The Unwanted Daughter

Page 23:The truth she needed

by @hauwajaywrites

CHAPTER 23: THE TRUTH SHE NEEDED


Irfan was constantly showering Hajiya with a lot of money, shi yasa yanzu ta sauko masa tana sake masa fuska After all, har hira suke zama su yi tare


“Hajiya, those two girls, are they your granddaughters?”


Hajiya ta ce “Not those two, Babban dai ita ce jikata”, Ya ɗan daure fuska “Ban gane ba”


Hajiya ta masa bayanin komai, har da labarin inda aka ɗauko Aneesa da kuma rasuwarta, ta ƙarasa da cewa


“Banda rashin godiya irin na Usman, me kuma zai yi da wata matar bayan ga Zahra? Ya ɗauka mu ana mana kishiya ne? Duk danginmu, idan mun shiga gidan aure, toh ba batun kishiya sai bayan ranmu”


Irfan was speechless


Shi yasa ya fara fahimtar dalilin da ya sa yarinyar take zama always uncomfortable, ya tuna ranar da ya je event center, maganganun da Amrah take faɗa mata ita da friends ɗinta. Secondly, a gidan Hajiya, as early as possible, za ka ganta tana wanke-wanke cikin sanyi da sassafe ko kuma tana yin wasu ayyuka, despite the fact that there are housemaids in the house


Irfan never met Mr Muhammad Usman personally. He had only seen him once at a function, amma bai taɓa ɗauka cewa shi ne mijin Zahra ba. Zahra ma rabonshi da ita tun kafin ta haifi Amrah, so there was no way he could have known them properly


Not to blame Irfan, after high school, he was sent abroad for further studies…


Irfan yana tsaye, hannayensa a cikin aljihun wandonsa, ya kurawa Dua ido da take ta faman mopping ɗin gidan da ƙyar take yi saboda matsanancin zazzabin da yake addabanta kwana biyu da suka wuce


Bayan ta gama, ta zo za ta ɗauki bucket ɗin mopping ɗin da niyyar fitar da shi, sai ta ji muryarsa a bayanta


“Let me help you”


Bai jira amsarta ba, ya ɗauka ya fitar mata da shi. Ita kuma ta yi hanyar ɗakinsu, sai ta sake jin muryarsa

“What’s wrong with you, Dua?”


Ta tsaya ta kalle shi “Ya Irfan zazzabi ne, Can you help me with some paracetamol?”


Ta ƙarasa maganar, hawaye na bin kuncinta


Dummm!


When her voice fell on Irfan’s ears, he felt something weird. His adrenaline rushed through his whole body, and he could feel his heartbeat getting faster


Bayan wani lokaci sai ya realize inda yake yayi saurin cewa “You said what?”


Ta maimaita


 “Okay” Kawai abin da ya iya cewa kenan, sannan ya bar wajen


Yau ne za su tafi, Hibbah za ta zo ita da autarta Ayrah su ka gama shirinsu da wuri saboda morning flight ɗin da za su bi


Ta ce da ɗanta Sadeeq “Kiramin wannan number” Ta faɗa tana miƙa masa wayarta


“Da layi na kenan?”, Ta ce “Eh”


Ya kira, ya miƙa mata wayar

“Hibbah ce Hajiya Abidah, So yanzu za mu airport, please kada ki sanar musu”


Ummi ta ce “Haba ke kuwa! Ni ko waya ban son su san muna yi, balle su ce nine informer ɗin gidansu”


Suka yi sallama, sannan Ummi ta yi kissing forehead ɗin Sadeeq “Ka kula da kanka”


“Safe flight Mummy. I wish ban da test ɗin dana raka ki, da na raka ku har airport”


Daddy ya ce “Ka na son ka maida kanka jariri ko? Bayan aure zamu maka soon”


Dukkansu suka yi dariya, Ayrah ta fake idon iyayenta ta ce “Akhie!” Da ya juyo, sai ta masa gwalo


“Zan kama ki ai”


Suka yi sallama, ya wuce school, Daddy kuma ya kaisu airport..


Ayman was almost done with everything, ya kira Ammi, suna video call


“Yanzu kam ai zaku ƙyaleni in dawo Nigeria, you know I damn missed you” Ya faɗa yana langwabar da kansa gefe


Ammi ta ce “Zama ka faɗa gaskiya ai”


Ya yi wata dariya “My one and only Ammi, ke kam kullum baki rabuwa da zolaya”


Ta ce “Toh canza min magana”


Ya kuma yin dariya“Ammi, kin san Dada tana faɗin wai nazo Nigeria amma ko leƙata ban yi ba, I guess this time around, in na dawo, zan je in yi mata some days saboda ta huce haushin da take ji na”


Ta ce “Da ka kyauta kam. Lalle yaro ya girma tunda ya fara irin wannan tunanin”


Ya yi dariya “Ammi kenan, yanzu fa I’m 29, Please ki daina”


Ta ce “Ni kam kar ka isheni, ga Abban ka ma ya dawo, sai anjima”


Ba ta jira cewarsa ba, ta kashe kiran


Ya yi dariya “Indai Abbah na nan, toh Ammi bata da attention ɗinsa” Ya yi murmushi shi kaɗai


Yau da dare, Dua ita kaɗai ce a bayan gidan tana fitar da kayan wanke-wanke. Gashi ko’ina shiru, ba ka jin ƙarar komai sai motocin da suke wucewa a kan titin unguwar


Gashi ita tana da muguwar tsoro, kuma ba Lantana balle ta taimaka mata as usual, tana tunanin in dai kafin ta ƙarasa, wani abu mai ban tsoro zai bayyana, sai an ɗau gawarta


Tana fitar da kayan wanke-wanken tana tafiya a hankali, sanda-sanda, tana zama  kenan, sai ga Irfan ya zo wajen, har ta tsorata za ta gudu, ya ce


“Calm down, it’s me”


Sai ta dawo ta zauna tana riƙe da kirjinta “Don Allah, za ka jirani?” Ta tambaya


“Sure, amma dafatan ba za ki yi min ƙarya ba”


Ta ce “Daman Ammi na, sanda take raye, ta hana ni”


“Ayyah sorry, Amma what’s wrong with you? Kullum kina ƙara ramewa Banda tunanin da kike yi kuma?”


“Ba ni da lafiya ne”


“Since when?”


“Tun ranar da muka dawo gidan nan”


Ya yi shiru yana nazarin maganarta. Sai can ya ce “Miko min ruwan Omo, mu fara kafin dare sosai ya yi mana anan”


A karo na farko a rayuwarsa da ya ga tana dariya, yana kallon ta without blinking


Sai da ta tsaya tana kallonsa, sannan ya ce “What’s so funny?”


Ta ce “Daman maza suna yin wanke-wanke ne?”


“Ni ai tayaki zan yi”


Ya fara taimaka mata “Say it out. Let me be your therapist”


Ta yi shiru kamar ba ta ji shi ba


“Uhum, I’m all ears” Ya maimaita


Ta kalle shi“On what?”


“On your life, I know everything about you, kawai dai baki sanni bane”


“Yauwa, I wanna ask you this. Tun ranar da ka zo gidanmu waje na, kai ne a wajen event ka biyoni?”


“Sure nine, yanzu zaki yarda da maganata?”


“Yeah I do, but how?”


“Let me inform you in brief, duk wani abu da na sani, sai da ya faɗa mata”


She was so shocked da ta ji ya sani


Sai ya ce da ita “Then now, let me be your therapist. Say it out plsss dear”


Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce

“Is it Hajiya or Mummy that sent you?”


Ya yi dariya “Never, In fact, I don’t have any case with them. Alhaji Baba nayi min mazaunin Kaka ne, kuma I knew your mummy once, ta ce please I should make you happy when she’s no more”


Hawaye ne suka fara zuba a idonta. Zazzabin da ta fara jin ya sauka yanzu sai ta ji ya dawo mata fresh. Kanta da ya daina ciwo yanzu ta sake jin shi yana mata ciwo


“Ya Irfan, please take me to any orphanage that you know. I don’t want to stay here, nor do I want to stay at Daddy’s house, Please ka taimaka ka kaini na gwammaci wulakancin gidan Marayu da zama cikin family na at least gadon Mahaifiyata”


Ya girgiza kansa “No I can’t do this, ki yi haƙuri”


Ta fashe da kuka, ta fara ba shi labarin rayuwarta, wanda shi ma sai da ya ji hawaye na bin kuncinsa


Sure, ya tausaya wa rayuwarta, Allah sarki, he couldn’t imagine a young, beautiful girl like her going through such a life


Sai ya ce “Dua there’s only one way that I can help you, amma ba zan iya kai ki gidan Marayu ba”


Ta share hawayenta “What’s that? I’m ready to do it”


Ya ɗan yi shiru kafin ya ce “Zaki yarda ki aure Ni?”


Ta girgiza kanta “No”


Ya ce “Please don’t be so quick to say no, I just want to help you out Dua, Hakan ya isa, you can’t take this anymore kin yi karama ma wannan wahalan”


Ta sunkuyar da kanta “I’m scared, please, bana son nayi aure Yarinya ta ma ta shiga halin Dana shiga”


Ya duba time a wayarsa, lokacin har ƙarfe goma sha biyu ta wuce. Ya nuna mata lokacin


Ta kama baki “Ohhh, Ya Salaam! Na shiga uku, za ta kashe ni”


Ya ce “Just go in, da safe sai ki je ki yi arranging ɗinsu, tunda yanzu dare ya yi”


Ta ce “No it’s better in je in aje su a kitchen, inyaso sai in yi da safe”


Ya rakata kitchen, sannan ya rakata zuwa ɗakinsu, a ransa yana ayyana no matter what gwara ya aureta Duk da yasan ba karamin daro za’a yi da Hajiya ba