ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )
PAGE 2
***
https://www.arewapen.com/book?id=6ab8fc22c237adaad549e3a2
***
………………….
ZAREN ZUMUNCI
(The thread of family bond)
WRITTEN
BY
IBTISAMWRITES ✍️
PAGE 2
MAFARI
Wani babban gida ne wanda kana sako ƙafarka cikin layin shi ne zai fara ɗaukar idonka. Tun daga waje, kalar paint ɗin da aka yi da yadda aka tsara gidan shi zai fara tafiya da kai.
A yanayin na girman gidan ,kai tsaye zaka iya kiran shi da mansion. Gida ne da ake masa laƙabi da Gidan Sojoji, ba wai don gidan sojojin bane, aa, sai because the owner of the house is a soldier.
ASALIN WAYE ME GIDAN
Alh. Aliyu Guruntum is a businessman alongside being a military man. He was a commando during his time in the military, and he is a very respectful person. He is loved by all.
A lokacin shi da yake a matsayin commando, kafin yayi retire, yayi yaƙi sosai inda ya taimaka ya kwato waɗanda aka sace a ƙasar aka ƙetara su zuwa wata ƙasa.
He has a wife. Her name is Hajiya Zuwairah.
Hajiya Zuwairah kam mata ce da ba ta san a raina ta. She wants everything to be according to her liking, not the other way round.
Ta fi son komai ta faɗa a cikin gidan nan ya zauna, ko da kai abin bai yi maka ba, sai ka yi haƙuri da shi ka karɓa a haka.
She is very strict, especially ma wajen zaɓa wa ’ya’yanta mataye da mazaje. A cewar ta, ba kowa za a je a kwaso mata a kawo mata cikin gida ba.
Sannan ba ta yin sana’ar komai, sai ta saka ido a gida don kar a kawo mata baraka.Bayan wannan kuma ita din matuniyar kirki ce.
A cikin wannan gida, Alh. Aliyu da Hajiya Zuwairah suna rayuwar ce mai kyau, irin ta babu saɓawa babu fitarwar nan, saboda kowa ya riga ya gama fahimtar ɗan uwansa. Sai dai aka ce ita rayuwa, zo mu zauna, zo mu saba ce. Haka nan suma suna ɗan samun saɓani irin na ma’aurata.
Haka a cikin rayuwar nan Allah ya ba su ’ya’ya guda shida. Sunan su shi ne:
Kabir Aliyu Guruntum shi ne babban ɗa, sai Isma’il Aliyu Guruntum, Kamal Aliyu Guruntum, Yusuf Aliyu Guruntum, Aliyu Aliyu Guruntum, and Fauziyya Aliyu Guruntum.
Haka duka waɗannan ’ya’ya suka taso cikin so da ƙaunar junan su, sannan mahaifin su ya ba su ilimin addini da na zamani duka.
To, bayan sun kammala karatun nasu, both Arabi da boko, sai suka fantsama aikin soja.
Baba Kabir da Uncle Yusuf Business Administration suka karanta. Babba Kamal kuma Economics ya karanta. Shi kuma B. Isma’il ya karanci Law ne. Daddy Aliyu kuma ya karanci Accounting, sai kuma Mama Fauziyya ta karanci Biochemistry.
A bangaren Islamiyya kuma duk sun yi sauka. A ciki ma Kabir, Yusuf da Aliyu sun haɗa har da Hadda.
Mazan gaba ɗaya sun taso ne da son su bi sahun mahaifin su na zama businessmen da kuma zama sojoji.
Toh, wannan duk Allah ya cika musu burukan su, su zama abin da suke da buri.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da nitsuwa.
A kwana a tashi, babu wuya sai ga shi ana ta shirye-shiryen tarbar baki da za su dawo.
Alh. Lawal Shu’aibu is a well-known and respected businessman. That is where they align in the business world.
Yana da mata guda biyu, Haj. Zainab da kuma Haj. Lubna.
Hajiya Zainab ya aure ta ne anan Nigeria, daga nan sai ya tafi da ita Spain tun da anan yake aiki.
Bayan tafiyar su Spain daga shekara biyu, Allah ya azurta su da samun ƙaruwa na ’ya’ya guda biyu inda suka ci suna Aina’u da Asma’u, shekara ɗaya ne tsakanin su.
Ibtisamwrites✍️