BINTOTO

Episode 3

by @mamanteddy

*ALHERI WRITER ASSO. 📘🖊️*

*A.W.A*

***

_________________________________

```ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ƙungiya masu aiki domin taimakon Al'umma, ƙungiya masu aiki da naxari da ilimi, Alheri daƙo, Alheri gadon barci```

_____________________________________________

*~Not edited~*

Baba mai gona kuwa ganin su bintoto sun haɗe ma ganin sa da ɗalibai yasa shi don dole komawa, yayin da tuni su bintoto suka shige ajin su, wanda tun a aji suka fara rabon mangoro, wanda sai shogowar malaman suce suka dawo daga duniyar shan mangoron.

Bintoto ne tayi saurin ɗaukan hijabin ta haɗi da sakawa tana mai cewa"a miƙo mata mongoron don ta kaima innan ta, nan kuwa cike da tsoron ta lami ta miƙa mata dayawa wanda sai da kanta tace mata ta isa sannan ta bar mata haka.

Su uwani kuwa ido kawai suke bin su dashi haɗi da haɗiye yawu, don sun san ko since bintoto ta sammasu baxata basu ba, musamman yanda sukaƙi bin tana su su shiga wannan gona. Haka suka dinga binsu da ido da mangoron, wanda in bintoto sun haɗa ido sai ta gallara masu harara ta kauda kanta gƴefe.

A haka har aka tashe su xuwa gida, wanda akan hanya bb irin tsiwan da bintoto batayi shiba, ta daki wannan ta tsokani wancan, a haka dai har Allah ya kaita gida lafy.

Bin gidan da tashiga nayi da kallo, wanda gida ne rugurgusashe don ko a ƙauyen daka gani kasan gidan yalakawan tilis ne, don amaimakon ginin jar ƙasa kaman na sauran mutanen ƙauyen to su nasu da kara aka xagaye.

Da shigan ta gida ta tadda innah na surfen waken aikatau, wanda inta surfe baifi abata ladan 20 ko 30 ba, a hakan kuma dashi suke samu suci abinci.

Jiyo sallaman bintoto yasa innah saurin juyowa haɗi da cewa" sannu da dawowa autana. Allah dai yasa ba'ayi tsokanan faɗa ba.? Jin maganan innan yasa bintoto yin murmushi handa ya bayyana dimple ɗin ta wanda shine kaɗai mai kyau a fuskan ta, nan tace"a'a innah yau ba wanda na kula duk da tonona ma da su tanimu keyi, amma sam ban kulasu ba.. Cike da jin daɗi innah tace"yauwa bintoto na haka makeson ji, maxa cire kayan jikin ki kixo ki ɗauki ɗumen tuwon da ɗaxu ta sallah takawo mun. Tohh tacw haɗi da fito ma innah da mangoron da ta'ajiye mata, nan tace inna ta kalla mongoron dana kawo maki.

Kafin innah tayi mgn ne sukajiyo sallaman Abdurrahamanu wanda cike maida hankli nsu gareshi inna ta amsa banda bintoto datasan halin shi sam baya raga mata, kullum a ƙarafi da ita yake, gashi kullum shikenan aikin cewa'tayi tsokanan faɗa wata xubin in innah bata nan har duka take sha.

Kallon ta yy haɗi da cewa"innah wai wanan yarinyan bata wanka ne, tunda na doso nakejiyo tsami ya faɗi yana mai ya mutsa fuska, nan ya wani daka mata tsawa haɗo da cewa"kehhhh wuce ga tuwa can kiyi wanka idan kuma naje na dawo bakiyi ba Allah sai na dakaki a gidannan. Wuce ki bani wuri ƙaxamiya kawai.

Jin tsawan da yy mata yasata saurin nufan madafi haɗi da fara ƙoƙarin juyo tuwan xafin, yyin da take ƙunƙuni tana cewa"mutum kullum a yita damun shi, ita har ga Allah in tayi wanka ciwo takeyi, gashi ayi ta damun ta, ae dauɗa ƙarin ƙarfi ne ya Abdurrahamanu kaida baka sani ba shiyasa kake wanka.

Da fitowamta da ruwa taji inna ta rufe Abdurrahamanu da faɗa akan ya rabu mata da Autan ta, idan ba haka ba kuma xasu saka ƙafan wando ɗaya da shi.

Haka taxo saɓal² don haka jikinta yake, intana tafiya ko inah na jikinta rawa yakeyi, gakuma garin jiki, don bintoto duk saur8 girma ce, datayi dare ɗaya, don a shekaru bayafi 13 ba, amma nonuwa sin cika ƙaiji dam dasu, wanda kace budurwace ƴar shekara 15.

Plz kuyi manage kwans biyu muna ta shagalin biki ne🤩

Amma kuyi manage nasamu kaina tukun, naji comment ɗinku gasky ina godiya sosai, 😍

Sanan naji wasu wai suna vewa bintoto saboda muninta wai ita ba mutum bace lol😂 Tohh mutum ce cikakkiya don ni ƴar team bintoto ne. 😍🤩

*Plz Share to another group*

maman teddy ce🧸 [5/4, 9:10 AM] ***: *Tyiping......*

*🌹BINTOTO🌹*

*Written by:* Aysha moh'd(maman teddy🧸)