HARAMTACCIYAR GADA

CHAPTER 20

by @hafnancy

*HARAMTACCIYAR GADA.*


_*{Ha蓷uwar rayuka da 茩addara ta tattara wuri guda.*馃敟馃挃}_


*NA*


*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*


*SADAUKARWA GA UWAR茒AKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*


*BOOK 1*

    

 *Page 20.*


"Wallahi ban san komai ba, amma na tabbata ba nemanta yake ba musamman idan yana da sanin cewa yar'uwarki ce. Kawai iyalan Yallabai sun 蓷auka cewa ita budurwarsa ce shiyasa Hajiya ta cutar da ita."


"Hmm Aliyu karya kake! Na tabbata Haj. Nafeesa kamasu tayi dumu-dumu shiyasa ta kai ga cutar da ita. Don haka kabar raina min wayau, kai ne amintaccen yaron Yallabai, duk wani sirrinsa ina kyautata zaton a tafin hannunka yake kawai wannan cin amanan ne kake kokarin 蓳oye min don kar hankalina ya tashi."


Zuwa yanzu ta kai shi wuya, ya ce"Idan kina zargin nemanta yake, Ok so be it. Ke wacece da ba za aci amanarki ba? Have you forgotten so soon that ke ma 蓷in cin amanar uwar dakinki kikayi? Secretly got married to her father?"


Sosai Jidda ta cika da mamakin maganganun da ke fitowa daga bakin Aliyu.


Kafin ya ankara hawaye ya fara rushing kan fuskarta, muryarta na bala'in rawa ta ce"Aliyu ni zaka kalla ka gaya min maganganu son ranka? Kar ka manta fa matsayina da na Haj. Nafeesa 蓷aya ne a wajen ubangidanka."


A zafafe ya ce"Wallahi kar ki yaudari kanki da tunanin cewa matsayinku 蓷aya ne. Ita Haj. Nafeesa duniya ta san da cewa matar Executive Chef Jalal ce. Amma ke fa? Waye ya san da ke a rayuwarsa? Waye ya san irin matsayinki a wajensa? kin zab'i ku ci gaba da rayuwa a cikin duhu."


Ya girgiza kai ya ce"Let me tell you wallahi kanki kike cuta saboda shi namiji ne kuma yana iya canzaki a duk lokacin daya so kuma babu abin da ya dame shi. Idan baki sani ba aurenku a yanzu rawa yake sosai tun wuri ki farka daga dogon baccin da kike kafin lokaci ya kure miki."


Jikinta na rawa sosai ta ce cikin tsananin mamaki "What? Dama duk wani abin da ke faruwa tsakanina da Yallabai ashe ka san komai? Kwashewa yake yana gaya ma?"


Murmushin ya yi, ya ce"Hmm naki wasa ne, ai tsakanina da Yallabai akwai kyakkyawar alaka da amana. Yallabai baya 蓳oye min damuwarsa kamar yadda nima bana 蓳oye masa, Jidda komai na sani har cikinsa da kike 蓷auke da shi. Shiyasa nake son kiyi amfani da damar da Allah ya baki domin Yallabai mutumin kirki ne, idan kika bari ya juya miki baya baki yi abin da ya kamata ba, to ina mai tabbatar miki ba zaki iya mayar da hannun agogo baya ba saboda shi mutum ne da idan ya yi gaba baya waiwayan baya."


Ji tayi kamar an da蓳a mata wu茩a a 茩irji saboda maganganunsa ba 茩aramin sukarta suka yi ba.


Har ta bu蓷e baki za tayi magana ya rigata.

"Please idan ba zaki damu ba hannayena sun gaji da rike kayan nan, kuma na tabbata by now ta riga ta farka kuma babu mamaki ta fara jin yunwa, idan na kuskura nayi sakaci da aikin da aka dora ni akai, Yallabai zai kama ni da laifi, So pls allow me to perform the duty assigned to me."


Yana gama fa蓷in hakan ya rab'a ta gefenta ya shige ciki da saurinsa, ta bishi da kallo hankalinta a matukar tashe.


'Idan har ba wani matsayi Saffy take da shi a wajen Yallabai ba meyasa zai 蓷aukaka ta haka?'


Taso ta shiga amma aka hanata wai sai Saffyn ta kammala breakfast. An san yar'uwarta ne amma ansa tsassauran doka na hana mutane ganinta saboda yanayin condition 蓷inta.


At exactly 7:40am daidai Chef Ali ya shiga cikin 蓷akin da aka kwantar da Saffy, ya tarar already ta tashi har ma tayi kokarin rama bashin sallolin da ake binta. Zaune take kan sallaya tana jan carbi lokaci zuwa lokaci tana sa tissue tana goge ruwan hawayen da yake 蓷an zubowa daga idonta.


Chef Sam dake zaune yana latse-latsen waya, yana ganin Ali da kaya ya mike ya nufesa ya karbi leda 蓷aya.


A hankali Saffy ta waigo ta dube shi ta ce"Good morning sir!"


Chef Ali ya 蓷an kago murmushin dole ya ce"Good morning Ma! Ya jikin naki?"


A kasan makoshi ta amsa da "Alhamdulillah!"


Chef Sam yace" Idan kin idar ga breakfast ya iso kizo ki karya kafin likita ya shigo."


"Har yanzu yar'uwata bata iso ba?"


Kallon juna suka yi shi da Chef Ali kafin Chef Sam ya ce"Ta iso tana waje har ta shigo ta dubaki lokacin kina bacci, amma yanzu dai ki samu kisa abu a ciki kafin mu bari masu dubiya su fara shigowa dubaki idan likita ya bada umarni."


Kuka ta fashe musu da shi tana fadin"Dan Allah ku batta ta shigo ina son ganinta please."


Dakyar suka amince Jidda ta shigo ganin yadda ta daga hankalinta ainun.


Chef Sam ne ya fita kiran Jidda, ita ma dayake a jiraye take, da sauri ta biyo bayansa, burinta kawai tayi ido biyu da yar'uwarta.


***


A can station, isar Yallabai babu jimawa DPO ya iso akan lokaci kamar yadda yayi alkawari, kusan a tare suka shigo tare da Dr. Haseeb da shi ma yazo a san abin yi, daga nan zai tafi asibiti don tabbatar da cewa Saffy na samun kulawar data dace.


Bayan DPO ya zauna kan seat yasa aka ba Yallabai da sirikinsa Dr. Haseeb damar shigowa ofis. Sun gaisa a mutunce sannan ya basu damar zama.


DPO ya ba wani 蓷an sanda umarnin yaje ya taho dasu Haj. Nafeesa sannan yasa aka karbo report 蓷insu ya fara dubawa.


Yana cikin dubawan ne ya samu kira kai tsaye daga CP wato kwamishinan 'yan sanda.


"A kashe case 蓷in attempted murder of wata Safiyya Kabir sannan a hanzarta sallamar Samha Jalaludden Alkaleri da mahaifiyarta da ke tsare a wajenku, kuma banaso a sake tada zancen."


Sai da DPO ya bar gabansu Yallabai ya fita waje sannan ya iya bashi amsa "Amma ranka ya da蓷e meyasa za kace a kashe wannan case 蓷in ka tuna fa laifin Nafeesa Jalaludden Alkaleri mai girma ne saboda abin da ta aikata kusan daidai yake da wanda ya aikata kisan kai because hakan ya nuna idan har ta samu dama tana iya kashe yarinyar."


"Abin da ka fa蓷a gaskiya ne amma umarni na baka, kawai ayi gaggawan sakesu."


Sam DPO bai yi mamakin jin hakan daga gareshi ba tunda yasan kasar tamu ta riga ta lalace da cin hanci. Ana iya siyan shari'a, ana siyan aiki, har ma ana iya siyan karya akan gaskiya wanda typical example 蓷in abin da ake kokarin yi kenan a game da case 蓷in Safiyya Kabir da Haj. Nafeesa Jalaludden Alkaleri.


DPO bai isa ya yi ja-in-ja da ubangidansa ba, ya yi gyaran murya ya ce"Kasan da cewa hukuncin ita Haj. Nafeesa shine a turata gidan gyara hali har na tsawon watanni biyar amma tunda ka nemi alfarman a sallamesu, to ranka ya dade kayi hakuri a kar蓳i tara. Haj. Nafeesa za ta biya tarar naira miliyan 蓷aya sakamakon illar da tayi ma yarinyar. Ita kuma 'yarta Samha zata biya naira dubu 蓷ari biyar saboda goyon bayan data ba wa mahaifiyarta. Shi kuma direban, za a kar蓳i naira dubu hamsin daga hannunsa, saboda ha蓷in kan da ya bayar."


CP naso yayi magana sai DPO yayi maza ya ce"Sir, don Allah ina so kayi min wannan alfarman saboda kada a kamamu da laifin rashin gaskiya."


Ajiyar zuciya CP ya sauke sannan ya ce" To shikenan kayi abin da ya dace nasan bazaka bani kunya ba, amma don Allah suna biyan ku蓷in a sallamesu babu 蓳ata lokaci."


"In sha Allah sir."


DPO ya furta sannan sukayi sallama ya kashe waya, a sanyaye ya koma ofis ya zauna yana ba su Yallabai hakuri kan da蓷ewar da yayi yana waya.


Zamarsa keda wuya aka shigo da su Haj. Nafeesa. Sai wani tafiyar takama take tana wani hura hanci don tasan abin da ta taka. A daren jiyan nan suka samu wani 蓷an sanda dake kan duty ya basu aron wayarsa, Samha ta samu tayi waya da CP dayake dama tana da 蓷aurin gindinsa shiyasa take cin karenta babu babbaka a garin Kaduna.


A take ya yi mata alkawarin kashe case 蓷in da basu sallama da gaggawa amma sai da suka tsadance kan ihsanin da zata bashi bayan ta fito, haka ma 蓷an sandan daya ara musu waya sun yi alkawarin bashi alheri mai tsoka muddin suka fita.


Da Shigowar Haj. Nafeesa tana arba da Yallabai sai kawai ta fara zaginsa, bata damu da cewa a hannun hukuma take ba take fa蓷in"Wallahi ko an sakeni har yanzu ina kan bakana, idona idon yarinyar nan sai na kara yi mata illa a inda nasan ba zata warke ba."


DPO ya mike yana buga tebir ya ce cikin 蓷aga murya"Baki da hankali ne? kar ki manta a inda kike amayar da wannan mummunar kudirin naki. Wallahi idan kika bani haushi zan sa a mayar da ke cell insa a miki irin hukuncin da ba'a miki shi koba."


Tun daga kasa ta wani kwaso shi da kallo har zuwa sama sannan ta watsar gefe tana gunguni. Ita fa duk takamarta nan 'yarta na damawa da manyan mutane don haka babu wanda ya isa ya takasu ya tafi ba tare da ya fuskanci hukunci ba.


Sosai kan DPO ya dauki caji.


'Taya ma za ayi tunanin sallamar wannan mahaukaciyar matar ba tare da an hukuntata daidai da laifin data aikata ba?' Ya ayyana haka a ransa.


Gashi har da ikrarin ko an saketa sai ta sake illata yarinyar. Yanzu shikenan fa Allah ya kawomu zamanin da an daina tsoron hukuma, gaba 蓷aya an rainasu sabida cin hancin da wasunsu ke kar蓳a.


A fusace DPO ya mike bayan ya gama 蓷an guntun nazarinsa ya ce da 'yan sandan da suka kawosu 

"Maza ku mayar min da ita Cell zan 蓷an koya miki hankali ki gane cewa kakin nan namu ba abin rainawa bane." Ya furta yana jan kwalar rigarsa.


'Yan sanda suka sara masa sannan suka nufeta don cika umarninsa, ta fara kuka" Wallahi bazan koma ba sai dai ku kashe ni."


"Good, ina son mai taurin kai, yanzu zan sa a bu蓷e min idanunki don ga dukkan alamu har yanzu baki san inda kike ba."


DPO yasa aka kira masa 'yan sanda mata suka tisa keyarta back to cell, amma fa dakyar don har sai data fara fuskantar barazana daga garesu sannan ta mika wuya.


"Jalal you must pay for all."


Shine abin da take ta nanatawa har ta 蓳ace daga ganinsu. Kan Yallabai a kasa yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa tamkar za ta fasa kirjinsa ta antayo waje.


Fitar da aka yi da Haj. Nafeesa yasa Samha rushewa da sabon kuka a guje ta nufi inda mahaifinta yake zaune, gefensa kuma Mijinta Haseeb ne da shi ma tsananin damuwa ya lullu蓳e shi.


Samha ta durkushe gaban Daddy ta kamo kafafunsa tana kuka mai ta蓳a zuciya" Daddy don girman Allah ka yafe min wallahi bazan sake biyewa mummy ba."


Janye kafarsa yayi daga gareta sannan ya sauke rinannun idanunsa a kanta ya ce"Samha go and face the law, my hands are off." 


Ya furta yana daga hannayensa sama.


Ta kalli Haseeb daya kasa ha蓷a ido da ita, ta ce"Haseeb, please kasa baki daddy ya yi hakuri."


Kafin Haseeb ya kai ga magana DPO ya daka mata tsawa"Tashi ki koma inda kike kafin kema

Kisa na canza ra'ayi a kanki."


Da gudu ta mike ta koma inda ta tsaya.


DPO ya yi gyaran murya ya ce"Zaki biya taran naira dubu 蓷ari biyar sabida goyon bayan da kika ba wa mahaifiyarki."


"Kai kuma." Ya ce da Direba" Zamu kar蓳i naira dubu hamsin a hannunka saboda ha蓷in kan daka bayar."


Direba ya 蓷an russunar da kai ya ce"Nagode ranka shi dade." Don a hakan ma yana ganin an musu sau茩i.


A fusace suka ji Yallabai ya ce"Ranka ya da蓷e, ina so a rubuta shaidar cewa daga yau na sallami wannan mutumin daga aikin direba a gidana don abin da ya faru ya tabbatar min da cewa yana iya bada ha蓷in kai a cutar da ni."


Ya kalli direban ya ce cikin 蓷aga murya"Daga yau duk wata ala茩a da ke tsakanina da kai ta 茩are, bani mu茩ullin motana."


Direba na jin Yallabai ya kore shi aiki ya zu蓳e kasa ya fashe da kuka yana bada hakuri"Yallabai don Allah ka..."


"Na ce ka bani ma茩ullin mota ko!"


DPO ya ce"Yallabai kar ka damu! An riga an kar蓳i mu茩ullin daga hannunsa. kuma zamu bada shaidar sallamarsa daga aikin direba a gidanka. Daga yau, ba zai sake samun damar kusantar wannan gida a matsayin ma'aikaci ba."


Babu irin magiyar da Manu direba bai yi ba amma fafur Yallabai yaki hakura. Haka dai ya hakura aka bashi takaddar sallamarsa daga aikin direba a gidan Executive Chef Jalal. Aka kuma ba shi damar zuwa wani ofishi na musamman domin biyan tarar da aka 蓷ora masa.


Bayan DPO ya sallami Direba, ya dubi Samha ya ce"Kema idan kin shirya kina iya bin bayansa ki biya naki taran sannan mu sallameki." 


Samha ta ce"Mahaifiyata fa?"


"Ita wannan ki batta tukunna don alamu ya nuna tana so ta 蓷an ta蓳a zaman cell. Hukuncinta shine a turata gidan gyara hali na tsawon wata biyar amma a haka muke kokarin mata adalci asa ta biya tara. Sai dai na fahimci so take sai ta kai ni bango tasa in yi abin da zai sa tayi nadama."


Samha tayi shiru bata ce komai ba. Yallabai da Haseeb suka yi musabaha da DPO.


DPO ya ce"Yallabai, za mu tura jami'ai biyu daga cikinmu su je su duba halin da mara lafiyar take ciki. Bayan an tattara ku蓷in tarar da za a biya, za a ba da izinin wani daga cikin mutanenta da aka amince da shi ya zo ya kar蓳a."


Sosai Yallabai ya cika da tsananin farin cikin ganin za'a ba Safiyya tara na lahanin da aka yi ma fuskarta. Ko ba komai an 茩wato ma yarinya ha茩茩inta, sai dai ance idan an cuceka kawai an cuceka. Ku蓷in dai zai taimaka wajen rage zafi ne kawai.


Daga Yallabai har Haseeb babu wanda yabi takan Samha balle ya taimaka mata, haka suka fito suka barta, duk da Haseeb yaso taimakawa amma Yallabai ya hana, so yake a koya musu hankali daga ita har Uwar. 


"Ka kyalesu su biya da hannunsu saboda idan suka ji haushin fitar da ku蓷i daga aljihunsu, ina ganin gobe ba zasu 茩ara ba."


Dr. Haseeb ya fahimce shi kuma yadda Yallabai ya yi shi ne daidai. Suna fitowa station duk suka nufi asibiti.


DPO ya bada izinin a ba Samha wayarta da suka kwace domin ta samu damar biyan taran dayake transfer ta ce za tayi. Haka ta ja jiki zuwa gaban kanta, ta samu 蓷an sandan da wayar ke hannunsa yana 蓷aukan statement 蓷in wani mai laifi sai yace ta 蓷an jira ya kammala sannan ya bata.


Manu direba dai tuni ya biya nashi taran, shi ma transfer ya yi. Yana ta jin haushin an sa ya ta蓳a ku蓷in da yake tari ga kuma aikin da Haj. Nafeesa tasa ya rasa. Sai tsine mata kawai yake ta yi a ransa. Yana zaune yana jiran a sallame shi ya tafi.


***


_ASIBITI._


Saffy ce zaune kan dadduma, gabanta breakfast ne take ci da Chef Ali ya kawo daga gidan abincinsu. Jidda kuma na zaune kan kujera tana fuskantar ta. 


A karo na biyu ta 蓷ago dakyar tana kallon Jidda a sanyaye ta ce" Yaya, tunda kika shigo nake ta rokon ki sauko mu ci abinci amma kinki sai wani irin kallo kike watso min wanda na rasa gane wa, meke faruwa ne?"


Jidda ta ta蓳e baki ta ce" Menene ma bai faru ba ? Safiyya in tambayeki man."


Ta fa蓷a tana gyara zamanta kan kujera, dama su biyu ne a 蓷akin, tunda Jidda ta shigo su Chef Ali suka basu waje.


"Ina jinki."


"Meke tsakaninki da Executive Chef Jalal mai Alkaleri's Kitchen?"


Jidda ta watsa mata wannan tambayar, idanunta kikam a kanta ko kyaftasu taki yi, ga fuskan nan a murtuke babu alamun wasa a tattare da ita.


Saffy ta ce" Ce miki akayi akwai wani abu tsakanina dashi bayan abin da ya sameni a gidan abincinsa?" 


Ta yi tamabaya tana nuna fuskarta da 蓷an yatsa kan ta ci gaba "Ban ta蓳a saninsa ba sai bayan wannan mummunan lamarin da ya same ni a gidan abincinsa. Kuma naji ance shi ya 蓷auki nauyin jinyata tunda incident 蓷in a gidan abincinsa ne ya afku. Ko don irin 蓷aukakanin da kika ga yayi ne yasa ki tunanin akwai wata 蓳oyayyiyar alaka tsakanina da shi? Ina nufin sakin bakin aljihu da kika ji ance yayi na biyan ku蓷in jinyata? Da kuma yaransa daya sa su tsaya su kula da ni? har da 蓷awainiyar abinci?"


Tsawa Jidda ta doka mata "Enough! Kar ki raina min hankali, duk wannan abin da ya yi miki bazai miki shi a banza ba dole akwai kyakkyawar alaka tsakaninku, haka nan kawai Haj. Nafeesa ba zata..."


Saurin taran numfashinta Saffy tayi ta 蓷aga mata hannu. Za tayi magana sai ta 茩ware da abinci, da sauri ta jawo kofin ruwa ta sha, sai sannu Jidda take mata.


Bayan ta samu natsuwarta ta ci gaba da bayani yadda Jiddan za ta fahimci farkon abin da ya fara shiga tsakaninta da Yallabai kafin a kai ga zuwan Haj. Nafeesa.


"Wallahi tallahi ni ban san cewa owner of Jay. Alkaleri's Kitchen bane sai da mahaukaciyar matarsa ta fa蓷o kamar daga sama ta illata ni. Tana zargin da akwai alaka tsakanina da mijinta."


Tana kawo wa nan a bayaninta ta yi shiru tana jiran jin ta bakin Jidda data kura mata ido.


Ganin shirun ya yi yawa yasa ta marairaice ta ce"Yaya ki yarda dani babu wata alaka tsakanina da shi."


Hawayen daya cika kwarmin idanunta ya gangaro, tayi saurin sa tissue ta goge. Ita dai Jidda sai kallonta take amma ga dukkan alamu bata gamsu ba, kuma bata sake ce mata komai ba har ta kammala cin abincinta sannan ta koma ta mike a kan wata doguwar kujera don kwanciyar gadon ya isheta.


Jidda sai ajiyar zuciya take ta saukewa a jere, maganar da take so ta fitar ya makale a ma茩oshinta. So take ta bayyanawa Saffy cewa shine mutumin data ta蓳a gani a gidanta kwanaki har tace mata mijinta ne da suka yi auren sirri amma sai taga ba zata iya ba.


  ***

Ana ba Samha wayarta nan take tunanin neman Jidda ya fa蓷o ranta. Ita kawai zata sa ta turo mata 500k daga asusun gidan mata don bata so ko ka蓷an ta ta蓳a kudin akawunt 蓷inta.


"Ina zaman zamana Mummy tasa zan 蓷ebi kudin dana sha zufa wajen tara su. Naira na gugan naira har dubu 蓷ari biyar daga asusun gidan mata in ba wata banza can da bata san wahalar dana sha kafin na samesu ba." 


Tana wannan maganar ne take kokarin kiran Jidda don already har tayi dialing layinta.


Jidda na ganin kiran Uwar 蓷akin nata tace da Saffy "Ina zuwa." Sannan tasa kai ta bar 蓷akin jikinta na 蓷an rawa.


"Salamu alaykum ranki ya da蓷e barka da warhaka."


Dayake ba a cikin natsuwarta take ba yasa bata tsaya su wani gaisa ba tace" Kisa min 500k cikin akawunt 蓷ina yanzu yanzun nan ina da bukatarsu, kuma kar ki 蓳ata lokaci ina jira."


"An gama ranki ya da蓷e, yanzu zaki ga sako."


Samha ta kashe waya, a yayin da Jidda ta bi screen da kallo. 


'Allah sarki yanzu Samha fa da mahaifiyarta suna hannun hukuma.' Haka ta ayyana a ranta.


Bata tsaya 蓳ata lokaci ba ta aika mata da ku蓷in, sai data tabbatar da cewa ta gani sannan ta mayar da waya jaka. 


Har ta mur蓷a hannun 茩ofa zata koma ciki sai taji muryan Chef Ali daga bayanta yana fa蓷in" Ranki ya da蓷e da kinyi hakuri ki 蓷an jira ka蓷an don yanzu Yallabai zai shigo tare da tawagarsa domin duba mara lafiyan. Ba zamu so wani mummunar abu ya sameki ba muddin aka ganki kusa da shi tunda dama ke ake nema ruwa a jallo. And possibly Madam za ta iya sa ana monitoring duk wani takunsa, So please kindly refrain from associating with him openly so you don't put yourself in big trouble."


Ai bai gama rufe baki ba ta hango Yallabai tare da tawagarsa suna tahowa, yana gaba a yayin da sauran suka take masa baya. Abokansa ne da yake ji dasu suka nemi zuwa ganin Safiyya, to bayan sun baro station sai ya ha蓷u da su, daga nan suka rankayo zuwa asibitin.


Babu karya kowanne a cikinsu akwai capacity amma Yallabai daban yake don sai da gaban Jidda ya buga a lokacin da tayi ido biyu dashi, sosai ya kara mata kyau, looking very young kamar kodayaushe.


Ganinsa tare da capacitated men yasa hankalinta ya kara tashi. Bata gama tsinkewa da lamarin ba sai data hango ana biye dasu da ba茩a茩en leda ta dubiya.


"Yanzu duk wannan 蓷aukakar Safiyya ce ake tayi ma? Kuma a haka take ikrarin babu komai tsakaninta da Yallabai? Wallahi ban yarda ba."


Tuni ta ji wani irin kishi ya cukwikwiye zuciyarta, wasu zafafun hawaye suka zubo mata. Da sauri ta matsa can gefe ta manne da bango ta basu baya.


Chef Ali na gama magana bai jira yaji ta cewarta ba yabar wajen ya nufesu da fara'arsa.


Yallabai sam bai lura da Jidda ba don suna tahowa yana hira da likitan da ke kula da lafiyar Saffy ne, ga kuma Dr. Haseeb a daya gefensa suna tattaunawa kan ciwonta.


Tana jin takun tafiyarsu gab da kunnenta taji kawai gabanta ya tsananta bugu......


**Few more pages to go馃珷**