ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )
PAGE 1
………………….
ZAREN ZUMUNCI
(The thread of family bond)
WRITTEN
BY
IBTISAMWRITES ✍️
PAGE 1
Kano, Nigeria
Gaba ɗaya ahalin gidan Alh. Aliyu Guruntum ne zaune cikin kyakkyawar parlorn da ke tashin ƙamshin turaruka daban-daban, har ba ka iya tantance wannan ƙamshin ne na wane ko wannan na wace.
Duk da sanyi da raɓa na AC da ke aiki kusurwa-kusurwa na parlorn, bai hana wasu daga cikin mazauna parlorn tsatsafo gumi ba, ciki har da Aliyu da ya ji maganar Inne ɗin tamkar saukar aradu a cikin kansa.
Fara kuma dirarriyar matar da ba za ta haura shekaru arba’in da biyar ba zuwa hamsin, sai dai kuɗi da kuma hutu sun danne shekarunta, ta gyara zama tana bin ’ya’yan nata da kallo.
“Toh, kun ji shawarar da muka yanke, sai ku fara shiri don auren. Za a saka nan ba da jimawa, in shaa Allah.”
Aliyu da ya kasa cire idanunsa kanta, ganin da gaske take ba wai da wasa ba, ya sa ya katse shirun da parlorn ya sake ɗauka a karo na biyu.
Ya ce,
“Ina da magana, Inne.”
Ta watsa masa wani kallo, don ba ta maraba da abin da zai katse mata burin da ta ɗauka a kansu samm. Ta tsura masa idanu tana fata kar ya nemi ja da maganar ta, don ba za ta taɓa amincewa hakan ya kasance ba.
Ya sauƙar da idanunsa, zuciyarsa na bugawa, ya ce,
“Inne, ki yi haƙuri. Ba wai zan ja da maganarki ba ne, kuma ba zan ƙi zaɓinki ba, amma ni akwai wacce nake so da kuma burin aure. Auren haɗi ba ya cikin tsarina, Inne. Don Allah a duba lamarin nan.”
Shiru ne ya wanzu a parlorn na dakiku masu yawa, don babu wanda ya taɓa tunanin Aliyu zai iya buɗe baki ya ja da maganar mahaifiyar tasu, har ita kanta ba ta taɓa kawo hakan ba.
A zatonta, ta ɗora su ne kan turbar biyayya kawai, ko da da ra’ayinsu ko babu.
Gaba ɗaya ta kasa magana, sai idanu da ta tsura masa, yayin da ya yi ƙasa da kansa yana jin ƙyallin idanun nata a jikinsa. Sai dai bai yi nadamar buɗe baki ba, saboda tauye shi ake shirin yi, ba zai iya shiru ba.
Ta yaya zai fara auren wacce bai taɓa gani ko sauraron muryarta ba?
Ta yaya ma zai fara watsar da Amna da suka shimfiɗa soyayya mai tsafta, suka kuma kafa alkawurra masu girma, ciki har da na rayuwa na har abada?
Ba zai yiwu ba!
Hajiya Zuwaira ta katse shirun bayan dogon lokaci, ta ce,
“Aliyu!”
Ya ɗaga kai ya kalleta.
“Wace ce kake son ka aura? Kuma waye ubanta a faɗin ƙasar nan?”
Dukka su babu wanda ya yi tsammanin cewa Inne za ta yi tambaya akan ƙara wata magana cikin tsarinta da Aliyu ya yi. Hakan ya matuƙar ba su mamaki.
Shi kuwa Aliyu, ganin akwai fuska, ya sa ya ji ransa ya yi haske, fargabarsa ta kau cikin lokaci kaɗan. Muryarsa ta cika parlorn da bayanin wacece Amna.
“Inne, sunanta Amna, ’yar asalin ƙasar India ce kuma a can suke rayuwa. Mun haɗu ne a makaranta. Mahaifinta public figure ne a can, da ake ji da—”
“Rufe mini baki, Aliyu!”
Tsawarta ba shi kaɗai ya firgita ba, har sauran ’yan uwansa da suke zaune tamkar ruwa ya ci su.
Ibtisamwrites✍️