16
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
Page 1️⃣6️⃣
Neman su aka fara yi dan bada kyauta.
Tashi sukayi suka tafi inda sauran students din suke
Amba nabila award na punctual and obedient student and best in biology
Ita Kuma Jalila na neatest student and best in chemistry
Anisa Kuma best student in all calculation subjects and the most nicest and obedient student
" Uhmmm kaga nicest student, ga neatest a kusa da ita"
Yayi maganar yana kashewa da dariya ya ƙara cewa
"Allah basu san award din me suka baku ba ke Anisa ke din ce nice, duk wannan shegen tsiwar taki, ke Kuma neat su neat anji jiki, daman ita nabila i know she's obedient ta cancanci award ɗinta"
Yafaɗa yana kashe wa nabila ido, ita dai sunkuyar da kanta tayi tana murmushi dan harga Allah ya Ahmad na bata dariya a times
Ita dai Anisa hararar shi tayi bata ce komai ba dan jinta take duk a takure, saboda tana jin idon shi na yawo akan ta Amman taƙi ta kalli inda yake
Jalila ce ta ce
"To ya Ahmad me kake nufi am not neat Ko me" ta faɗa tana wani murguɗa baki
"Matar da se ki fi kwana 2 da the same kaya shine wani neat"
Ammah ta faɗa tana ɗan dariya
"Kaiii Ammah pickles din tawa" faɗin Anisa tana supporting Jalila
"To meye banbancin daga ke har itan ai duk kanwar ja ce" fadin Ammi
"Ai duk haka suke sedai shiriya kuma"
Ahmad ne ya kalli nabila yace
"Kema haka"
Kunya ya bata kawai ta ja hannun Anisa tace kuzo muje wajen su Maryam
Duk tashi sukai suka bar gurin,
shidai Umar ko uppan bece ba saidai ido daya kure Anisa dashi Amman taƙi ta juyo ma ta kalle shi, kuma yasan tana jin kallon nashi tunda ga alamar ta takura Amman taƙi kallon nashi,
Shifa gaba ɗaya ji yake kamar yayi hauka a gurin, kawai maintaining yake yana composing kanshi kar yayi wani abun, saboda ganin wannan na kusa dashi din ya kureta da ido har yanzu
Har sun ɗan yi nisa kaɗan daga inda su Ammah suke Amman suna iya hago su wannan wanda ya zauna kusa da ya Umar ya ɗan sha gaban su
"Heyyy dear, sunana Habib kefah"
Ya kalli Anisa Yana maganar
Ita dai ko kallon shi batayi ba ta fara jan hannun nabila dake kusa da ita
"Ki tsaya mana, ki samun phone numbern ki mana ko gaisawa ne mu ringa yi" yayi maganar yana miƙa mata wayar shi, bata amsa ba ya kara cewa
'' wallahi beautiful kina da kyau sosai fah, irin na mind blowing ɗinnan''
Ƙoƙarin kara shigewa sukayi ba tare da ko kallon shi tayi ba amma ɗan anacin ki ya kara tare gabanta
'' tun kuna stage nagan ki kuma gaskiya kin tafi da imanin Habib ki taimaka ki saka mun numbern Please !!!!!!'' ya ja kalmar Please ɗin yana marairaice fuska cike da barikanci, cikin zaƙuwa da ɗan hasale dan gaba ɗaya yanayin shi be mata kama da kamilallen mutum ba tace
"Malam plea.."
Bata karasa maganar ba taga an kwace wayar dake hannun shi anyi jifa daita wani gefen
Juyowa tayi taga waye yayi jifan suka haɗa ido da Ya Faruq
"Kun bar gurin nan ko sai na ɓalla ku, dan rashin sanin ciwon kai ne zaki wani tsaya kina ma irin wa'anan mazan magana, wallahi na ƙara ganin ki kina ma wani magana a gurin nan sai na karya ki, ku wuce ku bani guri, nonsense tsabar baku san ciwon kanku ba wuce ki bar idona in dai na ganin ki kafin inyi ƙasa ƙasa dake yanzu"
Yaja tsaki yana wani watsa ma gayen mugun kallo,
Saurin barin gurin sukayi jikinta na ɓari ta riƙe hannun nabila gam kamar zata karya ta dan duk saninta dashi ba abinda ke haɗa su bare akai ga irin wannan faɗan sedai ta hanga yanayi Amman be taɓa mata irinsa ba se yau da taji kamar ta sume a gurin ki ta saki fitsari dan yanda idon sa sukayi ja har jijiyar kansa na tashi
Tun sanda Habib ya tashi ya nufi inda suke zuciyar sa ce dukan uku uku, kasa daure wa yayi sanda yaga zasu tafi ya ƙara shan gabanta har yana wani miƙa mata banzar waya,shi idan ba idonsa ke mai gizo ba gani yayi kamar ma amsa zatayi tana washe ma sakaren baki
Su Anty basu Ankara ba sai sanda sukaga yana cilli da wayar wani
"Kai Ahmad yaushe Umar ya tashi daga nan" faɗar Ammah
Shima saida ya ƙara juyawa ya kalli inda yake zaune da inda ya gan shi yanzu
"Wallahi ban sani ba Anty nima saida kika yi magana nayi noticing"
"Malam lafiya zaka jefar mun da waya"
"Last warning zan maka, she belongs to me and only me, karka bari musa ƙafar wando ɗaya, dan bazaka ji da daɗi ba, kabar wajen nan yanzu dan zan iya illata ka idan ina ganin banzan face dinka" ya faɗa yana wani huci kamar wani murucin zaki
Shima ganin yanayin face ɗin ya Umar din ne yasa be biye mai ba bare ya mai nashi kalar haukan dan yasan a duke se Faruq ya jibgi ukun shi ba ma iya shi kaɗai ba dan a murde yake shiko gashi bushashshe a gurin kamar an daura wa mucciya zani dan dai kawai ba laifi yana da ɗan kyau
tafiya yayi ya barshi a gurin zuciyarsa na mugun ta fasa, wani jaki mara sense dashi zai so yana wani kure abinda yake mallakin sa da kallo, belonging dinshi fah, she is his and only his, baayi wani bayan shi ba, he even have the guts da zai yi mata magana
Ji yake kamar ya harbe shi ya huta ko zai ɗan samu sassaucin abinda yake ji sedai duk abinda ze faru daga baya ya faru
Ammi ce tace ma ya Ahmad ya kira su jalila su zo su tafi
Bayan ya kira su ne suka fito zasu tafi, daman ya Umar ma da mota yazo
Sudai sun san ko karen hauka ya cije su ba abinda zai shigar dasu motar shi barin ma yanda yake a fusacen nan
Hanyar motar Ya Ahmad suka nufa, har sun kai bakin kofa suka ji Muryar shi
"ku shiga wancan, su Ammi sai su shiga wannan"
Hantar cikin Anisa ne ya kaɗa, dan itafa a tsorace take bare ga yanda ya mata wannan faɗar dazu kamar zai cinye ta, sai tayi dauriyan cewa
"Amm yah tunda sun riga da sun je bakin motan mu Bara mu shiga nan tare da Anty"
Wani mugun kallo ya watsa mata har zaiyi magana kawai ya fasa yayi kwafa
A fusace ya bude motar ya shiga suma su Ammah suka shiga ya ja motar
Gashi ba damar ya ja motar da gudu tunda su ammi ne aciki bare ya rage takaici da ɗacin zuciyar da ta ƙunsa mai a yau dinnan, ai da ta shigo motar nan yau duk wani kwandon bala'i da rashin mutuncin dake cin shi seya juye mata shi tass
Wani uban kwafa ya buga da seda amma dake zaune a side din shi ta kalli shi, kafin ma tayi magana Ammi ta rigata da fadin
'' wai babban yaya me aka maka ne yau gaba ɗaya naga kamar ranka a ɓace, yanzu kuma kana haɗe mana rai harda buga kwafa..''
___________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺