KANWAR SHEHU

Chapter 13

by @nanamaryama394

Alhaji da zai tafi sai da ya ba "Inno" dubu goma, mama dubu goma Rabi'ah dubu biyar ita kam hajiyar uwar tafiya dubu ashirin ya bata' wai a haka ma tai hakuri saboda abinda ya so bata ya fi haka, ga tsaraba nan abaya ce guda uku sai shadda ɗaya laishi ɗaya mayafi uku kaya dai na gani da faɗa ya masu sallama ya tafi..... 


                Sai da ya tafi ne aike ta murnar abin da ya bada, Rabi'ah ta ce ka ga Matar masu abaya! 


  Ita abin ma kunya ya bata kawai ta tafi ta bar masu ɗakin..... Ƙarfe tara na dare suna zaune ita da inno ta ce yanzu wannan kayan ya za'a yi dasu? 

          Ya fa za'a yi dasu jawahir a kira "gwaggo dai a nuna ma kayan nan abinda nake so da ke kenan!" 

                       Shikenan inno in Sha zan faɗa mata, yanzu dai bari na kira Alhaji naji ya ya sauka lafiya? 

         Innalilahi wa'inna ilahir raji'un lalle ƴar nan ashe baki da kunya ma' gaba na kike faɗar wannan maganar? I ta bakin Rabi'ah ɗin aure kike so kuma na yarda da maganar,.... 


           *
Zaune take kan dadduma tana lazimi cikin zuciyar ta tunani kala da kala take yi, ubangiji Allah ya kar kato da hankalin Alhaji nan wajen su, su dawo kamar yadda suke da aunty ce ta shigo da yogout a hannun ta ce "sister" ga shi ki sha bana san kina zama da yunwa fa! 

           Ohh Aunty I love you so much....

      Mai gari ni idan basu da matar da zasu aura ina da ɗaya wacce zan bashi don Allah... 
      Murmushi ya yi ya ce'' to badamuwa Malam Nura, jira muke lokacin da muka ɗibar su to muna jira dai muji da mai zasu zo ne sai mu san abin yi... "

          To badamuwa dai amma ina saurare idan basu samu ba! 

                     Yauwa kasanme yanzu?
 Yaron ya girgiza kai alamar a'a..
            To tunda dai tana aje wayar gida ka je ka ɗauko min ita, kada ka bari a gani...

    Zaro ido yayi tare da faɗin inna ta idan ta gani fa? Mai zance mata zata duke ni ne...

                  A'a zo ka ji in faɗa maka a kunne ya raɗa mai a kunne idan kaje ka ɓoye duk dai ya rada masa yadda zai yi yaron ya tafi da gudu, domin ya ɗauko masa...

                        **
Malam daga yau ai an gama ko?

     Murmushi ya mata saboda yana jin daɗin ta sosai' ya ce daga yau an gama tabbas sai dai akwai wani abu guda da nake so na faɗa maki..!

       To Allah yasa alheri ne dai, mainene kuma kar dai ace Abeed ba zai aure ni ba?

       Kusan haka dai amma ko za'a yi auren dole sai kin zauna a gida na na tsawon wata huɗu, saboda akwai tsumin maganin da za'a maki ya kama jikin ki to tabbas duk inda abeed yake Sai ya zo gare ki kada ki damu da hakan!

                         Gabanta ne ya faɗi tasan irin azabar da take sha lokacin da ake wankan maganin nan' ina ga ance wata huɗu sannan tabbas tasan dai sai an tausaya mata!

            Kije gida ki shawara da ita duk Abinda ta ce sai ku faɗa min a waya' kin ga dai yanzu an fara aiki idan har kuka bari kuma aiki zai dawo baya dole a kara wankan maganin, sannan a daura da tsuma ki...

        Ni ba sai naje mun yi shawara ba ' kawai na amince ita da ta mallake Alhaji ta yi shawara dani ne? A'a nima bazan yi ba yadda ta mallake sa nima haka nake san mallake ɗan sa gaskiya!

    
                  Dariya ya yi sosai ya ce kenan kina san mamlakar shi? To komi zai zo da sauƙi tunda kin amince...


                        Wayar ya kawo masa tare da faɗin don Allah kai sauri ɗan birni, saboda ta kusa dawowa yanzu!

         Amsa ya yi tare da faɗin jira nazo, ka zauna nan kaji ko?

   Daga can gefe ya matsa ya sa number Aunty daman ya hadda ce ta, ya sa ya kira har sau uku bata daga ba kamar yai kuka ya ke ji innalilahi wa'inna ilahir raji'un ya furta tare da faɗin Please aunty don Allah ki daga ki ji damuwa ta.....

         Kira ya ƙara kira ko zata daga amma shiru sai da ya mata kira huɗu sannan ta daga tare da sallama ya na ji ya ce Aunty please ki kira wannan layin yanzu don Allah...!

             Katse kiran tai tare da kwala ma sister kira ta zo abeed a kan layi, ta kira ta sa a speaker suka gaisa ya ce Aunty tin da muka tafi nake neman wayar ki ban samu ba ba network ɗin mtn sai aitel duka garin ya idasa maganar kamar zai yi kuka!


          Fatan dai kuna Lafiya? Ina Haroon? Garin Akwai dadi ko?

    Ƙwalla ce ta zubo masa tare da faɗin Aunty ba'a zaman garin dole sai kana da mata yanzu haka sun ce ko dai muyi aure da wanda muke so' na garin mu ko kuma a bamu ƴan matan garin Aunty na rasa mai ke min daɗi .....!

       Innalilahi wa'inna ilahir raji'un ta faɗa tare da faɗin ka ga abinda na ke faɗa maka yanzu ko? Idan da ace ka yi auren ka yanzu ai da shikenan ba mai maka wannan maganar' yanzu ko dole ka amshi zaɓin su tunda dai baka da wadda kake so!


     Zai yi magana wayar ta mutu ba caji...

        Haroon da yake tun ɗazu ya ce......