ZAREN ZUMUNCI(The thread of family bond )

PAGE 3

by @ibtisamwrites01

***

https://www.arewapen.com/book?id=6ab8fc22c237adaad549e3a2


***




………………….
                         ZAREN ZUMUNCI
               (The thread of family bond)

                               WRITTEN 

                                    BY

                       IBTISAMWRITES ✍️







PAGE 3
 
A wannan lokacin ne ya haɗu da Haj. Lubna, inda anan suke da zama ita da mahaifanta, amma mahaifin nata shi ma daga Nigeria yake, irin Alh. Lawal ɗin.
 
Anan suka dai daita kansu, amma kafin a ɗaura auren sai da ya samu ya zauna tare da Haj. Zainab ya faɗa mata zai ƙara aure.
 
Da ya faɗa mata, sai ta yi shiru. Sai kuma ta ce,
 
“Allah ya sanya alkhairi.”
 
Anan Alh. Lawal yayi mamaki matuƙa, amma bai nuna ba. Duk da bai yi tunanin cikin sauƙi za ta yarda haka ba.
 
Haka ya tashi ya tafi yana mai farin ciki kamar dai wani ɗan yaro.
 
Sati ɗaya da yin maganar da Haj. Zainab, aka ɗaura auren Alh. Lawal da Amaryar sa Lubna. Ta tare a gidan ta.
 
Haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya, da daɗi babu daɗi, inda Hajiya Zainab ta ƙara samun ƙaruwa, ita ma Haj. Lubna ta samu nata.
 
Hajiya Zainab ta haifi su Abdulahad, Zuhra, da Khausar, inda ita kuma Haj. Lubna ta haifi guda biyu, Lamin da Maryam.
 
Khausar da Maryam sa’annin ne, wata biyu ke tsakanin su, da Lamin da Zuhra kuma sati biyu ne.
 
Suma duk ya saka a makaranta for both Islamiyya and western, kuma duk sun kammala.
 
Dama Alh. Lawal ya faɗa wa matansa cewa fa ƙasar Nigeria ta yi kira. Ya ce business ne ya kawo ni kuma na samu ci gaba, don haka zan koma can don ci gaba da kasuwancina.
 
Suka yi na’am, don su ma sun gaji da zaman ƙasar. Kowa na son komawa gida wurin ahalinsa. Dukkansu har da ’ya’yan za su koma Nigeria.
 
Haka dukansu suka shirya, bare ma ’ya’yan cewa za su koma Nigeria suna ta murna.
 
A yau ne suka sauka a Airport na Malam Aminu Kano, inda Alh. Aliyu ya turo da drivers don su ɗauko su daga airport zuwa gida.
 
Alh. Lawal ya faɗa wa Alh. Aliyu cewa fa yana nan dawowa ƙasar. Sannan ya sayi gida a kusa da gidan Alh. Aliyun, inda za su zama maƙotane kuma ’yan uwa.
 
Tun da dai sun zama ’yan uwa, saboda Alh. Aliyu Guruntum da Alh. Lawal Shu’aibu are friends since childhood, so basically they have become family.
 
Bayan dawowar su Alh. Lawal da iyalan sa ƙasar Nigeria, sun samu baƙuncin ’yan uwa don zuwa yi musu ban gajiya. Kusan sati biyu aka yi suna karɓan baƙuncin mutane kafin su samu su sarara musu.
 
A wannan tsukin dawowar tasu, Haj. Zuwairah ba ta leka ba, a cewar ta ta fi son ta je in mutane sun ragu da yawa.
 
Kuma daman can ba wai ba sa gaisuwa bane, aa, suna yi, don kusan kullum suna cikin waya ne. Har children nasu ma duk sun saba da juna like a real family.
 
Bayan dawowar tasu ma ta kira a waya ta yi musu ban gajiya kafin ta shiga.
 
Haka Haj. Zuwairah ta shirya cikin shiga mai kyau ta alfarma, ta yi adon ta, ta ce wa ɗanta autan ta Fauziyya ta zo su je gidan Alh. Aliyu su yi musu ban gajiya.
 
Ta so ta ce,
 
“Aa, Inne, ki tafi ke kaɗai.”
 
Amma kallon da ta jefe ta da shi yasa ba ta ce komai ba. Ta shirya suka tafi.
 
Duk da ba wani tazara ne da su ba, amma a mota aka tafi kai su. The difference is, su Alh. Aliyu a farkon street ɗin suke, inda su kuma Alh. Lawal a kusan ƙarshen suke.
 
Bayan sun ƙarasa gidan, Hajiya Zuwairah ta ce Fauziyya ta ɗauko basket ɗin da suka zo da shi ta biyo ta.
 
Suka fara biya wa ta ɓangaren Haj. Lubna, suka gaisa kafin ta tafi ɓangaren Haj. Zainab ta yada zango.
 
Anan suka ci, suka sha, suka yi hirar yau she gamo har ƙarfe 9. Suka yi haramar tafiya, sai ga ’ya’yan gidan sun dawo.
 
Su ma sun je gidan grandparents nasu ne, inda suka yi nan musu, sai yanzu suke dawowa.
 
Nan dai suka koma suka zauna. Yaran suka gaisar da Inne, sannan suka gaisa da Fauziyya har suka ja ta suka shiga ɓangaren su suna hirar yau she gamo.
 
Ba su bar gidan ba dai sai 10, saboda daɗin an ga juna, ko time ba sa ƙura da shi. Haka dai ba don sun so ba, suka rabu.
 
Ibtisamwrites✍️