Page 22: The weight of Home
Hibbah ce take waya da Ummi
“Yanzu saboda selfishness irin nasu ne suka tura ta, saboda ’yar tasu bata kai Dua ba”
Ummi ta numfasa “Hmm, ke dai bari kawai I tried my possible best, naga an fasa, amma yadda suke nuna min ai ’yar su ce”
Hibbah tace “Suna shiga hakkinta wallahi”
Ummi ta ce“Gashi ni duk damuwata kar ta miss zuwa musabaqa dinta, ga kuma scholarship ɗin da take da shi”
“Zasu sa ta fara ganin kamar karatunta ba shi da amfani, tunda bata da anyone to support her
“I’m telling you” Hibbah ta ɗan yi shiru kafin ta tambaya “Yanzu Hajiya Abidah, ba za ki iya haƙura ba idan na iso sai ku tafi tare?”
Ta amsa “Hibbah ba haka bane, but anyway, I will wait”
“Toh, sai mun zo ɗin?”, Ta ce “Safe flight” Sannan suka yi sallama
Dua na shiga ɗaki, bacci mai nauyi ya ɗauke ta, ga stress, ga rashin baccin da bata yi ba, ga kuma uwa uba kukan da ta ringa yi, duk suka haɗu suka sa mata zazzabi. A kan dadduman da ta shimfiɗa bayan Sallar La’asar, bacci ya ɗauke ta
Hajiya kuwa hira suke yi da Amrah har Magariba ta yi, suka tashi suka yi Sallah tar sannan suka wuce dining domin yin dinner. Alhaji ma ya zo ya same su, suka fara cin abinci tare. Jim kaɗan sai ya gyara murya “Ina yarinyar nan take? Ita ba za ta ci abinci ba?”
Hajiya ta amsa “Ka san kanta na ciwo, so Amrah ta kai mata abinci tun dazu”
“Yauwa, ko ku fah?”
Suka gama cin abincin, Alhaji ya tafi part ɗinsa. Har lokacin Dua tana cikin baccin zazzabi. Hajiya ta kalli Amrah
“Amrah, ni kam ina yarinyar take?”
“Granny, har yanzu ma bacci take yi, bata tashi ba”
“Lallai ma, ai ba hutu aka turo ta yi ba, mikomin wannan kofin ruwan ki gani”
Amrah ta mika mata, sannan suka wuce ɗakin da Dua take
Suna zuwa, ta banka ƙofar da ƙarfi sannan ta shiga without any second thought, ta kwarawa Dua ruwan Dua ta farka a firgice sannan ta zauna, saboda ruwan da ya shiga har hancinta ya sa tari ya sarƙe ta kamar zata fito da kayan cikinta
Granny ta kalleta “You’re not here for a break da za ki samu time kina kwanciya kina bacci, maza tashi ki wuce waje, go and do the dishes, sannan ki shiga ki gyara kitchen. Kin san uwarki ma a ƙasƙance aka ɗauko ta daga gidan marayu, kuma dole ta yi biyayya balle ke, za ki wuce ne ko sai na ƙara miki?”
Da ƙyar tari Dua ya tsaya. Ciwon kanta ma, maimakon ya ragu sai abin da ya ƙaru, Ita har mamakin kanta take yi da ta yi bacci mai nauyi haka bata tashi ta yi Sallah ba, domin ita, ko baccin da take yi ya yi nauyi sosai, lokacin Sallah ya yi jikinta zai gaya mata sannan ta farka
Ta dafe kanta da ta ji yana neman tsagewa, ta kama hanyar backyard ta fita, hawaye na bin kuncinta, ta rasa abin da ta yi wa mutanen nan da suka extreme hate her. Lantana da take ta observing ɗinsu amma bata da ƙarfin cewa komai, sai ta ƙaraso wajenta ta riƙe ta ta zaunar da ita, ta fara bata haƙuri a hankali. Ta ƙasa-ƙasa take mata magana, tana nuna mata cewa ita ma bata kaunar Hajiya, amma ba zata iya faɗa ba, a bakin aikinta ba
“Amma kin yi Sallah?” Lantana ta tambaya
“No, I just woke up” Dua ta amsa.
Suna jin muryar Hajiya na doso su, da sauri Dua ta mike ta nufi wajen wanke-wanke, Lantana kuma ta gudu ta buya
Hajiya ta buɗe ƙofar “Ke!”
Ta wurga mata goran Morning Fresh
“In kin so ki yi da sauri ki gama, in kin so kuma ki yi ta yi da sannu da sannu har asuba ki kasance a wajen, dan wannan ke ya shafa”
Sai ta juya ta wuce.
Lantana ta fito ta zo wajen Dua
“Bari in je in yi mata sallama, sai mu ga ko yanzu zata shiga ɗakinta”
Lantana ta je ta haɗa mata tea ɗinta na dare sannan ta shiga parlour
“Barka da warhaka, Hajiya”
“Yauwa”
“Naga kamar yanzu da wuri kike shiga ciki, shi yasa nace bari in haɗo miki tea ɗin, tunda yanzu sanyin ya sauko, ni ma ina son komawa ɗaki”
“Kamar kin san abin da nake so, to ajiye min shi akan mirror, yanzu zan shigo”
Lantana ta shiga ta ajiye mata tea ɗin sannan ta fito “Ko dai na kawo miki ne, kar ya yi sanyi?”
“A’a leave it, ganinan zuwa ma”
Suka yi sallama sannan Lantana ta fita, direct taje ta samu Dua
“Yanzu ta shiga ciki, so tashi ki yi alwala, ga ɗakina, sai ki shiga ki yi Sallah”
“Toh nagode Anty”
Dua ta shiga ta haɗa har da Isha’i, tunda already lokacin ya wuce, kafin ta fito, Lantana ta gama aikinta
“Thank you, Anty”
“Ba komai, je ki yi arranging ɗinsu a kitchen, kar in shiga Hajiya ta kama ni”
“Hakan ma ai na gode”
Lantana ta ce “Allah sauwake”
Ta kwashe kayan ta bi ta cikin gidan…
Sai dare Irfan ya iso gidan, lokacin har Hajiya ta shiga ta kwanta, Alhaji ya kira ta, sai kukuni take yi da masifa ƙasa-ƙasa, ta fito parlour ta haɗe rai ta zauna akan kujera, ƙafa ɗaya akan ɗaya tana girgiza su
Alhaji ya kalli Irfan “Toh Irfan, ni zan shiga ciki, Idan ka ci abinci sai ka wuce ɗakin da kake sauka”
“Toh Alhaji, nagode ”Sannan ya juya ya gaishe da Hajiya, amma ko amsa masa bata yi ba
“Hajiya, dama wannan tsaraban naki ne” ya fadi yana mika mata kayan.
Ta juya ta kalli kayan da ya ce nata ne sannan ta amsa tana mai godiya, shi kuma yana mamakin son abin duniya irin na Hajiya. Yanzu-yanzu har ta canza masa fuska
“Ba komai Hajiya, sai da safe” Daga haka ya mike, Ta ce “Tsaya mana”
Ta kwalawa Amrah kira “Amrah! Zo ki ɗauko wa yayanki lemu da snacks, ki haɗa da abinci ki aje masa a dining”
“Toh” Tunda ta fito yake kallonta, yasan fuskar nan, but where? Ya kasa tuna inda ya taɓa ganinta, har ta zo gabansa ta tsaya
“Everything is ready there” ta faɗa, sannan ta yi wucewarta
Ya tashi ya wuce dining, yana mamakin rashin kunyar yarinyar. Ko gaisuwa bata iya ba ne? Yana cikin tunani sai ya ji ƙarar an buɗe ƙofar backyard an shigo, sannan ya ji footsteps a corridor suna doso dining ɗin
Kawai ya fara jin bugun zuciyarsa yana ƙaruwa. He tried so hard to control himself, but he couldn’t
Ya tashi zai bar wajen, kawai sai ta shigo, har za ta wuce, sai ta ga alamar mutum, amma bata tsaya ta kalli fuskar wanda yake wajen ba. Sai ta ɗan rusuna da kayan hannunta “Ina wuni”
Ya kasa cewa komai, sai kallonta kawai yake yi, Ita kuma ta wuce kitchen ta fara arranging the plates
After a few seconds, kamar wanda aka jawo shi, ya shiga kitchen ɗin
Ji kawai ta yi ya ce “Who washed all those plates?”
Ta ɗan juya ta kalle shi sannan ta ɗauke kanta “Ni ce”
“Ba ga sink ba a cikin kitchen ɗin? So why are you stressing yourself by doing it outside? Plus, kina son zazzabi ya kama ki?”
“Anan Hajiya ta ce ayi”….
Har ya koma ɗaki, tunani kawai yake yi “Wai kawai su Kaduna, dama sun san Baba Alhaji ne ko kuma side ɗin Hajiya ne? Me yasa aka tara mata wannan tulin wanke-wanken ita kaɗai, while ga mai aiki in the house, plus her own sister? Why can’t they do it together? But if he could remember that day, Amrah ba sonta take yi ba. Are they not sisters?”
Ya kwanta da niyyar samun amsoshin tambayoyinsa gobe da safe
Dua na shiga ɗaki a lokacin da Amrah ke waya, ta ce da wadda take waya
“Excuse me”
Ta kashe kiran sannan ta fashe da dariya “Kin yi tunanin kin zo hutu ne? Well, you’re wrong, sai ki yi maza ki kwanta a kan tiles, saboda yau ba gado”
Ta ci gaba da dariyar mugunta. Har ta gama, Dua bata ce mata uffan ba. Ta ɗauki wani zani da towel ɗin wankanta, ta shimfiɗa su, ta kwanta sannan ta rufe jikinta da hijab ɗinta kawai
Nan take maganar Ammi ta shekaru takwas da suka wuce ta dawo mata a kunne
“Ohh, my darling, bana hana ki kwanciya a tiles ba, amma ba kya jin sanyi zai kama ki? Oya, tashi”
“O’o, so nake ki ɗaga ni, sai in ga ƙarfin ki”
“Funny baby, as usual. Bari in goya ki toh”
Ta share hawayen idonta “Ammi, I missed you. Allah ya jikanki”
Kuka take yi tana bitar rayuwarta, ga kuma wahalhalun da take sha, ga waɗanda nan gaba bata san wanne za ta haɗu da su ba
Su Ayesha kuwa, yau ne za su tafi Germany. Dukkansu sun hallara a school tare da iyayensu. Ayesha ta kalli Haidar
“Allah sarki, da yau har da Dua. Ko yanzu wane hali take ciki, Allah ne ya sani”
Haidar ya amsa
“I always think about her, shi yasa nake ƙara tsanar that doll girl, Amrah”
Suna cikin magana ne aka sanar musu su shiga mota, za a wuce da su airport. Daga nan kuma duk suka shiga jirgi. Aka sanar da kowa ya saka seatbelt, sannan jirgin ya tashi
Ayesha ta kalli kujerar da take kusa da ita, zuciyarta cike da kewar ƙawarta
“I’ll miss you, Dua”
Vote pls ❤️
Share pls ❤️
Comment pls ❤️
Follow my acc pls
Jazakillahu khayran