ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )
PROLOGUE
…………………..
STORY
WRITTEN
BY
IBTISAMWRITES ✍️
PROLOGUE
A rayuwa, akwai abubuwan da mutum ba shi da iko a kansu. Ko da kuwa abin yana da matuƙar muhimmanci a gare shi, sai ya sha wahala, ya yi haƙuri, ya dage kafin ya samu abin da yake nema.
Akwai kuma abin da zai iya zama alheri a gare ka, amma mutane su ƙi ka samu shi. Ba don abin ba shi da kyau ba, sai don kawai ba su ga ya dace ya kasance naka ba.
Wani lokaci, sai ka tsaya da ƙafafunka biyu, ka fuskanci waɗanda suke son hana ka abin da zuciyarka ta riga ta zaɓa.
Amma fa… ba kowane yaƙi ne ake cin sa da ƙarfi ba.
Wasu yaƙe-yaƙen rayuwa, haƙuri ne ke cinye su.
Wasu kuma… sai lokaci ya fallasa gaskiyar da aka daɗe ana ɓoyewa.
Domin zumunci ba koyaushe yake nufin komai zai tafi daidai ba. Wani lokaci, shi ne mafarin farin ciki. Wani lokaci kuma, shi ne dalilin hawaye.
To amma me zai faru idan abin da zuciya ta ɗauka a matsayin alheri ya zama abin da wasu suke ganin bai kamata ya faru ba?
Me zai faru idan aka samu wanda yake son hana ka abin da ka ɗauka a matsayin rabonka?
Kuma ina zumunci zai tsaya idan zuciya da alaka suka shiga sabani?
Ku biyo ni cikin Zaren Zumunci (The Thread of Family Bond)… domin sanin me ke faruwa.