Episode 1
BABI NA FARKO — Lallen Amarya
Auren Saida ya kusa. Gidan Alhaji Bakir ya cika da hayaniya tun safe. Mata suna kai-komo, wasu suna shirya abinci, wasu kuma suna taimakawa wajen gyaran kayan amarya. Dariyar ‘yan uwa da kawayenta ta cika gidan, yayin da ƙamshin turaren wuta ke yawo a ko’ina.
A cikin ɗakin Saida kuwa, komai ya yi shiru fiye da sauran gidan. Saida na zaune a gefen gadonta, hannayenta biyu shimfiɗe a gabanta, tana kallon lallen da aka yi mata.
Zahida tana zaune kusa da ita, yayin da Aisha ke tsaye a gabansu, ta sunkuya tana kallon hannun Saida sosai.
“Kaiii!” Zahida ta furta, ta kama hannun Saida a hankali. “Wallahi lallen nan ya yi kyau sosai!”
Aisha ta matsa kusa.
“Lallen nan na yayye!” ta faɗa cikin dariya. “Saida, yau kam kin zama amarya ta gaske.”
Saida ta yi murmushi, ta sunkuyar da kanta.
“Ku daina mana…”
“Mu daina me?” Zahida ta yi dariya. “Ai gaskiya muke faɗa.”
Aisha ta zauna a gefen gadon.
“Amma gaskiya, Saida, har yanzu ban yarda za ki yi aure ba.”
Saida ta ɗago kai ta kalle ta.
“Me ya sa?”
“Saboda kin yi shiru kamar ba ke za a aura ba,” Aisha ta amsa. “Duk da wannan lallen, kina nan kamar wadda aka kawo mata labarin auren wata.”
Zahida ta fashe da dariya.
“Wallahi kuwa! Tun da aka fara maganar auren nan, ban taɓa ganin Saida ta zauna ta yi mana cikakken bayani ba.”
Saida ta sake kallon hannayenta.
“Me zan ce?”
“Za ki ce mana yadda kike ji,” Zahida ta amsa.
Saida ta yi shiru.
Tambayar ta shiga zuciyarta fiye da yadda kawayenta suka sani.
Yaya nake ji?
Gaskiya ita ma ba ta san amsar ba.
Aure ba sabon abu ba ne a gidansu. Ta ga yayyenta da ‘yan uwanta suna yin aure, ta ga yadda mata ke barin gidansu su fara sabuwar rayuwa.
Amma ita kanta… yanzu ne komai ya fara zama na gaske.
Ta taɓa yin mafarkin aure sau da yawa tun tana yarinya. Ba wai tana neman dukiya ba. Abin da ta fi so shi ne ta samu miji mai kirki. Wanda zai girmama ta. Wanda zai saurare ta. Wanda idan ta yi farin ciki, zai yi farin ciki da ita, idan kuma ta yi kuka, zai tambaye ta abin da ya same ta.
Ta so gidan da zai kasance cike da natsuwa.
Amma mutumin da za ta aura… Nadeem.
Har yanzu sunan yana da ɗan nauyi a zuciyarta.
Ba don ta san shi ba. A’a.
Ta san shi ne kawai daga abin da aka gaya mata.
Mutum mai matsayi. Mai kuɗi. Jami’in gwamnati. Mutumin da mutane ke girmamawa.
Kuma, kamar yadda Zahida ta sha gaya mata, kyawunsa ma ba ƙaramin abu ba ne.
Sai dai Saida ba ta taɓa zama da shi su yi doguwar magana ba. Ta ɗan san fuskarsa ne kawai.
Ta san yadda yake kallon mutum cikin nutsuwa, kamar yana lura da abubuwan da wasu ba sa lura da su.
“Saida?”
Muryar Zahida ta dawo da ita daga tunaninta.
“Hmm?”
“Kin yi shiru.”
Saida ta yi murmushi.
“Ina tunani ne kawai.”
“Game da Nadeem?”
Fuskar Saida ta ɗan canza.
Aisha ta yi dariya.
“Kin ga ta yi shiru!”
“Ku bar ni mana,” Saida ta faɗa cikin kunya.
Sai aka ji ƙwanƙwasa ƙofa.
Dukansu suka kalli ƙofar.
Wata ƙanwarta ce ta shigo.
“Saida, Mama ta ce ki zo ta gan ki.”
“To,” Saida ta amsa.
Ta tashi a hankali.
Zahida ta kalli Aisha, sannan ta rada mata:
“Ga amaryarmu nan…”
Saida ta juyo ta kalle su, ta yi musu wani ɗan murmushi kafin ta fita.
Ba ta san cewa wannan rana, wadda take tunaninta a matsayin farkon sabon farin ciki ba, ita ce ranar da za ta fara shiga wani labari da ba ta taɓa mafarkinsa ba.
Ba ta san cewa mutumin da za ta kira mijinta yana ɗauke da wani sirri da ya bar ma kansa sani ba.
Sirrin da ya fara ne tun kafin Saida ta san ma’anar kalmar aure.
Kuma sirrin da Nadeem ba kowace mace ce zata iya ba.
— By Khadija Sayyida ❤️