DAN SHAYE SHAYE

Free page 9&10

by @mamanteddy

*🔥 RANGWAMEN LITATTAFAI NA MUSAMMAN! 🔥* *📚 MASU SON KARATU, GA WATA DAMA TA MUSAMMAN A GARE KU!* 📚

Kana/kina son karanta littattafai masu kayatarwa, soyayya, drama, da labarai masu jan hankali? 😍📖 To, wannan damar ba za a so a rasa ta ba! 🔥 ✍️ MAMAN TEDDY ta kawo muku babban rangwame na musamman! 🎉❤️ 💥 Yanzu DUK LITTAFINA ₦300 NE KACAL! 💥

Eh! 😱🔥

Littattafan da a da suke ₦500, ₦600, ₦1,000 har ma da ₦2,000, yanzu duk za ku iya samunsu da: 🥳🔥 ₦300 KACAL A KOWANE LITTAFI! 🔥🥳 📚 Ga wasu daga cikin littattafan da ake da su: ✨ Fyade ✨ Kwarton Manya ✨ The Sexy Boss ✨ Gidan Kwarata ✨ My Lady Boss ✨ Sexy’s House ✨ X World ✨ Sex Before Marriage ✨ Rainon Soja ✨ Siyasata ✨ Matar Hariji ✨ Yar Tsakar Gida ✨ Walijaam ✨ Rainonta Zanyi ✨ Kwaryar Sama ✨ Bafullatanan Ruga ✨ Zaki ✨ Dijama Yar Fulani ✨ Yar Waye ✨ Zuma Da Madaci ✨ Tabara ✨ Yar Aikina ✨ Bintoto ✨ Gidan Zaurawa ✨ Sadaka Yalla ✨ Gidan Maza ✨ Sandar Girma ✨ The Virgin Maid ✨ Yar Maula ✨ Mr. Romantic ✨ The Boss ✨ Dan Shaye Shaye — ANA CIGABA DA RUBUTAWA 🔥ON GOING....! 💰 LITTAFI ƊAYA = ₦300 KAWAI! 📚 Littattafai 2 = ₦600 📚 Littattafai 5 = ₦1,500 📚 Littattafai 10 = ₦3,000 🔥 Kada ki bari a baki labarin abin da ke cikin littafin—ki karanta da kanki! 😍📖 💳 HANYAR BIYA: Account: Aisha Mohamed Opay: 8081202932 📩 Bayan kin biya, ki turo da shaidar biyan kudin tare da sunayen littattafan da kike so. 🔥 ₦300 KAWAI! ₦300 KAWAI!! ₦300 KAWAI!!! 🔥 📚❤️ Ki zaɓi littafinki, ki biya, ki fara karatu. Daga yau 14 promo din Nan zai kare ,littafann mu zasu koma yanda kudin su yake a baya. Yau ne last day na Wannan promo 💃 .

*

Pheenart ta ci gaba da kallon saƙon da ke wayarta, amma duk da cewa kalmomin ba su da yawa, sun yi nauyi a zuciyarta fiye da yadda wanda ya aiko su zai iya tunani. “Muna buƙatar ki ƙara kusantarsa. Lokaci ya yi.” Ta karanta su a karo na biyu, sannan ta kashe screen ɗin wayar ta ajiye ta a kan gadonta, amma hannunta ya kasa barin wayar gaba ɗaya kamar tana tsammanin wani sabon saƙo zai sake shigowa. Ta zauna a gefen gadon tana kallon ƙasa, tunaninta ya koma ranar da aka fara shirya mata komai kafin ta auri Ameen, lokacin da aka gaya mata abin da za ta yi, abin da za ta tambaya, wanda za ta kusanta da wanda za ta guje wa, da kuma dalilin da ya sa bai kamata ta bari zuciyarta ta shiga cikin lamarin ba. A lokacin komai ya kasance a gare ta kamar aiki ne kawai; Ameen attajiri ne, mijin da za ta aura domin wata manufa, gidan da za ta shiga domin wata manufa, har ma da murmushin da za ta yi masa yana cikin shirin da aka tsara mata. Amma yanzu komai yana fara sauyawa a hankali. Ta tuna yadda Ameen ya tsaya gabanta da safe yana kallonta, yadda ya ce mata “my wife,” da irin murmushin da ya yi mata bayan ta amsa masa. Ta rufe idanunta, ta yi ƙoƙarin kawar da wannan tunanin, amma sai ta ji wani ɗan murmushi ya kubce mata ba tare da ta shirya ba. “Me yake faruwa da ni?” ta faɗa cikin zuciyarta, sannan ta girgiza kai kamar tana son ta dawo da kanta hayyacinta. “Ba don wannan na aure shi ba.” Ta ɗaga ido zuwa madubi, ta kalli kanta na ɗan lokaci sannan ta ce, “Pheenart, ki tuna dalilin da ya sa kika zo.” Amma zuciyarta ta yi kamar ba ta ji ba, domin a can cikin zuciyar ta wani sabon abu ya fara girma, wani abu da ba ya cikin shirin da aka tsara mata—ƙaunar da ba ta san lokacin da ta fara ba.

A lokacin da take cikin wannan tunanin, sai ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, Dije ta shigo ɗauke da wasu tufafin da aka wanke. Da farko Pheenart ba ta lura da ita ba saboda hankalinta yana wani wuri, amma da ta ji motsin ƙofar sai ta ɗaga kai ta kalle ta. Dije ta tsaya a bakin ƙofa cikin ladabi, ba tare da ta kuskura ta matsa kusa da ita ba. “Hajiya, na kawo kayan da aka wanke,” ta ce a hankali. Pheenart ta kalli kayan, sannan ta kalli Dije, amma a wannan karon ba ta yi mata irin wulakancin da ta saba yi ba. “Ajiye su can,” ta ce kawai. Dije ta yi mamaki saboda yadda muryar Pheenart ta kasance cikin nutsuwa, amma ba ta ce komai ba. Ta shiga ta ajiye kayan a inda aka nuna mata, sannan ta juya za ta fita. Kafin ta kai ƙofa, Pheenart ce ta kira ta, “Dije.” Jin kirar da tayi mata yasa Dije ta tsaya ta juyo tana furta. “Na’am, Hajiya?” Pheenart ta kalle ta na ɗan lokaci, sannan ta ce, “Kin taɓa ganin mutum ya shiga rayuwar Wani da wani shiri, amma daga baya komai ya sauya?” Dije ta yi shiru saboda ba ta fahimci dalilin tambayar ba, sai ta amsa, “Ban sani ba, Hajiya.” Pheenart ta yi murmushi mara ƙarfi ta ce, “Ni ma ban sani ba.” Dije ta kalle ta cikin mamaki, amma ba ta ƙara tambaya ba. Ta fita daga ɗakin, yayin da Pheenart ta sake komawa gaban madubi. A zuciyarta ta san cewa akwai wani abu da yake faruwa da ita, kuma wannan karon ba ta iya zargin kowa ba saboda ita kanta ce ke yaƙi da zuciyarta.

A can hospital kuwa, Ameen yana cikin wani yanayi na aiki da ba ya ba shi damar samun lokacin zama. Tun lokacin da ya shiga asibitin, ya shiga daga wani ɗaki zuwa wani, yana duba marasa lafiya, yana karɓar rahotannin likitoci, yana duba sakamakon gwaje-gwaje sannan yana ba wasu daga cikin ƙananan likitocin umarni kan yadda za su kula da marasa lafiya. Duk da haka, duk lokacin da ya sami ɗan ƙaramin lokaci na hutawa, tunaninsa ba ya tsaya kan aikin kawai; kalaman Mom Nadia suna dawowa masa, musamman “Ka kula da wanda ka yarda da shi.” Ya tsaya a bakin wata window yana kallon harabar hospital, hannunsa ɗauke da coffee, yana tunanin abin da mahaifiyarsa ta gaya masa, sai Abdoul Maleek ya zo kusa da shi ya ce, “You look distracted today.” (Kana kama da wanda hankalinsa yake wani wuri yau.) Ameen ya kalle shi ya yi ɗan murmushi, “Maybe I am.” (Wataƙila haka ne.) Maleek ya ɗan ɗaga gira ya ce, “Is it work?” ya furta Yana Murmushi....Jin Hakan yasa Ameen ya girgiza kai, “No. It's family.” Maleek ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya tambaye shi, “Your mother?” Ameen ya kalle shi sosai, ya ce, “Yes. She called me this morning. Ya furta Yana Dan rintse dulu dulun idanun sa ,Maleek ya yi kamar bai damu ba, Kuma kamar bai fahimci zancen ba amma idanunsa sun sauya na ɗan lokaci kafin ya tambaya, “Did she tell you something?” (Ta gaya maka wani abu ne?)

Ameen ya lura da tambayar, amma bai nuna hakan a fuskarsa ba abin ka ga miskili. “Maybe,” ya amsa a taƙaice.

Jin Hakan yasa Maleek ya yi murmushi, “You know your mother. She has always been mysterious.” (Ka san mahaifiyarka. Tun da daɗewa tana da sirri.) Jin Hakan yasa Amin shiru sammm Bai ce dashi komai ba , duk da Aminin sa ne , Kuma yasan Mom Nadia sosai , Ameen bai amsa ba, sai ya ci gaba da kallonsa kamar yana neman gano wani abu daga cikin fuskarsa.

Maleek ya yi ƙoƙarin sauya zancen zuwa aikin hospital, ya ɗauki wani file daga gyefen sa yana cewa, “We have another case in the emergency unit.”

Jin haka yasa Ameen ya ɗauki file ɗin nan take, kuma kamar yadda ya saba, da zarar aikin likita ya zo gabansa sai hankalinsa ya koma kan aikinsa gaba ɗaya. Ya shiga emergency unit tare da Maleek, inda suka tarar da wani mara lafiya da yake buƙatar kulawa cikin gaggawa. Ameen ya ba da umarni cikin sauri, ya duba mara lafiyar da kansa, sannan ya yi aikin da ya kamata cikin ƙwarewa har yanayin mara lafiyar ya fara daidaituwa. Likitocin da ke kusa da shi suna kallonsa cikin girmamawa, domin duk da halin shaye-shayen da mutane suka san yana yi a rayuwarsa, idan ya shiga aikin doctor sai ya zama wani mutum daban—mai nutsuwa, mai kaifin tunani, kuma wanda ba ya barin kuskure ya tsere masa. Maleek yana kallonsa daga gefe, amma a cikin zuciyarsa ba aikin Ameen ne kawai yake kallo ba; yana kallon yadda Ameen yake ƙara zama mutum mai wahalar sarrafawa, kuma hakan yana fara damunsa saboda duk wani shiri da aka yi a ɓoye zai iya rikicewa idan Ameen ya fara haɗa abubuwa a kansa.

Da yamma, Ameen ya koma office ɗinsa bayan ya kammala zagayen marasa lafiya. Ya zauna a kujerarsa, ya cire agogon hannunsa ya ajiye shi a kan table, sannan ya ɗauki wayarsa. Ba tare da ya shirya ba, sai ya buɗe hoton Pheenart da ke cikin gallery ɗinsa. Ya tsaya yana kallon hoton na ɗan lokaci, sannan ya yi shiru shi kadai , ai ba laifi ne don mace tazo mun a lalace ba , may be da Wani kaddara da ya fada mata ne ,tamkar dai ni din Nan da na tsinci kaina a SHAYE SHAYE. Rintse idanun sa yayi fuskar yarinyar da Bai San tana fado masa ya hau masa gizo , mtswww “Me ya sa kike shigar mun tunani haka?” ya faɗa a hankali. Yana mai ajiye wayan , Ameen ya san cewa wannan ba irin yadda ya saba ji ba ne; shi mutum ne da bai yarda ya bari mace ta mamaye tunaninsa ba, amma Yana yawan tunanin Wannan yar aikin DIJE , hmmmm ko don itace personal maid dina...?tana yin abin da bai taɓa tsammani ba Yarinyar kaman ba daga kauye tazo ba ta iya girki ga iya kula da tsaftar Gida hmmmmmm".

Ganin haka tunani ya fara masa yawa yasa Ameen miƙewa daga kujerarsa ya ɗauki jacket ɗinsa, yana shirin komawa gida, amma kafin ya fita sai wayarsa ta sake ringing. Ya duba screen ɗin, sai ya ga ba ajiye sunan mai kiran ba. Ya ɗaga wayar, “Hello?” Daga ɗayan ɓangaren aka yi shiru na wasu seconds, sannan wata murya ta ce, “Ameen Saleh Moddibo… akwai abubuwa da yawa da ba ka sani ba game da mahaifinka.” Nan take Ameen ya tsaya cak. “Who are you?” (Kai wane ne?) Ya tambaya cikin wata irin murya, amma mutumin ya katse wayar ba tare da ya amsa ba. Ameen ya kalli screen ɗin wayar, sannan fuskarsa Nan take ta sauya. A wannan karon ba wai kawai kalaman Mom Nadia suka dawo masa ba ne, har ma ya fara fahimtar cewa wani abu daga baya yana ƙoƙarin dawowa cikin rayuwarsa. Ya ɗauki wayarsa da ƙarfi, ya fita daga office, amma a zuciyarsa abu ɗaya kawai yake: waye yake ƙoƙarin buɗe masa sirrin mahaifinsa, kuma me ya sa yanzu??? Mene Kuma ya faru da Mahaifin nasa...??? har yakai kasan stairs sai ya dawo da baya Yana komawa office din. A hankali zuciyar sa ke furta " Ameeen Kai fa namiji ne Zaki , babu Abin da zai tsorata ka just stay calm .

**

Sai can dare Ameen ya dawo gida bayan ya kammala aikinsa a hospital, amma yanayin fuskarsa ya nuna cewa yau ba irin ranakun da yake komawa gida cikin nutsuwa ba ne , duk da Bai shaye shayen ba yau ,sigari ne kawai ya shigo Yana Sha a hannun sa , domin kuwa Tun daga lokacin da ya samu waccan kiran da ba a san wanda ya yi masa ba, tunaninsa ya kasa zama wuri ɗaya.....Shi Mutum ne mara tsoro Wanda ba don haka tun bayan mutuwar Mahaifin sa da yanzun shima ya bar duniyar saboda barazanar da yake gani a kullum......Kalmar mutumin tana ta yawo a cikin kansa, musamman yadda ya ambaci mahaifinsa da wani sirri da bai taɓa saninsa ba. Ya shiga gidan ba tare da ya kula da kowa ba, ko securities din da masu aikin da suke gaishe sa saaam Bai takan su ,don dama ba gwanin zancen ba ne. Da shigar sa falon sa ya cire jacket ɗinsa ya ajiye a kan kujera, sannan ya zauna a falon yana jingina bayansa da kujerar. Ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, yana mai ɗaukar numfashi a hankali. Gajiya ta yi masa yawa, amma abin da ya fi nauyi a kansa shi ne tunanin da yake yi a kullum.

A wannan lokacin ne Dije ta fito daga kitchen don taji shigowar sa ,Kuma dama it's ko Baraka sune masu kawo masa duk Wani Abu da zai bukata ,har sai ya basu umarnin tafiya sannan, nufo Inda Ameeen yake tayi tana ɗauke da glass cup na ruwa. Da ta gan shi zaune shi kaɗai, sai ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonsa....samm Bai San da isowar ta ba ,don yayi nisa a tunani ,Ba kasafai take ganin Ameen cikin irin wannan yanayin ba. Mutumin da kullum yake da wata irin ƙarfin hali a fuskarsa yau ya yi kama da wanda yake ɗauke da wani abu mai nauyi a zuciyarsa....Gashi sigari kawai ya kunna yake Sha , babu barasa .

Matsawa Dije tayi kusa da shi a hankali. “yallabai, ga ruwa,” ta ce cikin ladabi. Ameen bai amsa nan take ba. Sai da ya buɗe idanunsa ya kalle ta, sannan ya karɓi gilashin daga hannunta. “Thank you,” ya ce a taƙaice. Dije ta tsaya kusa da kujera tana kallonsa, amma Ameen ya lura da hakan. “Me ya sa kike kallona haka?” ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba ,fuskar sa tana hadewa. Dije tace “Saboda yau ba ka yi kama da kai ba.”

Jin Hakan amsan da ta bashi sa yasa Ameen ya ɗaga gira ,Yana cewa. “Kuma kin san yadda nake kenan?” Dije ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, “ina aikii a wannan gidan kullum fa. Mutum yana iya fahimtar wasu abubuwa ba tare da an gaya masa ba.” Wannan amsar ta sa Ameen ya ɗan yi murmushi. “Kina da magana sosai .” Abin da yace kenan Yana Kai Ruwan bakin sa a miskilance , dan Murmushi tayi tana Mai cewa “Na faɗi abin da na gani ne kawai yallabai.”

Ameen ya sake kallonta, wannan karon na ɗan lokaci fiye da yadda ya saba. Akwai wani abu a yadda Dije take magana da shi da yake sa shi manta da tunanin hospital na wasu seconds. “Dije,” ya kira ta a takaice. “Na’am?” Ta ɗaga kai. “Kin taɓa ganin mutum yana neman amsar wani abu, amma duk inda ya duba sai ya ƙara samun tambaya?” Dije ta ji kalmar ta shiga cikin zuciyarta tayi mata nauyi ,saboda ita kanta tana cikin irin wannan halin a yanzu. “Eh,” ta amsa a hankali. “Wani lokaci gaskiya tana ɓoyewa ne saboda lokacin da za a gano ta bai yi ba.” Ameen ya kalle ta sosai. “Kina magana kamar kin san abin da nake ciki , sannan maganar ki yafi shekarunki.” Dije ta girgiza kai. “Ban san komai ba. Amma na san yadda mutum yake ji idan yana ɗauke da sirri.”

Ameen ya yi shiru. Wannan kalmar ta sa ya fara kallonta da wata irin kulawa. “Sirri?” ya maimaita. Dije ta gane kusan ta faɗi abin da bai kamata ta faɗa ba, sai ta yi saurin gyara maganar nata. “Ina nufin…ammm ammm kowa yana da abin da yake ɓoyewa a zuciyarsa.” Ameen ya yi murmushi mara ƙarfi. “Kowa kenan?” Dije ta kalle shi, sannan ta ɗan murmusa. “Kowa.” Bai sake magana ba haka itama Bata Kuma cewa dashi komai ba ".

Na ɗan lokaci falon ya yi shiru. Ba a jin komai sai ƙarar agogon da ke jikin bango da AC Dake falon , Ameen ya kalli Dije, ita kuma ta kasa ɗaga idonta sosai don ta Kusa baro zance. .....Wannan yasa duk ta kosa yayi mata umarnin tafiya don ita Allah yayi ta ne da surutu , fadi ba'a tambaye ka ba, Wannan shiru ya kasance daban da sauran shiru da suka saba yi ,ya rasa me yasa ya kasa ce mata ta ta fin , duk dashi ba Mai son damu ba ne .

Sai Ameen ya miƙe a hankali. “Ina jin gajiya sosai,”. “Ka je ka huta , idan ka fito zuwa 9:pm abincin dare ya sauka inshallah.” ba tare da ya Kuma cewa da it's komai ba ya nufi Wani corridor da zai sada shi da Underground, sannan ya tsaya ya juyo. “Dije.” “Na’am?” “Thank you… ya furta cike da kamala kaman ba Ameeen din da ya Saba shigowa a buge ba” Dije ta ɗan yi murmushi. “Ba komai.” Ameen ya kalle ta na ɗan lokaci sannan ya nufi Under ground . Dije ta tsaya tana kallonsa har ya ɓace daga ganinta. Da zarar ya shiga, sai murmushin da ke fuskarta ya ɓace. Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalli hanyar bedroom din Pheenart wacce taga kaman a lokacin aka rufe kofan , hasubunallah Allah yasa Bata ga maganar mu da Yallabai ba ,don tace na dai na kula shi. Hmmmm sai Kuma ta juya da Sauri tana nufar kitchen a zuciyar ta tana furta “Me ya same shi yau?” ta tambayi kanta. Ba ta san cewa amsar wannan tambayar tana da alaƙa da sirrin da ita kanta ta zo da shi ba. Ko wacece Dije....? Muje zuwa masoya uwar teddy free page zai kare a ko wani lokaci , kuyi payment kar ayi gaba a bar ku a baya ".

Bayan wasu mintuna, baraka ta shigo Nan Dije ta bar mata aikin , tana barin bangaren tare da nufar bangaren da aka basu , dakin ta tashi ga Kai tsaye, ta zauna a gefen gado. Ta kasa daina tunanin yadda Ameen ya kasance a falon. Ta lura cewa yana cikin damuwa, kuma hakan ya sa ta fara tunanin ko akwai wani abu da ya faru a hospital. Ta san cewa bai kamata ta shiga cikin abubuwan Ameen fiye da yadda aka buƙata ba, domin babban dalilin zuwanta gidan har yanzu yana nan a ɓoye. Amma duk da haka, zuciyarta ta fara gaya mata cewa bai kamata ta bar shi cikin wannan yanayin ba tare da ta san abin da yake faruwa ba.

Wannan ya sa ta sake tunanin takardun da ta zo da su. Ba ta zo gidan nan saboda Ameen kawai ba. Akwai wani babban al'amari da ya shafi wasu filaye da kusan rabin ƙauyensu, kuma wasu daga cikin takardun suna ɗauke da bayanan da suka haɗa da dangin Ameen. Ta buɗe ƙaramin akwatin da ta ɓoye kayanta a ciki, ta fito da takardun, sannan ta fara bincika su ɗaya bayan ɗaya....domin Dije ta iya hausar boko A wannan karon ba ta nemi sunan filaye kawai ba; tana neman wata alaƙa da zata iya haɗa abin da ke faruwa da Ameen da abin da ita kanta ta zo nema.

Sai idonta ya tsaya kan wata tsohuwar takarda.

Akwai wani suna a kanta da ta riga ta sani.

Sunan mahaifin Ameen Wato SALEH MODDIBO.

Dije ta yi shiru, zuciyarta ta buga da ƙarfi. “ Ta ɗaga takardar, tana ƙoƙarin karanta ƙaramin rubutun da ke ƙasa. Akwai wani abu da aka rubuta a can, amma takardar ta tsufa sosai har wasu kalmomin ba su bayyana sosai ba.

Dije ta rufe idanunta na ɗan lokaci.

A yanzu ta fara fahimtar cewa abin da ta zo nema na iya zama mafi girma fiye da yadda ta yi tsammani.

Kuma abin da ya fi tsoratar da ita shi ne, Ameen yana kusa da gano cewa zuwanta gidan nan ba kawai don aiki ba ne. Domin ta lura Mutum ne shi Mai basira Kuma Mai hangen Nesa gashi Ba shi da yarda da duk Wanda yake jikin sa...........!

Bayan tafiyan Ameen babu dadewa a Wannan Daren Pheenart ta kasa sukuni , gaba Daya Ameeen baya ta kanta sannan ta lura Wannan yarinyar Dije na kokarin kutsowa cikin rayuwar su , Wannan ne yasa Pheenart ta fito daga dakinta a hankali, amma tunaninta yana kan Dije. Tun bayan abubuwan da ta lura da su, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Ta yanke shawarar zuwa kitchen domin ganin abin da Dije take yi. A Wannan lokacin Dije ta dawo don Taya Baraka yin saving zuwa dinning area...... Pheenart ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonta na ɗan lokaci, sannan ta ce, “Dije.”

Dije ta juyo da sauri. “Na’am, Hajiya Sannu da zuwa.”

cike da izza phinart ke takawa zuwa ciki kamin ta furta “Me ya sa kike ɓoye mini wasu abubuwa?” Dije ta ɗan tsaya, hannunta ya daina motsi. “Ban fahimta ba, Hajiya. Me kike nufi?”

“Ki daina yi min kamar ba ki sani ba!” kina yar kauye Zaki nemi Raina mun wayo....! Pheenart ta faɗa cikin fushi. “Tun kwanakin nan ina lura da ke. Akwai wani abu da kike ɓoyewa.”

Dije ta sunkuyar da kanta. “Wallahi Hajiya, babu wani abu da nake nufi da shi, Aiko kadai ya kawo ni gidan Nan Kuma shi nake yi”

Sai Pheenart ta ji haushin yadda Dije ke ƙin faɗin gaskiya. A cikin fushinta ta ɗaga hannu, amma kafin abin ya wuce gona da iri, tasan tasss zata iya Shan bugu a hannun phinart Nan Dije ta ja baya, Pheenart kuma ta dakata. Shiru ya mamaye kitchen ɗin.

“Ki kula da kanki, Dije,” Pheenart ta faɗa cikin murya mai Zafi amma cike da gargadi. “Ba na son a sake samun wani abu da za a ɓoye mini a wannan gidan.”

Dije ta kalli Pheenart, amma ba ta amsa ba. A zuciyarta kuwa, ta san cewa Pheenart ta fara kusantar sirrin da take ƙoƙarin ɓoyewa....." Tho itama tafara fahimtar ta bare Kuma Ameeen...?

A dai dai lokacin ne Baraka ta dawo daga dinning din da taje ajiye dinner . Amma wannan karon, Dije ta fahimci abu ɗaya: Pheenart ta fara zargin ta sosai. Shigowar Baraka yasa Pheenart ficewa daga kitchen din cike da kunar Rai , Bin ta da kallo Baraka tayi kana tace " Wai duk akan Yallabai ne ko?. Gyada Kai Dije tayi alamun eh . Hmmmm numfasawa Baraka tayi tana Mai cewa " shikenan ki rabu da Yallabai tun da Abin zai zama matsala , Hajiya tana da kishin mijin ta sosai , Sannan Abin haushin ma Bai damu da ita ba ,yanzu ki Daina Kai masa komai ni zan rinka yi Kya kina Aiki a kitchen kawai ya isa Dije ". Thom ". DIJE ta furta tana cigaba da Ayyukan ta ".

*Kasar Switzerland* Wani irin kayataccen Gida ne da ya gaji da haduwa da tsaruwa ,tun daga Waje da bayan gidan an kyawaye da flowers masu kyau ,Wanda suka Kara kayata gidan da kyawunsa .

Wani hamshakin Alhaji ne na Gani zaune tumbi russs a gaba , ga tozon wuya sai dai bakin Fata ne dagani kasan Dan Nigeria ne , Amma ya tare dukiya ba kadan ba , Wannan shine Alhaji Nasir moddibo Mahaifin Pheenart 🤔 . Alhaji Nasir ya zauna cikin nutsuwa, hannunsa ɗaya yana kan tsohuwar takardar da ke gabansa laptop , d *D'AN SHAYE SHAYE* *Romantic and Erotic story* 🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬🚬

_*Last free page*_