17
by @zeeykumurya
Sosai ta yi aman, hakan ya ƙara galabaitar da ita. Taimaka mata Inna ta yi ta wanke fuskarta ta cire kayan jikinta ta sauye wani ta koma ta kwanta tana numfarfashi. Inna tana gyara mata kwanciya ta ce. "Sannu, bari na je chemist na karɓo miki magani da audiga." Ɗaga mata kai ta yi duk da ba ta fahimci audugar me take nufi ba. Murɗawar cikin nata ya yi mata sauƙi, hakan ya sa take ta sauke ajiyar, wani irin abu take ji yana fita daga jikinta wanda ya kasance baƙo a gurinta, tunani ta dinga yi akan hakan amma ba ta fahimci komai ba har Inna ta je ta dawo.
Bayan ta yi wanka Inna ta ba ta pant ɗin da ta saka mata pad a jiki kamar yadda Nurse ɗin dake zaune a chemist ɗin ta yi mata bayani. Cikin mamaki A'isha ta ce. "Inna mene wannan na ji shi a jikin wandon?"
"Auduga ce, wadda za kina amfani da ita har jinin al'adar da kika fara ya ɗauke, ai kin san mene ne shi ko?"
Gabanta ne ya faɗi, jikinta ya yi wani irin sanyi ƙalau, ta san me jinin haila yake nufi, Malamar da suke zuwa gurin ta karatu ta yi musu bayani a kan shi sosai, ba tare da ta san dalili ba ta ji hawaye ya zubo mata.
"Ki saka wandon kar ki kuma ɓaci mana."
Cikin tsananin jin kunyar Inna ta fashe da kuka tare da saka wandon. Umarni inna ta ba ta akan ta zauna za su yi magana, ba ta yi musu ba ta zauna tana sharar hawaye. Cikin nasiha Inna ta ce. "Mene na kukan kuma? Abin da ba kanki farau ba, duk macen da kika gani a duniya tana yin jinin al'ada in dai ta kai munzalin farawa, wanda ba sa yi kuma yawanci ciwo ne, a yanda aka ce ma zai yi wahala su haihu in ba wani ikon Allah ba." Ita dai ba ta ce komai ba sai kukanta ta cigaba da yi. Nasiha sosai Inna ta yi mata akan yanzu girma ya hau kanta, an fara rubuta mata zunubi da lada kamar kowa, don haka ta ji tsoron Allah a duk inda take tare da tsare mutuncinta, ita dai ba ta tanka ba, kunya da yanayin da take ciki ya hana ta magana. Bayan ta ci abinci ta sha magani ta kwanta bacci.
Hayaniyar Iya da ta shigo tana yi wa inna tijarar da ta saba ce ya tashe ta daga baccin, lokacin har an yi Sallar Isha'i. Tsaki ta ja tare da tashi ta fito tsakar gida cikin lalaben hanya. Duk da yanda take jin rashin ƙwarin jikinta da cikinta da ya ɗaure mata, amma ta daure ta cewa Iya. "Wai don Allah Iya me muke tsare miki ne a gidan nan da kullum kike zuwa ki ishe mu da masifa?" A ƙufule Iya ta ce. "Ban sani ba, wato wuyanki ya yi kauri ko? Yar mitsitsiya dake amma har za ki faɗa mini wannan maganar? Ki ji da rashin ganin da ba kya yi mana, masu idon ma sun yi shiru sai ke makauniya ce mai bakin magana."
"Ai Allah ne ya yi Ni a haka ba ni na yi kai ba..."
"Ke! Rufe mini baki, me ya fito dake ma daga ɗaki?" Inna ta katse ta cikin tsawa.
Kuka ta fashe da shi ta ce. "Toh Inna kullum sai ta zo ta dinga zagin ki kuma ba ki yi mata komai ba?" Ta yi maganar cikin tsantsar takaici.
"Ki cigaba da magana, tunda ban isa in ce ki yi shiru ki yi ba."
Ƙwafa iya ta yi ta juya ta fita tana cigaba da masifa.
Duban A'isha Inna ta yi ta ce. "Kar ki kuma yi mini haka A'isha, ko sa'ar ki ce Iyan da za ki dinga mayar mata da magana?" A raunane ta ce. "Ki yi haƙuri ba zan kuma ba."
"Shikenan, bari na haɗa miki ruwa ki yi wanka, dama yanzu nake shirin tashin ki."
Ba ta ce komai ba ta samu guri ta zauna, zuciyarta cike da damuwar rashin jin Umar da masifar gidansu da ba ta ƙarewa. A sanyaye ta ce. "Ina wayar nan Inna? Bai kira ba ko?" Girgiza kai Inna ta yi cikin tausayawa ta ce. "Bai kira ba, ki yi haƙuri ki cire damuwar hakan daga ranki, addu'a ya kamata ki yi masa Allah ya sa yana lafiya."
"Insha Allahu, ya ce akwai karatun Alkur'ani a cikin wayar, ki ɗauko ki kunna mini."
"Ai ban san ta yadda zan kamo ba, amma bari anjima idan zan je shago siyayya, sai mu biya gurin mai chaji ya kunna miki."
Kwana Uku A'isha ta yi tana jinin sannan ya ɗauke, kamar yadda Inna ta sanar mata alamar da za ta ji ta san ya ɗauke, tana ji ta sanar da ita, duk da an koya musu yadda ake wankan tsarki amma sai da Inna ta ƙara yi mata bita domin ta yi shi yadda ya kamata. A ranar Inna ta ƙirga kuɗaɗen da Umar ya ba ta ranar da zai tafi, dubu ɗari da goma ne, ta zazzari wasu sun yi amfani da su saura dubu ɗari da biyu. Cikin farinciki ta haɗa musu kayansu don tafiya asibitin Kano gobe a duba A'isha, dama jira take ta samu tsarki sai su tafi.
"Wai Haulatu ba za ki bar kukan nan ba? Na ce ki kwantar da hankalinki in dai Umar ne zai zo da ƙafafun shi har inda muke, ina nan ina shiri akan hakan."
Haulatu dake gunjin kuka ta ce. "Yaushe zai zo to? Tunda ya tafi kike ce mini haka, kuma yau an fi sati da tafiyar tasa bai dawo ba." Cikin lallami Uwa ta ce. "Gaggawar me kike ne? Ki bi komai a sannu ze zo ne ai." Zunɓura baki ta yi ta ce. "Gaskiya ni dai na gaji da jira, so nake kawai na gan shi ko na ji muyar shi, ki je gurin Sarki ki karɓo mana lambarsa, na san ba zai rasa ba." Shiru Uwa ta yi cikin nazari sannan ta ce. "A baya na je na karɓo lambar Mahaifiyarsa, yanzu kuma na koma na karɓo tasa? Ba zai yiwu ba gaskiya, kin san Sarki da saurin gane abu, dole zai fuskanci akwai abin da muke ƙullawa, sai dai mu je gurin su waccar makauniyar yarinyar, na san ba za su rasa ba."
"Kina ganin za su ba mu kuma Uwa?"
"Na san me zan ce musu da dole za su ba mu, tashi ki ɗauko mini gelena mu je yanzu-yanzu, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe."
Cikin farinciki Haulatu ta share hawayen fuskarta tare da miƙewa.
A'isha tana zaune a tsakar gida ta yi tagumi tana tunanin Umar su Haulatu suka kwaɗa sallama. A sanyaye ta amsa musu. Haulatu dake bin ta da Kallon tsana ta ce. "Asaben ba ta nan ne?" Cikin jin haushin yadda Haulatu ta gatsa mata sunan Inna A'isha ta ce. "Me ya faru?" Kafin Haulatu ta kuma magana Inna ta fito daga bayan gidan da ta zaga, da fara'a take duban Uwa.
"Ku ne a tafe? Sannun ku da zuwa, ku zauna mana, kwa tsaya a tsaye." Ta yi maganar tana ware musu tabarmar da A'isha take zauna. Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa Uwa ta dube ta, ta ce. "Asabe lambar waya muka zo karɓa a gurin ku." Cikin mamaki Inna ta ce. "Lambar wayar wa?"
"Ta Umar baƙon yaron da ya zauna a gidanmu, don mun san ba za ku rasa ba."
Dam! Gaban A'isha ya yanke ya faɗi, da sauri ta ɗago kanta amma ba ta ce komai ba.
"Ayya, ai kuwa ba mu da lambar shi, don kwana uku mun je gurin mai chaji akan ya duba mana cikin wayar da ya bar mana ko akwai lambar waya amma ya ce ma babu, daga ta kamfanin layi sai ta layin da yake cikin waya....."
"Sai dai in ba za ku ba mu ba ne kawai, amma mun san kuna da ita." Haulatu ta katse Inna cikin rashin ɗa'a."
Inna ba ta ce komai ba sai kallon yarinyar da take cikin mamaki. Ɓata fuska Uwa ta yi ta ce. "To ai shi ya ce mu zo mu karɓa a gurin ku, saboda yana so su dinga waya da Haulatu, da zai tafi kuma ya manta yana sauri bai ba ta ba, abin da ya sa ma muka zo saboda kar ya gaji da jiran kiran mu, ga rashin jin muryata da ba ya yi zai iya jefa shi cikin wani hali, kin san ba ƙaramin ƙaunar ta yake ba."
"To sai ku jira idan ya gaji da rashin jin murya tata ya dawo garin ya ba ku lambar da kansa, ina ganin hakan zai fi kyau ko?" Inna ta faɗi haka cikin haɗe rai.
"Ko ba ki faɗa ba ma zai dawo, tunda ya gani yana so, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu, yarinya ƴar dangi da asali zai aura ba baƙin haure ba."
Ɗan murmushi kawai Inna ta yi ba ta ce komai ba. Zuciya babu daɗi su Uwa suka zira takalmansu suka fice.
A'isha da ta yi mutuwar zaune cikin bugawar zuciya tun lokacin da Uwa ta ambaci soyayya tsakanin Umar da Haulatu ta ji wasu hawaye masu ɗumi sun shiga rige-rigen zuba akan kuncinta, ba tare da ta san dalili ba. Ita tana nan tana zaman jiran kiran shi ashe ba ta ita yake ba, ko tantanma ba ta yi wannan dalilin ne ya hana shi kiran ta.
"Kada ki bari wannan zancen ƙanzon kuregen ya yi tasiri a zuciyarki, na san yanzu ƙaramin tunanin ki ya ba ki abin da ba shi ba ne." Inna ta faɗi haka cikin tausasa harshe.
Ajiyar zuciya ta sauke ba don kalaman Inna sun gamsar ita ba, duk da ƙarancin shekarun ta amma kalaman Uwa ba ƙaramin dukan zuciyarta suka yi ba, ba ta san mene ne so ba balle kuma kishi, abin da ta sani kawai ta damu da Umar, a halin yanzu babu abin da take buƙata sama da ta ƙara jin muryarsa, ta ji shi a kusa da ita yana yi mata hira, ta ji daddaɗan ƙamshinsa gami da dariyarsa mai sa ta ji sanyi a cikin ranta. Gocewa ta yi ta kwanta a gurin saboda jin kanta ya fara juya mata. Wani irin haushin Haulatu ta ji ya cika mata zuciya, tsaki ta ja a fili ba tare da ta san ta yi hakan ba. Inna dake lura da yanayin da take ciki ta miƙe don cigaba da haɗa musu kayansu, don gobe asubanci za su yi zuwa Kano.
Kamar a mafarki wayar da Umar ya bar musu ta fara ringing, wata irin zabura A'isha ta yi ta fara laluben wayar dake gefen ta, jikinta har rawa yake saboda tsabar zaƙuwa da zumuɗin jin muryarsa da take.