kan Italian bed ɗinta, idonta ya tsaya kan ceiling yayin da tunani iri-iri ke ta yawo a zuciyarta

Anya ba zan ɗauki hutu daga aiki ba kuwa?

Tana missing home sosai. Ba wai akwai mutane da yawa da take kewarsu ba, amma aƙalla tana da only brother ɗinta, her only biological blood, da kuma iyalinsa. Jininsu kwata-kwata bai hadu da na waccan muguwar Zahra ba

Amma yarinyar nan fa? Wataƙila she’s trying to hurt herself again 

Tunani ne ya yi ta zagaye kanta har sai da wayarta ta fara ringing. Ta miƙa hannu ta ɗauka, amma da ta ga unknown caller da country code ɗin +234, ta ɗan tsaya

Definitely family, kenan suna missing ɗinta ma Murmushi ya bayyana a fuskarta kafin ta ɗaga wayar “Hello?”

A gefe guda, Ummi na zaune ita kaɗai, zuciyarta cike da tunani iri-iri. Tun da ta yanke shawarar kiran Hibbah, take ta ƙoƙarin samun ƙarfin guiwar yin hakan

Hibbah mace ce mai kirki, Mai mutunci, Mai ladabi. Mai sauƙin kai. Tun tana raye, Aneesa ta kasance mai kirki a gare ta. Yanzu kuma lokaci ya yi da za ta biya wannan alherin

Lokaci ya yi da ita ma za ta taimaki Dua ko me zai faru, ko da menene ta riga ta yanke shawara, kuma babu ja da baya

Da ma Allah ya sa an ɗaga tafiyar daga yau zuwa gobe. Da yanzu ta makara, amma har yanzu akwai lokacin da za ta yi wani abu

Ta danna number Hibbah, zuciyarta na bugawa. Tana Allah-Allah ta ɗaga, saboda ba ta san ko za ta ɗauki unknown caller ba, dan bata santa da wannan layin ba

Sai ga shi an ɗaga “Assalamu Alaikum” Wata irin nutsuwa ta sauka a zuciyar Ummi

“Waalaikumus Salam Hibbah, nasan baki gane mai magana ba ko? To, it’s Hajiya Abidah, matar abokin yayanki, Alhaji Tukur, baki da wannan layin nawa ne”

“Ahhh, ohh yeah! Allah sarki, ya everyone?”

“Well, fine Alhamdulillah”

Suka ɗan yi hira na ɗan lokaci kafin Ummi ta shiga kan abin da ya kawo ta
“Hibbah, I have some observation akan gidan yayanki, Banda korafin baya yanzu ma gani”

Hibbah ta ɗan yi shiru
“Okay, I’m all ears. What happened? What that devil did again?”

Ummi ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta fara ba ta labarin duk abin da ta lura da shi tun lokacin da ta fara ganin yadda ake mu’amala da Dua Duk dai wata Abu daya boye mata a baya yau dai ta mata filla filla

Ta gaya mata yadda yarinyar take rayuwa cikin tsoro, yadda take yin kusan dukkan ayyukan gidan, yadda ake nuna mata bambanci

Hibbah ta saurare ta ba tare da ta katse ta ba

A wannan lokacin Ayesha ta shigo gidan kai tsaye. Ba tare da ta ɓata lokaci ba, ta nufi ɗakin su Dua

Da ta shiga, sai suka yi four eyes da Amrah, Amrah ta harare ta

Ayesha ma ta mayar mata da kallon kafin ta nufi gefen gadon Dua ta zauna

Ba da daɗewa ba Dua ta fito daga bathroom, jikinta har yanzu da ɗan ruwa, da ta ga Ayesha, fuskarta ta haska da murmushi, ta nufi wajenta suka rungume juna

“Welcome friend, I thought ba zan ganki ba sai bayan mun dawo Kaduna. Ashe za ki zo?”

Ayesha ta ɗan daure fuska“Wani Kaduna kuma?”, Dua ta kalle ta “Wacce dai kika sani”

Ayesha ta ɗan juya ta kalli ɓangaren da Amrah take, sannan ta mayar da kallonta kan Dua

“Dua, don’t tell me kin zaɓi tafiya yawo akan musabaqar ki. Don’t tell me baki gaya wa iyayen ki kina da musabaqa ba, because I guess ba wanda zai zaɓawa ’ya’yansa zuwa yawo akan karatu”

Dua ta yi saurin ɗaukar wayar Ayesha. Ta shiga notes ta rubuta mata abin da take son faɗa mata, sannan ta miƙa mata wayar

Ayesha ta karanta ‘sun ƙi barina sun ce I must go to Kaduna, which I can’t say no. Kuma tafiyar gobe ne. And please stop that habaici habaici, cos at the end ni za ki sa a ciki’

Ayesha ta tabe baki “Mtsww, heartless people”

Dua ta juya ta kalle ta “And so?”

Amrah kuwa tana can tana ta yin habaici, amma babu wanda ya kula ta

Ayesha ta sake kallon Dua
“Yauwa Dua, dama I’m here to ask you akan wancan maganar scholarship ɗin nan. An bar ki ne za ki je?”

Dua ta yi mata kallon da ta saba yi mata
“You always know the answer, which is always NO”

Sai suka ji Amrah ta fashe da dariya daga can, amma babu wanda ya kula ta

Ayesha ta ci gaba
“So, sun ce we’re going maybe next week. I wish harda ke ma”

Suka ɗan yi hira kafin Ayesha ta miƙe “Tashi ki rakani”

Suka fita daga ɗakin tare, da suka fita wajen gate, Ayesha ta hango wata mota

“Ga motar fa, za ki rakani ne, ba wai kin tsaya anan ba”

Dua ta yi tsaki “Mtsww, always problem”

Ayesha ta yi dariya “Oho dai, indai za ki rakani”

Suna isa wajen motar, sai aka buɗe ƙofar gaba, da Dua ta ga wanda ke zaune a ciki, sai ta sake baki

Ahmad ne, sai Haidar ma ya buɗe ɗayan ƙofar, ya zagayo ya nufe su

Dua ta kalle shi da mamaki
“Haidar, is that you? Allah sarki, I so much miss you dude, musamman in muna musu”

Haidar ya fashe da dariya, Ahmad ma ya yi murmushi. Nan dukansu suka yi dariya tare

Dua ta gaishe da Ya Ahmad, shi kuma ya amsa mata “Mun zo miki sallama ne, tunda za ki Kaduna”

Dua ta juya ta kalli Ayesha. Ita kuma ta ɗaga mata kafaɗa kamar wadda ba ta san komai ba

Suka ɗan yi hira kafin Dua ta ce za ta koma gida saboda tana jin ta not comfortable sosai saboda Ya Ahmad yana wajen. Duk da haka, a ranta tana jin daɗin kasancewarsu

Ahmad ya kalle ta “Okay, but before then, ban number ɗin da zan same ki, just to check on you”

Dua ta girgiza kai “Like I said before, banda waya, kuma ban san nawa zan baka ba”

“Your sister fa”

“Never! Ko na bayar, zai zama laifi”

Ahmad ya yi shiru na ɗan lokaci
“Toh yanzu haka za ki Kaduna babu yadda za a san kina Lafiya or not?”

Dua ta yi murmushi kaɗan
“At least you care, and care matters, Thank you for that”

Ta juya za ta koma, amma kafin ta tafi ta kalli Haidar “Safe flight when the day comes”

Suka yi sallama, sannan Dua ta koma gida, har ta kai bakin gate ɗinsu, sai ta ji muryar Ayesha daga bayanta “Dua, can’t you wait for me?”

Ayesha ta juya tana ƙoƙarin ɓoye dariyar da ta fara ji. Da suka haɗa ido, Ayesha ta kasa controlling kanta, sai dariya ta ɓarke daga bakinta

Dua kuwa haushi ya fara kamata. Ta kalli Ayesha har sai da dariyar ta lafa

“Finally”

Dua ta ɗaga gira “Finally what? Wait, ya aka yi kika san su ne a motar? And how did he know I’m travelling to Kaduna?”

Ayesha ta gyara tsayuwarta tana dariya

“Dua, your first question, ya aka yi nasan su ne a wajen? Tare muka zo. Haidar ya kawo shi gidanmu, sai ya tambaya ko za ki Germany ne ko a’a, tunda an yi fixing date. I replied him for now dai no, kuma na ba shi labarin komai. Sai ya ce bari mu zo mu gan ki. Bayan mun zo kofar gidanku ne ya ba ni number ɗinsa, ya ce if yes I should text him. Ni kuma na text him no, kuma Kaduna za ki. That’s all. Shi ya sa yasan da wannan”

Ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da murmushi “Dua, like I said before, wallahi Ya Ahmad yana sonki. Just believe me”

Dua ta yi tsaki “Ni kam ban son wannan shirmen naki. You always know one thing, and that thing for sure is love. Shi kenan, ba ki da aiki”

Ayesha ta yi dariya
“Joke apart, kin san da ya zo gidanmu ina kan gaya masa halin da kike ciki. And I saw his white eyes turn red. I believe yaji zafin abin da ake miki ne. Kuma kinga ai he’s handsome enough, young rich guy. Ohh Dua, can’t wait for this match. Kinga za ki huta da wannan muguwar so-called Mummy, mtsww”

Dua ta kalle ta da haushi
“Please it’s okay, Good bye then”

Ta juya ta wuce, tana jin Ayesha na ci gaba da magana a bayanta, amma ta share ta

A ranta, abin da ya fi bata mata rai shi ne yadda Ayesha ta gaya wa wani halin da take ciki, Me ya sa Ayesha za ta faɗa wa wani irin wannan abu?

A ɗayan ɓangaren, Mummy tana karɓar kuɗin da za ta yi wa cousins ɗinta tsaraba daga wajen Daddy, sai wayarsa ta fara ringing.

Daddy ya kalli wayar “Dear, mikomin wayar, Who is that calling?”

Mummy ta ɗauki wayar, amma da ta kalli screen ɗin sai ta ga sunan ‘My Only Blood’

Ta yi tsaki wannan yar’uwar taka, so-called Hibbah ko mene oho

A ranta ta fara tunani ‘Me ta zo da shi yau? Hope ba za ta san maganar tafiyarsu Dua Kaduna ba

Daddy ya karɓi wayar, kuma da zarar ya ji muryar Hibbah, wani irin farin ciki ya bayyana a fuskarsa

Suka gaisa, ya tambayi lafiyar family ɗinta, suka ɗan yi hira kafin Hibbah ta tambaye shi
“Yaya, ina yaran nawa suke ne?”

“Aryan ya raka Sultan unguwa. Duk da ba a san ko sultan ɗin ke ja shi yawo ba, amma ai suna tare. Amrah kuma tana ɗakinsu. Gobe ma za su tafi Kaduna hutu”

Hibbah ta yi shiru na ɗan lokaci “What?”

Daddy ya ɗan yi dariya
“Ai gidansu Zahra za su je. Kinga bakomai, ai tinda wajen kakansu za su je”

“Amrah alone or and Dua?”

“Two, both”

Hibbah ta sauya murya
“Yaya, just send Amrah alone, ka bar Dua, ko kuma duk su biyun su fasa zuwa”

Daddy ya daure fuska “Why?”

“That’s what I want. In har dai ni kanwarka ce, kuma ka yarda ’ya’yanka nawa ne”

Daddy ya sauke ajiyar zuciya
“And Zahra wouldn’t be happy”

Hibbah ta amsa nan take
“And so? Kai ka san ba su son Dua. In har ranta zai baci saboda hakan, then send Amrah alone”

“Hibbah, stop that”

“Sure. Na faɗa maka view dina, and I’m coming back home soon. Make sure zan samu Dua a gida”

Daddy ya ɗan yi shiru kafin ya ce
“Hibbah, don’t try me what’s your problem with that teenager?”

Hibbah ta cije leɓenta, sannan ta amsa cikin fushi
“Because of your selfishness…”

Sai ta yi shiru na ɗan lokaci, saboda ranta ya fara baci “Bye Yaya, See you soon”

Ta kashe wayar.