👑♥️ THE PRINCE OF DESIRE♥️👑By Maryam Sulaiman Miss Nasir ♥️✍️

THE PRINCESS OF DESIRE 👑 ♥️

by @angelbossauthor


THE PRINCE OF DESIRE👑♥️

       😉THE SEXY GUY🫦

By Maryam sulaiman 

miss Nasir ♥️ ✍️ 

[26/9/2026]

[6:49am]

Book1 

Page 7&8

A hankali ya karasa karkashin shower Yana mai sakawa kansa ruwan dumi sosai ruwa ke dukan jikin sa a hankali yaji Damuwar sa na sauka Yana karfafawa kansa gwai shifa bawai auren ne bayaso ba Amma Shi Kar ace wannan yar iskar yarinyar maras kunyar za a hadashi da ita yar kanwar Fulani Rukayya,
Towel ya daura Yana mai fitowa jallabiyya ya sanya da shorts Yana mai sanya alkebba Fara a Kai yanufi masalacin cikin fada,

Musaddiq Yana zuwa bangaren Fulani Bilkisu ya Shiga Kai tsaye kwance take shame shame akan gadon ko motsi batayi 
Hankali a tashe ya karasa wajen da suke 

Mommy mekuke Baku dauke ta akai hospital ba musaddiq ai kasan jinyanta Bana hospital bane dole muje anemo babban malamin Muslimci fita kawai yayi Yana mai nufar Yadda yai parking din motar sa 

Rayyan 

Bai dawo ba sai da yayi sallah isha'i ko wajen Fulani Bai jeba saboda yasan ita yasa Mai Martaba hada wannan auren 

Yunwa yake ji Amma baiji zai iya sanya Abu mai nauyi a cikin sa ba Zama yayi a parlourn ganin anjere masa abincin akan draining yasa ya mike ganin abinci yayi Amma haka kurin yaji abinci Bai kwanta masa a Rai ba kumawa yayi ya zauna Yana mai sauke ijiyan zuchiya shifa gabada maganar Zuwa NAWARA tafi bata mashi Rai to mai Zeke yayi bacin sun riga sun hada ai basai yake ba tsaki yaja Yana mai mike wa ya nufi khicken Yana mai hada coffee machine 

Yana gamawa ya nufi upstairs bedroom din sa yashi Yana Zama a Kan stool din mirror a hanka yake sipping din coffee din Yana lumshe idanu saboda Yadda yake ratsa mishi cikin sa 


Kano

Abbey nayin alwala ya fice daga gidan 
Yanufi masalacin 
Umma najin fitar sa ta fito tsakar gidan tana goge fuskar idon take ya sauka akan Yumna da ke zaune Kan kujera gaba dayan mazaunanta sun baje kujerar na tsakiyar au saboda Yadda suke da girmamawa karasawa tayi kusa da ita Yumna kinyi sallah magrib ne
Aa umma to Maza tashi kije kiyi sallah mikewa tayi tana daukan buta ta nufi bandaki 
Bayan ta umma tabi da kallo sosai girman Yumna yake bata mamaki duk da yanayin jikin tane ta gado to Amma fa Yumna tafita gata yarinya Kara Amma tayi saurin girma shiya duk mazane unguwa da malaman makaran kuwa hari yake kawo Mata saboda Yadda Allah yamata Kira mai Jan hankali 
Dauke kwallan da zubu Mata tayi
Tana mai dauke kayan abinci da Abbey ya shigo da Shi.

Tsaye yake a bakin masalacin Yana Jiran su idar da sallah duk kasancewar baiyi tasa sallah ba Amma Bai iya Zuwa yabi jam’i saboda Baya cikin nutsuwarsa ganin Liman da yayi Yana kukarin barin masalacin yasa yayi saurin Shan gabansa,

Barka da dare Malam,
Barka dai samari lafiya kuwa
Malam muna da marar lafiya ne kuma kunyar Bana asibinti bane shine akace na Kira babban malamin shine nazo Nan 
Subhanallah to Allah ya bada lfy a inane 
Cikin masarauta ne Saida yayi Dan Jim kamin yace to muje suka shiga mota suka nufi masarai.

Rayyan 

Mike yayi Yana ijiye muck din coffee din ya mike Yana mai shiryawa cikin pajamas dinsa masu taushi brown colour Saida yayi duk wani Abu da yama al’ada a wajenshi kamin ya kwanta Yana mai Addu'ar kwanciya bacchi.
Bai dauki lokacin da yawa ba bacchi yadauke Shi saboda a mugun gajiye yake.

MISS NASIR♥️✍️