free Page 1-2
by @mamanteddy
Wannan labarin kirkirarrene banyarda wani ko wata suyi ammfani wajen juyamun ita ba".
Gareku masoyana na kusa da nesa Ina matukar godiya a bisa ga Soyayyar da kuke nunamun a kullum a kuma koda yaushe,Allah yabar kauna❤️.
```Wannan labari ne da yaxo maku da sabon salon da nasan Zai nishadantar da Masoyan wannan labari,don labrn ya kunshi abubuwa da ban daban,Chakwakyiyar Auren Fullo tayanda aranar Al'adarsu ta Shad'i aka sace Amarya". Koya zata kasance kuma waye musababbi??? Duk Ku biyo ni wannan matashiyar marubuciyar bafullatanan da ta Saba kayatar daku a cikin Littafanta,don nasan baxaku manta da BAFULLATANAN RUGA BA. dama sauran littafan ta dayawa,Idan baki karanta wannan labari ba Agsky an barki baya....Daya daga cikin Zafafan ALHERI WRITERS ASSO".```
*DEDICATION* _wannan littafin gaba Dayarta sadaukarwa ne ga Mahaifiyata,Allah yakara maki lfy da Nisan Kwana Ameeen......"_
*____________________________________________*
*ALHERI WRITERS ASSO📚*
*A.W.A*
```k'ungiya d'aya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da kuma ilimi,Alheri sai D'an Alheri```
***
~*Da sunan Allah mai Rahma mai jink'ai".*~
*_____________________________________________*
"Yafindo...... yafindo...." Wata Yarinya ce dauke da Kwaryan nono saman kanta Wanda a shekaru baxata wuce 12 ba a duniya". Kwada kirar Yafindow take,babu kakkautawa,wanda cikin saurin naga Wata Yar Tsohuwar Bafullatana sanye cikin shigarta ta saken Fulani ta fito daga Gyewayen Bukka tana nufo inda Yarinyan nan take a tsaye". Cikin Harshen fulatanci Yafindo ta fara mata magana da"Ah Nusaiba?!! badai har zaki tafi majalisar Ki saida nonon ba?". Kallonta tayi hadi da Sauke kwaryar nonon sannan Nusaiban tace" a'a Yafindo na tsaya ne na baki labarin Wannan dinnan!!!. Cikin sauri da ganin Lokacin ne ta damuna Yanxu ruwa xai iyah tsinkewa yasa yafindo ta dauki Kwaryar nonon hadi da Kara dorashi saman kan Yar Jikarta ta,tana fadin ehhh Ammara nikaina na kosa naji labarin Wannan din,amma ki je ki dawo,idan kindawo sai ki fadamun yanda Ya kasance a wannan Karon". Cike da gamsuwa da maganar Yafindo ta maida kwaryan nonon tana cewa"Tom Yafindo sai na Dawo". Adowa lfy tayi Mata kan Takoma bayan bukkan ta can nesa tana mai cigaba da tatsar nonon shanun". A majalisar fulanin Rugar ne tun daga nesa Jabb'e yafara washe baki yana bin Nusaiba da kallo,kallon su batayi ba don itah a rayuwar ta na duniya babu Wanda tafi tsana Sama da mazanjen Fulanin su,acewanta duka yan iskah ne,basu da aiki sai cewa suna son mata,da zancen banxah na Idan anyi Auren su da matayensu,a ranta kam dad'a cewa take sai kace matan Azo agani,duka² nawa ne muke Ohoooooo,Ta kurewa dai a Rugar nan kaga yarinya ba'a aurar da itah ba xa'afara tsegumi tom yarinya takai Shekara 13. Sukam mazan harda mai shekara 19 aure ake masa,kwata-kwata basu San darajar mace ba".basa da imani tana kallon kanta ne hadi da tausayamawa kanta,data fito acikin wannan a halin Rugar tana maganan a zuciyarta". Daure fuska tayi tamau hadi da Kauda Kai ta wuce hadi da nufan Inda Aminiyar ta Ta'irriga ke ta aikin Washe Mata baki". Dan miskilin murmushi ta sakin Mata,kan ta karasa ne taji muryan Ja'eee Wanda yake Abokin Jabb'e ne yake cewa"Hoooohoooooo Aradun Allah Jabb'e kayi dacen Mata,wannan kyau haka er duma-duma". Cikin dan Jin dadi Jabb'e yake cewa"Ai Ja'eee Aradu na Auri Ammarah KO kiwo baxan fita ba". Ina tare da itah". Don Nonon da zamu dinga sha tun kan bikin Zan ajiye su". Kirjin Nusaiba ne ya buga dammmmmm---dammm juyowa tayi tana kallon Jabb'e tana mai kasa fahimtar su,Haka abunda suke cewa".don a yanxu sun koma Yaran Hausa ne,don ita bata jin Hausa Sam...tun tasowar ta bata taba barin cikin Rigar su ba,balle kuma har ta fita taje inda ake yin Hausar taji". Su kan jabb'e har gayu da kaudi ake akan iya Hausan nan tasu". Don su suna fita subar Rugar nasu,saboda kiwon su ta shanaye ahaka ne suka iyah Hausan duk da ba sosai bane suma,amma ahaka suke kafille,gashi insun dawo Ruga yammatan Fulanin ayita nan-- nan dasu adole sun waye sun xama yan birni"!!.
Sauke Kwaryan Nonon tayi hadi da durkusawa Kwallah na ciko kwarmin idon ta". Shikenan yanxu Duk ganin sa da nakeyi ya tashi a iskah??? Dama kaman yanda Yafindo ke fadi cewa"Duk shirmen mafarki ne hakan yake?". Abunka ga Fulani da iyah dauriya ga miskilanci kawai sai ta dake hadi da kokarin mayar da kwallahn I donta". "Nusaiba ki share su karki damu,Wlh wannan ne mijinki ba Jabb'e ba". Kawai ki sharesu,ni ta'irriga na fadeki". Kallon ta'irriga Ammarah tayi hadi da cewa"A yaushe ne zan gansa? Hmmm Na fara tunanin kodai abun da Yafindo ke fadi gsky ne?". A yaushe ne zai taho ya rabani da Jabb'e da fitinan sa?'!.
Dafota Ta'irriga tayi hadi da cigaba da cewa"Zaki gansa Inshaaalhu,ki manta da Jabbe a rayuwan ki". Shifah KWARYAR SAMA NE,mai bugun ta kasa,bana tunanin shidin mutum ne kaman saura". A yannda nake ganin sa ko yan birnin mu bai Kama da suba". Shiru Ta'irriga tayi don a rayuwarta tanason labarin Wannan Din nan dasuke masa lakabi da KWARYAR SAMA". Hmmm Yau wani irin Mafarkin shi kikayi ne Nusaiba"?. Dariya Nusaiba tawa Ta'irriga kan ta kuma gyara zama tana Fara cewa"Yowa na Ganshi cikin wata irin shiga ta Alfarma,Wanda nikaina idan na tuno yake sanyawa naji wani irin nishadi mai wiyar misaltuwa". Tuni fulanin sayar da nonon suka Fara kyewaye Nusaiba,don kowa yariga da yasan labrn man Nata, tana koro masu bayani....suna Washe baki, keeeee Nusaiba wani saurayi ne kkyi??. Tab Nusaibah yau darana zakiyi ne??? Aradu Sai antsayar mana da Shaidawar Auren mu a Yau". Na gaji gakinan kin girma tun kina shekara hudu nake rikon ki,yau zanje nasamu Hardo,kuma namawa Liman magana". Kallon sa batayi ba tamaishe shi kaman Gaulah.
Kaman iskah don har tsalle yake saboda rashin kiba ya juya yyn da su Ja'eee suka Mara masa baya da Fadin A wannan Tauraron ayi komai a gama kawai Jabbe"..... Tuni Ta'irriga cikin ta ya Dora ruwa". Nusaiba munga banu yooo". Ya zamuyi yanxu?". Shiru tayi kan tace"Abun da Allah yanufah shi xai faru Ta'irriga,amma a yo kona Auri Jabb'e tabbas na fadeki zan Auri Ammaru". Cikin sauri Ta'irriga tace"Ban gane ba,ta yaya kikasan Sunan sa"?. Murmushi tayi hadi da xubamawa Wani yaro nonon da yaxo siya sannan tace" a Mafarkina mana". Sauran fulanin da basu San kan maganar bane harda Inna Wuri suka jahhh tsaki suna cewa"Wai yanxu dama Wannan labarin mai Dadi duk a mafarki ne?". Shine kuka zauna kuna 6ata mawa mutane lokaci"!. Daure fuska Nusaiba tayi kan Ta'irriga tace Ku dai kuka Zauna,ai babu Wanda ya xaunar daku". Cike dajin Zafi Don Innah Wuri Kanwar Ja66e ne nan tace"Hauka kikeyi acikin Daji,don Jar6e KO kinki KO kinso shine Angonki,kuma a wannan satin za'afara shirye-shiryen Shad'i". Tana fadin Haka ta dauki kwaryar Nonon ta don dama ta kammala sayarwa ta bar Majalissar". Da kallon sama da kasa suka bita har ta wuce sannan kowa takoma ga Sana'ar ta". Kafin lokaci kalilan tuni suka gama sayar da Nonon suka tattaro hadi da nufo hanya". Sunayi suna ta6a hiran su Wanda yawancin sa akan Ammaru ne". Sai da Takai Ta'irriga har bukkan su sannan ta nufo hanya tasu Bakkun". A hanyane tafara tuno da maganar Ja66e aiko kawai sai ta juya hadi da Fara shiga cikin wata Daji mai Wuyar fasaltuwa". Wanda dagani kasan ba irin Abun da baza'a gani a cikin ta ba". Tafiya tayi mai nisan gaske,wanda a haka ta Fara Hango Mahaifinta kyewaye da shanayen sa yana aikin basu ruwa a Wani Rafi". Kan dutse ta nema ta Zauna tana tunanin Rayuwarta Dana Mahaifin Nata".anyahhh xata iyah Rabuwa dashi kuwa?". Sosai tayi nisa a tunanin Rayuwarta da yanda Ja66e yake sanya Mata ido". Shikam Hardo tuni ya hango Diyar tasa, tun isowanta shiyasa ya ajiye sandar kiwon hadi da Fara nufar inda take a Azaune". Sam bata Lura da zuwansa ba,saboda tunanin da ta lulah". Nusaibatu". Cikin sauri ta dago hadi dabin Hardo da Kallo". Sai tasakin masa murmushi tana fadin Abbah Hardo nazo Ganin Kane kan nakoma bukka wajen Yafindo". Murmushi yy cike da dan jindadi ganin diyartasa ta Saki,yace"Daga ina ne kk yanxu?". Dandali". Na sayar mawa Yafindo da Nono ne?". Kallon ta yayi hadi da cewa"tom maxa ki tafi Ruga,kinga yafindo na nan tana jiranki tom Abbah". Tace hadi da kwasan Kwaryan nonon tana dorasu bisa kanta". Tafara tafiyane ta dawo da baya tana cewa"Abbah Hardo Ja66e ya taho nan?". Binta da kallo yy don dama sai a sannan ya fahimci damuwanta". Daga Mata Kai yy,kan a hankali ta juya tafara barin wurin,jikin ta sosai yayi sanyi"........
Tana tafiya tana tunain tabbas tasan bazata Kara mako guda da Iyayen nataba". Haka take tafy kaman kwai ya fashe Mata a ciki". Babu abun da takeyi sai tunano da Ammarun Mafarkin ta".
*K'ASAR SUDAAN*
Kwance yake yayi nisa wurin yin Abun da yazama masa jinin jikinsa". Gudu take tana kwada kirarsa yyn da gaba dayanta binta da kallo yake kaman wata halitta ta dabam". Cikin Sauri ya Fara tahowa hadi da kusantota,amma kuma sai tana jah baya". Wanda kan yy Aune yaga tayi baya Hadi da Fadawa cikin Wani irin rami mai Zurfin gaske wanda sam baya iyah Hangota". Cikin Wata irin muryan Firgici da Rikicewa Ya Kwada kirar Sunan ta da OUMMU AMMMARAH"...!!!
Gigiffff ya farka yana mikewa daga kwancen da yake Zufah ya jigashi shar6am kaman Anwatsa masa Ruwa". Shaheedat dake gyefen sa tana Dannah laptop ne tayi saurin jiyowa jin ya ambaci sunan Yarinyan da tafi kowa tsana a duniya". Sunan da ya ambatane ya Fara yimata yawo a kwakwalwa,wanda da Alahma Abarcin sa ne yy furucin!". OUM AMMARAH". komawa yayi ya lumshe ido yyn da cikin sauri ta nufesa tana Dago kansa ta Dora saman cinyarta tana shafa Sumar kansa cikin Harshen larabci naji tana masa magana da cewa" Ya Nury Ma'asabikkk??? Shiru yy bai bata amsa ba,sai sauke ajiyar zuciya da yakeyi,Shirun da Takuma jine yasa ta Kara kiran sunan"Nury?". Bude idon nasa yayi wanda sai a sannan nayi duba xuwa garesah". Subhanallh". Kyawunsa bakaramun furgitani yy ba". Matashin Saurayi ne wanda a shekaru baxai Haura 28 ba. Yana da Dara-daran Ido,duk da kasancewar su a lumshe Wato Segxy Eyes....yana da Dan karamin Bakin wanda Labbansa na kasa yana da Dan tudu kadan,hancin sa Kam da gani kasan Na larabawa ne Usulll don dauke yake da Madaidaicin Tsawo,wanda yake da dan kauri kadan,fuskan sa kam keyewaye da Siririn saje da ya hade da Sumar Kansa baki mai sheki kwantacce luff.
Kallon fatansa Baki ne ba Fari ba,amma yanayin kyaun fatan nashi tafi ta Fararan kyau da Daukan ido.... Wanda kalon Ake kirar sa da Bb colour". Cije la66ansa yayi wanda cikin dan nauyi da Miskilanci na rashin son magana cikin Harshen larabcin su yace"Shaheedat Kiramun Ammie na".Zaro ido tayi cikin kissar Su ta larabawa takai bakin ta dai-dai saman lips din sa tana Kissing,hadi da shafa sumar kansa,sauke ajiyar xuciya ya farayi wanda bata daina ba sai da taga yasamu natsuwa hankalinsa ya dawo jikinsa". Ka kwantar da Hankalin Nury, Kayi bacci yanxu".
ta karke maganar tana Kokarin jamasu bargo". Mikewa yayi yi hadi da bin Wrist watch din sa da kallo, wanda naga an rubuta A.A.Y. Ajikin ta". Ba tare da yabata Amsa ba ya nufi wadrop wanda cikin sauri tabi bayansa tana fiddow masa Da Kayan da Zai bukata,fuskar sa tamau don dama Haka yake ta mika masa Rigar Wankan sa,nan ya nufi Toilet don Watsa Ruwa". Biyo bayanshi tayi da nufin tayashi wanda cike da dakewar murya wanda dagaji kasan Namiji ne tsayayye da ya amsa sunan sa yace". Ya isah". Ya fadi yana daga Mata hannu batare da ya juyo ya kalli inda take ba". Turuss tajah baya ta tsaya". Yyn da shikuma yy cikin Toilet don watsa ruwa KO yaji sassauci a xuciyar sa". Yana a tsaye ne sai yaji knocking,wanda cike da ixxah ya ce"yes come in". Yayi maganan saboda sanin mai kula dashi da masa irin wannan hidimar wato Shirley Baturiya ce". Jiki na Rawa ta shigo wanda kallonta bayyi ba ya zauna akan wani dan Tum-tum mai Kama da Resting chair.
Cikin sauri baki na Rawa ta duba garesa tana masa barka da Warhaka".amma sai naga ya kawar da kansa gyefe yana Kara kishingida kaman yasamu Irin lafiyayyan Falon nan,daga kansa yayi yana bin dankareren plasman dake makale jikin bango daga sama da kallo". Itakam Shirley komawa tayi hadi da jah baya ta nufi Baf din ta cikashi da Ruwar dumi da Sabulai masu kamshi wasu gyefe guda". Mika masa rigar wankan sa tayi yyn da shi kuma yasaka Hannu ya Amshe fuska babu Annuri ya wani hade girar sama da takasa". Juya masa baya tayi saurin yiiiii....yyn da A abunka ga Balaraben Sudaaan Sam basu wani San Darajar Kansu ba indai ga mata ne". Cire Kayansa yafara yyn da Yana cire t.shirt din jikinsa ya Daura Towel din a kugunsa wanda yake gyefen sa,sannan ya cire komai na jikinsa". Nufan Baf din yayi kan ya juyo ya kalleta"okay Sir". Abun da tace kenan wanda kan yace wani Abu tuni ta fahimci komai". Juyawa tayi hadi da ficewa yyn da sai A sannan ya Shiga Baffff din domun ya Watsa Ruwan,lumshe idonsa yayi yana Tunano yanayin da ya Ganta, da yanda Hawaye kebin kuncinta". Lokaci daya idonsa ya kada daga fari xuwa jahhhhh.....Cije lips din sa na kasa yy yana Furta Ina Zanganki OUM AMMARAH?. Tsawon wannan dakikun yana aikin tunanin ta Wanda ya kasance kuma ya zaman masa jinin jikinsa". Daga bisani ne yafara motsa hannun sa don watsa Ruwan".
Hohooohoooo Nusaiba Ayyiiiriiiiriii Allah ya nunamun wannan lokaci nusaiba Amaryan Ja66e Kai mashaallhu,Aradun Allah Jikata taxo da Tauraro mai Haske". Duk yafindo ne mai wannan maganan tana yi hadi da Rawa da Hannun ta tana Juya kwaryan dake cike da nonon Fulani". Tuni idon Nusaiba yakawo ruwa kasa cemawa Yafindo komai tayi don takaici,Ya isah yafindo!!. Ta fadi hawaye na bin kuncinta". Juyawa tayi ga Ummah dake tatsan nonon Shanu a tsugunne don itakan ta Tausayin Yar Nata takeyi". A cewanta nun Yarinya Ce karama,kuma ta fahimci Sam babu shakuwa tsakanin ta da Jah6e".
Oumma Shatu kiji fah Abun da Yafindo ke fadi??. Kice ta barmun wannan maganar,ni baxanyi aure ba Aradu!!". Kee!!!! Kulll!". Ya isah,Auren ne baxakiyi shiba?,tom be xakiyi? Kar na sakeji,KO Umman ki gata nan shekararta 10 akayi Aurenta da Hardo,kuma a haka suka Haifeki,kya amma shekarar ki 12 kina Wani magana,tom Nan da mako Biyu xa'ayi Auren ki da Ja6e,don haka wannan shanuwan dakike mgn kinaso,ita xan bai maki". Turo ba Nusaiba tayi kawai sai ta juya hadi da shigewa Bukkan Oumman ta tana maijin Zafin Ja66e.
*ABUJA*
Misalin karfe 8:30pm. Familyn Alh.Ahmad Garba ne duka Zaune a Dinning Area don yin dinner din su,kowa ka gani fuskar sa Dauke da Farin ciki,wanda badon komai bane ba sai don dawowan Mahaifin nasu.....Haj. Hindu ne zaune gefen Mijin Nata,sai Yarinyan ta Nahilart wanda dagani kasan gata da sangarci yayi mata yawa. Sunan tana kujera ne Amma ta Dora kanta bisa kafadan Mahaifin Nata tana masa kukan sangarci. Cike da masifah Fauzan Yasoma cewa'"Momy Nahilart tana damuna banason Koke-koken nan Mara Amfani". Calm down my son.....".Haj. Hindu ta fadi tana Dafo kafadan Fauzan da ranshi yayi k'ololuwar b'aci akan rigimar da Naheelat take masu mara Ma'anah........
More typing........... More comment
--------------------------------------------------------
```Kardai Ku sha'afa 🤩 Wannan littafin Zazzafa ne daga cikin gwarazan zafafan Alheri writers....Wanda suka had'a da:```
_*K'WARYAR SAMA🙄* zazzafa daga Alk'alamin *Maman teddy🧸*_
_*JININ SARAUTA(the gorgeous royal blood)* zazzafa daga Alkalamar *Hassenart Bamalli(oum Aphnan)*_
_Idan kinason biyan *NORMAL PAYMENT* ne ,to kowanne littafi d'aya *#100* ne duka biyun ne *#300*_
_Idan kuma *VIP* ne kikeson biya toh,kowanne daya *#200* ne ,in kuma duka biyunne *#500*_
_Idan kuma *SPC* ne kikeso toh kowanne d'aya *#300* duka biyun kuma *#700*_
_Zaki iya biyan kudinki ta daya daga cikin wannan hanyoyin biyan:_
_*BANK PAYMENT*_
7782217014 Mohammed Hassana Fcmb
_*VTU TRANSFER*_ ***
_*MTN CARD PAYMENT*_ ***
_*SAI KI TURA SHAIDAR BIYANKI TA HANYAR SCREEN SHOTTING EVIDENCE DINKI TANAN👇:*_
***
_SAI MUN JIKU MASOYAN AMANA,KUYI ZUWA DAYA KU KAFCI RABONKU CIKIN SASSAUK'AR FARASHIN GASKE🤌_
_Maman teddy🧸_ _Oum Aphnan takuce_v [7/7, 1:47 AM] Maman Teddy🧸: *⛲K'WARYAR SAMA⛲*
*Na Ayshatou* *Mmn teddy🧸*