A SILENT RETURN
Tap the link below ⬇️ to join my WhatsApp group
***
COMMENT SECTION ⬇️
***
⛔️ WARNING!
Duk wanda ya sake taba min ko da harafi ɗaya ne a cikin littafina, ya shirya fuskantar tsautsauran mataki. Wallahi ba zan kyale ba!
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER EIGHTY ONE:81*
*A SILENT RETURN*
*JIDDAAH BARKUM*
————
A hankali ya ajiye wayar a gefen sofa, sannan ya juya da wancan takun nasa mai cike da izza da kwarjini, ya nufi corridor ɗin da ɗakunan suke.
Raihana kuwa bata sake tsayawa bata wani lokaci ba, da sauri ta fara maida buttons ɗin rigarta yadda suke, hannuwanta suna ɗan rawa saboda irin yanayin da take ciki. Ta janyo veil ɗinta da ya riga ya kama gabansa tuni, ta maida shi ta dukunkune shi ba tare da ta damu da ya yi kyau ko bai yi ba ba. At this point, she just wanted to leave, kai tsaye ta juya, ta kwashi takalmanta a hannu, sannan ta yi waje da sauri.
Honestly, ba don tana tsoron ta tafi ya sake ɗaukar zafi ko ya bi ta da wata muguwar manufa ba, musamman yanda yake cewa ta raina shi, wallahi da babu abin da zai hana ta yi tafiyarta kawai. Amma sai ta ji tana wani mugun shakkarsa, wani irin shakku ne da ita kanta bata iya bayyana masa suna ba. A dole ta tsaya a gefen motar tana jiransa, takalmanta a hannunta, kanta a sunkuye, seconds suka fara wucewa, then minutes.
Wasa-wasa, sai da ya yi kusan mintuna ashirin kafin ta fara jin alamun ana rufe ƙofar falon, da sauri ta ajiye takalmanta ta zura su a kafarta, duk da jin ƙarar ƙofar, saida zuciyarta ta buga da mugun ƙarfi tamkar zata fasa kirjinta ta bullo. Amma ko da wasa bata yi gangancin juyawa ba, domin kuwa iya uban bugun da zuciyarta ke yi ma na each step da yake ɗauka zuwa wajen motar kaɗai ya isheta. Ta tsaya kawai tana kallon ƙasa, tana damke da gefen abayarta wacce taci uban squeezing, sai dai duk wani taku da take ji yana matsowa kusa da ita yana ƙara mata nervousness, har sai da ya iso wajen motar.
Ba tare da wani dogon bayani ba, ko kallonta bai yi ba, ya buɗe driver seat ya zauna. Raihana ta sauke wani irin numfashi a hankali, sai ta juya a hankali za ta buɗe backseat, saboda wallahi bazata iya zama a kusa da shi ba har su je gida. Ta kama handle ɗin ƙofar, tana shirin shiga kenan, muryarsa ta daki kunnenta, “Waye driver ɗinki?” Raihana ta tsaya still, ta ɗan ɗago kai, kamar bata fahimci abin da ya faɗa ba, ta dan kalle shi ta gefen ido, shi kuma bai sake cewa komai ba, kawai ya zauna a driver seat ɗinsa yana jiran ta dawo gaba.
Raihana ta kalli backseat ɗin, ta sake kallon shi, ta sake kallon ƙofar da take riƙe da ita, Zayd har yanzu yana zaune shiru, sai kawai ya juyo da kai a hankali, idanunsa suka sauka kanta, wannan kallon nasa… shanyayyun idanun nan nasa da ba sa buƙatar explanation. Raihana ta haɗiye yawu, ba shiri ta saki ƙofar backseat ɗin ta maida ta ta rufe, Zayd bai ce komai ba ya maida kanshi gaba.
Ta zagaya zuwa front seat, ta buɗe ƙofar, ta shiga a hankali, sannan ta zauna tana takurewa a gefe, jikinta ya manne da ƙofar kamar kazar da aka tsamo a ruwa. Zayd bai sake wani yunƙuri ba, kawai ya saka key, ya kunna motar, daga nan ya fice daga guest house din cikin nutsuwa.
Raihana kuwa ta zauna shiru, hannayenta a haɗe a kan cinyarta, idanunta a kan window, a zuciyarta, babu abin da take saƙawa sai tunanin yadda za ta iya kallon mutanen gidan, gani take kamar kowa zai fahimci abin da ya faru, musamman yadda take a yanzu a burkice, confused, kuma har yanzu jikinta cike yake da firgici, “Ya Allah… ta yaya zan shiga gidan nan?” Ta sauke numfashi a hankali, ta sake kallon window, tana ƙoƙarin haɗa nutsuwarta waje ɗaya.
Motar ta ci gaba da yanke tituna cikin nutsuwa, amma a wajen Raihana kamar tana kan kaya take, literally sitting on needles and pins, kowane ƙaramin motsin motar sai ya ƙara mata tunanin abin da ya faru. Abin da ya fi ba ta mamaki kuwa shi ne Zayd, shi dai ko a ƙwallar rigarsa yana nan yadda ya saba kasancewa ko yaushe, in fact, a yadda yake zaune a driver seat ɗin, hannuwansa steady a kan steering wheel, face ɗinsa blank, idanuwansa a kan hanya… za ka ɗauka kamar bai san Allah ya yi ruwanta a wajen ba ma, kamar babu komai, kamar babu abin da ya faru, kamar shi ne mutumin da ya fi kowa calm a cikin duniyar nan.
Raihana ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, “How can he possibly be this calm?” Ta ayyana a ranta, ta buɗe idanunta a hankali, ta sake kallon window, a zuciyarta kuwa, tunani ɗaya ne kawai yake ta dawowa ba kakkautawa, yanzu idan Ummie ta kalle ni fa? Idan Suhaila ta tambaye ni ina mu ka je fa? Idan suka lura da yadda nake? Ta haɗe hannayenta sosai a kan cinyarta, tana ƙoƙarin danne tashin hankalin da ke cikin zuciyarta. Amma Zayd… yana nan, shiru, calm, composed, zero care in the world, fuskar nan tashi ɗauke da wata irin cold, unbothered composure da ta saba zama alamarshi, ko kaɗan babu wani alamar guilt ko wani remorse a tare da shi, shi a wajensa, it was just another casual day, yayin da ita kuma take kokarin maida nutsuwarta yadda take, shi kam kamar dai kawai yana driving ne, ba tare da ya san cewa matar da ke zaune kusa da shi tana ƙoƙarin tsira da embarrassment ɗinta ba. Raihana ta ɗan lumshe ido, “This man is unbelievable,” sai ta sake kallon hanya ta window, ta ƙi kallonsa ko da sau ɗaya ta cigaba da ƙidayar seconds ɗin da suka rage kafin su isa gida.
A can kuwa, Seeyama da Safina suna driving a hanya, motar Seeyama na yanke titin cikin sauri. A wani ɓangaren kuma, Zayd ya karyo kwana ya ba kokarin canja lane zuwa wanda zai sadashi da hanyar estate din ARMAAN. Zayd ya ɗan ɗaga idanunsa zuwa rear-view mirror, duk da sun yi ɗan nisa da juna, sai ya dan rage gudu sosai kaamr yana son tabbatar da abinda yake gani har sai da motar Seeyama ta zo crossing ɗin da suke bi, kiris ya rage ace ga motar ta ga tashi bumper to bumper, sai idanuwansa suka kama wata number mota da ke bayan su da kyau yana tabbatar da motar, ya ɗan kalleta na seconds kaɗan, sannan ya sake maida hankalinsa kan hanya, ya kara gudu sosai, a ransa kuwa ya ayyana, wato sai da ta fita, ya sake kallon mirror ɗin a hankali.
A lokacin ne Safina ta ɗan karkata kanta, tana kallon motocin da suke wucewa a gefensu, sai kawai idanunta suka sauka kan motar da ke ɗan gabansu, abinda ya ja attention dinta bai wuce ganin motar t rage gudu sosai ba sai kuma kaamr wanda aka zabura ta sake figa a guje, ta ɗan matse idanunta, kamar tana ƙoƙarin tabbatar da abin da ta gani, ARMAAN 004, “Kallii, Safina… kee, wancan motar kamar Zayd ne a ciki.” Safina ta kalli motar da kyau, amma kafin ta sake cewa komai, motar ta riga ta wuce su dan tayi nisa sosai, ta ɗan juya kai tana kallonta har ta ɓace daga ganinta, “Haba! Mr. Armaan ɗin ne zai fito a lokacin nan da ranar Allah ƙarfe uku fa? Ba wani guards, ba convoy… sai dai wani a cikin yan gidan.”
Seeyama ta daki steering ɗin da hannunta, ta cije lips ɗinta cikin frustration, “Ban taɓa jin na tsani tinted ba sai yau kinga da yanzu na kore shakku na gano waye…” Ta sake kallon glass din gaban motar, tana ƙoƙarin gano motar da ta riga ta wuce, ta yi tsaki, “But kin san Suhaila is hardly ta fita ita kaɗai.” Safina ta juyo ta kalle ta, “Idan ma shine, meye? Yanzu da kin amince an miki maganinshi da zakiji wani darrr ne dan kin haɗu da shi a hanya saboda kin fita ba izini?” Seeyama ta ja tsaki, ta ƙara ɗaure fuskarta sosai, “Ki daina min maganar wannan mutumin.” Safina ta kalle ta na ƴan seconds, sai kawai ta harare ta, bata sake cewa komai ba, ta ɗauke kai ta maida kallonta gaba. Seeyama kuwa ta ci gaba da driving, zuciyarta cike da saqe saqe.
Motar Zayd ta tsaya a daidai bakin gate, gateman da ya ji horn ɗin ya fito da sauri, yana son ganin waye, da ya ga motar, sai ya juya da sauri zai buɗe gate, amma Zayd ya kirashi, “Come back.” Gateman ya dawo da sauri, Zayd ya kalle shi a nutsuwarsa, sannan yace masa, “Ba sai ka buɗe ba, ba shiga zan yi ba.” Gateman ya ɗan tsaya, ya kalli Zayd sannan ya sunkuyar da kai, “Yes, sir,” ya juya ya koma bakin gate din.
Raihana kuwa ta ɗan kalleshi ta gefen ido, wato shi ba zai shiga ba… ita ce zata shiga? Nan take wani irin malolon baƙin ciki ya sake tokare mata wuya, ta haɗiye yawu da ƙyar, idanunta suka tara ƙwalla, ya juyo a hankali ya zuba mata wani shegen kallo daga sama har ƙasa, kallon da ya sa Raihana ta taji kamar ya juyo ta zabga masa maruka sabida takaici, sannan yace a taƙaice, “Fita min a mota.”
Raihana bata sake wani irin tunani ba, ta sa hannu ta buɗe motar, ba tare da ta kalli direction ɗin da yake ba, amma hakan bai hana ta jin yadda idanuwansa ke yawo a kanta ba, ta sauka daga motar, ta gyara veil ɗinta da sauri, sannan ta fara tafiya, kanta a ƙasa, ba ta son ta ɗago ta kalli ko ma waye, amma yanda take dosar ƙofar gidan, ji take dama ta buɗe idonta ta ga kanta a ɗakin Suhaila, a kan gadon da ta fi zama. Zayd kuwa ya bita da kallo, wani ɗan iskan murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, he knew how she was feeling, ya san wannan kunyar da take ji, ya san irin embarrassment ɗin da take ƙoƙarin ɓoyewa, amma wannan shi ne maganin mara kunya da bakinta baya tauna magana kafin ta furta masa, sai ya ɗan girgiza kansa a hankali, snn murmushin ya ɗan ɓace daga fuskarsa.
Daga nan ya fara tunanin wajen zuwa, ba don yana da wajen zuwan ba, sai dai shi da kansa ya san cewa ba zai iya shiga gidan tare da ita ba, ya zauna na ɗan lokaci a driver seat, hannunsa har yanzu a kan steering wheel, sannan ya ja numfashi a hankali, ya kunna motar, kamar babu abin da ya faru, amma kafin ya tafi, idanunsa suka sake bin hanyar da Raihana ta bi, sai kawai ya ga ƙofar gidan ta rufe a bayanta daga nan kawai ya fice daga unguwar.
A haka Raihana kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, kanta a ƙasa, amma dai tana ƙoƙarin daidaita kanta, ta yi sallama, ta shiga lounge ɗin, gabanta na tsananta faɗuwa, kowa kam ya amsa sallamar, amma akwai wata bakuwar murya a kunnen Raihana wacce bata saba jin ta a gidan ba. A nutse, kanta a ƙasa, ta ƙarasa gaban Inno, ta sunkuyar, ta fara gaisheta, Inno ta amsa, tana kallonta ƙasa-ƙasa, sai ta ɗan ɗago kai a kunyace, ta gaida Ummie ma dake kallonta, itama fuskarta a sake ta amsa, “Welcome daughter.”
Raihana ta sake sunkuyar da kanta a hankali tana jin kamar Ummie ta gane wani abu, ta dan damke gefen abayarta kamar tana neman ya bata courage ne. Daga nan ta juya, Haj Hauwa ce da Haj Balaraba zaune a kan two-seaters, kowacce cikinsu taci uban gwalagwalai, wannan tana wane, wannan gasu nan kamar wasu matan shugaban ƙasa, sai baza kamshi suke a binsu, Raihana ta ɗan sunkuyar da kanta tana gaishe su, tana ƙoƙarin yin murmushi duk da zuciyarta da take neman tserewa daga ƙirjinta, amma sai Haj Hauwa tayi ƙaraff ta kamo hannun Raihana, tana janyo ta, ta rungumeta, tana wani murmushi, “Daughter! Ina kika je ne? Tun dazun na zo nace rabon da na ganki, tun da muka je can gidan, gashi har kin kwana uku a nan bamu haɗu ba!” Sai ta ɗan janye ta daga rungumar, amma har yanzu bata cikata jikinta gabadaya ba, tana bin fuskarta da wani kallo bakinta dauke da murmushi, wani irin murmushi ne da ya sa Raihana sake sunkuyar da kanta, ta sake kakalo murmushin yaƙe a fuskarta, ta na haɗiye yawu, ta sake sunkuyar da kanta.
A ranta kuwa, ya Allah… don Allah kar su fara tambayata ina na je, domin a wannan lokacin, ita kanta bata san yadda za ta yi musu bayanin komai ba. A hankali ta sake dago idanunta, nan take kuwa suka yi arba da na Ummie, Inno, da ma Haj Balaraba, kurrrr, kowa na kallonsu da nashi tunanin a zuciya. Ummie kuwa ta sauke wani irin numfashi a hankali, tana kallon Raihana wacce take kamar tana neman inda za ta ɓoye kanta, sai a cikin sanyin muryarta tace, “Daughter, go upstairs and get some rest. Later, she’ll come and do everything for you here at home, okay?” Raihana ta ɗan ɗaga kai, sannan ta sauke ajiyar zuciya, a zuciyarta kuwa, ta gode wa Allah da ya sa Ummie ta kuɓutar da ita daga wannan wajen da bata jin daɗin zama ko second ɗaya.
A hankali ta zame daga jikin Hajiya Hauwa, ta gyara veil ɗinta, sannan ta fara tafiya a nutse, ta nufi upstairs, amma yayin da take tafiya, ta kasa ɗago kanta, domin har yanzu idanun jama’ar wajen suna cigaba da binta, kowacce fuska da ta wuce sai ta ji kamar suna kallonta da wani irin tambaya. Raihana ta ƙara saurin takunta kaɗan, ta haura matakalar a hankali, tana sauke nunfashi da godiya ga Allah, amma still a cikin zuciyarta… ta san babu wanda ya bar ta cikin wannan lounge ɗin da bai yi mata aƙalla tambaya ɗaya a zuciyarsa ba.