1
}
(Start your day with Amrah)
Hadari ne ya haɗu, garin sai iska ake yi. Wata yarinya da ba za ta wuce shekara ashirin da uku ba ce zaune a wani lecture hall tana duba gyaran da supervisor ɗinta ya yi mata. Jin yanayin garin ya sa ta janye idanunta daga kan system ɗin ta, ta kalli window da sauri. Ta miƙe, ta harhaɗa kayanta, sannan ta fita daga lecture hall ɗin. Sai yanzu ma ta yi realizing cewa ashe sauran mates ɗinta duk sun tafi.
Tana cikin tafiya ta ji an ce, “Lalle ma bestie, da tafiya za ki yi ki bar ni?”
Chak ta tsaya tana murmushi, ta juya. Jin muryar Mufydarh ce. Jerewa suka yi har suka isa inda Amrah ta yi parking. Mufydarh ta ce, “Me yasa yau kuma kika yi parking a nan?”
Ta ce, “Dazu naga project supervisor dina ne, shi ya sa kawai na bar motar a nan, na koma lecture theatre da ƙafa for exercise”
Tabe baki Mufydarh ta yi sannan ta ce, “I’m just doing so for our unborn baby. Ni dai ki kula, ba ki ba kanki wahala da sunan exercise ba”
Amrah ta ce, “Gida na za mu je ko gida zan sauke ki?”
“Gidan ki”
Sai da suka yi nisa Mufydarh ta ga suna bin wata hanya, ta ce, “Malama, ina za ki yi da mu ne?”
Ta ce, “Mall ne. Coffee na ya ƙare kuma ban da kayan tea. Kinga anjima ko mutuwa zan yi, yayanki ba tsayawa zai yi ba, and I’m addicted to it yanzu”
Da sauri Mufydarh ta kalle ta ta ce, “Daman yana nan ne?”
“Sure”
“Definitely drop me here, na fasa zuwa gidan naki”
Duk yadda Amrah ta so su je tare, Mufydarh ta ƙi. A ƙarshe ta sauke ta a hanya, ita kuma ta ci gaba da hanyar mall ɗin.
Tana parking, wani mota ma ya zo ya yi parking opposite, adjacent to her car. Kallon motar take yi; it’s tinted. Ɗauke kai ta yi ta wuce cikin mall ɗin. Direct wajen kayan tea da other stuffs ta nufa, ta ɗebo different flavors. Abin da ya kawo ta kenan, so ba ta buƙatar ɗaukar wani stuff.
Ta ji mutum a bayanta, amma ba ta juya ba har ta kai wajen cashier. Kirjinta na duka uku-uku, yanayinta duk ya canza, kawai daurewa take yi.
Cashier ta miƙa mata ATM card ɗinta. Juyawar da za ta yi ke nan, and she saw him.
Gabanta ya yanke ya faɗi. Da ƙyar ta yi gathering courage ta ce, “Farouq! Umar Farouq, is that you?”
Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa. Ya karɓi ATM card ɗinsa sannan ya kama hanyar fita. Ba ta yi sanyi a gwiwarta ba, ta fara binsa.
“Farouq, please wait. Magana ɗaya zan faɗa maka”
Farouq bai tsaya ba, ita kuma ba ta haƙura da binsa ba har ya kai wajen motarsa.
Ta ce, “Yanzu Farouq, ni kake wulakantawa?”
Juyowa ya yi ya kalle ta for some seconds, sannan ya zare bakin spaces ɗin da ke fuskarsa ya ce, “What do you want to tell me, Amrah? Ƙaryar da kika saba ko miye? Look at you, you are enjoying your life more than anyone expected. Kalli har rabo kin samu. So please, kar ki ƙara nuna kin san ni saboda ban jima da healing ba. Bissalam”
Ya buɗe motarsa ya shiga ya bar ta a wajen.
Yayyafin da ake yi ne ya soma yawa. Numfashinta da ke ƙoƙarin ɗaukewa ne, da ikon Allah, ya fara dawowa. Ta juya ta kalli motarta sannan ta fara tafiya a hankali har ta isa wajen motar.
Ba ta damu da yadda ruwan ya jika ta ba. Sai da ta zauna a cikin motar for about five minutes tana kiran sunayen Allah sannan ta samu ta dawo daidai. Ta tada motar ta kama hanyar gidanta. A hankali take tuƙi saboda gaba ɗaya ba daɗi take ji ba.
Tana isa ta yi horn. Maigadi ya zo ya buɗe mata, ta shiga da motar ta yi parking.
Kallon motar Sultan a parked a wajen ta yi, sai da ta ji sinking na gaba. Ta rufe idanunta, hawayen da take riƙewa ne suka gangaro.
Ita yaushe ne za ta fara jin daɗin rayuwarta? Jikinta ba ƙarfi.
Haka ta wuce, ta shiga parlour. Stairs ɗin da ke cikin parlour shi za ta bi ya sada ta da bedroom ɗinta. Ita kuma yanzu da cikinta ya girma, ba abin da ke mata wahala wajen hawa kamar stairs.
Sai da ta yi rabin stairs ɗin ta ji muryarsa
“Hey you! Make something light and fast for me. Yunwa nake ji kuma ba zan iya fita a cikin ruwan nan ba”
Juyowa ta yi ta kalli direction ɗin inda ta ji voice ɗinsa. Idonsa na kan wayar hannunsa, yana zaune a resting chair. Yayi maganar ma ko kallonta bai yi ba.
Kamar mai tsoron magana, a hankali ta ce, “Ya Sultan, please just give me 2 minutes. Zan cire jikakkun kayan jikina sai na zo na daura”
Ya janye idanunsa daga kan wayarsa ya zuba mata. Hakan ya sa ta fasa zuwa ɗakinta, ta sauko ta wuce kitchen.
Tunani ta shiga yi, kawai ta deciding dafa jollof spaghetti with kifi. Ta sarrafa komai kafin ya dafu. Ita kuma ta haɗa nata black tea, ta haɗa da cookies ta fara ci. Saboda zafin tea ɗin, sanyin jikinta ya ragu.
Tana gama sha, spaghetti ya nuna. Ta juye a wani warmer, ta kai dining. Ta kai ruwa da drinks ɗin ma dining, sannan ta karasa inda yake.
Ta ce, “I’m done. Na yi arranging a dining”
Ko kallonta bai yi ba, balle ta sa ran zai mata magana. Hakan ya sa kawai ta tashi ta yi hanyar stairs.
Ganin La’asar ya yi, sai da ta fara hawa sannan ya ce, “Nan za ki kawo min?”
Wani abu ya tokare ta a throat. Ba yadda za ta yi. Haka ta sake saukowa, ta kwaso abincin ta zo ta jera masa a gabansa.
Ta ce, “Na kawo”
Buɗewa ya yi ya kalli abincin. Wani irin tsaki ya ja, hakan ya sa ta ɗago kanta da sauri ta kalle shi.
Fada ya fara mata, “Da kikiya, ba abin da kika iya. An wani lankaya min ke. Just common simple word ba ganewa kika yi ba? Do you really expect zan ci spaghetti at this time ne? Ko ba ki san scheduling nake yi ba?”
Ya kuma yi tsaki ya bangaje ta ya wuce ya fita. Ta yi saurin dafe wani abu don gudun kada ta faɗi, hawaye na zuba a idanunta.
Ita ba ta ga laifin da ta yi ba. Shi ne ya ce something light and fast.
Ta wuce ɗakinta, ta yi wanka ta canza kaya, ta sa light gown. Ta yi sallah, ta yi azkar ɗin yamma sannan ta kuma sauko.
Plate da ruwan ta kwashe abincin, ta kuma juye shi a wani warmer. Ita ba za ta iya ci ba. Ta sa hijab ɗinta har ƙasa.
Lokacin ruwan ya tsaya, ta fito. Wannan karan ba ta ga motarsa ba. Hakan ya sa ta gane ya fita. A parlour ɗin waje ta fita direct gate ɗin ta nufa, ta buɗe ta shiga.
Neighbors ɗinsu ta yi wa sallama. Wata yarinya da ba za ta wuce shekara biyar ba ta fito da gudu jin muryar Amrah tana cewa, “Oyoyo, Anty Amrah!”
Amrah ta rungume ta ta ce, “Mami na nan?”
Ta ce, “Eh, Anty. Granny na ciki”
Ta ja hannunta har suka shiga parlour. Ayrah sai hira take yi mata, sai can ga Mami ta fito. Matar da ba za ta wuce shekara hamsin ba, daga gani Ayrah jikarta ce.
Ta ce, “Sorry Amrah, na barki kina jira na ko?”
Ta yi murmushi ta ce, “Aa Mami”
Suka gaisa. Ta ce, “Yanzu zuwa na a asibiti, ruwa ne ya riƙe ni, shi ya sa na makara. Sallar La’asar ma na makara”
Amrah ta ba ta abincin ta ce, “Mami, ga abinci. Amma taliya ne”
Murmushi Mami ta yi ta ce, “Kamar kin san yunwa nake ji. Yau masu aikina ma ba su zo ba. Ina tunanin ruwa ne ya riƙe su. Ayrah kuma cornflakes ta sha”
Mami ta ringa yabawa da girkin Amrah, hakan kuma ya sa ta ji daɗi.
Mami ta ce, “Yanzu ya jikin naki?”
Ta ce, “Da sauƙi, Mami”
Ta ce, “Gobe zan leka asibiti, so ki shirya. Ina son na sake duba ki. Fatana kuma Allah ya sa yanzu kin rage wannan damuwar. Kin san ba yadda za mu miki CS, jininki kullum ƙara shooting yake yi”
Amrah ta yi shiru. Ita fa har bargon jikinta take ji; a haihuwa za ta mutu tun da kullum doctors suna faɗa mata game da yawan tunani.
Ga Mami ma, duk da ba danginta ba ce, kawai makwabtaka ce, amma ta ɗauke ta tamkar ’yar da ta haifa. Kullum tana kan duba lafiyarta da ta baby.
Ganin Magrib ya yi, sai ta ce, “Mami, barin tafi”
Mami ta kawo mata masara da ta saya a hanya, domin ta san Amrah tana so. Ta karɓa tana mata godiya, sannan ta fita ta wuce gidanta.
Bayan Sallar Isha’i ta gama tattare abin da za ta tattare. Har lokacin Sultan bai dawo ba.
Tana shirin kwanciya ta ji ana kiran ta. Ta duba wayar ta ga Bestie ce ke kira. Hakan ya sa ta yi murmushi ta ɗauki wayar.
Hira suka sha sosai, hakan kuma ba ƙaramin rage mata kewar gida yake yi ba.
Mufydarh ta haɗa ta da autansu, Farhan. Ya ce, “Anty Amrah, yaushe za ki dawo gida? I miss you wallahi”
Ta ce, “Soon, ɗan kanina”
A haka har suka yi sallama, ta kwanta. Bacci mai daɗi ya ɗauke ta.
Sultan bai dawo gidan ba sai passed 1 a.m. Haka ya shigo gidan, idonsa ya yi mugun ja, alamun ya bugu. Amma ya fara sakinsa har ya wuce ɗakinsa, sai kuma ya dawo ya bangaje ƙofar ɗakin Amrah.
A mugun razane ta farka tana kallonsa. Zuciyarta ta mugun sinking. Ta tabbata da cikinta ƙarami ne, da ya zube.
Da wani irin kallo da murya ya ce, “Ki haɗa min black tea, ki sa enough lemon”
Sannan ya wuce abunsa.
Hawaye ne suka fara sintiri a fuskarta. Ita ba ta san me ta masa ba, shi ko tausayinta ba ya yi. Kamar yadda ita ba choice ɗinsa ba ce, haka shi ma ba choice ɗinta ba ne shi
… it’s Force Marriage to them all.
Let’s meet at the next page.
Share please.
JazakAllah khayr.